Showing 3001 words to 6000 words out of 140150 words

Chapter 2 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

175

babyn sun Gani ba?"ta fad'a tana kallan gimbiya Bilkisu.

Dumm!!! gaban gimbiya Bilkisu ya ansa kafin ta taso tace Cikin sanyin murya .

"Yaya gimbiya!wai kina nufin babyn Bata gunki?".ta fad'a cikin fad'uwar gaba.

"Take ita itama gaban gimbiya Aysha ya ansa Amma saita maze tace.

"A'a ai tana gunki da nace ki kaiwa su goggo ita".

Gimbiya Bilkisu ta fara duba falon kafin tace

" mun had'u da wata mata danaga zata shigo nan falon ga nikuma fitsari ya matseni alokacin,danaga Ina gab da toilet d'in d'akin Dake corridorn yasa na Bata babyn nace ta rik'emin ita kafin na fito,dana fito Kuma bangan taba d'auka Tama ko ta k'arasa shigowa ta kawo Miki ita".ta fad'a cikin fad'uwar gaba Dan bataga matar a falon ba yanzu.

Itama gimbiya Aysha juyawar tai tana kallan mutanan Dake falon kafin tace.

"wacece kika bawa babyn ?".ta fad'a tana k'arewa sauran wad'anda suka rage afalon kallo Wanda duk yawancinsu ma 'yan cikin palace d'in ne da basu k'arasa tafiya ba suna hira.

Gimbiya Bilkisu tana zare ido tace .

"wata me nik'af ce Banga fuskarta ba",ta fad'a cikin rawar murya.gimbiya Aysha tace .

"Me nik'af kuma?... gaskiya Banga wata Mai nikaf ta shigo falon nan ba"ta fad'a tana k'arewa mutanan falon kallo kamar zataga Mai nik'af d'in.

Sai Kuma ta shiga tambayar su da cewa sunga wata Mai nik'af ta shigo falon lokacin da bata nan?kowa yace a'a Dan sun dad'e afalon suma kuma tabbas basuga wata Mai nik'af Koda wasa ta shigo falon ba,take duk suka rikice suka fara Neman matar data d'auki babyn,ko kuma ta bawa wasu Amma shiru kakeji tun suna nema cikin falon har aka bazama zuwa cikin palace d'in Neman babyn part by part ko Kuma Wanda yaga matar Amma shiru kakeji wasu sunce tabbas kamar sun ganta Amma kuma Basu kula da inda tai ba,take suka K'ara shiga cikin Tashin hankali cikin k'an k'anin lokaci palace d'in nan tasan halin da ake ciki na jaririya ta Bat'a hankalin wasu duk ya tashi ya za'ayi ace acikin palace za'a zace jaririyar da satin ta D'aya a duniya.haka aka dinga NEMA Amma ba'a ganta ba zuwa lokacin har gimbiya Aysha ta sare sai kuka take Dak'yar goggoninsu suka kamota suka shigarta d'akinta sai kuka take gwanin ban tausayi suna Bata Baki,gimbiya Bilkisu kuwa zamu iya cewa tafi Mai jegon ma shiga tashin hankali tunda ita ce sanadin komai har Mai martaba yaji shima take ya shiga cikin Tashin hankali Amma Bai nuna ba saiya D'an Dake yana Basu hak'uri da kwantar musu da hankali da cewa yasa ayi bincike in Sha na za'a ga baby Zainab.


Anan wannan rugun tsumin a cikin palace anan kuma su safara har sunbar gari tareda baby Zainab sai Wani dogari haladu Wanda sukeyiwa shakundum aiki da yake driving.tafiya sukai ta kusan two hours Dan su kansu basusan Ina suke nufa kawai su burinsu suyi nesa da masarautar sannu su aikata Abinda aka umarcesu Dashi.


Basu Tsaya a ko Ina ba sai a jejin can wajen gaba da Abuja iyaka Abuja da minna anan suka tsaya sukai parking motarsu Nan wajen Bakin titi inda babu motsin Wani mahaluk'i ko motoci babu a Hanyar ko tsoro basaji saboda zuciyar su ta riga da ta tsike da Rashin imani.haladu ya juya Yana kallan safara wacce ke rik'e da baby Zainab wacce ke sharar bacci abinta Bai war Allah da Batasan komai ba yace.


"Safara gashi munzo saiki cika aiki tunda ni kin hanani Yi ga kwalin nan sai ki jefata aciki mu wullarta cikin dajin nan tun kafin a farga bama cikin masarauta"ya Fad'a Yana kallan safara data k'urawa baby Zainab ido tana kallan ta.


Safara Ta d'ago tana sauke numfashi kafin tace .


"Ni ansawa ganin haladu gara mu jefata cikin kwalin kawai da ranta basai mun kashe taba.
,Dan na tabbata kafin safiya ta mutu tunda ko sanyin nan da ake na gari zaisa ta mutu banaso mu kasheta ne kar zunubin yayi mana yawa"ta fad'a tana kallan haladu da tun lokacin data fara magana yake kallanta.


Haladu yace .

"A'a safara yanzu idan aka ga yarinyar kinsan Wallahi hukuncin kisa ne namu". ya fad'a a tsorace.


Safara tace . "babu Wanda zai ganta ma haladu kagafa a inda muke jejine iya jeji kana fa ganin ko motoci babu a Hanyar".ta fada tana kallan wajen.


Haladu yace.

"Shikenan safara tunda kinci haka jefata a kwalin kije ki jefarta".Babu musu safara ta Bud'e kyakkyawan towel d'in da baby Zainab wacce alokacin ta fara mutsu mutsu Amma Hakanan safara rufeta cikin towel d'in ta jefata ta rufeta a cikin kwalin ta fita daga motar .

ta fara shiga jejin harta fara nisa ta juya taga haladu na waya ta ajiye baby Zainab ta Bud'e kwalin ta lek'ata Taga ta Bud'e ido tasa hannu abakinta nan da nan tausayinta ya d'arsu azuciyar safara da har zata rufe kwalin sai Kuma ta Bud'e kad'an kafin ta juya tafi tabar wajen tana Jin yadda baby Zainab ta fara k'ananun kuka Amma Bata juyoba ta koma motar.


Tana zuwa bayan ta shiga haladu yace.

"Ya! kin ajiyetan?..".

Safara tace a Sanyaye.


"Eh mutafi". Haladu yace.


"Anya ko safara shawarar nan taki tayi kuwa? gaskiya nake ganin kamar akwai matsala".

Safara tace.

"Babu wata matsala haladu mu tafi kawai haladu ya ta-da motar suka bar wajen suka bar baby Zainab daga ita sai ya ubangiji.....




__________?&


Acikin palace kuwa Har k'arfe biyun dare ba'a ga baby Zainab ba nanfa gimbiya Aysha ta sare take ta yanke jiki ta fad'i nan su goggo sukai kanta suna K'iran sunanta, Amma babu inda ya motsi ajikinta take aka k'ira Mai martaba aka fad'a masa.yace za'a turo mota a d'auke ta akaita asibiti. ganin wannan halin da gimbiya Aysha ta shiga yasa itama gimbiya Bilkisu itama ke Neman fad'uwa take itama aka tarota suka zaunar ta a kan sofan Dake d'akin suna Bata hak'uri.gimbiya Bilkisu kuka kawai take kamar ranta zai fita haka takeji Dan Gani take itace silar faruwar komai.Aranar dai mutanan palace sunga tashin hankali ba kad'an ba,Dan sun shiga Irin tashin hankalin da Basu tab'a shiga bane tun atarihin masarautar.


Shiyasa a ranar kuwa palace Shiru tai kamar Babu mutane acikinta daga cikin gidan har su kansu masu gidan.





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD







*


(The love e&? story)



*Paid book=???*


*Free pages*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*




*___(MRS SARAKIES =???)=?1?___*



*Bismillahirrahmanirrahim*




Page 3??


___________?&


Washe gari da safe har k'arfe bakwai Saura gimbiya Aysha Bata farka daga doguwar Sumar da tai ba, gabad'aya hankalin su goggo ya gama tashi dashi kansa Mai martaba,iya da bugun zuciyarta ne kawai doctors d'in suka Gane cewa tana a yare .da k'yar da k'yar dai likitocin suka samu nasarar dai dai tuwar numfashinta kafin su d'auki mataki ja gaba .ganin numfashin nata ya dawo normal tana kuma buk'atar hutu yasa sukai mata allurar bacci kafin su fito suna sharce gumin wahala.


Gabad'aya daga kan gimbiya Bilkisu zuwa kan su goggoninsu suna nan Cikin asibitin suna zaune a k'ofar d'akin da aka kai gimbiya Aysha kafin daga baya akaisu Wani d'aki Dake cikin asibitin na musamman Dan su huta dan har K'arfe ukun dare a tsaye suke sun kasa sama saboda tashin hankali Dan Suma dai basuyi baccin ba yadda sukaga dare haka sukaga rana a wannan dare.


Wajen k'arfe takwas da Rabi Mai martaba yazo asibitin direct d'akin da gimbiya Aysha take ciki akai mishi rakiya .Yana zuwa Yana Bud'e k'ofar d'akin bak'insa d'auke da sallama zuciyarsa na bugawa da halin da zaizo ya tadda matarsa aciki idonsa ya sauka akan gadon adai dai lokacin da gimbiya Aysha ta Bud'e idonta Dan da kuka ma ta farka tana daga kwancen da take.k'arar Bud'e k'ofar da kamashin turaran da taji yasata juyo tana kallon Bakin k'ofar Dak'yar ,ido hud'un da sukai da Mai martaba yasa Bata d'auke idonta akansaba Dan gani take kamar zata ga babyn ta a hannunsa ya kawo mata ita ,tana kallansa harya k'araso cikin d'akin ya zauna nan kan kujerar Dake gaban gadon Yana kallan gimbiya Aysha har lokacin.


Gimbiya Aysha ta motsa lips d'inta kad'an tana k'ok'arin dai dai ta kanta tace.


"Rankai Dad'e ba'a ga baby naba ko?,ta fad'a tana kallansa .Mai martaba yay jimmm yana kauda kansa daga kallanta Dan Wani Irin rauni yakeji idan yaga matar sa Abar alfaharinsa tana wannan kukan ya Dake ya juyo Yana kallan ta yace cikin nutsuwarsa.


"Kiyi hak'uri da abinda zan fad'a Maki fulani!, hak'ik'a wannan abun daya faru muk'addarine daga ubangijinmu ,kiyi hak'urin sanar mikin da Zanyi cewar har yanzu ba'a ga Mai sunan Daada ba , Amma Kuma muna nan muna binciken yadda za'a sameta, yanzu haka kafin na taho saida natara zama na gaggawa a cikin masarautar nan tundaga kan ma'aikata har masu sarauta Dake cikin gidan nan ,nai tambaya ga duk Wanda yasan yaga zuwan matar da akace ta d'auki Mai sunan Daada da kuma fitar da ita daga cikin masarautar nan, Amma kowa yace shi bai ganta ba, sannan nasa a ciki tamin duk Wanda yazo taron sunan nan tun daga kan 'yan gidan nan Wanda suke AURE a waje har Wad'anda ke wajen masarautar nan duk nasa ayi bin cike yanzu haka ana kan binciken so Dan Allah Ina rok'anki da kiyi hak'uri Dan Allah Fulani"ya fad'a cikin lallashi.


Tunda ya fara magana gimbiya Aysha take kuka marar sauti tana kallan Mai martaba cikin rawar murya tace.


"Yanzu shikenan rankai Dad'e na na rasa baby nah jaririyace fa yaushe aka haifeta yaufa satin ta D'aya a duniya meyasa za'a rabani da ita? Metai musu ko kuma ni Mai nai musu Dana can cancin wannan sakayyar daga wajen su ,Ni Yanzu babbar damuwata shine bansan a Wani Hali take ciki ba zuciyata zafi take mun kamar ta fashe haka nakeji rankai Dad'e"ta fad'a cikin gunjin kuka .


Mai martaba ya mik'e daga zaunan da yake cikin nutsuwa ya Tako har zuwa gaban gadon ya d'ago gimbiya Aysha zuwa jikinsa Ya zauna nan akusa da ita tana jikinsa har lokacin.


Yay k'asa da murya yace.


"Na sani Fulani Amma kiyi hak'uri Wallahi Nima Ina cikin damuwa Amma in Sha Allah za'a ganta"ya fad'a cikin damuwa.


Gimbiya Aysha ta d'ago tana kallansa kafin tace cikin Damuwa.


"Yanzu Ina sultan yake?Dan Allah ka kula min dashi shima karsu rabani dashi".ta fad'a fuskarta na bayyanar da tsoro.


Mai martaba ya shafa kanta yace ..

Babu Wanda zai rabaki da sultan Yana tare dasu goggo, please ummu sultan kiyi hak'uri"ya fad'a shima cikin rauni.


Gimbiya Aysha kasa shiru tai Dan gabad'aya jinta take kamar ba itaba yanzu Shikenan anrabata da 'yarta wacce take mutuwar so da k'auna, tunda tai ido hud'u da babyn bayan haihuwar ta datai lokaci D'aya taji babyn gama tashiga ranta ashe bama zata rayu da itaba yanzu ko a wani Hali take oho. idan ta tuno da wannan Abu shike sawa taji Wani kunci ya mamaye mata zuciya.knocking k'ofar d'akin da akai yasa Mai martaba matsawa daga kusa da gimbiya Aysha ya koma kan kujerar ya zauna kafin ya Bada iznin shigowa.daya daga cikin doc din suke kula da gimbiya Aysha ce tashigo da sallama abakinta ta gaida Mai martaba cikin ladabi ,Mai martaba ya ansa mata Batare da ya kalleta ba ta sanar dashi tazo duba Jikin gimbiya Aysha ne, take mai marataba ya Bata iznin ,ta tafi ta k'arasa gaban gadon gimbiya Aysha ke zaune akai har lokacin tana sunkuye da kanta k'asa tana share hawayen dayak'i tsaya mata doc tai mata magana cikin ladabi akan tazo duba tane,Da ka gimbiya Aysha ta ansa mata nan doc ta fara duba gimbiya Aysha cikin nutsuwa ganin jinin natama ya sauka yasa ta rubutu Mata sallama tareda prescription d'in da zata siya bayan ta gama ta Kalli Mai martaba da Ladabi tace.


"Rankai Dad'e za'a iya sallamarta, yanzu haka ma na rubuta sallamar".ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.


Mai martaba ya jinjina kai kafin yace cikin nutsuwa.

"Ok doc bari naje yanzu sai su Bilkisu su shigo su taimaka mata" Yana fadar haka ya Maida dubansa kan gimbiya Aysha, tuni doc d'in ta fice daga d'akinta


Mai martaba Yana kallan gimbiya Aysha yace .



"Allah ya K'ara lafiya Fulani Dan Allah kada ki k'ara sawa kanki Wata Damuwar please kinsan bazan iya d'auka ba koh?...."ya fad'a Yana mata Wani Irin kallo.


Gimbiya Aysha ta sunkuyar da kanta k'asa tana gyad'a masa kai hawaye na zirarowa a saman fuskarta tuni Mai martaba ya kau da kansa Yana barin d'akin gimbiya Aysha ta d'ago ta bishi da kallo .


___________?&


Alokacin da su safara suka jefar da baby Zainab Basu dawo gidan ba Dan wanna umarnin shakundum ne saboda tace Dan kada a zargesu karsu sake su shigo masarautar a wannan lokacin har sai anshiga masallaci Dan yin sallahn ASuba, alokacin ne idon mutane baya kan kowa saboda a wannan lokacin da kowa yana masallaci ne Dan yin ibadah,Aiko haka akayi Dan awannan lokacin suka samu damar dawowa masarautar kuma da sukai Sa'a babu Wanda ya gansu Daga nan suka cigaba da aikinsu. Awannan dare haka shakundum tai bacci Irin Wanda ta Dad'e batai irin Saba ,Dan Yanzu kan ta k'udiri aniyar idan har Sau Dubu gimbiya Aysha zata haihu to itama sau dubu saita salwantar mata da abinda ta haifa Dan bazata fasa ba .Ai Allah nema yasa wannan cikin zaizo duniya Amma tun ranar da ta San gimbiya Aysha tana da ciki tai ta D'ana mata tarkon mugunta tana tsallakewa Allah ne kad'ai yasa zata haihun sai gashi yanzu bayan ta haihun asannan burin nata ya cika.yanzu sultan ne kawai ya rage Shine matsalarta ta rasa yadda akai har haryau sultan yak'i mutuwa duk da abubuwan da tasa akai tai masa Amma sultan yak'i mutuwa Kuma tabi duk wata hanya da sata sa a b'atar dashi abinci yaci tura, to shiyasa Yanzu tunda hak'arta ta kasa cinma ruwa akan sultan yasa tasa masa ciwo kullum acikin ciwo sultan yake baida ishashshiyar lafiya baya zuwa ko Ina acikin gidan sarautan nan ada ko school baya zuwa sai dai ai masa lesson Amma taga yanzu ya fara zuwa school d'in dole ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kuma ta k'ara dak'ile wannann hanyar sultan kusan 10years yake a Shekaru Amma Yanzu idan kika ganshi kamar D'an shekara 5 saboda yadda ya koma baya shiga cikin mutane kullum Yana part d'insu, part d'in nasuma sai dai d'akin uwarsa ko kuma Wanda ake kula dashi.yanzu haka tana zaune bakin gado tashinta daga bacci kenan ta zauna take wannan tunanin farin ciki ne fall zaciyarta tai Wani murmushi kafin Tace a fili .


"wallahi Aysha ni sarauniya Hajara Kuma shakundum indai Ina numfashi a duniya baki isa kin haihu da Mai martaba agidan nan ba matuk'ar ni ban haihuba". tana fad'ar haka ta Mik'e Dan shiga toilet danyin wanka bayan ta fito a gurguje ta shirya tunda taji labarin cewa an sallamo gimbiya Aysha tun d'azu daga asibitin Hakan yasa zataje tai mata jaje Dan kada a zargeta..haka ta fito hadimanta sukai mata rakiya har part d'in gimbiya Aysha Wanda alokacin suma 'yan cikin masa rautar suna ta zuwa dan Yi mata jaje.


__________?&


Goggo hauwa ta dubi gimbiya Aysha wacce ke kwance saman gadon d'akin nata zazzab'i ya gama rufeta ruf tace cikin kwantar da murya.


"Dan Allah gimbiya Aysha kiyi hak'uri idan Mai sunan Mai babban d'aki (sunan Daada kenan mahaifiyar Mai martaba Ina fatan kun Gane shi akasawa jaririyar)rabo ce Za'a ganta Dan Allah kiyi hakuri kinji"ta fad'a cikin sigar rarrashi.dan tunda suka dawo daga asibitin nan gimbiya Aysha take kwance Bata tashi ba .


gimbiya Aysha batai magana ba Dan ita kad'ai tasan halin da take ciki ayanzu.


Gimbiya Bilkisu ce dake zaune kan kujera dake d'akin ta haday Kanta da gwiwa damuwa fal ranta idonta ya kumbura yay suntum saboda Kukan da Tasha tace cikin rawar murya wacce k'iris ya rage ta saki Kukan da take rik'ewa.


"Dan Allah Yaya gimbiya kiyi hak'uri nasan nice silar faruwar komai Dan Allah ki yafemin wallahi idan na tuno da cewa nice silar faruwar komai sai naji kamar zan Mutu saboda Damuwa,Dan Allah Yaya gimbiya ki yafemin".ta fad'a tana Wani Irin kuka Mai ratsa zuciya.


Jin Muryar k'anwar tata yasa Gimbiya Aysha ta Bud'e idanta kad'an da suka kumbura saboda Kuka tana kallan gimbiya Bilkisu tace cikin dashashshiyar Murya.


"Ko kad'an Bakimun Komai ba Bilkisu dama can Allah ya tsara koba ta silar kiba sai an rasa babyn mu ki daina fad'ar Irin wannan nidai banga laifin kiba "ta fad'a cikin rawar murya.


Gimbiya Bilkisu ta Kalli gimbiya Aysha tace.


"Nagode da kika fahimceni Yaya gimbiya in Sha Allah za'a ga babyn duk Wanda ya d'auketa ma Allah bazai tab'a Basu damar cutar mana da ita ba"ta fad'a tana share hawayen ta.goggoninsu duk suka ansa da in Sha Allah.itadai gimbiya Aysha kukun zuci kawai take .aranar haka akai ta zuwa yiwa gimbiya Aysha jaje wasu basa samun damar ganinta saboda halin da take ciki.hajiyarsu data ji wannan Abu haka tai ta K'iran gimbiya Aysha tana Bata Baki ita ko Daada mahaifiyar Mai martaba tana can india ganin likita shiyasa Bata san halin da ake ciki ba ,kuma Mai martaba da kansa ya hana a fad'a mata saboda karsu ta-da mata da hankali Dan batanan akai haihuwar tana can, aikuwa tunda taji labarin haihuwar da Kuma takwarar da akai mata take ta murna da muradun dawowa taga takwararta.


Wasa wasa har baby Zainab tai sati D'aya da Bat'a ba'a ganta ba Babu labarinta babu dalilinta nan dai gimbiya Aysha ta sare da samun 'yarta Dan tasan tunda har aka kai wannan lokacin ba'a gantaba tofa samunta sai dai tsananin rabo .Ahaka dai ta fawwalawa Allah lamuranta tana addu'a babu dare babu Rana akan idan 'yarta tana raye Allah yasa ta tafad'a Hannu nagari idan kuma Bata raye Allah yay Mata Rahma Dan ita yanzu tama daina kukan filin sai dai na zuci ta Mik'awa Allah duka Al'amuranta.A Ranar da baby Zainab ta cika sati biyu da Bat'a a Kuma ranar su goggo hauwa suka tafi bayan sunyiwa gimbiya Aysha nasiha sosai tunda dama sun D'an K'ara zamane dan kwantar wa da gimbiya Aysha hankali Ba Dan komai ba, itadai ta nuna musu ta karb'i k'addara ahaka har akai wata D'aya ba'a ga baby Zainab ba zuwa lokacin Kuma gimbiya Aysha harta gama fiddarai daga samun baby Zainab wacce ko nickname ba'a sa mata ba Mai martaba da hajiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login