Showing 15001 words to 18000 words out of 140150 words

Chapter 6 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

187

harma taci abincin ita ta K'irani ma tace min lamid'o yazo". Baba magajiya tai murmushi tace.


"Auto shikenan ranki Dad'e dama na d'auka bata tashin bane shiyasa nake tambaya Amma tunda ta tashin ai shikenan,Allah ya K'ara lafiya da Nisan kwana ranki Dad'e". Ta fad'a tana murmushi.


Ammie ta ansa da Ameen daga haka Baba magajiya ta koma kitchen,Ammie Kuma ta Maida hankalinta kan lamid'o suka cigaba da hira sun jima suna hira a falon har su ya Zarah suka fito suka gaida shi Amma Banda HUYAAM dam tunda ta shiga d'aki bata k'ara yarda ta fito ba ,can lamid'o yayi wa Ammie sallama ya tafi Dan dama haka lamid'o yakeyi yakan shigowa for time to Time ya gaida Ammie indai Yana masarautar to yanzu ne Kuma da yake a Lagos saidai yazo musu break haka ya koma.



K'arfe uku na yamman Ranar saura su Huyaam sukai shirin tafiya islamiya ko Wacce tai shiri cikin dogon hijab na islamiya.suka fito daga part d'in nasu har Inda motar da ake kai school ke jiransu bayan sunyiwa Ammie sallama Dan gabad'ayansu ne suka tafi harda ya Zarah tunda su su Huyaam yau basu da paper.



__________?&


*Ingiland =????*


*Metallic industrial limited and car resources*



Company ne Wanda ya ansa sunansa company a wannan k'asa.Wanda,ake sarrafa k'arafa da Kuma k'era motoci acikinsa .wannan company ma mallakin bak'ar fatane a nan k'asar mu ta gado wato Nigeria.


Companyn babban company ne iya hasashen Mai karatu Dan fad'ar na zayyane muku ma b'ata lokacine saboda girmansa da Kuma had'uwarsa kawai abinda Zance shine ku k'iyasta a ranku.


A cikin wani babban office Wanda ya gaji da tsaruwa Had'i da had'uwa Wanda bana kowa bane saina na head of companyn . acikin office d'in na hango Wani matashin saurayi zauna kan kujerar Dake gaban Wani had'add'en table wasu turawa kuma suna zaune kan visitors chair d'in Dake gaban table d'in inda matashin nan ke zauna . Da dukan alamu magana suke Mai matuk'ar muhimmanci koma nace business ne ya kawo su, tunda naga ya Basu All ears d'insa Yana sauraransu Saida Wanda yake maganar ya kai point sannan matashin nan ya sauke ajiyar zuciya kafin ya zuba hannuwansa kan table d'in Yana kallansu ya motsa lips d'insa kad'an yace cikin husky voice d'insa.


"Alright, don't worry mr.but are you with your own choice or something like u wanted" ya fad'a Yana kallansu.


D'ayan yay saurin cewa.

"No! No!! No!!! we didn't have it, but if you have yours u would find it to us Mr Afeef"ya fad'a Yana murmushi.


Afeef ya Jin Jina kai Kafin yace cikin deep voice d'insa.

"ok I understand.so we have a new design that would find it this year can I show it to you ,then may be you would find yours here".ya fad'a Yana kallansu suka Jin jina masa kai alamar yes yace.

"Ok" Yana fad'ar haka ya Bud'e wata locker Dake nan gaban table d'in nasa ya d'auko musu album d'in da aka zana new design car da za'a k'era su this new year a fitar da su .


Ya Mik'a musu suka Karb'a nan suka zab'i wata latest car wacce itace the best car da za'a fitar da ita this year a wannan company Amma fa sai uban kud'i bayan sunyi pointing out wadda suke so d'in suka nunawa Afeef. Afeef ya karb'a bayan ya Gani yace.

"Ok don't worry we would do it in Sha Allah"nan da nai sukai appreciating sukai ta godiya kamar Wanda za'a Basu kyauta kafin su karb'i account number na companing take a wajen sukai payment sannan saukai masa sallama suka tafi.Daga nan Afeef ya cigaba da karb'ar Baki har k'arfe biyar da Rabi tai time d'in tashinsa daga company yayi kenan.nan ya d'auki brief case d'insa ya fito nan harabar office d'in nasu ya Tarar Drivernsa da yake Zaune Yana jiransa tuni ya taso da sauri ganin uban gidan nasa ya a fito nan ya karb'i brief case d'in Hannunsa ya wuce zuwa wajen motar Afeef na biye dashi a Baya duk inda ya gifta ma'aikata wajen ne kawai suke gaida shi dayake gabad'ayansu turawa ne su suke aikin k'era motocin bak'ak'en fatar Basu da yawa haka sukai ta gaida shi shi Kuma Yana ansa musu har ya k'araso motar ya shiga bayan already driver ya Bud'e masa back seat drivern Kuma ya zaga driver seat ya shiga suka fita daga cikin company gabad'aya direct gidansu suka wuce g Dake Nan ingiland d'in.



Da Daddare wajen k'arfe 8 da Rabi na daren Ranar bayan Afeef yayi wanka yasauya kaya ya fito daga falon gidan gabad'aya zuwa compound d'in gidan Dan fita zaiyi zaije Mall ne ya rage siyayyan da zaiyi idan zai koma gida Dan haka yake indai zashi gida tofa ba haka yake zuwa ba dole sai yayiwa kowa siyayya ya kai musu,Dan baya zuwa haka,yanzu ma Dan Dan zaiyi tafiya me zuwa k'asar china akwai kayan aikin motocin da zai Gani a can yayi order su akawo kafin ya tafi to shiyasa yakeso ya rage siyayyan Dan Bai San for how long tafiyar zata d'auke shi Bai dawo ba...haka ya fito xuwa compound d'in gidan sanye yake cikin k'ananun kayan da sukai masa bala'in kyau kansa Daya sha gyara sai Wani shining yake kamar ba dare ba Dan Afeef kyakkyawan ne na ajin k'arshe dogone Shi, sannan shi ba fari ba kuma Shiba Bak'i ba haka yake tsaka tsakiya ne gashi da manyan idananuwa da dogon hanshi dai dai da fuskarsa sai Wani baza k'amshi yake har ya k'araso compound d'in gidan dama already driver ya fito da motar da zasu fita acikinta Dan tun suna hanyar dawowa gida d'azu daga company Afeef yake fad'a masa cewa zasu fita.shiyasa baiyi nisa ba ya Tsaya yana jiran uban gidan nasa har ya k'arasa gaban motar ma'aikatan gidan sai gaidashi suke cikin girmamawa Yana ansa musu .Nan yashiga back seat bayan driver ya Bud'e masa ya shiga already Mai gadi ya danna Wani D'an Abu take Gate d'in ya wangale suka bar gidan gabad'aya ma'aikatan suna musu fatan dawowa Lafiya.


A Wani k'aton mall Wanda ko a k'asar ma ba kowane yake iya zuwa ba Dan saika cika Mai kud'in gaske sannan mutum yake iya zuwa saboda tsadar kayan Dake ciki da Kuma had'uwarsa.driver yay ya parking ya fito da sauri bud'ewa Afeef bayan motar yana matsa baya da sauri,Afeef ya fito cikin nutsuwa sannu a hankali yake tafiya har ya shiga cikin Mall d'in driver Kuma ya tsaya Yana jiransa.


Koda Afeef ya shiga Dayawa ma'aikatan wajen sun sanshi nan suka hau gaidashi da bashi girma tunda kowa Yasan companyn su fuskarsa ba boyayyi bace ba sannan Kuma yakan zuwa yayi siyayya a wajen time to Time .haka suka hau gaishe shi yana ansa musu da kulawa a haka harya ya nufi wajen manager na Mall d'in Ganin Afeef yasa Shima ya taso da sauri ya nufo Afeef suka gaisa cikin harshen turanci nan Afeef ya buk'aci a had'a shi da worker Wanda zai d'auka masa trolley, Babu musu mutumin yay Kiran D'aya daga cikin workers d'insu na Mall d'in bayan ya k'araso yace ya d'auko trolley yabi Mr Afeef zaiyi siyayya Aciki,Babu musu worker din nan ya tafi ya d'auko Yana jin Dad'i aransa ganin afeef harya dawo ,ganin ya dawo yasa Afeef yay wa manager godiya sannan yay gaba shi kuma worker d'in Yana biye dashi a Baya rik'e da trolling.wajen dogayen riguna suka fara zuwa ya ilahi haka na ambata araina Dan wasu luxurious kayane na ajin k'arshe a wajen sai wani d'aukar ido suke Yi da walwalin duwatsu ajikinsu.idan Afeef ya sauka akan wasu dogayen riguna guda biyu Wanda suka kasance Iri D'aya sak kalar pitch color nan yasa aka d'auko masa su Dan Yana tunanin zasu yiwa HUYAAM da Huda babu musu aka d'auko aka Mik'a masa aikuwa Yana duba size d'in sai yaga zasu musu nan ya Mik'awa worker d'in shikuma yasa cikin trolling shikuma yay gaba Saida ya d'aukowa su Huyaam dogayen riguna guda hur hud'u duk masu bala'in kyau da tsada sannan kuma ya d'aukawa ya Zarah da muneefa,sai ya'yan Fulani Salamatu suma duk ya d'auka musu kai D'aya suda 'ya'yan baba turaki su ikleema dukansu Suma sai Kuma 'ya'yan baba wambai su safnah dukansu Suma gabad'aya haka ya siya musu babu abinda ya ban banta dan haka yake baya tab'a siyawa K'annensa Abu Bai siyawa duka Yaran gidan ba.


Daga wajen dogayen riguna Kuma sai ya wuce wajen kayan maza nan ya d'aukar su muneeb da duka Sauran yaran gidan Maza bayan ya gama dasu sannan ya wuce wajen hands bag da takalma nan ya siyawa su Huyaam masu bala'in kyau da tsada ko Wacce biyu biyu sai Kuma ya wuce wajen jewelleris nan ma ya d'ibar musu daham gabad'ayansu sai kuma ya d'aukowa su Ammie gold ko Wacce biyu biyu masu bala'in kyau d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a tsada daga k'arshe yasa sauran ma'aikatan suka Taya wannan worker d'in na farko suka tayashi d'aukar kayan saboda yawan su daga nan Kuma sukai wajen payments akai counting din kud'in gabad'aya aka fad'a masa babu Wani musu haka ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in suka Mika masa ya karb'a ya fita waje wajen mota ma'aikatan suka biyo shi da kayan Nik'i Nik'i tunda driver ya hangoshi ya fito ya Bud'e musu boots d'in haka suka zube kayan gabad'aya aciki Bayan sun gama Afeef ya biya sannu ya shiga back seat Wanda driver ya Bud'e masa ya shiga daga nan Basu zarce ko Ina ba sai gida......







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*



*paid book =???*



*Free pages*




*NA*



*___(MRS SARAKIES =???)__*




*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 9??



____________?&



Sai da su Huyaam sukai kwana biyar cif basuje school ba saboda Interval d'in exam da Suke dashi.basa zuwa ko Ina sai dai suyi karatu da yamma Kuma su tafi islamiya....Ranar Sunday da safe Huyaam tana kwance saman gado tana bacci har wajen k'arfe 11 :20am Bata tashi ba ta baje akan gadon ga gashin kanta yadda ya bar baje nan saman pillow sai sharar bacci take abinta.bud'e k'ofar d'akin akayi Huda ce ta shigo shigowarta na ukune kenan tana zuwa tana duba taga ko Huyaam ta tashi?, Amma sai dai ta tadda Bata tashi ba. yanzunma Ammie ce ta aikota akan lallai ta taso Huyaam ko Bata tashi ba, shine yasa tazo ta.


Tsayawa tai kawai Daga nan Bakin k'ofar tana kallan Huyaam da mamakin yadda take sharar baccinta hankalinta kwance ,Huda ta sauke numfashi ta k'arasa shigowa har cikin d'akin zuwa gaban gadon ta kai hannu ta yaye blanket d'in da HUYAAM ta rufa dashi har saman kanta tana Kuma K'iran sunanta at the same time.


Cikin bacci Huyaam taji muryar Huda tana K'iran sunan ta, nan ta Bud'e idonta kad'an Wanda suke cike da bacci tana kallan Huda dasu .Huda tana rik'e da bargon a hannunta har lokacin tace .


"Kike Kallona? ki tashi baccin ai ya isa haka koh?..." ta fad'a tana Jan blanket d'in. HUYAAM ta had'e Rai ta damk'e blanket d'in da k'arfi ganin Huda na Neman yaye mata shi tace cikin shak'akk'iyar murya Irin ta Wanda bacci Bai ishe ishe Shiba.


"Banaso Huda miye Hakan? banaso ki K'yaleni". ta fad'a tana tura Baki gaba.


Huda tai murmushi ta k'ara Jan bargon da k'arfi tana cewa.


"Wallahi sai kin tashi Ammie ce tace nazo na taso ki ai,baccin ya isa haka sai kace Mai baccin mutuwa"ta fad'a tana k'ok'arin fusge bargon daga rik'on da HUYAAM tai masa .


Ganin haka yasa Huyaam ta yunk'ura da sauri ta mik'e Zaune itama ta fara jan bargon nanfa suka fara jaye jayen bargo da ko kawa. ganin da Gaske fa Huda take saita janye bargon yasa Huyaam Tai kanta da sauri cikin b'acin Rai tana yiwa Huda magana. Ganin haka yasa Huda ta saki bargon da sauri ta nufi k'ofar fita daga d'akin da gudu tana K'iran sunan Ammie .. Huyaam tai murmushi Jin abinda Huda keyi ta Maida bargon nan saman gadon sannan ta wuce toilet Dan yin brush da Kuma wanka.


Sai k'arfe Sha biyu Saura Huyaam ta fito daga d'aki,ta sauko downstairs nan main falorn gidan cikin shigar atamfa D'inkin doguwar riga A shape wacce tai mata bala'in kyau sai Wani walwali take acikinta saboda d'inkin da aka zubawa rigar. haka tafito sauko daga stairs d'in.Babu kowa a falon daga Huda sai muneefa ne kawai a falon suna zazzaune kan kujera suna kallo a TV kamar ance muneefa ta juya sukai ido hud'u da Huyaam wacce ke shigowa falon cikin sand'a zatai wajen da Huda take. muneefa ta Bud'e Baki zatai wa HUYAAM magana Huyaam tai saurin d'aura Hannunta saman Bakinta tana kallan muneefa alamar kada tai magana . muneefa ta koma ta zauna a hankali Dan kada Huda ta ganta tana gimtse dariyarta Dan tasan mai Huyaam take nufi tunda sun Saba.


Huyaam ta sauke numfashi a hankali ta fara takowa cikin sand'a har zuwa wajen da Huda ke zaune wacce tai backing d'inta ta Bata Baya tana zuwa tai saurin rufe mata fuskarta da tafukan Hannunta ta baya Huda.me muneefa zatai inba dariya ba nan ta saki dariyar da tai ta rik'ewa.itako Huda batai mamakin waye ba tunda ga k'amshin turaran HUYAAM nan tana shak'a nan ta Gane itace.


Ta rik'e hannun Huyaam wacce ta rufe mata fuskarta K'am tak'i saki, Huda ta Bud'e Baki tace .


"Huyaam miye haka ki cire Hannunki daga fuskata banaso"ta fad'a tana k'ok'arin cire Hannun HUYAAM daga fuskar tata.nan Huyaam tak'i saki saima K'ara damk'e fuskar Huda da tai, nan fa Huda ta fara k'ok'arin k'wace fuskarta Amma ta kasa ita Kuma HUYAAM sai murmushi take can Huda ta kai hannunta zata kamo rigar HUYAAM,tuni HUYAAM ta saketa tai baya da sauri Huda ta Mik'e zatai kan Huyaam tuni HUYAAM ta haye stairs tai d'akin Ammie da sauri har tana had'awa da gudu tana yiwa Huda dariya.Huda tai k'wafa ta koma ta zauna tana murtsuke idonta.


Ammie na zaune bakin gadonta tana gyara wasu kayanta HUYAAM tai knocking k'ofar Had'i da turawa ta shigo tare da sallama a bakinta.


Ammie ta d'ago tana kallanta ta ansa mata sallamarta. Huyaam ta k'araso d'akin tana sauke numfashi tana Kuma murmushi Had'i da juya banyanta tana tunanin ko Huda ta biyo bayan ta.


Ammie tana kallan Huyaam da mamaki tace .


"A'a keda waye Kuma? Kika shigo kina haki?...."ta fad'a tana kallan bayan Huyaam ko zataga me Huyaam d'in takewa waigen oho.


Huyaam ta sauke numfashi tace.


"Babu kowa fa Ammie".

Ammie ta sauke numfashi tace.

"keda Huda ne ko?..."


Huyaam tai murmushi batace komai ba nan Ammie ta Gane itada da Huda ne k'ila abinda suka Saba sukayi wato tsokanar juna.


Ammie tana kallan Huyaam tace.

"Yanzu kika tashi daga baccin ko?...."

Huyaam tai shiru tana shafa kanta . Ammie tace .


"Wallahi Huyaam idan Baki daina Irin wannan baccin ba Agidan nan ki kai har wannan lokacin Baki tashi ba zansa k'afar Wando D'aya nida ke agidan nan,sai kinje ulcer ta kama ki kizo kina ciwo ciwo Allah ma ya kiyaye". Ammie ta fad'a tana kallan HUYAAM.


Huyaam ta sauke idonta k'asa tana sauraran Ammie.


Ammie tace .


"Kinji ko Baki jiba?..."Huyaam ta d'ago kanta tana kallan Ammie da raunan nin idanuwanta Dan arayuwarta bata so taga Ammie cikin damuwa.a hankali ta k'araso kusa da Ammie ta rungumeta tace cikin sanyin murya.


"Kiyi hak'uri Ammie bazan K'ara ba"ta fad'a tana K'ara shigewa jikin Ammie.


Ammie tai murmushi tana shafa kan Huyaam Dan itama dolene take sawa taiwa Huyaam fad'a badan komai ba sai Dan ta gyara abinda take tunda ita macece duk mun daran dad'ewa ba'a gidan zata dauwama ba gidan Wani zata.Ammie ta sauke numfashi tace.


"Naji na hak'ura. but dear kinsan banason duk abinda zai B'ata Miki Rai ko? So please ki kiyaye, ni tsorona kada ki dinga zama da yunwa har Wata cutar ta kama ki". Ta fad'a tana Shafa kan Huyaam.


HUYAAM ta gyad'a mata kai tace a shagwab'e.


"In Sha Allah Ammie kema kin hak'ura ko?.."Ammie ta d'agota tana kallan fuskar ta da Murmushi tace .


"Na hak'ura dear dama bakimun Komai ba karki damu kinji?..." Huyaam tace "Thank u lovely mother".ta fad'a tana murmushi.


Ammie itama murmushin tai ta rik'e fuskar HUYAAM da tafukan Hannunta tana kallanta tace .


"Nevermind lovely daughter"ta fad'a tana fad'ad'a murmushinta .Huyaam tai murmushi tai kissing Ammie a Kumatu.


Ammie ta shafa fuskarta tace.

"Thanks dear fatan kinci abincin dai koh?..."


Huyaam ta girgiza mata kai tace cikin k'asa da murya.


"Yanzu zanje naci".


Ammie ta kalli Wani Dan k'areren agogon bangon Dake d'akinta sai Kuma ta juya tana kallon Huyaam tace.


" past 12 fa Huyaam, Amma kike zaune Bakije kinci abinci ba? oya wuce kije kici".ta fad'a tana nuna mata hanyar k'ofa.Babu musu HUYAAM ta juya ta fita daga d'akin bayan ta kullowa Ammie k'ofar.


" LAmmie ta sauke numfashi tana girgiza kai tare da cigaba da abinda takeyi.


Huyaam tana sauka k'asa tun kafin ta k'araso sukai ido hud'u da Huda wacce take Harararta. Ganin haka yasa Huyaam ta sauko downstairs d'in a hankali tana Murmushi ta had'a hannayenta biyu alamar roko tace.


"Dan Allah kiyi hakuri lovely twin". Ta fad'a tana murmushi.

Huda ta d'auke kai kafin tace .


"Sorry for your self Yarinya ,Dan bazan tab'a hak'ura ba sai na rama ,Kuma karkiyi tunanin ma yanzu zan rama,Dan idan zan rama ma ai ba yanza ba sai kin sakan kance kamar yadda Nima kikai min". tana fad'ar haka ta Maida hankalinta kan TV ta cigaba da kallonta.


Huyaam tai murmushi ta k'arasa dining d'in cikin sand'a ta zauna kan kujera har lokacin a tsorace take da Huda Dan Gani take a kowani lokaci Huda zata iya tasowa kanta .ta bubbud'e warmers d'in tana k'ok'arin d'ibar Abinda zata iya ci...



_____________?&



Washe gari Monday Huyaam basuda paper sai washe gari wato Ranar Tuesday. Aranar kan suna da paper zasuyi second to the last paper itama ta safe ce Danma yau D'aya zasuyi ba biyu ba,Dan haka da wuri suka Tashi sukai shiri suka tafi makaranta.basu suka dawo ba sai wajen k'arfe biyu da Rabi na Rana Shima suna dawowa sukai shirin islamiya k'arfe uku da 'yan mintuna Kuma suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login