Showing 114001 words to 117000 words out of 140150 words

Chapter 39 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

204

Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*






0706650376_________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*

*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*


My channel link =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y



*Bismillahirrahmanirrahim*


*Saura 1 page mu gama free pages ku hanzarta ku biya kud'in Karatunku*


PAGE 4?? 1??


_____________?&


Muryar Siyama da Huyaam taji tana cewa ita ce ta Bud'e mata k'ofar yasa Huyaam Sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama Jin ba Afeef d'in bane kamar yadda take tunani ba,A hakan ma ba wai ta dawo dai dai bane daga fad'uwar gaban da takeji kawai dai ta d'anji nutsuwa ne Jin siyama ce.da k'yar da k'yar ta iya Tashi ta sauko daga saman gadon ta nufi k'ofar walking slowly tana tafiya har ta Isa Bak'in k'ofar inda tasa Hannu ta Bud'e k'ofar, tsuke fuska tai Ganin siyama yasa ta tsaya tana kallan Siyama wacce itama kallon nata takeyi.siyama ta ce "Mai ya faru kike Kuka ne? tafad'a tana kallan fuskar HUYAAM wacce tai JAA Lokaci D'aya Saboda Kukan da Tasha.harara Huyaam ta maka mata batai magana ba,nan siyama ta sakar mata murmushi ganin yadda take Hararar ta da Gaske kafin ta ce "toni Ban hanya na wuce ciki" ta fad'a tana gimtse dariyarta ta .k'ara tsuke fuska HUYAAM tai Ganin lallai ma siyama ta Raina Mata hankali wato dariya ma take mata koh? Su jaza mata bala'i Amma Kuma su b'uge ta yi mata dariya.kwafa tai ta matsa gefe tana bawa siyama hanya har ta shigo d'akin kafin itama tabi bayanta ganin ta shiga ciki. Zama tai kusa da siyama wacce ta zauna bakin gadon har lokacin murmushi ne a saman fuskarta tana kallon Huyaam ta ce "hope everything is going well sisto?" sai Kuma ta gyara zamanta tana kallan Huyaam wacce ta fara hawaye lokaci D'aya,dafa kafad'arta tai ta ce cikin damuwa "Mai ya faru Kuma kike hawaye?" Sauke hannun siyama Huyaam tai daga saman kafad'arta ta ce cikin rawar murya da b'acin Rai "siyama Kun cuceni Saida nace muku Yaya zai iya zuwa ya samemu tunda Yana gidan Amma kuka ce lallai bazai ganmu ba idan ma ya ganmu Babu abinda zai min to gashi yanzu kunja ya ganmu wallahi Kuma nasan kashe ni zaiyi na shiga uku" Ta fad'a tana fashewa da gunjin Kuka. Jikin siyama ne yay sanyi lokaci D'aya Jin wai Afeef ya gansu, sai kuma taji Bata ji Dad'i aranta ba Dan kuwa tabbas su suka jaza mata Amma saita dake ta ce cikin k'asa da murya "ya ganku fa kika ce Huyaam? Gyad'a mata kai Huyaam tai tana goge hawayen fuskarta. Siyama ta ce "Kuma Mai yace miki? Huyaam ta kalleta sai Kuma ta ce " Wallahi Wani kallo yamin Kuma indai Yay mana Irin wannan kallon munsan Mai yake nufi Allah ne kad'ai yasan Irin hukuncin da zai mun, Dan wallahi sai na Sakan kance zakiga ya nemeni.ni yanzu babban damuwata siyama bansan Wani Irin hukunci zai min ba, wallahi gabad'aya yanzu a tsorace nake da abinda Yaya zai min" ta fad'a hawaye nabin kuncinta.rasa abin cewa Siyama tai sai Kuma can ta sauke numfashi ta ce cikin lallashi "ki kwantar da hankalinki Huyaam in Sha Allah Babu abinda zai miki tunda ai yanzu biki ake bazai tunanin Wani abun bane ba,idan ma ya k'iraki zai tambayeki kice masa mantatuwa kikai amotar shine ya biyo ki ya kawo Miki" Huyaam tai mata wani kallo ta ce "tab' Baki San waye Yaya da brain bane wallahi tsaf zai Gane,ni tsorona ma Allah yasa Bai Ji abinda ya Aziz d'in ya fad'a min lokacin dana juya zan shigo b'angaren mu ba" siyama ta Bud'e ido Cikin mamaki ta ce "Mai yace Miki? Huyaam ta harareta ta d'auke kanta ta ce "bansani ba duk ba kune kuka jamin ba sannan yanzun kizo kina tambayar Mai yace min to bazan fad'a ba" ta fad'a tana tura Baki gaba. dariya siyama tai har tana rik'e ciki kafin ta tsagaita ta ce "ohh! yau Kuma mu ake b'oyewa abinda ya Aziz d'in ya fad'a kenan?" Huyaam ta ce "eh d'in Dan Allah tashi ki bani waje ni bacci Zanyi" siyama ta sa dariya ta ce "kefa yarinyar nan mu kike rainawa hankali Amma kin fara kamuwa da son ya Aziz kawai kece dai Baki sani ba har yanzu, Amma nasan soon zaki San hakan" Huyaam ta harareta ta ce "Allah ya sawak'e wallahi kije ki wanke bakinki dan baida tsarki yanzu" dariya siyama tai ta mik'e ta ce "Abdallah shattima fa nasan shima dai am masa wuri acan k'asan zuciya ko?" Ta fad'a tana gimtse dariyarta.Huyaam ta wawuro filo ta bugawa siyama tana cewa wallahi zatai mata rashin mutunci. Siyama ta kauce da sauri tana dariya ta ce "to na daina Dan Allah kiyi hak'uri bari na shiga wanka Dan yau a d'akinki zan kwanta" banza Huyaam tai mata ta hau saman gadon ta juya mata baya .nan siyama ta k'arasa inda towels d'in Huyaam suke ta d'auko D'aya Dake jikin hanga acikin press sannan ta shiga Wani lungu ta cire kayan jikinta ta d'aura towel d'in sannan ta fito ta nufi toilet har lokacin murmushi take tana satar kallan Huyaam.ita dai HUYAAM tai banza ta k'yaleta ta nuna Bata ma San tanayi ba saima latsa wayarta da take, ganin siyama ta shige toilet d'in yasa itama ta mik'e ta nufi press d'in ta d'auki Wani towel d'in daban sannan ta fita daga d'akin Dan zuwa tai wanka a d'akin Dake nan kusa da nata......

Washe gari har k'arfe Sha biyu na Rana Huyaam Bata yadda ta sauko downstairs ba tana tsoron kada ta fito su had'u da Afeef. tana zaune a d'akin ta kasa fita ko nan da can Dan ko break fast ma Bata sauka tayi ba sai Huda ce ta kawo mata har d'akin.da Ammie ta tambayi Huda cewa lafiya yau bata ga Huyaam ta sauko ba? Nan Huda ta ce mata lafiyarta lau kawai dai ta ce yau Bazata sauko downstairs d'in bane ba. Ammei bata takura tace wai saita sauko ba ta k'yaleta tunda taji ance lafiyarta lau....yanzu haka k'arfe D'aya Saura ne na Rana,tana zaune Saman gadon ta tana chatting bayan ta gama waya da Abdallah shattima Wanda Shima Dak'yar tai picking call d'in nasa bayan yayi mata text message na rok'o da magiya akan ta daure tai picking call d'in nasa shiyasa tai Amma da baza tai ba.tana nan zaunen lokaci lokaci take kallan Bakin k'ofar duk a tsorace take Dan Gani take ko da yaushe Afeef zai iya shigowa d'akin nata ya sameta shiyasa duk tak'i sakin jikinta,tunda har yanzu Bata Ji ya Aiko yace taje ba ko Kuma shi yazo ya sameta ba... K'iran Aziz ne ya sake shigowa wayarta a karo na Babu adadi nan ta duba wayar ganin shine yasa taja tsaki da k'arfi tai rejecting call d'in tana k'unk'uni k'asa k'asa Dan tun safe yake Nacin K'iranta Amma tak'i picking,azuciyarta ta ce bayan duk kai ka jawomin zaman d'akin yau sannan kai tunanin idan ka k'ira Zanyi picking ai baka Isa ba" tsaki ta K'ara ja Jin ya sake k'ira ta kashe wayar ma gabad'aya ta jefar nan saman gadon tana huci.babu dad'ewa Huda tai knocking k'ofar ta turo lokaci d'aya ta shigo d'akin.d'aga kai Huyaam tai tana kallan Bakin k'ofar Ganin Huda ce yasa ta kauda da kanta gefe tana ansa mata sallamarta ta ciki_ciki.Huda ta k'araso ta zauna a gefen gadon rik'e da wayarta a hannunta tana kallan Huyaam tai murmushi ta ce "sai kace wata amaryar kulle kinzo kin d'aurawa kanki zaman d'aki shi Wanda Kike Yi domin shi d'inma k'ila ya manta kawai kece dai kika bi kika sa kanki a damuwa" ta fad'a tana kallan Huyaam, Kallanta Huyaam kawai take Bata ko kiftawa Jin abinda Huda ta fad'a kafin tai mata wani kallo ta ce "eh ai dole kice haka tunda ba kece a condition d'in da nake ba,duk ba ku kuka jamin zaman d'akin ba ,ai komai nai kune kuka ja,ko kin manta waye Yaya? ke kanki kinsan baya mantuwa baya hukunci lokacin da kai Laifi sai ka manta sannan shi zai Maka nasa hukuncin saboda haka ko Mai nai Babu ruwanki" ta fad'a tana k'ok'arin juyawa huda baya hawaye na taruwa idonta.sauke numfashi Huda tai sai kuma tai k'asa da murya ta ce "to kiyi hak'uri Dan Allah nasan duk mu muka ja Miki d'in,Amma Dan Allah kiyi hak'uri ki yafe mana? Banza Huyaam tai da ita ta k'yaleta saima gyara kwanciyar ta da tai.Huda ta mik'e ta koma ta side d'in da Huyaam take passing ta zauna ta kamo hannunta ta ce cikin k'asa da murya "kinji sisto Dan Allah kiyi hak'uri" Huyaam ta kalleta sai Kuma ta Sauke Idonta k'asa ta gyad'a mata kai alamar taji" Huda tai murmushi ta ce "thank you so much sis in Sha Allah Babu abinda Yaya ma zai miki" ita dai HUYAAM Bata tanka taba Dan Wani Irin d'aci take Ji aranta a duk lokacin da ta tuno da Irin kallon da Afeef yay mata a daren jiya da Kuma tunanin hukuncin da zai mata Sai taji duniyar tai Mata zafi.Huda ta ce " yauwa ya Aziz ya k'irani ya ce tun safe yake K'iranki Amma kink'i kiyi picking call d'insa daga k'arshe ma kika kashe wayar Mai yasa sis?" ta fad'a tana jiran ansar Huyaam. Kamar Huyaam baza tai magana ba Jin wata tambayar rainin hankali da Huda tai mata kamar Batasan Mai ya faru ba, ita a tuna ninta duk irin abinda Yaja mata a daren jiya gashi har yau bata fita daga cikin Saba zatai picking call d'in sane. Huda ta ce "bakiyi magana ba? Huyaam ta mik'e Zaune tana kallan Huda ta ce a fusace "nai picking call d'in sa fa kika ce Huda? Duk abinda Yaja min a daren jiya kina Tunanin Zanyi picking call d'insa ne?" Ta fad'a tana hucin b'acin Rai.Huda tai k'asa da murya ta ce "ba haka nake nufi ba,Amma Kuma Huyaam Hakan bazai sa kik'i picking call d'in Saba" Huyaam ta ce "oh! ke a ganin ki Bai kai ba ko? Sai Kuma tai wani murmushi mai ciwo ta ce "to ni a gani na ya kai har yayi yawa ma" Huda tai k'asa da murya ganin Huyaam ta hau ta ce "naji ya kai Amma Bai kamata ki kashe wayar ki gabad'aya ba,yanzu dai kiyi hak'uri kiyi ki Bud'e wayar ki zai k'iraki Yanzu in Sha Allah! ,da ya ce na had'u ku a wayata Amma tunda ga wayarki bari na tafi Dan Allah ki kunna taki zance ya k'iraki ta layinki Yanzu" Huyaam ta ce tana girgiza kai "nifa Bazan tab'a picking call d'insa ba" Huda ta kamo hannunta ta ce cikin lallashi "Dan Allah Huyaam ki tausayawa bawan Allah nan tunda har kikaga ya k'irani ya fad'a min wallahi abun ya dameshi ne, ya Aziz Yana mutuwar sonki HUYAAM ke shaida ce, Dan Allah ko baza kiyi magana ba kiyi picking call d'in sa ko zaiji Dad'i Dan Allah Badan niba" huda ta fad'a da sigar rok'o. Huyaam ta girgiza mata kai ta ce "jiya ma Haka Kuka min keda siyama har Saida kuka ja min Yaya ya ganmu,to yau d'inma so kike ya kamani Ina wayar ya kasheni ko ya_ya? gaskiya Huda bazan iya ba kiyi hak'uri wannan Karan bazan tab'a iya bin maganar kiba" ta fad'a tana kauda kanta gefe.Huda dai kallan ta Kawai take sai Kuma can ta ce "Dan Allah fa nace Huyaam, kiyi hak'uri ni wallahi tausayi yake bani shiyasa har nazo nake rok'ar ki wallahi karkiga Irin damuwar D'aya shiga ko ke kikaji sai kin tausaya masa ga magiya da rok'on Daya dinga min akan nazo na Baki hak'uri na taimaka na had'u kuyi magana sannan ki Bud'e wayarki shiyasa Yanzun ma nazo" Huyaam ta kalli Huda zatai magana wayar Huda tai ringing Huda ta kalli wayar sai Kuma ta dawo da kallonta kan Huyaam ta ce cikin sanyin murya "ya Aziz ne Dan Allah ki karb'a" Bata jira cewar taba tai picking ta ce "Hello Ya chiroma gata bari na Bata" daga haka ta Karawa Huyaam wayar kunnenta.uffan Huyaam Bata ce a wayar ba duk da Irin magiyar da Aziz yay tai mata Amma Bata tanka Saba.ita dai Huda kallan HUYAAM kawai take tana mamakin wai yau ya AZIZ ne yake mata magiya tare da ban hak'uri Amma Huyaam ta had'e Rai tak'i yin magana. tana ji yace Mata Dan Allah tai hak'uri ta kunna wayarta zai K'irata anjima, da k'yar ta ansa masa shima sai da huda tai mata magiya da Hannu sannan.godiya ya hau jero Mata kafin ya ce mata zaije masallaci.d'auke kanta tai Jin ya kashe wayar Huda tai murmushi ta ce "thank you so much sisto me bari naje nai sallah Nima" daga haka ta Mik'e.ita dai HUYAAM batace mata komai ba har Huda ta bar d'akin nan itama ta mik'e ta shige toilet d'in Dake d'akin nata Dan d'auro alwala....


Wunin yau haka Huyaam tayi shi a d'aki har dare Koda wasa bata yadda ta Sauko downstairs ba, Ammie data Kasa jurewa ta shigo ta duba ta ganin Lafiyarta lau yasa ta fice daga d'akin..har washe gari Huyaam bata fito ba sai wajen k'arfe hud'u da Rabi na yamma shima ta dalilin a ranar su Anty khadija zasu koma Abuja shiyasa ta fito saboda zasu musu rakiya zuwa airport,kuma da tai Sa'a ma Afeef baya gidan tun bayan Azhar ya fita Kuma har lokacin Bai dawo ba sannan ya Haidar NEMA zai kaisu. A hankali ta sauko downstairs d'in kowa kallanta yake ta Tarar da duka 'yan gidan suna tsaye a falon suna sallama dasu.Anty Khadija na sallama da Ammie Wanda har an Kai musu a kwatunsu zuwa mota.Anty khadija tai murmushi tana kallan Huyaam ta dafa kafad'ar ta ta ce "daughter yau zamu koma gida in Sha Allah" Huyaam tai mata murmushi ta rumgumeta ta ce "we are going miss you mummy" Anty khadija ta d'ago ta ta ce "Nima haka daughter Amma Baga waya nan ba zamu dingayi in Sha Allah" sai Kuma ta Kalli Ammie ta ce "Anty fulani zamu tafi" Ammie ta ce "Allah ya Sauke ku lafiya a gaida Ambassador" Anty khadija ta ce "zaiji in Sha Allah!" daga Haka tabi bayan su HUYAAM da siyama da Huda Wanda har sun fita daga falon gabad'aya... Anty khadija na kallansu su Huyaam Wanda suka rungume siyama bayan sun isa airport d'in da k'yar suka saki juna ganin time na tafiya suka K'ara yiwa Anty khadija sallama ta ansa musu suka tabmna rik'e da Hannun Imaan suka shiga cikin airport d'in.nan suma suka juya suka nufi Wajen motarsu Haka nan suka Rabu
Suna kewar Junan su k'afin su shiga mota Su koma gida......


____________?&


*Bayan sati D'aya*

Da daddare Afeef na zaune a falon Mai mar taba kansa a k'asa Yana yiwa Mai martaba magana cikin ladabi har ya kai k'arshen zancen sa. Mai martaba ya Sauke numfashi bayan ya gama sauraran Afeef kafin ya ce "to Alhamdulillah! yanzu dai ka gama Musu registration din Kenan? Afeef ya ce "eh Abba" Mai martaba ya ce "yaushe zasu fara zuwa Kuma? Afeef ya ce "nan da sati biyu in Sha Allah rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "okay ai harma Za'a Kai Huyaam Egypt d'in su dawo kafin su fara zuwa ko? Afeef ya Jin Jina kai ya ce "eh in Sha Allah Abba" Mai martaba ya ce "to masha Allah! Allah yay Maka Albarka" Afeef ya ce "Ameen rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "jibi ne tafiyar ko? Afeef ya ce "eh rankai Dad'e jibi ne" Mai martaba ya Jin Jina kai ya ce "Kai kuma yaushe zaka koma Ingiland d'in?" Afeef na Shafa kansa ya ce "nan da one weeks ne in Sha Allah!" Mai martaba ya ce "da kai za'a kai Huyaam Egypt d'in ne ko ya_ya? Afeef ya K'ara sunkuyar da kansa k'asa ya ce "eh haka nake tunani rankai Dad'e" Mai martaba ya Sauke numfashi ya ce "Allah yayi jagora yasa adace ita kuma Allah ya Bata lafiya" Afeef ya ansa da Ameen.daga nan Kuma suka koma hirar company....


Da daddare Wajen k'arfe 2 na dare cikin masarautar zazzau.Razik'a ce tsaye a cikin wannan d'akin inda suke had'uwa ita da maina a duk lokacin da zasu k'ulla duk wani makircinsu da suke k'ullawa a cikin palace d'in. Ta kalli maina Wanda yake ta kai da komowa acikin d'akin duk da duhun dake Dakin Wanda Babu haske ko kad'an, Amma Hakan Bai Hana maina safa da narwar da yake Yi ba,Dan tunda yaji abinda Razik'a ta fad'a ya kasa nutsuwa waje D'aya Sak'awa da kwancewa kawai yake Saida ya maula Dan kansa sannan ya tsaya kusa da Razik'a fuskar sa daf da tata Yana kallanta ya ce "Razik'a kika ce jibi za'a koma da gimbiya Ayush Egypt d'in? Razik'a ta ce "eh Maina jiya Dana shiga dubata naji k'anwar ta Ameenah Suna waya da 'yar uwarta tana fad'a mata" Jin jina kai maina yayi ya ce cikin wata iriyar murya "indai hakane aikinmu a daren gobe zamu aiwatar dashi kenan" Razik'a ta ce "tabbas wannan haka yake" maina yayi Wani murmushi ya ce "shikenan kije

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login