Showing 90001 words to 93000 words out of 140150 words

Chapter 31 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

176

dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =???)__*


My channel link =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y


PAGE3?? 4??


___________?&


Kwance tashi Babu wuya a wurin Allah gashi yanzu har su Huyaam sunyi kwanaki biyar a Abuja, rayuwarsu suke cikin walwala da Jin Dad'i agidan Anty khadija duk abinda suka ga dama shi sukeyi, Amma ba Wanda ya Sab'a dokar addini ba ko kuma al'ada kawai duk dai Wani abinda ya Dan ganci Jin Dad'in rayuwa Wanda zai sasu nishad'i to shi sukeyi Dan babu laifi Anty khadija tana San Yara sosai musamman akace 'ya'yan 'yan uwan tane nanfa zakiga nuna soyayya kamar 'yay'an data haifa a cikinta. Yanzu haka k'arfe biyar Saura na yamman ranar saturday shiri kawai suke zasu fita unguwa ne za'a kaisu su ga gari sannan a zaga dasu suga ko Ina a garin Abuja da kewayenta.huyaam na gaban mirror tana shafa lip balm leb'enta bayan ta gama ta juyo tana kallon Huda Dake gyarawa siyama kwallin Daya D'an zazzago ta k'asan idonta.siyama ta kalli HUYAAM bayan angama mata tace. "Wow Masha Allah! kinga yadda kikai kyau kuwa? HUYAAM tai murmushi tace. "Thank you so much sis kema kinyi kyau ai" siyama ta D'an Bat'a Rai tace. "Ya za'ayi nai kyau bayan duk kun kama kunsa kaya iri D'aya ni Kuma nasa nawa daban gaskiya bazan yadda ba saidai Wani ya cire ya sauya Wani kayan in yaso ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?duk mu fita with differents dresses" ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.Huyaam tai murmushi ta ce "to ke in Banda abunki wayake Raba hanta da jini". Siyama ta ce "Allah sarkie ni wato Dan Kunga ni kad'ai ce bani da 'yar uwa shine za'a min gori ko? Huda ta rik'o hannunta tana Murmushi ta ce "da wasa take Miki fa, mu mun Isa muce haka kema kinsan mu 'yan uku ne ba 'yan biyu ba" sai Alokacin siyama ta saki murmushi taiwa Huyaam gwalo. Huyaam ta ce "zamu had'u ne yarinya" Ramma ce tai knocking k'ofar tare da sallama suka Bata Iznin shiga.turo k'ofar tai tashigo tana kallansu ta ce "Anty tace ko fito driver na jiranku a waje" ansa mata sukai da to.sannan ta juya ta fita daga d'akin bayan ta rufo musu k'ofar. Huyaam ta d'auki hand bag d'inta da wayarta a hannunta ta ce tana kallansu"ku fito mu tafi Dan Allah" Daga haka tai hanyar k'ofar fita bin bayanta sukai bayan suma sun d'auki wayoyinsu da handa bag suka fito daga d'akin gabad'aya bayan sun kullo k'ofar...a Falon downstairs Suka Tadda Anty khadija Zaune saman kujera sai imaan akusa da ita Hassan da Hussain Kuma suna can back yard d'in compound suna ball . Anty khadija na kallansu ta ce "Kun fito kenan?" Suka ansa mata ta ce "to Maza ku wuce ku tafi tun d'azu driver ke jiranku ko duk kwalliyar aka tsaya Yi ne" ta fad'a tana kallan su .sunkuyar da kai sukai k'asa suna Murmushi Amma basuyi magana ba.Anty khadija tai murmushi ta ce "to ko dai siriki za'a min a garin Abujan ne ban sani ba" ta fad'a da sigar tsokana.ai tuni suka rufe fuskokinsu da tafukan Hannayensu suna Murmushi suka hau cewa "a'a mummy" Anty khadija tai dariya ta ce "aishikenan Allah ya tsare" ansa mata sukai tareda Yi mata sallama. tana kallansu ta ce "karku kai Dare fa" sukace in Sha Allah" d'aga haka suka nufi hanyar fita daga falon gabad'aya imaan tasa rigima akan zata bisu mummy ta hanata ta rarrasheta tukunna ta hak'ura....tunda suka fito daga cikin unguwar nan gabad'aya acikin mota suna tafiya Batare da sun fad'awa driver Ina zai fara kaisu ba,hirar su kawai suke a Bayan motar.jin shiru Basu Fad'i inda zasu ba gashi driver sai tafiya yake Bai San Ina suka nufa ba yasa drivern ya ce Yana kallan gabansa "ranku ya Dad'e Ina zamu fara zuwa? Siyama ta Kallesu ta ce "Ina ya kamata mu fara zuwa? Huyaam ta ce "ai kece 'yar gari ke kikasan wurare" Huda ta ce "tun da an bamu zab'i nidai muje ShopRite ko Kuma Wani park haka " Huyaam ta ce "Nidai indai akwai wurin zuwa mutum yayi wasa ko ya hau kan Doki ko Kuma mota to akai mu can" siyama tai murmushi ta ce"ai duk irin wuraran da kuke so a Garin Abuja akwai just choose the one and go" Huda ta kalli HUYAAM ta ce "to wanne ya kamata muje" Huyaam tai fari da ido ta ce "nidai inda na fad'a shi nake son zuwa" Huda ta ce "to muje" siyama ta kalli driver ta fad'a masa inda zasun .yasan wurin Hakan yasa Babu musu ya ansa musu suka kama Hanyar wajen...wurin shak'atawane babba Wanda aka gina shi na musamman for Irin 'yay'an anjeboters d'in nan like them.wuri ne Mai d'auke da differents places of plays and enjoyment. Tun da driver Yay parking Suka sauko daga cikin motar ya juya zai kai motar inda kowa yake parking idan yazo Huyaam ke kallan wajen Wani irin farin ciki ne Kawai ya kamata bisa ga tozalin da tai da abuwan enjoyments d'in da take so awurin, take taji ta matsu su k'arasa cikin wurin...cikin nutsuwa suke tafiya suna cin karo da 'yay'an Manyan garin Abuja Suma sunzo wurin just for enjoying they self.Saida suka fara zuwa sukai payment na shiga wurin da duk irin abinda zasu buk'ata na kayan ciye_ciye duk suka biya sannan suka nufi cikin wurin. tun daga nesa suka hango differents people like Maza da mata Yara da manya duk kansu 'ya'yan masu kud'i ne wasu 'ya'yan ministers wasu Kuma 'ya'yan senators wasu Kuma 'ya'yan 'yan majalisu ke dukkan wad'an da suke cikin wurin nan dai 'ya'yan manyan mutane ne.ga 'yan matan nan wasu tare suke da samarinsu anfito outun wasu Kuma su kad'ai suka zo wurin just for enjoying they self. kowa da kika gani harkar gabansa kawai sukeyi awajen.wani D'an k'aramin waje su Huyaam suka nufa Wanda Babu mutane sosai awurin.wurine na musamman Mai d'auke da green grass carpet sai Wani kushin marasa k'afafu guda hud'u.daga gefe Kuma Wani D'an k'aramin swimpool ne Mai d'auke da blue din ruwa aciki sai wasu dokuna na wasa na roba da motocin roba sai machines da su kifin Roba da sauransu ke kayan dai wasa kala kala Babu Irin wanda Babu acikin pool d'in nan. zama sukai kan kushin d'in Dake wurin bayan sun k'arasa suka ajiye hand bag d'insu nan saman table d'in gaban kushin d'in.numfashi Huyaam ta sauke tana k'arewa wurin kallo ta ce "gaskiya wurin nan is so much sweetness and enjoyment, I like it so much I swear" ta fad'a tana Murmushi siyama ta ce "ko Ina ma ni kan I like it , Dan Wani time d'in idan zaman gida ya isheni nakan tambayar mommy nace Ina San zuwa sai tasa driver ya kawo mu Nida su Hussain" Huda ta ce "uhmm muma ko a kano akwai?" siyama tai murmushi ta ce "akwai mana kawai dai Dan bakya yawone shiyasa" Huyaam ta ce "aikuwa idan mun koma zan tambayar mana Abba muma ana kaimu time to Time" Huda dai tai shiru batai magana Dan tasan Tatsuniya kawai Huyaam takeyi Amma Dak'yar idan Abba zai yarda.suna wannan zan cen D'aya daga cikin waitress d'in ta kawo musu kayan mak'ulashan da sukai selecting ta ajiye musu nan kan table d'in gabansu sannan ta juya ta bar wajen.Huyaam na kallansu ta Mik'awa siyama wayarta ta ce "ni dai a fara min pictures first before anything, hope kin iya dai?" siyama ta karb'i wayar tana harararta sai Kuma ta ce "wallahi saina fasa" HUYAAM tai murmushi ta had'e hannayenta waje D'aya alamar rok'o ta ce "am sorry sis da wasa nake miki ni na isa nace miki Haka"Jin jina kai siyama tai sannan ta fara d'aukarta pictures kala kala.bayan Wani lokaci HUYAAM ta jawo Huda kusa da ita tace "ai musu tare" nan siyama ta cigaba da Yi musu pictures d'in kamar Babu gobe daga k'arshe Huyaam ta karb'i wayar a hannun siyama zatai wa Huda ita kad'ai Bayan ta gama yiwa Huda tai musu tare da siyama Suna cikin d'auka sai ga wasu 'yan mata nan Irin anjeboters d'in nan sunzo wucewa har zasu wuce sai Kuma suka tsaya suna kallon yadda sake d'aukar hoton sunyi kyau ba kad'an ba .Hakan yasa d'ayar ta jawo hannun wacce suke tafiya taren ta ce"zo muje gunsu" daga haka suka K'araso wajen su HUYAAM suna Murmushi suka ce "wow Masha Allah! Yo look gorgeous gaskiya Kuna da kyau sosai" Huda tai murmushi ta ce "thank you" d'ayar da yake tafi surutu tana kallan Huyaam Dake d'aukar su siyama pic ta ce "ki shiga cikinsu ki kawo nai Muku gabad'aya"Huyaam batai musu ba Dan dama haka take so ai musu pictures d'in gabad'aya ta ce "okay" sannan ta mik'a mata wayar.karb'a tai HUYAAM Kuma ta koma cikin su Huda suka Saka siyama a tsakiya akai ta d'aukar su pictures d'in...wow! Wow! Kawai 'yan matan ke Cewa saboda yadda sukai kyau a pictures d'in har suka gama d'auka" godiya su Huyaam sukai Musu bayan sun karb'i wayar daga hannunta haka suka bar wajen bayan sun karb'i contact d'in Huyaam.Dan takurawa sukai akan Huyaam ta Basu contact d'inta Babu yadda ta iya haka nan ta Basu... Zama sukai kan kushin d'in suna sauke numfashi kamar Wanda sukai gudun tsere Huyaam na kallonsu ta ce "nifa I'm eager to go that pool wallahi"Huda ta ce "ke Kuwa ki huta mana ko gajiya Baki ba? Ta fad'a tana Sauke numfashi.Siyama tai murmushi tana kallan Huda ta ce "wannan Numfashin da kike saukewa fa?" Huda ta lumshe idonta ta Bud'e lokaci D'aya tana D'an murmushi ta ce "ke wannan d'aukar pictures d'in da nai har naji na gaji" siyama ta ce "tab' d'ijan to wannan idan muka hau kan kan motocin nan baza ki moru ba kenan? Huyaam ta ce "tunda mun huta Dan Allah ku tashi Muje itafa dama Huda raguwa ce"Huda ta ce "eh naji ki Fad'i koma meye amma Dan Allah mu K'ara mintuna biyar". K'yaleta sukai ganin yadda har ta jigata tunma Basu je wajen wasan ba. bayan Wani lokaci suka mik'e suka k'arasa wajen swimming pool d'in ganin yadda HUYAAM ta nace aje.dokin Dake Bak'in ruwan Huyaam ta kama zata hau Huda ta rik'ota ta ce "ke bakida hankali zaki hau kin iya ne?" Huyaam ta kalleta ta ce "yanzu ke meye abun wahala a hawa wannan dokin bafa na Gaske Bane ba Kuma ai ana iya control d'insa" Huda ta girgiza kai ta ce "Dan Allah karki hau Huyaam gara ki hau motar" Huyaam tai murmushi ganin yadda Huda ta tsorata yasa ta ce "to naji cikani" sakinta Huda tai Huyaam ta kamo motar ta shiga cikinta siyama ma ta shiga wata suna kallon Huda sukace "ke baza ki shiga ba?" jimm Huda tai kamar Mai tunani sai Kuma ta ce "to wazai mana pictures da videos d'in idan ni na hau? siyama ta ce "bari Huyaam tai mana K'iran yarinyar nan ta d'azu sai tazo tai mana" Huyaam ta ce "a'a ni banda contact d'inta itace ta karb'i tawa" siyama ta ce "laa! Aiga su can ma basuyi nisa ba bari na K'irata" daga haka ta shiga K'iranta ,kamar jira take ta taho da sauri bayan ta k'araso Huyaam ta sake Bata wayarta ta ce ai musu pictures da videos babu musu ta karb'a,sai alokacin Huda ta shiga motar Dake bayan siyama daga haka suka kunna Wani Abun take motar tai gaba tana zagaye ruwan dasu.gefe D'aya kuma ilham tana tai musu pictures da videos haka sukai ta zaga ruwan nan sannan suka sauka suka hau saman Wani kifi na roba sai wata kada (crocodie) sai Doki shine daga k'arshe Huyaam kamar ta iya Doki haka ta dinga iyo dashi acikin ruwan nan Huda da siyama suke ta mamakinta ayina ta iya haka.itadai ilham sai Kod'a su take akan sunyi kyau ba kad'an ba Saida suka gaji Dan kansu sannan suka sauko.suka fito daga cikin ruwan gabad'aya suka koma wurin zamansu suka zauna suna sauke numfashi.daga can gefensu Kuma wajen wata rumfa Wani matashin saurayine Wanda hutu Had'i da Jin Dad'i suka bayyana ajikinsa, gashi fari K'al kamar Wani bature saboda kyau, tun d'azu Daya shigo wurin Bada dad'ewa ba bayan su HUYAAM sun zauna yake kallansu D'aya bayan D'aya Yana k'are Musu kallo.idonsa Daya sauka akan Huyaam ne wacce ta ke gyara mayafin abayar jikinta yasa nutsuwarsa ta bar jikinsa gabad'aya kallanta Kawai yake baya ko kiftawa itako Bata ma San Yana Yi ba Dan gabad'aya hankalinta na kan abinda takeyi...Saida suka huta sannan suka mik'e Dan tafiya saboda yadda lokaci Yaja sosai Kuma sunaso Ad'an zaga dasu garin Abuja before su koma gida.fitowa sukai daga wajen gabad'aya suka nufi wajen motar ta su. driver na hango su ya tafi da sauri zai fito da motar....tunda suka fito yake binsu abaya Batare da sun sai ba.binsu kawai yake Yana Tunanin ta Ina ma zai fara Yi Musu magana, dakewa yayi ganin sun tsaya nesa dashi yasa ya k'arasa har Inda suke tsayen kafin ya D'an dawo ta gefensu yayi gyaran murya ya ce cikin nutsuwarsa da zazzak'ar muryarsa "Assalamualaikum warahmatullah" haka sallamar tasa ta Doki dodon kunnuwansu. a tare suka kalleshi cikin mamaki kafin su D'an matsa baya da sauri ganin yadda ya tsaya daf dasu suna kallansa cikin Rashin fahimta.Siyama ce kawai ta iya ansa masa sallamar tasa kafin ta ce "lafiya Malam?" yay murmushinsa Mai kyau kafin ya ce "lafiya lau, nazo Neman wata Alfarma ne Kawai" Huda ta ce cikin Rashin fahimta"Alfarma Kuma ? Yana d'an murmushi yayi nodding kansa ya ce "yeah Alfarma" siyama ta Sauke numfashi ta ce "to ka Fad'a muna Saurarenke Dan tafiya zamuyi" ya ce "in Sha Allah zaku iya ma" amma kafin nan Dan Allah idan ba badamuwa inason magana da 'daya daga cikinku" gabad'aya suka Kalli juna kafin Huda ta Dafe k'irji kamar Wanda ya Fad'i Wani babban zunubin ta girgiza kai ta ce "a'a kayi hak'uri" yay murmushi ya ce "magana fa nace ba Wani abun ba" Siyama ta ce "to dawa zakayi" ya nuna Huyaam ya ce "da ita idan har zata bani dama?" Huyaam ta Wani had'e Rai tana kallansa ta ce "wace Irin magana ce da dole sai iya dani kad'ai zakayi?" ya ce "ai kamawa tai" girgiza masa kai Huyaam tai tana kallansa ta ce "ka Fad'i abinda zaka fad'a a gaban 'yan uwana" yay murmushi ya ce "okay tunda kince haka please contact D'inki nake so ki bani" zaro ido waje HUYAAM tai sai kuma ta girgiza kai ta ce cikin tsoron Daya shigeta lokaci D'aya "bamu da waya" yace.
"wannan wayar da nake Gani a hannunki fa? Ta had'e Rai Ta ce "kaga malam to baza mu bayar ba shikenan" daga haka ta kamo hannun Huda da siyama ta ce " ku taho mu tafi suka bar wajen suka k'arasa wajen motar da driver har ya fito da ita su kawai yake jira shiga sukai ciki da sauri Jikin Huyaam har lakacin rawa yake Bai daina fad'uwa ba,ga yadda kirjinta ke dukan uku uku dan babu abinda ya fad'o mata arai Daya ce ta bashi contact d'in ta Irin worning d'in da AFEEF yay musu Dan har yau abun ya Kasa goguwa a k'wak'walwar ta.Niko nace hmm" wai ahakanma Dan Batasan da Mai yazo mata bane ba...tunda suka shiga motar sukai shiru Babu Wanda yayi magana acikinsu kowa da tunanin da yake.driver ne ya katse musu shirun ta hanyar cewa "Ina zamu yanzu? Duk suka juya suna kallan Huyaam sai Kuma suka ce "mu koma gida kawai"Huyaam ta juya tana kallan su ta ce "Akan Wani dalili zamu koma gida? Huda ta ce "to munga kinyi Shiru ne gabad'aya" HUYAAM ta kalli driver ta ce "Malam ka zagaya Damu gari kafin dare yayi" Babu musu driver ya ansa musu daga haka suka sauya hanya..


_____________?&


Shiko tunda su Huyaam suka bar wajen ya bisu da kallo baya ko kiftawa har Saida yaga sun shiga motar Sanan ya farga Ganin tafiya zasuyi. juyawa yayi zuwa inda yayi parking motar sa, ya shiga cikin sauri ya ta-da motar yayi reverse yabi bayansu..tafiya kawai yaga sunayi kamar basu san inda zasu Suba, Amma duk da haka baiji ya sareba ko kuma gajiya haka nan yadinga bin bayansu ,daga yaga sunbi ta wannan titin saidai yaga sun b'ulle ta Wani titin abindai ya d'aure masa kai ganin sunyi tafiya ta kusan mintuna 40 gashi har ankusa sallahn magrib Amma Basu je inda zasun ba,Shima Kuma Bai canza ra'ayi akan binsu da yake Yi ba Haka nan ya daure yake bin bayansu...suko su Huyaam suna cikin motar sai zance suke suna tambayar duk inda basu sani ba Wani siyama ta Basu ansa wani Kuma driver ya Basu Dan wannan nishad'in da suka shiga har sun manta da sun Had'u da Wani a wannan wurin. ganin time d'in magrib is approaching yasa suka cewa driver ya juya ya kaisu gida kawai .Babu musu driver ya ansa musu.har lokacin Basu kula da motar Dake bin bayansu ba... tunda yaga sun shigo wannan layin ya daina binsu yayi parking daga gefe yadda baza su tab'a ganin Saba bare har su fahimci Yana binsu. A kofar gidan dayaga motar ta karya Kwana ta tsaya anbud'e mata gate ta Shiga yasa ya Sauke numfashi ganin komai zaizo masa da sauk'i tunda dai har ya Gane inda suke.yay zooming up sannan ya ja motar yay gaba....


Agajiye suka k'arasa shiga cikin falon Imaan ta taho ta rumgume su tanai musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login