Showing 93001 words to 96000 words out of 140150 words

Chapter 32 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

198

oyoyo Anty khadija Dake zaune falon ta sauke ajiyar zuciyar salama tana kallan su ta ce."Yanzu nake tunanin ku ganin har ana K'iran sallah Baku dawo ba"Huyaam tai murmushi ta ce "mummy ai gashi mun dawo" Anty khadija ta ce "to sannunku da dawowa" k'arasowa sukai har gaban ta sukai hugging d'inta tare da mata barka da gida.ansa musu tai tanai musu barka da zuwa Suma sannan ta ce "zata je tai sallah ne suma su wuce d'aki suje suyi" ansa mata sukai da to sannan suka haura sama... k'arfe 10 da mintuna na dare suna kwance a d'aki hirar inda suka je d'azu da abuwan da suka Gani kawai suketayi Wani suyi dariya Wani Kuma suyi murmushi "Huda Dake rik'e da wayarta tana kallan status ta d'ago ta Kalli HUYAAM ta ce "wai har kinyi status? Huyaam ta ce Tana kallan ta "eh mana ai saima gobe wannan na good night ne kawai nasa ki jira zuwa gobe kiga" Huda ta ce "ah Nima to bari nayi" siyama ta ce "aini tun d'azu Data turamin na D'ora" HUYAAM ta ce "ai Irin wannan ba'a jira da zafi zafi ake dukan k'arfe"siyama tai dariya ta ce "Sosai fa" Huda dai murmushi kawai tai tana latsa wayarta zata D'ora status diny itama ta ce "aiku Baku da dama". Huyaam ta ce "ai Babu d'aga k'afa" siyama ta tab'o Hayaam ta ce "ke mu cigaba da zancenmu" Huyaam ta gyara zamanta nan Suka cigaba da hirar da sukeyi Wanda duk akan inda suka je d'azu.....



# # # #

Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =?G?

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =?G?
07066508376



*Yan Niger 07066508376



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*

*Assalamualaikum warahmatullah*
*Ina kuke manyan mata masu capacity =???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*


My channel link =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y

PAGE 3?? 5??


___________?&

Washe gari da safe wajen k'arfe 10 Saura na safe,fitowar Huyaam daga wanka kenan tana zaune saman stool d'in Dake gaban mirror tana parking gashinta bayan ta gama shafe shafenta ita kad'ai ce a d'akin Dan tashinta daga bacci kenan ta shige toilet tai wanka,su Huda Kuma tun d'azu suka tashi har suka shirya suka fita can main falor suka barta a d'akin.wayar tace dake kan side drawer tai K'ara Alamar shigowar message juya tai ta jawota ta duba, tsaki taja da d'an k'arfi ganin number Da tun washe garin da suka sauka a Abuja kullum da safe sai number tai mata text message na barka da safiya da Kuma kalaman soyayya ,zata aje wayar kenan Wani sak'on ya K'ara shigowa da wata number a again, Bud'e ido tai da mamaki bayan taga different number ne da Wanda yake mata wannan text message d'in karanta contents d'in ta farayi kamar haka "Assalamualaikum warahmatullah. Good morning my princess how are you wake up today.from your lovely, and I love you from all my heart e&? princess.can I call you to introduce my self if you are ready? Am waiting for your answer, till I hear you good bye". iya abinda ya rubuta kenan sai emojies na love Daya tura daga k'arshe,tunani HUYAAM ta farayi na waye yake mata wannan sms d'in Kuma gashi ba mutum D'aya bane bare ta tsaida tunaninta waje D'aya, different number ne kawai ke mata sms d'in,tayi deleting Irin wannan messages d'in sunfi a k'irga tun zuwansu Abuja kullum sai an mata message Irin wannan Tarasa waye yake k'ok'arin sata Adamuwa haka tana zaman_zamanta tsaki taja da k'arfi sannan tai deleting message d'in ta ajiye wayar a nan Saman Gadon tana tura Baki gaba, K'arawa tai gaban wardrobe inda suka jera kayansu aciki ta d'auko riga da Wando na jeans tasa bayan ta saka hula a kanta sannan ta feshe jikinta da turaruka ta d'auki wayarta ta fita daga d'akin zuwa falorn inda su Huda suke bayan ta jawo k'ofar.ta samu su Huda a falon har sun gama breakfast suna ta hira ita da siyama Suna dariya, kallanta sukai ganin sai yanzu ta fito nan suka tsokanar ta, Harar su tai ta kau da kanta tana kallan Anty khadija Data fito daga kitchen ta Kalli HUYAAM ta ce "yanzu na fito nake cewa zan sa siyama taje ta_ta tasoki kiyi breakfast naga Baki fito ba Ashe kin ma tashi" Huyaam ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi ta risina ta ce "mummy Ina Kwana" Anty khadija ta ce "lafiya lau oya Maza ki k'arasa kiyi breakfast kafin Anty Fulani ta k'ira Dan Kinsan tamin worning akan indinga sa Miki ido kina cin abincin akan time" Huyaam tai murmushi ta Jin jina mata kai sannan ta k'arasa dining d'in.Anty Khadija Kuma ta k'arasa shiga cikin falon tana kallan imaan ta ce ta biyo ta daga haka ta haura sama....Huda ta Kalli HUYAAM Dake zaune saman kujera a falon tana koyawa imaan Wani assignment ta ce "Ana K'iran wayarki fa tun d'azu" d'ago da kanta Huyaam tai daga zaunan da take tana kallan Huda kafin ta ce "waye? Huda ta Kalli wayar sai Kuma ta ce "I don't know" Huyaam ta ce "okay Mik'o min" Mik'a mata wayar Huda tai ta karb'a sai taga number ne ke K'iranta tun bayan data gama breakfast ta dawo falon ta zauna tana gwadawa imaan yadda zatai assignment wannan number ke doka mata k'ira a Kuma time d'in tai picking sai taji muryar namiji ne shiyasa tai saurin kashewa tana mamakin waye?shine Kuma Ba'a fasa kirinta taba haryanzu.harta ta gama ringing ta katse Wani K'iran ya Kara shigowa batai picking ba ta zubawa wayar ido kawai ne tana kallo. Huda dake kallanta ta ce "ba k'iraki ake ba,kiyi picking mana?" Kamar Huyaam baza tai ba sai kuma tai takai kunne tai shiru.daga D'aya bangaren taji wata sassan murya Mai Dad'i da d'aukar Hankali tai mata sallama.nan da nan taji gabanta ya yanke ya Fad'i jin muryar mutumin, ciki sanyin murya ta ansa masa sai Kuma tai saurin cewa "please waye? gyaran murya yayi ya ce cikin nutsuwa "baza ki bari mu fara gaisawa ba kafin ki tambayi waye d'in? Huyaam ta harari wayar kamar shine a gabanta ta ce "kaga Malam ya za'ai bansanka ba Kawai ka k'irani kana damuna? tukunna ma a Ina ka samu contact d'ina da har Zaka k'irani? Ta fad'a cikin b'acin Rai. Lumshe ido yayi Yana sauraran dadd'ar muryarta tare da damk'e filon da yake kai Yay Wani miskilin murmushi Yana gyara kwanciyar a saman gadon sa da yake kwance ya ce "ni na sanki kece dai Baki sanni ba?Kuma kema nasan da zaki ganni zaki Gane ni" ya fad'a Yana murmushi.Huyaam da duk ta k'agu waye ta ce cikin k'osawa "please let straight to the point I said who are you?ko ka fad'amin waye kai ko Kuma na kashe wayata" ganin fa da Gaske take kashe wayar zatai yasa yay saurin mik'ewa zaune ya ce "please Huyaam dont cut my call please " Huyaam ta ce "ok to waye? Ya ce "masoyin kyakkyawar budarwa ne Irinki" HUYAAM ta zaro ido waje Jin abinda ya fad'a ta Kalli siyama da Huda taga kallanta suke Hakan yasa tai saurin katse wayar ta jefar nan saman carpet tana dafe k'irji kamar Wanda ta d'auki wuta. siyama Data gama Jin duk Wani conversation d'insu tai murmushi ta ce "waye ne halan?. Huyaam da idonta har ya kad'a saboda gigicewar da tai ta ce cikin rawar murya "I don't know who's Kawai K'irana akai" Huda tai murmushi ta ce "kodai munyi D'an uwane bamu sani ba ake b'oye mana? Ta Fad'a tana k'unshe dariyar ta ganin yadda HUYAAM ta Wani kalleta a fusace. Siyama ta ce "Kai Dan Allah fa? Ta fad'a da mamaki tana kallan Huda wacce tai maganar.Huyaam ta ce "sai dai abinda yafi D'an uwa ba D'an uwa ba a'a D'an uba.ta cigaba ta ce "nashiga uku wannan mutumin so yake ya jamin masifa yanzu idan Yaya yaji fa kinsan fa ya ce kar mu sake mu kula kowa kuma wallahi ni bansan waye ba bansan ma ayina ya samu contact d'ina ba wallahi blocking d'insa Zanyi"ta fad'a tana k'ok'arin d'aukar wayar tata.me Huda da siyama zasuyi idan ba dariya ba .Anty khadija ce ta shigo falon tana kallansu D'aya bayan D'aya taga yadda suke dariya k'asa k'asa ga sai Wani kallon Huyaam suke alamar da ita suke nan ta juya ta tsaida donta akan HUYAAM ganin yadda take a firgice tana latsa wayarta cikin tashin hankali.Anty Khadija ta ce "Mai ya faru HUYAAM? Siyama ta ce tana kunshe dariyar ta har lokacin "mummy wai Wani ne ya K'irata yanzu shine duk ta firgice haka" ta fad'a tana kallan Huyaam.Anty khadija ta zauna a kan kujerar kusa da Huyaam tana kallonta tai k'asa da murya ta ce "daughter waye ya k'irakin? Huyaam ta d'ago da dara daran idanuwanta tana kallan Anty khadija kamar zatai kuka ta ce "I don't know mummy wallahi bansan Shiba Dan Allah ki yarda Dani Kinga su Kuma sai dariya suke min Dan Allah Anty kar Yaya yaji wallahi idan yaji saiya dawo Nigeria ya zaneni"ta fad'a tana matse k'wallar D'ata zubo mata. Anty khadija tai murmushi Jin abinda ta fad'a sai Kuma ta dafa ta ce "waye shi d'in? Huyaam ta ce "wallahi mummy Bansan Shiba ki yarda Dani kawai k'irana yayi Kuma d'azu mafa ya k'irani nai picking naji muryar namiji ne yasa Nai saurin kashewa mantawa ma nai banyi blocking d'insa a time d'in ba,yanzu Kuma muna Zaune kawai ya k'irani Dana ga shine ma da bazanyi picking ba Huda ce tasa nai picking shiyasa nai Amma Wallahi mummy banso nai picking d'inba".ta fad'a tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana sheshshek'ar kuka.Anty khadija dai murmushi kawai take tana kallan Huyaam Ganin yadda duk ta tashi hankalinta ta rud'e lokaci D'aya.sai Kuma Taga ta d'auko wayar tata ta rik'e Anty khadija ta ce "Mai Zakiyi? Huyaam ta ce "blocking d'insa Zanyi mummy Dan kada ya sake K'irana". Anty khadija ta karb'i wayar tana girgiza mata kai ta ce "kar kiyi blocking d'insa" Huyaam ta zaro ido Jin abinda Anty khadija ta fad'a d'aukar tama itama d'in zatai mata fad'a ne Amma shine taji ta ce haka.Anty Khadija ta dafata tana kallanta cikin nutsuwa tai k'asa da murya ta ce "Huyaam ki tsaya saureni Kiji Abinda zan fad'a miki, kince Bakisan waye ya k'iraki ba ko? Saurin Gyad'a mata kai Huyaam tai.Anty khadija ta cigaba ta ce "Daya k'irakin Mai yace miki? Huyaam ta sunkuyar da kanta k'asa ta kasa magana.Anty khadija ta ce "ce wa yayi Yana sonki?" Ina k'asa take Huyaam ta Shige saboda kunya sai Kuma tai saurin ta girgizawa Anty khadija kai kafin ta ce cikin sanyin muryar "wai haka ya ce masoyine" Anty khadija tai murmushi ta ce "ai haka zaice da kin saurareshi". Huyaam ta kalleta da mamakin abinda ta fad'a. Aunty Khadija ta gyad'a mata kai ta ce "karkiyi blocking d'insa kinji daughter ki tsaya ki Saura reshi kiji da Mai yazo ba'a yiwa saurayi haka indai har mutum ya furta Maka kalmar soyayya to ko Bai Maka ba baka sanshi ba'a Yi masa haka kabi shi a hankali har ku rabu lafiya ina fatan Kin fahimta" Huyaam ta gyad'a mata kai sai Kuma ta ce "Anty Yaya fa ya hanamu kula samari dan lokacin Daya bamu waya haka yace Babu kula samari Kuma yasa a dinga sa mana Ido ko Baya nan yanzu idan ya Gani fa ko Kuma aka fad'a masa cewa Ina kula saurayi wallahi Anty saiya kusa karya ni besides ni banma Isa Kula samari ba tunda ko jami'a bamu shiga ba". Ta fad'a tana tura Baki gaba tareda da wasa da yatsun hannunta.anty Khadija ta kalleta Baki sake tana Jin Jina wawta da yarintar Huyaam sai Kuma ta ce "waye Wani Yaya? Kinga Huyaam karki sake ki biye Afeef Yana Ina ma yasan Mai yake faruwa to idan ya hanaku kula samari so yake Ku zauna a gaida kenan Babu AURE kome? Ke Kuma dayake Sha Sha Sha ce ke shine kika d'auki maganar tasa, Nima bance ku kula samari ba Amma indai mutum da Gaske yake Yana sonku da AURE mai zaisa baza a bashi dama ba Koba yanzu zakuyi auren ba ai Kun saurari mutum" su dai su siyama da Huda sunyi shiru suna kallan mummyn nasu" Anty khadija ta juya tana kallonsu ta ce "Kuma bari na had'a daku Kunga yanzu Jami'a zaku shiga idan har saurayi Yana sanku indai har da aure yake son naku Kuma kun kaga yayi dai dai da zab'inku to kuce yazo gidan ku ya samu iyayenku bance wai ku kula samari ahanya ko Kuma a school ba Banda wannan ku kawo su har gida a San dashi Ina fatan kunji? K'walo ido waje sukai dukansu suna kallan Anty khadija Jin abinda ta fad'a siyama ta ce "nidai mummy ban Isa AURE ba tunda ko university ban shiga ba". Anty khadija tai mata dak'uwa ta ce "ungo naki siyama an fad'a miki Yanzu girma da shekaru har Wani Wahala ce dasu ai yanzu zakiga har kunshiga Jami'a Kun gama wuyar ta dai ku Shiga d'in,yo ko
Kafin ku gama school d'inne indai har kunsamu mazajen AURE Mai zai Hana ai muku auren in yaso kwa cigaba Agidan mijin naku Yanzu a wannan zamanin fa ba'a wasa da dama indai ka samu dama kawai Kai amfani da ita rufe fuskar sukayi alamar Kunya Anty khadija ta cigaba ta ce "Nidai abinda nake daku shine kar kuyiwa wad'an da suke sanku Rashin mutunci Kuma bance a tsaida Ku awaje ko titi ku tsaya ba duk wanda yake sonku kuce yazo har gida ya samu iyayenku ina fatan kunji dai" gyad'a Mata kai sukai dukansu alamar ansawa" ta juya ta Kalli HUYAAM tana kallanta da sigar tsokana ta ce "waya sani ma ko a fitar da kukai jiyane Allah ya ansa addu'a ta na samu siriki D'an Abuja Kunga shikenan 'yata zatazo kusa Dani tai AURE dama Ina kewa" dariya sukai gabad'ayansu Huyaam ta Mike ta haura sama da sauri har tana had'awa da gudu saboda kunya Huda kuwa dariya kawai suke anty khadija ta mik'e tana D'an murmushin itama ta Kalli agogon bangon Dake falon ganin k'arfe D'aya Saura na Rana yasa ta ce "bari naje nai sallah ta fad'a tana barin falon Imaan ta d'auki littafin tabi bayanta siyama da Huda ma suka mik'e suka haura sama zuwa d'akinsu.......


___________?&


The same day Da daddare wajen k'arfe 9 da Rabi gabad'ayansu su ukun suna zaune a falo suna kallo saidai iya TV ce kawai take aiki Dan hankinsu bama ya kanta Yana kan wayoyinsu Tunda sukai dinner suka zaune Basu tashi ba Anty khadija Kuma tana falon babansu siyama daya dawo daga turai tun jiya . wayar Huyaam ce tai K'ara Alamar shigowar k'ira, nan Huyaam ta juya tana kallon number Bata ko kiftawa ilai kuwa shine tsaki taja da k'arfi tana rejecting call d'in har Saida ta jawo hankalin su siyama kanta Huda ta ce "ke Kuma keda waye kike Wani Jan tsaki ke kad'ai? Huyaam ta Wani kalleta kamar bazatai magana ba sai Kuma ta ce "wannan number ne mana aka sake K'irana da ita" siyama tai murmushi adai dai lokacin da aka sake k'ira ta ce "D'aga Kiji Mai zaice mikin" Huyaam ta yamutsa fuska ta ce "nifa wallahi gabad'aya tsoro nakeji kar naje Yaya ya sani" ta fad'a kamar zatai kuka. Siyama ta ce "ai mummy ta ce "babu komai kuma wazai fad'a masa tunda babu Wanda ya sani sai iya mu" Huyaam ta girgiza kai ta ce "siyama dan ba'a gabanki Yaya ya fad'a bane shiyasa zaki ce haka ita ai Huda ta sani shiyasa batai magana ba" Huda ta sauke numfashi ta ce "hakane Amma ai kinji dai abinda mummy ta fad'a ko?babu kyau kaiwa Wanda yake sonka wulakanci nidai anawa tunanin Mai zai Hana ki saurari da Mai yazo? Huyaam ta harareta tace "sai dai abinda yafi Wanda yake sonka ku kinji ance sona yake? Huda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login