Showing 63001 words to 66000 words out of 140150 words

Chapter 22 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

190

k'arfinta, Wanda Saida yasa Afeef ya rintso idonsa ya rik'o ta zuwa jikinsa Bata fasa kokawa dashi ba tana Neman k'wacewa hakan yasa Ammie ta k'araso ta rik'e ta itama Afeef ya sakar mata ita ganin Ammien ta rungumeta zuwa jikinta tana cewa. "HUYAAM menene? Stop it please sorry daughter ya Allah! Innalillahi wainna ilaihi rajiun". haka kawai Ammie take fad'a sannan ta jawota suka Zauna nan gefen gadon har lokacin huyaam tana jikinta rungume da ita .Afeef ya D'an matsa kusa dasu ya rik'o hannun Huyaam d'in Dake k'ok'arin fusge gashinta nan ya fara Yi mata addu'ar duk da tazo bakinsa Ammei na tayashi kafin ta kalli Huda Dake kallan Huyaam da tausayawa tana jero mata Sannu tace. "jeki d'auko mun maganinta a d'akina Yanzum nan". Babu musu Huda ta fita daga d'akin cikin sauri". Babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da goran maganin ta Mik'awa Ammie. nan Ammie ta karb'a ta Bud'e ta shafa mata a fuskarta sai da tai mata Sau uku har lokacin Afeef addu'a yake mata kafin can ta daina ihun ta fara sakin numfashi tareda ajiyar zuciya lokaci D'aya shi dai Afeef kallanta Kawai yake cikin tausayawa yadda fuskarta tai jaga jaga da hawaye,saida sukaga bacci ya d'auketa sannan Afeef ya daina mata addu'ar.Ammei ta kwantar da Huyaam nan saman gadon bayan sun gyara shi ta fara duba K'afar HUYAAM Dake d'igar jini da Hannunta take hankalinta ya K'ara tashi Ganin yadda kwalbar duk ta yanki Huyaam ta kalli Afeef tace cikin Damuwa. " Kaga fa Afeef ta yanke ko kwalbar ma ta shiga k'afar tata ne naga sai d'igar jini takeyi?..." Afeef da shima kallan k'afar Huyaam d'in yake da kuma hannun nata yace. "Bari a k'ira doc". Ammie na kallansa tace. " To Maza Dan Allah" Sai Kuma yace. "Wai dama har yanzu Bata daina wannan abun ba?.." Ammie tace cikin Damuwa "Eh! har yanzu Bata daina ba, Da ya lafa Amma naga Kwanan nan Yana yawan tashin mata".ta fad'a cikin Wani Irin sauti . Afeef ya Jin Jina kai yace. "Allah ya sawak'e". Ammie Tace. "Ameen jiki a Sanyaye so nake ma mu koma Egypt d'in tunda naga abun ya dawo". Afeef yace. "Bari na d'auko waya ta na kira doc". Ammie ta gyad'a masa kai batace komai ba harya fita daga d'akin.
Babu dad'ewa ya dawo yace. "Doc yace min gashi nan zuwa". Ammie tace. "Shikenan" daga haka afeef ya fita daga d'akin gabad'aya...bayan fitar sa Babu dad'ewa baba magajiya tai knocking k'ofar aka Bata iznin shiga, tashigo d'akin Bakinta d'auke da sallama suka ansa mata ta tsugunna ta gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa mata da kulawa.baba magjiya tace. "Ranki Dad'e ya Mai jiki". Ammie tana kallan ta tace. "da sauk'i". Baba magajiya tace. "Allah ya sawak'e bari naje zan dawo anjima". Ammie ta gyad'a mata daga haka ta fita daga d'akin......


___________?&


*Masarautar Zazzau*

"Ko baka fahimci Abinda nake ce Maka bane eh Abdallah da yaran Hausa nake maka magana fa?..." Hajiya inna ta fad'a tana kallan Mai martaba Dake zaune a falonsa . sarki Abdallah ya d'ago Yana kallanta sai Kuma yay k'asa da murya yace. "Eh inna da sanina ya tafi school d'in kuma abunda yasa ma na barshi naji yace suna da test d'in da zasuyi 11:30am kuma Kinga yau Friday da wuri ma zasu gama 12 ma zakiga ya dawo in Sha Allah".Haka sarki Abdallah ya fad'a Yana kallan mahaifiyar tashi.
Hajiya inna tace. "Amma wallahi kaidai Abdullah bakai tunani Mai kyau ba ya za'ayi ka biye masa kawai ka Barshi ya tafi wata boko bayan kasan shekaranjiya yadda muka ga Rana haka mukaga wannan dare da yaran nan yadda yadinga ihu Yana wasu surutai tsakiyar dare badan Allah yasa duk muna kusa ba munjiyoshi da wuri da haka zai gudu cikin dare bamu sani ba". Hajiya inna ta fad'a cikin b'acin rai..


Takawa yay shiru Yana kallanta sai kuma yace. "To Yanzu dai Inna na fahimceki Amma kuma Dan Allah kiyi hak'uri tunda yanzu dai test zasuyi kuma nasan ma yanzu haka sun kusan zuwa school d'in koma sunje,saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Babu abinda ma zai sa meshi in Sha Allah tunda kullum muna addu'a sannan ba shi kad'ai ya tafi ba,harda rakiyar fadawan gidan nan Kuma kinga hakanma ai mugodewa Allah tunda har Yana iya zuwa school d'in harma ya fuskanci Abinda ake koya masan, da da baya iya zuwan fa?...". Ya fad'a Yana kallan Hajiya inna.Hajiya inna tai shiru sai muka ta sauke numfashi tace. "Gaskiya ne wannan to Allah ya K'ara masa lafiya Amma wallahi ni abinda yay daren shekaranjiya ne shiya tsoratani , Amma tunda kace haka Allah ya K'ara tsareshi ya kuma Kara musu lafiya Baki D'aya". Mai martaba yay murmushi ya ansa da Ameen ,yace.

"nima yanzu Zanyi shirin tafiya masallacin juma'a naga lokaci Yana kusantowa". Hajiya inna tace


"Eh kuma Hakane to bari Nima na koma wajen su Ayshan duk da itama dai jikin alhamdulillah".daga nan Hajiya inna taiwa Mai martaba sallama ta fita daga falon nasa gabad'aya.a k'ofa sukaci karo da shakundum zata shigo falon cikin shiga ta Alfarma Hakan yasa tai saurin matsawa baya ganin Hajiya inna zata fito daga falon tana sunkuyar da kanta k'asa tace. "Barka da wannan lokacin Mai babban d'aki".ta fad'a kanta a k'asa.hajiya inna tace. "Yauwa" atak'aice tana yin gaba.shakundum ta bita da Harara kafin ta shige cikin falon takawa..... k'arfe Sha biyu da Rabi na Ranar anty Amina ce zaune a kusa da gimbiya Aysha waya ce a hannunta vedio call suke da Gimbiya Bilkisu wacce ke tambayar ta jikin gimbiya Aysha.anty Amina tana Murmushi tace. "Da sauk'i Yaya Bilkisu bari ma na Kara mata wayar a fuskarta ki ganta ko zaki fi yarda Dani". Daga haka ta kai wayar dai dai fuskar gimbiya Aysha Dake kwance akan gadon kamar yadda take a Koda yaushe.gimbiya Bilkisu tace tana kallanta cikin sanyin murya. "Ya jiki Yaya gimbiya " lumshe ido gimbiya Aysha tai alamar ansawa.gimbiya Bilkisu tace. Allah ya K'ara lafiya Allah yasa kaffarane, Allah ya tashi kafad'unki Yaya gimbiya".. ta fad'a cikin rawar murya
Gimbiya Aysha na Jin ta hakan yasa nan ma ta K'ara lumshe idon nata .ita dai gimbiya Bilkisu zuba mata ido kawai tai tana kallan yayarta tana tunowa da shekarun Baya a lokacin da yayar tata take cikin k'oshin lafiyarta take rayuwar ta cikin walwala da farin ciki Amma lokaci D'aya komai ya sauya take ta runtse idonta hawaye ya soma ziraro mata a saman fuskarta,ganin haka yasa anty Amina da tasan dama dole hakan saita faru shiyasa Wani lokacin ko gimbiya Bilkisu ta k'ira zataji ya jikin na gimbiya Aysha Anty Amina take ce mata tayi bacci saboda Kukan da take aduk lokacin da zasuyi waya harma Wani lokacin tasa itama gimbiya Aysha tai hawayen, juyawa anty Amina tai taga hawaye ya kawo idon gimbiya Aysha harya soma zirarowa zuwa Kuncinta, nan hankalin anty Amina ya K'ara tashi ga ta kasa kashe wayar shigowar da Anam tai d'akin yasa ta Mik'a mata wayar tace. "Jeki ku gaisa da Yaya Bilkisu" Anam ta karb'i wayar ta fita daga d'akin zuwa falo. Anty Amina Kuma ta zauna gefen gadon tana lallashin gimbiya Aysha da kalamai masu Dad'i.......




Family doctor d'in nasu da Afeef ya k'ira Bai samu zuwa da wuri ba sai k'arfe Sha biyu da kusan Rabi saboda go slow Daya tare shi a hanya. Bayan ya gama treatment d'in raunin da Huyaam taji ya d'ago yana Kallan Ammie yace cikin ladabi. "Ranki Dad'e angama Babu Wani abun dama kawai D'an yankewa tai kuma munyi treating d'in wajen in Sha Allah Babu Wani abun
".Ya fad'a cikin girmamawa. Ammie ta Kalli k'afar Huyaam sannan ta Kalli doc tace. "Doc kaga fa tasa k'afar ta tane cikin kwalaban data fasa,ka tabbatar Babu Wanda ya mak'ale mata acikin k'afar tata?..." Doc ya Jin Jina kai yace cikin girmamawa. "Eh Babu ranki Dad'e na duba ko ina Banga Wani Abu ba"
Ammie ta Sauke numfashi tace. "Shikenan mungode Allah yasaka da Alkhairi"
Doc yace. "Babu komai Allah ya Bata lafiya ranki Dad'e bari naje zan bawa yarima takardar magun gunan da za'a Siyo matan". Ammie tace. "Shikenan Babu damuwa". Daga haka doc ya fita daga d'akin Afeef Dake tsaye a gefe yabi bayansa Ammie Kuma ta zubawa HUYAAM ido ita tareda Huda suna kallanta da tausayawa har lokacin su muneefa Basu dawo ba Amma tasan suna hanya tunda lokacin tashin nasu yayi harma ya wuce......




# # # #



07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*
*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*


PAGE 2?? 6??


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*

*Assalamualaikum mutanan arziki.yauwa Ma dai na K'ara Zuwa muku da Wani sabo albishir d'in*

*Ina kuke manyan mata masu capacity =??=???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*



*Bismillahirrahmanirrahim*


___________?&


*Bayan kwana biyu*


K'arfe shida Saura na ranar Sunday. Dawowar su daga islamiya kenan bayan an sauke su a mota kowa ya shiga b'angaren su . gabad'ayansu suka shigo falon bakinsu d'auke da sallama.Babu kowa a falon sai hadiman Ammie da suke ta kai kawo a falon suna gyara ko ina ganin komai yayi tsaf tsafa Kamar yadda sukeyi koda yaushe.sannu da zuwa suka shiga yiwa su Huyaam bayan sun ansa musu sallamar tasu.ansa musu sukai da Kulawa suna musu sannu da aiki.kafin su shige Cikin falon gabad'aya ga dama sai K'iran sallahn magrib akeyi aduka masallatan Dake nan kewayen masarutar tasu harma da masallacin cikin palace d'in.haurawa sama sukayi kowa ya shiga d'akinsa Dan zuwa su rage kayan jikinsu.huyaam ce ta tura k'ofar d'akinta tashiga Sai Wani wak'e Wak'en larabci takeyi kamar ba ita bace tai Rashin lafiya shekaran jiya ba,gashi har ta warke kamar Bata tab'a wata jinya ba, kodan dama ita Irin wannan jinyar haka take na d'an lokaci ne idan kayi kana tashi Kuma Zaka jika kamar baka tab'a yin wata jinya ba .kullo k'ofar tai bayan ta shiga ta k'arasa cikin d'akin.rage uniform d'in jikinta ta farayi kafin ta k'arasa wodrobe ta d'auki wata sassauk'ar doguwar rigar roba marar nauyi tasa. Mararta ta dafe jin yadda fitsari ya cika mata ita tai hanyar toilet d'in da sauri tashiga ta rufo k'ofar Dan dama tun a school ta fara Jin fitsarin Amma Batai ba ta bari saita dawo gida sai tayi.babu dad'ewa ta fito jikin ta da Danshin ruwa alamar har alwala ma ta d'auro,ta k'arasa inda darduma take ta d'auko D'aya ta Shimfid'a anan tsakiyar d'akin kafin ta Bud'e wardrobe d'inta ta d'auko go geggen hijab d'inta tasa sannan ta dawo kan dar dukan ta ta-da sallah.bayan ta idar tai azkar d'inta tana gamawa ta mik'e ta linke dar duman ta Maida inda take sannan ta k'arasa inda Al'qur'aninta yake ta d'auko D'aya ta fito daga d'akin nata ta jawo k'ofar ta rufe sannan ta sauka downstairs har lokacin Bata cire hijab d'in jikinta ba. Tana K'arasawa falon ta tarar har su Huda sun fara tulawar haddarsu ta islamiya zama tai itama tai joining d'insu nan ta fara nata haddar itama.. K'iran sallahn isha'i da akeyine daga masallacin palace d'in yasa duk suka dakata da karatunda da sukeyi bayan sun kai aya sukai addu'o'i sosai.ganin za'a shiga sallahn yasa duk suka mik'e suka bi jam'i Dan babu Abinda basaji na Karatun sallan da ake daga cikin masallacin...

Ammie ce ta saukowa downstairs d'in ta tsaya anan bakin stairs d'in tana kallan baba magajiya dake jera warmers a dining d'in,kafin ta maida dubanta kan su Huyaam ta zuba musu ido tana kallansu, suna Zauna saman kujerun falon suna kallo Dan tun bayan da suka idar da sallahn isha'in Huda ta linke k'atuwar daddumar da suke karatun akanta ta Maida inda take sannan ta dawo suka zauna nan falon suna kallo. baba magajiya ce ta k'araso inda Ammie ke tsaye ta tsugunna har k'asa tana kallanta tace. "Ranki Dad'e an gama had'a teburin". Ta fad'a Cikin girmamawa. Ammie na kallonta tace. "To magajiya sannu da k'ok'ari yanzu zaku koma bangaren nakune?". Ta fad'a tana kallan ta.Baba magajiya na tsugunne kanta a k'asa tace. "Eh ranki Dad'e ko akwai abinda kike buk'ata ne?. Ammie tace. "A'a Babu komai kawai tambayar ki nai dama". Sai Kuma tace.
"yauwa! Magajiya idan kika shiga kitchen d'in akwai wata kula acan wajen fridge kan kanta ki d'auka ki tafi da ita". Baba magajiya tace. "To ranki Dad'e na nagode sosai Allah ya K'ara girma da sutura Allah yasa afi haka". Ammie tace. " Ameen tashi kije". Daga haka Ammie ta k'araso cikin falon.cikin girmamawa baba magajiya ta ansawa Ammie sannan ta mik'e ta wuce kitchen Dan d'aukar Sak'on da Ammie tace ta d'auka.


Ammie na kallan su ya Zarah tace. "To ku taso muje kuyi dinner".Babu musu suka mik'e D'aya bayan D'aya suka k'arasa dining d'in. Sunyi nisa da cin abincin ya Haidar ya shigo tareda Afeef Dan daga masallaci suke bakinsu d'auke da sallama.gabad'ayansu suka ansa musu suna kallansu.ya Haidar ne kawai ya k'araso dining d'in ya zauna yay joining d'insu har Yana tsokanar Huyaam itadai sai tura Baki take tana cewa ita ba haka bane ba . shiko Afeef kallo D'aya yay musu ya wuce stairs d'in b'angaren su tun kafin ma su samu zarafin masa magana.bai dawo ba kuma har suka gama cin abincinsan . Sun dawo falon suna zazzaune harda Ammie dake zaune a falon itama,ta kalli wayarta ganin k'ira ne ya shigo Kuma Afeef ne ke K'iran nata Hannu tasa ta d'auki wayar ta kai kunne, ajiye wayar tai bayan taji abinda ya fad'a mata tana kallan Huyaam tace. "HUYAAM". HUYAAM ta juyo tana kallon Ammie tace. "Na'am Ammie". Ammie tace. "Jeki had'owa yayanku abinci ki kai masa falonsa". Tana fad'ar haka tai shiru.huyaam ta ansawa Ammie kafin ta Mik'e ta k'arasa dining d'in dama tasan Mai yake so Dan shi ba ma'abocin cin abu Mai nauyi bane ba da daddare ba.k'aramin tea flask d'in Dake kan dining d'in ta d'auka wanda ke d'auke da ruwan zafi aciki sai cup D'an tasan coffee zai had'a kuma Yana da komai da zai had'a coffee d'in acikin d'akin nasa. sai wata k'aramar warmer data d'auka da plate da spoon duk ta D'ora akan Wani madai daicin tray sannan ta bari dining d'in ta haye sama zuwa b'angaren Mazan gidan . knocking tai a Bak'in k'ofar falon nasa bayan ta Isa .Afeef dake zaune a falon d'akinsa nan kan sofa Yana operating system d'inshi.Dan communicating suke da Mr Patrick Akan dai yadda suke tafiyar da aikin companyn nasu ne, duk da baya nan Amma Kuma Yana sanin duk wani abinda ke faruwa a can companyn.sannan Yana sanin duk Wani income da out come da suka samu,Dan dama haka suke tunda ya dawo gidan kullum sai sunyi communicating da Mr Patrick.Afeef ya d'ago da kansa Jin ana knocking k'ofar falon yasan bazai wuce Ammie ce ta Aiko akawo masa abinda yace akawo masa d'inba, iznin shigowa ya Bada.turo k'ofar Huyaam tai bakinta d'auke da sallama ta shigo da tray d'in hannunta ta k'araso ta ajiye nan Saman table d'in Dake gaban sofan da Afeef yake Zaune .ta d'ago tana kallan afeef Wanda ke sanye da black shirt sai dogon Wando Kuma har lokacin Bai d'ago da kansa daga abinda yake ba tunda ya kalleta saud'aya.tana murmushi tace. "Yaya gashi na kawo".. Wani kallo yay mata alamar tana ganin Yana waya Amma take masa magana.hakan da Huyaam taga yayi mata yasa ta Gane Mai yake nufi tai shiru tana kallansa,tsura masa ido tai Ganin yadda yake turanci cikin k'warewa ke bakyace ya iya hausa ba haka ta dinga kallan sa batare da ta sani ba. bata farga ba kawai taga har ya rufe laptop d'in bayan sun gama abunda suke tattaunawa .Yana kallanta Yace cikin tsuke fuska. "Kina da hankali kuwa Ina waya zakina mun magana akaina?..." Ya fad'a Yana mata wani Irin kallo.huyaam tai shiru tana tura Baki gaba Amma Batai magana ba.kallanta kawai yake Yana mamakinta sai Kuma yay tsaki k'asa k'asa ya Kali agogon bangon Dake manne a falon ganin 8: 30pm har tayi,Sauke numfashi yayi ya dawo da kallansa kan Huyaam Dake tsaye tana wasa da zoben hannunta, kallon zoben hannun nata yayi Shima Wanda ya K'arawa hannun nata kyau kafin ya d'auke kansa Yana kallan gefe yace.kije ki k'iramin su Aziza dasu safna ke dukanku 5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login