Showing 51001 words to 54000 words out of 140150 words

Chapter 18 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

202

dawo gidan ina ka fara zuwa kafin kazo nan?..."Aziz ya Kalli maman nasu da mamakin Irin tambayar da take masa kamar Wanda yay mata Wani mugun abun sai kuma ya Sauke idansa k'asa yace. "Eh naje b'angaren Ammie na kaiwa su Huda nasu kayan kafin nazo nan". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallon takaici tace .

"Hmm! ai dama na sani daga wajen k'anwar uwar take kake,kaje ka kaso musu mak'udan kud'ad'e ka d'auko saura ka kawo nan ,bama wannan ba shi kuma wannan kayan na nasuwaye da waye?..."Aziz ya sauke numfashi yace. Nasu Ikleema da safna da Aziza". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo kafin tace.

"Me yasa Su d'in Baka kai musu nasun yanzu ba?..." AZIZ yace . Saboda dare yayi shiyasa gobe sai ikleema ta kai musu nasun."Hajiya Lubabatu tace.

"Oh! mai zaisa suma Wad'anda ka kaiwan ka bari duk ka had'a ikleema takai musun da safen ko sun fisu Wani matsayi ne a gunka da ka tafi ka kai musun Yanzu da kanka". ta fad'a cikin b'acin Rai.Aziza yace cikin k'osawa da tambayar da maman nasu ke masa

"Haba Mama wai Dan Allah Mai kike tunanine akaina? yanzu Dan na Siya musu Abu na kai musu shine abin yimin wannan tambayoyin haba Dan Allah! Yanzu shi Afeef da yake musu siyayyar wacce ta linka tawa sau Dubu Ammie batai k'orafi fa sai ke ko shi kyauta ake basa haba Dan Allah!".ya fad'a k'irjinsa na sama da k'asa Saboda b'acin Rai". Hajiya Lubabatu ta saki Baki da hanci tana kallan Aziz da mamakin abinda yake fad'a mata sai kuma can tace. "Wato ni kake yiwa wannan shouting d'in ko Aziz? To kaje ka tattare dukiyar ma gabad'aya ka kai musu shine zansan Maryam tafini matsayi awurinka".shidai AZIZ huci kawai yakeyi.hajiya Lubabatu tai tsaki ta cigaba tace. "Ya bazan bazan Maka fad'a ba kana can kana almobazzaranci da kud'inka akan Wand'anda Basu ma damu da kai ba". Aziz ya kalleta yace. "Waya fad'a miki wannan maganar na tabbatar baki sani ba zuwa akai aka fad'a miki"
Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo tace. "Ni Babu Wanda ya fad'amin kawai jiki nane ya bani".shidai Aziz kallanta kawai yake". Hajiya Lubabatu tace ai kaima kasan Dole zan sani". Aziz yace. Amma mama kema Kinsan ko Mai naiwa 'ya'yan Ammei da Mai martaba kinsan ban biya suba ko? Kiduba kiga Irin wahalar da sukai Dani ko ko Mai martaba,aini d'aukata kece ta kan gaba wajen cewa nai musu Abun duniya Koda ko banyi niyyar yin hakan ba , Amma yau kece kike ganin nayi asara idan nai musu Abu ". Hajiya Lubabatu tace a fusace. "Karka sauya min magana ta ni ba haka nace ba Amma komai zakai Mai zaisa baza ka nemi shawarata ba,Aziz kasan mahaifinka kai kad'ai ya mutu ya bari yanzu dukiyar taka zaka sa agaba sai ka kashe musu ita du sannan Hankalinka zai kwanta ko yaya?..."shaidai Aziz yay shiru Yana kallanta da mamakin abinda take fad'a.haka Hajiya Lubabatu tai ta fad'a kamar zata Ari Baki ganin baza ta fasa ba Yasa Aziz ya Mik'e tsaye ya shiga k'walawa ikleema k'ira Dake cikin d'aki. ikleema da har ta fara bacci taji muryar Yayan nasu ta fito da sauri tana mitsuka ido har ta k'araso falon tana cewa. "Yaya Gani". Ta fad'a tana kallan yanayinsa Yace. " ki d'auki wannan kayan kishiga dashi ciki sai ki d'auki naki ki ajiye sauran gobe da safe Kuma ki kaiwa su safnah da Aziza". Yana fad'ar haka ya fita daga falon ko juyowa Bai yiba da K'iran da Hajiya Lubabatu ke masa ba Saboda gabad'aya ransa ya gama B'aci da abinda tai masan .da murnar ikleema ta k'arasa ta d'auki kayan ta koma d'akinta... Hajiya Lubabatu ta Kalli Salima tana huce tace. "Yanzu badan Allah yasa kin Gani ba da shikenan haka zaita kashe musu uwar kud'i ni uwarsa Bai kawomin komai ba". Salima ta tab'e Baki tace . "Saima Kinga uban kayan Daya siya musun wannan ai Kashi D'aya ya kawowa su ikleema akan Wanda yakai can b'angaren". Hajiya Lubabatu tai k'wafa tace ."rabu dashi zai dawo ya samenine kina fa ganin inai masa magana Amma ya fice ya barni saboda Ina fad'a masa gaskiya akan abinda yake ba dai dai bane shine ya gaba ya barni ni ban tab'a ganin Sha Sha marar hankali Irin Aziz ba kwata kwata bashida wayo ko kad'an "Salima tace . "Hmmm ai wallahi mama sai Kin tashi tsaye in ba haka ba haka zaita zuwa Yana kashe musu kud'i". Hajiya Lubabatu tace. "Aikuwa Wallahi bai Isa ba dai dai nake dashi". daga haka ta Mik'e tana kallan salima tace . "Tashi muje mu kwanta kuma Ina nan Ina jiransa Allah ya kaimu goben ai ba zama zaiyi a inda yaje d'inba ko".salima mik'e tai d'akinsu itama Hajiya Lubabatu tai nata d'akin tana ta masifa ita kad'ai datai Sa'a ma yau ba kwananta bane ba.......




Aziza ce ta sauko downstairs tana Neman mummynta motsin da taji a kitchen ne yasa ta K'arasa tashiga kitchen d'in ta Tarar da fulani Salamatu tsaye gaban gas tana kallan mummyn nasu tace. "Mummy". Fulani Salamatu Dake juye green tea a cup zata kai WA Mai martaba ta juyo tana kallon Aziza sai Kuma ta sauke ajiyar zuciya tace. "Har kin ban tsoro Mai ya fito Dake yanzu bakije kin kwanta ba?...."

Aziza Tana mutsuka ido tace. "Harna Kwanta na tashi Bayan na tuna abinda zan fad'a miki". Fulani Salamatu tace. "Menene abinda zaki fad'a d'in Baki fad'a min tun safe ba ko Kuma ki bari sai gobe?..." Aziza tace. "Dama so nake idan kinje wajen Mai martaba ki tuna masa zancen wayar tamu naga Yayan ya dawo Kuma har yanzu ba'a siya mana ba bayan naji ance Yana dawowa Za'a siya mana". Ta fad'a tana Wani tura Baki gaba. Fulani Salamatu ta sauke numfashi tace. "To naji zan fad'a masa".tafi ki Kwanta Aziza tai murmushi tace. "Thank you mummy wallahi gabad'aya friends d'ina kowa da wayarsa Amma Kuma yani ace Banda waya". Ta fad'a tana wani tura Baki gaba.fulani salamatu tace. "Ai nace miki zan fad'a masa ko?.." sai alokacin Aziza ta saki ranta tace.
" Shikenan good night ". fulani Salamatu tace. "Allah ya tashe mu lafiya".daga Haka ta juya ta tafi ta haura stairs. Fulani Salamatu tabita da kallo sai Kuma ta d'auki tray d'in tea d'in data dafa tai b'angaren mai Martaba dashi......





# # # #



*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =???.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =?G?*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =???=??? mutanan arziki.





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =???)__*



PAGE 2?? 2??


*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=???=????.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=?G?*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=?I?08135305790

*Sai mun jiku =???=???=???*





*Bismillahirrahmanirrahim*


____________?&


Yau dai da shirye shiryen tarb'an Bak'i mata aka tashi acikin masarautar kano.Bak'in Kuma ba wasu bane face Dangin angon ya Bahijja ne zasu kawo lefenta. tunda bikin yau Saura wata D'aya da sati biyu. Ita ya zulaihat ba yanzu za'a kawo nata ba tunda Dangin mijin da zata aura d'in basa k'asar sai sun dawo sannan za'a kawo natan. A b'angaren su Hajiya Lubabatu kuwa masu girki suka d'auko na musamman wad'anda suka San kan aikinsu a fannin girke girke kama daga fannin abinci Dana kayan fulawa ,zamu iya cewa ma wannan b'angaren suka karanta. Kayan snacks ne kawai da kaji ake sarrafasu kala kala a Cikin k'aton kitchen d'in Dake b'angaren Hajiya Lubabatu.sannan Kuma Hajiya Lubabatu na zuwa Tayi monitoring d'insu time to Time idan taga Wani abun da Bai mata ba tai musu magana su gyara Dan tace kayan fita kunya ne Wanda za'a tarb'i Bak'in dashi wanda ko agaba idan zasu Bada labari zasuce masarautar kano kaza kaza Babu k'arya anyi komai cikin girmama da mutunci.yanzu haka ma saukowarta downstairs kenan daga d'akin ta take k'arfe 10am na safe ta nufi hanyar kitchen d'in Wannan Karan shine zuwanta na uku kenan tana zuwa tana duba su karsuyi mata abinda Bai mata ba duk da kuwa tasan sun k'ware wajen aikin nasu Amma dai komai sai anayi ana Saka ido .tsayawa tai daga nan k'ofar kitchen d'in bayan ta Isa tana kallansu Sai Kuma ta k'arasa wajen Wanda suke soya kaji gabad'ayansu suka duk'a har k'asa sunai mata barka da zuwa tare da gaisheta lokaci D'aya, Dan indai ta shigo to Saida sun K'ara gaisheta.ansa musu tai Babu yabo babu fallasa kafin tace. "kun ware Wanda za'ayi papper chicken d'in dasu Aiko?..." Ta fad'a da sigar tambaya.cikin girmamawa wacce ita zatai aikin tace. "Eh ranki Dad'e an ware". Hajiya Lubabatu ta Jin jina kai kafin tace. "Shikenan nidai abinda nakeso daku shine please kuyi min Aiki Yadda ya kamata Dan Allah kada kusa naji kunya a gaban manyan mutane". Ta fad'a da sigar worning. Cikin girmamawa suka ansa mata da in Sha Allah. Ta Jin jina kai sannan ta juya zata fita suka bita da fatan Sauka lafiya....


K'arfe shad'aya da mintuna ya Zarah ce tsaye a falon su cikin Shigar hijab har k'asa zata fita school yau lecture d'in tasu ta Rana ce k'arfe shabiyu, Huyaam take jira zata kawo mata ruwa a kitchen Amma shiru kamar Wacce aka aiki bawa garinsu bata dawo ba, Dan tafi minti D'aya a kitchen d'in. d'aga murya ya Zarah tai tak'ira sunanta da "Huyaam wai me kikeyi ne a kitchen d'in tafiya fa Zanyi time na tafiya kefa nake jira". Ta fad'a cikin k'osawa.Huyaam ta fito da sauri tana goge hannunta tana murmushi tace. "Kai ya Zarah sai kace wacce na Dad'e bandawo ba". Ya Zarah ta karb'i ruwan tana harararta tace. "Aikema kin sani idan kin dad'e d'in idan ma Baki Yi ba".ta fad'a tana karb'ar ruwan daga hannun Huyaam sannan tasa acikin jakar ta ta. Ya Afeef ne ya sauko falon cikin shigar kayan sarauta Wanda sukai masa bala'in kyau Dan sai wani tashin k'amshi yakeyi ta ko Ina .kallansa Huyaam takeyi harya k'arasa saukowa downstairs d'in ido hud'u sukai da Huyaam da Bata daina kallan Saba dan babu K'arya wankan Dayay yayi masa bala'in Kyau ya D'an tsuke fuska Hakan yasa HUYAAM tai dariya tace. "Wallahi Yaya kayi kyau sosai". Ta fad'a har dimples d'inta suna lostsawa hagu da dama Wanda ke K'ara mata kyau.bai ansa ba yace.

"Ina Ammie take?..."kafin ta bashi ansa Ammie ta sauko downstairs d'in ta k'araso har tsakiyar falon tana kallan Huyaam tace .

"Ina Huda take?..." HUYAAM tace.

"tana d'aki ai Baki ganta bane ba". Ammie tace.

" na lek'a d'akin banganta taba". Ya zarah tace. "Tana d'akina tana graya min kayana". Ammie ta Jin jina kai.
" tace shikenan". Afeef ne ya
K'araso har gaban Ammie ya D'an zame hular kansa sannan ya duk'ar da kan nasa agaban Ammie Hakan yasa Ammie ta D'ora hannunta kan nasa tana murmushi ta shafa kan nasa tace .


"Allah yay Maka albarka Ina zuwa haka?...." Ya d'ago yana Maida hukar kansa yace.

"Zanje school d'in su Zarah ne akwai abinda zanje nayi". Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah! Sai ka dawo". ya Zarah da take tsaye zata gaida shi kafin ta tafi tace."Yaya ko zaka saukeni ne". Ta fad'a a d'ad'are Dan tasan bama d'aukar tata Zanyi ba . Amma ga mamakinta sai taji yace. "Ok".daga haka yay hanyar fita daga falon Huyaam na Jin haka tace. "Yaya Nima na biyoka sai mu dawo tare ko juyowa Bai yi ba balle ya ansa mata.ya Zarah tabi bayansa da Sauri bayan tai ma Ammie sallama.bayan fitar su Ammie na kallan Huyaam tace. "To idan ya tafi Dake d'in Ina zai kaiki?..."Huyaam tai shiru tana kallan Ammie". Ammie girgiza tace. "Wuce ki k'iramin Huda idan ta gama akwai aikin da zan saku". Babu musu HUYAAM ta haye sama da sauri.Ammie Kuma ta samu waje ta zauna a falon tana jiransu........


K'arfe biyu sauya fulani Salamatu ce tsaye a Wani k'aton store Dake b'angaren Hajiya Lubabatu inda aka ajiye kayan tarb'ar Bak'in anyi packaging d'insu an kammala komai tun Wajen k'arfe D'aya ,sannan an ajeye komai a inda ya dace komai yayi Masha Allah Bak'in kawai ake jiran zuwan nasu ta bakin na Hajiya Lubabatu Dake cewa ayi komai cikin girmamawa aikuwa anyi d'in Dan Babu laifi sunyi abu cikin girmamawa anyi Abun fita kunya sosai.Fulani Salamatu ta juyo tana kallon hajiya Lubabatu bayan ta gama ganin Komai tace. "K'awata komai yayi yadda ya dace Babu Wanda ya isa ya Raina mu gaskiya mutanan nan sun iya aiki sunyi komai yadda ya dace". Ta fad'a tana kallan Hajiya Lubabatu... Hajiya Lubabatu tace. "Babu laifi Nima naga k'ok'arinsu gaskiya sun iya aiki". Fulani Salamatu tace. "sosai ma kefa su suke yiwa gidan governor kano duk Wani kwangila da za'ayi indai anan government house d'in ne taro ko biki ke duk Wani Wanda yake ji da kansa a garin kano indai Yana so ya fita kunyar Bak'i na b'angaren abinda zai tarb'esu to ya k'irasu Dan sun iya aiki". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya nima na shaida Kuma na Yaba musu". Fulani Salamatu tace. "To ni dai bari na koma tunda dai naga abinda ya kawonin anjima kafin suzo zan dawo saboda mu shirya komai yadda ya dace". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya ne to Dan Allah ki dawo da wuri". Tace. "In Sha Allah da wuri zan dawo". Daga haka ta fita daga store d'in Hajiya Lubabatu na biye da ita har zuwa falon hadimar ta karima da tai mata rakiya ta mik'e daga zuben da take a falon tabi bayan ta bayan taiwa Hajiya Lubabatu sallama cikin girmamawa.......



___________?&


K'arfe Hud'u da Rabi na Ranar Ammie ce ta fito cikin shiga ta Alfarma itama tayi bala'in kyau ba kad'an ba Dan kamar ba wacce ta haifi yara d'ai d'ai har bakwai ba . sanye take cikin Wani ubansun less Wanda yalashe mak'uden kud'ad'e ta D'ora alkyabba akai Mai tsadar gaske sai Wani walwali take kamar wacce zata gasar kyau tana kallan su Huyaam Dake zaune falon su biyu sai muneefa shi muneeb Bai dawo ba tunda ya fita sallahr ASR ya haidar kan dama Yana wajen aiki nan companyn Mai martaba Dake jihar kano, ya Zarah ma tunda ta fita school Bata dawo ba .garama Afeef ya dawo d'azu Dan Bai Dad'e da sake fita ba.tana kallansu tace.

"Huyaam ku zauna zanje b'angaren Hajiya Lubabatu zamu tarb'i Bak'in nan".so banaso na ganku ko a compound ne kunji ai?.." duk da tasan ba fitar suke ba, kuma baza su fara yanzu ba amma dai tana musu worning ne.dayake yau alhamis babu Islamiya Kuma Babu inda zasu yasa suke Zaune a falon bayan sun gama karatun Al'qur'ani d'azu da sukai ASR prayer.har Suka had'a Baki wajen ansa mata da to kafin HUYAAM tace. "Ammie Kinga yadda kikai kyau kuwa?..." Ta fad'a cikin zuzu tawa .Ammie tai mata murmushi tace. "Ni bangani ba kece dai kika Gane min". HUYAAM tace . "Ai kuwa kinyi kyau sosai sai Kin dawo". Tace. "Allah yasa" ta fad'a tana gyara zaman alkyabbar jikinta.hadimarta baba magajiya itace take tsaye daga Bayan Ammie Dan ita zatai mata rakayi har b'angaren Hajiya Lubabatun .Ammie tai gaba Baba magajiya na biye da ita da Jakarta a hannunta tana ansawa muneefa Dake mata adawo lafiya.huyaam sukabi Ammie da kallo har ta fice daga falon gabad'aya.. Ammie da taje b'angaren Hajiya Lubabatu ta iske Fulani Salamatu tare da k'awar tata dukansu suma cikin shiga ta Alfarma kowacce Tasha less sai Wani walwali sukeyi. Fulani Salamatu sai Wani jiji da kai take da k'yar ta iya ansa sallamar da Ammie tai musu har suka gaisa Amma ita Hajiya Lubabatu da yake ita tasan ta kan duniya faran Faran suka gaisa da Ammie har take cewa "Fulani nayi fushi Kuna manyan iyaye sai Yanzu kuka zo? Ammie dai murmushi tai tace ai mata afuwa haka nan tai ta janta da zance kamar ba ita bace take zaginta idan suka had'u da Fulani Salamatu ba .itama kanta Fulani Salamatu kallan Hajiya Lubabatu take da mamakin yadda ta sakewa Ammie Amma Kuma batai magana ba tai shiru tana kallan iKon Allah.k'annenn Hajiya Lubabatu da 'yan uwanta da sisters d'in ta duk sunzo dasu za'ai tarb'an bakin suka risina suka shiga Gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa musu itama da kulawa, sisters d'in su baba turaki dai suna hanya Basu k'araso ba Amma ance saua k'iris su k'araso iya k'anwarsu ce D'aya da ba'a nan take AURE ba bazata samu damar zuwa ba.Ammie na nan zauna kusa da antyn su Ikleema Babu dad'ewa saiga Hajiya Aysha nan wato maman su safna, nan suka zauna suke gaisawa.ita dai Hajiya lubabatu ta juyar da kanta gefe sai faman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login