Showing 39001 words to 42000 words out of 140150 words

Chapter 14 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

219

yasa ta sauka downstairs sanin Ammien baza ta wuce nan ba..a stairs suka had'u da Huda wacce tazo K'iranta Jin shiru har lokacin HUYAAM Bata sauko ba.Dan tun d'azu su suka shirya ita kawai suke jira .Huda na kallon HUYAAM tace.


"Haba Dan Allah kefa muke jira tun d'azu fa?...."Huda ta fad'a kamar zatai kuka.huyaam ta k'yalk'yale da Dariya tace .


"To mama Huda ai Gani na fito yanzu ko?.."ta fad'a tana k'ok'arin rab'awa ta gefenta zata sauka.huda ta harareta tace .

"Wato abin dariya ma na zama ko?...."Huyaam ta zaro ido tace .

"A'a nidai bance haka ba Ya Huda ta fad'a tana gimtse dariyarta ganin Irin kallon da Huda take mata.Huda tai k'wafa tace.

"Wallahi HUYAAM ki canza hali Dan wannan ba Hali Mai kyau bane ba.Ace kullum kece k'arshen bacci a gidan nan Amma Kuma kece k'arshen tashi ga Kuma shirin ma kullum kece k'arshe". Ta fad'a tana biyo bayan Huyaam wacce har ta sauka k'asa tana dariya k'asa k'asa.A falor Huyaam ta Tarar da Ammie ta k'arasa ta rungumeta tace .


"Nagama shiryawa Ammie Sai mun dawo".t a fad'a tana murmushi.Ammie tace.

"Allah ya tsare".Huda tai hanyar k'ofar fita daga falon tana cewa. "Idan ma bakiyi breakfast ba ke kika sani mudai tafiya zamuyi,Kuma wallahi Baki isa kin makarar damu kince sai kin tsaya kinyi breakfast ba ku taho mu tafi time fa na tafiya". ta fad'a tana k'ok'arin fita daga falon.Ammie ta kalleta da mamaki tace.


"Huyaam d'in Bata ci abinci ba zakice wai ku taho ku tafi Huda? naga shi kansa karatun Sai anci Abinci yake yiwuwa ko?...". HUYAAM na
kallan Ammie tace.


"Laaa!! Ammie nayi breakfast d'inma fa tun d'azu". Ammie na kallanta tace.


"Yaushe kika Yi d'in?..." Huda itama kanta fasa fita tai ta juyo, tsayawa tai tana kallan Huyaam jin abinda ta fad'a, sannan taji Irin ansar da zata bawa Ammie.. Huyaam na murmushi tace.

"Wallahi d'azu nai time d'in duk Kon bar dining d'in,Dan Ina expecting ma Kuna gamayin breakfast ni Kuma na fito Saida nayi sannan naje nai wanka ma". Ammie tace.

"Nidai ban Yardaba zoki wuce kije kiyi breakfast D'inki su tafi su barkin nasan halinki Huyaam yin breakfast d'in ne kawai bakya son Yi". Huyaam ta marai raice Jin Ammie zata K'ara sata cin Wani abincin tace.


"Wallahi Ammie nayi idan Kuma Baki yadda ba ki tambayi baba magajiya ma Ina zaune ta shigo falon kuma taga lokacin da nakeyi".ko rufe Baki HUYAAM batai ba sai ga baba magajiya nan ta shigo falon hannunta rik'e da Jakar muneefa wacce ta d'auko mata a d'aki ta Mik'awa muneefa tana cewa.


"Gashi Auta na Samo miki". Ammie ta kalli baba magajiya tace.

"Magjiya da Gaske ne d'azu bayan barinmu dining Huyaam ta fito tayi breakfast tsakani da Allah zaki fad'a min?...."baba magajiya tana D'an murmushi ta kalli Ammie tace.


"Eh ranki Dad'e d'azu bayan Kun gama karyawa naga itama ta fito taci abincin". Ammie ta sauke numfashi tace.


"Shikenan na yarda tunda magajiya ta ganki". Huyaam tai murmushi Ammie tace.

" ai dama na fad'a miki.

Ammie tace.

"Yau yayanku zai dawo bansani ba ko zaku rigashi dawowa ko Kuma shi zai rigaku".ta fad'a tana kallansu. gabad'aya sai faskarsu ta washe da murmushi. Huyaam tace.


"Wayyo Ammie! yau Yaya zai dawo? Ta fad'a cikin farin ciki .


Ya zarah dasu huda suka ce Allah ya dawo dashi lafiya. Huda Kuma ta K'ara da cewa.

"Allah yasa mu rigashi dawowa Ammie". Muneefa tace.

"Ameen".Huyaam Kuma tana tura Baki gaba tace.

"shine Kuma dawowa unexpected ko a fad'a mana day d'in?...." Ammie ta rik'e hab'a tace .


"iKon Allah to Nima bai fad'a mini exact day d'in ba shiyasa ban fad'a muku ba, saboda shima Bai d'auka zai dawo a yau d'in ba saboda yanayin tafiyar tasu Dan zuwan nasa k'ila wa k'ala ne". Huyaam ta rausayar da kai tace.

"Shikenan Allah ya dawo dashi lafiya". Ammie tace.

"Shikenan wannan itace addu'a Mai kyau,ku kuce ku tafi time na tafiya". juyawa sukai suka fita daga falon bayan sun K'ara yiwa Ammei sallama...


____________?&


Tun k'arfe 10 na safe Afeef ya bar gidansa bayan yay sallama da ma'aikatan gidan ya Kuma barmu su ragamar kula dashi tunda dama sun Saba su suke kula masa da gidan ko Yana nan ko Baya nan to yanzu ma Hakan ce ta kasance... John ne yay parking a dai dai Wani k'aton building Dake cikin companing nasu fitowa daga cikin motar yay bayan John ya Bud'e masa.sannu a hankali ya fara takawa zuwa wajen Wani bature Wanda ke tsaye Yana jiran Isowar Afeef d'in tareda da yaransa Kuma shine Head na b'angaren gabad'aya ya taho da sauri da takarta a ahannunsa Afeef ya tsaya ganin ya Mik'a masa hannu suka gaisa baturen na murmushi yace.

"Well come Boss.the orders is here since yesterday afternoon".ya fad'a Yana kallan Afeef.

Afeef ya Jin Jina kai yay gaba Yana cewa "Alright, let's go nd see". Daga haka suka bi bayansa... Abubuwan da yay ordering nasu gabad'aya babu Wanda ba'a kawo musu ba komai sai da aka kawo su. fitowa Yay daga wajen bayan yaga komai Yana kallan baturen Dake rubuce rubuce jikin jotter hannunsa yace cikin harshen turanci.


"Mr Patrick I will take my lift not long in Sha Allah,so make sure everything is going well before I came back". Ya fad'a Yana kallansa.mr Patrick ya Jin Jina kai in a serious talk yace.

"I promise boss".Afeef ya Jin Jina kai yace.

"Thank you so much, but let me go to the office before I Left".Mr Patrick yay murmushi yace.


"Self trib boss u have great Nigeria also".ya fad'a Yana murmushi Afeef yay Murmushi da Bai shirya ba Bai San Mai yasa ba mr Patrick Yana San Nigeria indai akace Afeef zai tafi Nigeria tofa sai yace ya gaida Nigeria.dain murmushin yayi ya shige motar John ya shiga driver seat yay zoom off suka bar wajen sukai Wani building inda anan office d'in Afeef yake..... k'arfe D'aya da Rabi Saura idar da sallahr sa kenan ya fito daga office d'insa Yana kallan time .John Dake zaune cikin motar Yana jiransa yana kallan fitowarsa tun kafin Afeef ya k'araso Yay Maza ya fita daga motar ya Bud'e masa back seat Afeef ya k'arasa ya shiga Yana ansawa ma'aikatansa Dake mafan Yi Mai sauka lafiya dama....


Tafiyar mintun 30 ce ta kawo su airport d'in ya fito da sauri John kuma ya zaga boots ya fito masa da boxes d'insa har kayan da yaywa su HUYAAM siyayya suna ciki duk john ya fito dasu kafin ya bi bayansa.... Afeef na zaune a VIP dake cikin jirgin ya duba rantsatstsan agogon Dake tsintsiyar hannunsa yaga k'arfe biyu da mintuna 10 jirginsu ya fara tashi a hankali harya tashi zuwa sararin samaniya maida kansa yay ya lumshe ido Yana Jin yadda jirgin ke ratsa gajimarai....



Tun bayan tafiyar su Huyaam islamiya Ammie da baba magajiya da wasu masu aikinta su biyu suka had'u a k'aton kitchen d'in part d'in suna taya Ammie Dake had'awa Afeef Abinda zasu tarb'eshi dashi.. girki sukeyi kusan kala 6 ake masa duk Wanda za'a tarb'eshi dashi ne Kuma ko wanne kalarsa daban har Yanzu Daya kasance k'arfe biyar saura Basu gama ba Amma Saura kad'an su k'arasa.gabad'aya k'amshin girkin nan ya cika b'angaren Ammie.D'azu dai lokacin da su Afeef suka tashi ya k'ira Ammie ya fad'a mata sun taso Da yay sa'a Kuma jirgin direct kano zai sauka.....



Hajiya Lubabatu ce Zaune a d'akin da suka saba k'ulla duk Wani abubuwan su ita da Fulani Salamatu Suna zaune kan kujerun Dake d'akin.Hajiya Lubabatu tai k'asa da da tana kallan fulani Salamatu wacce tai sak'are tana kallanta Jin abinda ta fad'a. tace.


"Wallahi fulani kar kice wasa motocine gasu can na barsu a compound sabbi dal dasu Irin Wad'anda suke k'erawa d'in nan ne Wanda aka kawosu kwanaki ko ta tab'a bawansu ba'a tab'a yiba tunda aka kawosu gidannan kusan guda biyar anfito dasu an wanke za'a je d'auko magajin gidan dasu sai kace shine sarkin Danko sarki ne zai Yi tafiya iya comboi d'in da za'a masa kenan".ta fad'a tana Wani mele Baki... fulani Salamatu da idonta ya kad'a yay ja Jin abinda Hajiya Lubabatu ta fad'a mat ta sauke numfashi tace.


"Wato kullum Abin nan nasu K'ara cigaba yakeyi Lubabatu, ni kenan ba'a tani tunda 'ya'ya mata gareni shikenan ba'a tab'a sakani a lissafi 'ya'yan Maryam sune 'ya'ya a gidan nan.wato dawowar ma da Afeef d'in zaiyi har Wani comboi za'a masa aje d'auko shi ?..."Fulani Salamatu tace.


"Uhmm!! gashi dai can ana shiri ban sani bama ko harda Mai martaban Za'aje d'auko shin oho?.."da sauri fulani Salamatu tace .

"Banda shi baya nan tun d'azu ya fita shine ma yake cemin yau Afeef d'in zai dawo". Hajiya Lubabatu ta kad'a kai tace.

"Uhmm Ai dama nace Baki sani ba shiyasa nace bari nazo na fad'a miki. Ai maryam malaminta ya iya aiki karki Wani damu kinsan Allah asiri ne bayin kan Mai martaba bane ba, saida ta riga da tasan kan mai marataba tass sannan taje aka mallake mata shi ". fulani Salamatu ta sauke numfashi tace.

"Aikuwa Wallahi Bata Isa ba Dan saina k'ask'antar da ita agidan nan Dani take zancen yadda ta dasa min rauni a zuciyata wallahi ni kuma raunin zanji mata". Hajiya Lubabatu tace .


"Ai Bari kawai k'awata bari malam ya dawo wallahi bazamu zauna ba".sai Kuma ta d'aga kai ta Kalli time tana mik'ewa tace.

"Uhmm! Bari naje fulani yaran nan sun kusan dawowa daga islamiya karsu su zo su Tarar Dani". Tana fad'ar haka ta nufi k'ofa.fulani Salamatu tace.


"To idan sun tarar Dake sai mene?..."Hajiya Lubabatu ta juyo tace.


"A'a fulani Kar muje su shigo bamu sani ba muna wannan maganar suji abinda muke fad'a kar suyi mana wani kallo". Fulani Salamatu tabita da kallo batace komai ba Daga nan zaunan da take ta ansa mata sallamar da Hajiya Lubabatu take mata. tsabar abinda Hajiya Lubabatu ta fad'a mata ya bugeta ko iya tashi daga inda take zaune Batai ba kallan Hajiya Lubabatu kawai take har ta fita daga d'akin.....


K'arfe biyar da mintuna 10 motacin da aka wanke tun d'azu wanda za'a d'auko Afeef dasu suna jere a harabar gidan. drivers d'in da zasu ja motocin duk suna ciki sun ta-da su D'aya bayan D'aya suka fara fita daga cikin gidan bayan an wangale musu gate d'in. Sannu a hankali suke fita daga gidan Dan zuwa d'auko Afeef a air port kamar yadda Mai martaba ya Bada umarni tareda rakiyar wasu daga cikin fadawan gidan har motocin suka gama fita daga gate d'in gidan gabad'aya reras su biyar abin sha'awa.d'aya bayan d'aya suka hau kan titin motacin nan sai wani d'aukar ido suke saboda sabi ne dall aka fito dasu yau d'in nan aka fara hawansu direct Airport suka nufa Dan d'auko Afeef Wanda jirgin nasu baima sauka ba sai nan da k'arfe biyar da Rabi kafin lokacin Kuma sunje.......




# # # #



07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =???)__*




*PAGE 1?? 8?? *



*Bismillahirrahmanirrahim*



__________?&


K'arfe biyar da Rabi dai dai jirginsu Afeef ya sauka a airport d'in Aminu kano international airport.matafiya ne ke saukowa daga cikin jira wad'anda suka dawo daga zuwa k'asar Ingiland zuwa Nigeria.d'aya bayan D'aya passengers d'in suke saukowa daga matattakalar jirgin kowa Daya sauko zai wuce zuwa wajen d'aukar kayansa .can na hango Afeef sanye cikin k'ananun kaya riga da Wando Wanda da sukai masa bala'in kyau furkarsa rufe da face mask ya D'ora facing cap a kansa.sannu a hankali shima yake ta saukowar harya k'arasa saukowa gabad'aya.tun kafin ya k'arasa fitowa daga wajen ya hango dogarayen da suka zo d'aukar sa gabad'aya sun fito daga cikin motocin suna jiki suna zaman jiransa ko ba'a fad'a masa yasan daga gidansu suke . hangoshin da sukai yasa suma wasu daga cikin dogarayen suka taho cikin sauri Dan su tarb'eshi. Yana kallansu har suka k'araso wajen sa cikin girmamawa suka karb'i box d'in hannunsa guda d'aya wasu Kuma suka k'arasa suka d'auko sauran boxes d'in nasa . tun kafin ya k'araso wajen motar akai saurin Bud'e masa back seat tareda zabga masa kirari ta ko Ina .da ka kawai Afeef ya iya ansa musu har ya shiga motar suka rufe a hankali. Boxes d'in da suka d'auko suka gama Sakawa a cikin boot d'in motar Saida suka gama saka su du, sannan suka rufe boots d'in kafin su bar wajen cikin sauri kowa ya shige cikin motocin da suka zo a cikinsu...Alaye cikin nutsuwa motocin suka fara fita daga cikin air port d'in har suka gama fita gabad'aya,duk inda suka wuce acikin kano kallan motacin kawai ake saboda d'aukar idon da sukeyi da Kinga motocin ma kinsan babu k'arya sun Had'u iya had'uwa Dan acikin kano ma ba kowa zaki samu Yana da Irin motocin ba sai wanda kud'i suka zaunawa zai iya mallakarsu. cikin nutsuwa motocin suke tafiya akan lafiyay yan titin,shiko Afeef Yana zaune a bayan motar ya jinginar da kansa da kujerar motar idonsa a lumshe......



K'arfe biyar da mintuna Arba'in motar da ake d'auko su Huyaam daga islamiya ta shigo cikin palace d'in, k'arasawa tai tai parking a inda akeyi.bayan motar ta tsaya dogarin Dake gaban motar ne yay saurin Bud'e inda yake Zaune ya fito ya k'araso ya Bud'e musu murfin motar.D'aya bayan D'aya su Huda suka shiga saukowa daga cikin motar har suka gama fitowa gabad'aya daga nan Kuma kowa ya nufi b'angaren su .tun kafin su Huyaam su k'arasa shiga cikin falon k'amshin girkin da Ammie Sukayi ya cika hancinsu,Dan tunda suka shigo b'angaren k'amshine kawai ke tashi.da sallama suka k'arasa shiga har cikin falon, babu kowa aciki Dan haka kowa ya shige D'aki Dan sauya kayan jikinsa.A Dining din sama suka tarar da Ammie Dake tsaye a dining d'in tana K'arasa setting table d'in.nan ma sallamar sukai ganin Ammie falon.tsayawa tai daga abinda take tana ansa musu sallamar su muneefa ta tafi da sauri ta rumgume Ammie tana cewa.

"Ammie mun dawo".ta fad'a tana murmushi. Ammie ta rik'e ta tace.

"Sannunku da zuwa".dukkansu suka had'a Baki wajen gaida Ammie.nan ma Ammie ansa musu tai tana murmushi . Huyaam na cire hijab d'in jikinta anan falon tace .


"Ammie yayan ya dawo ne?.ta fad'a tana kallan Ammie..Ammie ta girgiza kai tana kallonta tace. "D'azu aka tafi d'auko shi,Amma nasan yanzu haka ma suna hanyar dawowa in Sha Allah".Huyaam ta sauke numfashi . muneefa tana kallan Huda tace.

"Ya Huda addu'a ta ta karb'u Yaya Bai rigamu dawowa ba".ta fad'a tana murmushi.huda ta gyad'a mata tace.

"Eh fa. tom Allah ya kawo su lafiya". Ammie da Huyaam suka ansa da Ameen. Ammie na kallansu tace.

"to Maza kuje ku shirya kafin su iso". Huyaam da Huda suka ansawa Ammie kowa ya shige d'akinsa ita dama ya Zarah tun tuni ta bar wajen tun bayan data gaida Ammie..Ammie Kuma ta kama hannun muneefa suka shige d'akinta Dan ta shirya ta itama ......


Horn d'in motar farko ce datai a bakin gate d'in yasa D'aya daga cikin fadawan Dake zaune a bakin gate d'in yay saurin mik'ewa Daga inda suke zaune,ya taso da sauri ya k'arasa har gaban gate d'in ya danna Wani D'an Abu take Gate d'in ya Wangale motocin suka fara danno kai cikin gidan D'aya bayan D'aya.gabad'aya dogarayen Dake Bakin gate d'in saida suka mik'e ganin shigowar yarima Afeef cikin masarautar. motacin na k'arasowa dai dai inda suke tsaye take suka zube a k'asa kawunansu na kasa da babbar murya suka Shiga jero masa Barka da zuwa had'i da kirari. bayan motocin sun gama wucewa Kuma suka mik'e gabad'aya wasu sukabi bayan motocin da sauri kowa Yana k'ok'arin yaga shiya Bud'ewa yarima Afeef motar da yake ciki duk da Basu San a wacce yake ciki ba Sauran kuma suka tsaya suna Tsaron gate d'in.gabad'aya suka zube a k'asa bayan sun k'arasa inda motocin sukai parking suka jeru gaban motar kaf ma'aikatan gidan sarki saida suka fito dan yiwa yarima Afeef barka da zuwa.motar Dake tsakiyar duka motoci hud'un na hango Wani dogari wanda dashi akaje d'auko Afeef a air port ya fito da Sauri Yana gyara zaman babbar rigar jikinsa Irin ta dogarai yasa hannu ya bud'ewa Afeef bayan motar da yake ciki ya ja baya da Sauri Yana kirari da cewa.

"Eh!! fitowarka Lafiya takawarka yariman kano magaji magajin masarautar kano idan Allah yaso ya yarda. gaisheka saraki madara Mai kama da nono d'a Mai kamar uba.ire Iren wannan kirarin suka dinga jero masa.yana jinsu Bai iya yace musu komai ba.illa K'afarsa D'aya daya fara zirowa sannan ya ziro da d'ayar ma kafin ya gama saukowa daga cikin motar gabad'aya .kamar had'in Baki haka dogarayen nan da suka zube tun k'arasorsu wajen suka shiga yiwa Afeef barka da zuwa kansu a k'asa Cikin girmamawa.matsawa daga jikin motar Afeef yay yana ansa musu lokaci D'aya Yana k'arewa gidan nasu kallo kamar Wanda ya sauya masa .ya haidar ne ya yazo wajen fuskarsa da murmushi Shima dawowar sa gidan kenan ya k'arasa har wajen yayan nasa ya bashi hannu tareda Yi masa side huge Afeef ya sake shi Yana ansa masa sannu da zuwan da yake masa kafin ya bar wajen ya haidar ya bishi suka jera zuwa b'angaren Ammie gabad'aya. tuni dogarayen suka Bud'e boots d'in suka kai kayan nasa bangaren Ammie.


Tun shigowar motacin da muryoyin fadawa da suke ta jerowa Afeef kirari Had'i da barka da zuwa su Huyaam suka San yayan nasu ne ya iso,ko Wacce tayi wanka ta shirya cikin shiga Mai kyau Huyaam da Huda kaya iri D'aya suka sa, doguwar rigar atamfa ce D'inkin beat work Mai bala'in kyau ga stone sai Wani walwali sukeyi.Huda ce ta shigo d'akin HUYAAM tana kallanta tace cikin farin ciki.

"Yanzu yaya suka iso ki taso muje falon k'asa muga shigowarsa".ta fad'a tana kallan Huyaam..Huyaam Dake gaban mirror tana kokarin Parking gabanta da ribbons tace ."jeki Gani nan Dan sai nayi sallah ma zanzo lokacin ya huta Dan yafi ganina da kyau".ta fad'a tana kallan Huda ta cikin mirror d'in . Huda ta tab'e Baki tace.

"To saikin fito bari nidai naje Dan naji kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login