Showing 78001 words to 81000 words out of 140150 words

Chapter 27 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

208

murmushi tace. "Ranki Dad'e tace maganin karya sihine". Anty Amina ta tab'e Baki tace. "Nifa banasan Irin wannan magun gunan na gargajiya da inna take cewa ayiwa Yaya gimbiya amfani dashi Dan wallahi ba so nake ba,Dan Wani ma bakasan ayina aka samo Shiba,Mai kyau ne marar kyau ne sai Allah Amma inna ta dage tace wai dole sai anyi amfani dashi". Ta fad'a cikin damuwa.baba uwani murmushi kawai tai kafin tace. "To Ranki Dad'e kar ayi amfanin dashi kenan?..." Anty Amina tai saurin cewa a'a ai dole idan Ba'ayi bama idan tazo kinsan saita tace mun Raina mata k'ok'arinta da takeyi". Baba uwani tai murmushi tace. "gaskiya kan to bari na shiga na Had'a ruwan wankan". Anty Amina ta ansa mata da to...Babu Dede'wa baba uwani ta had'a ruwan wankan ta fito daga cikin toilet d'in tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e an had'a". Anty Amina tace.
"to shikenan k'araso mu kamatan". Ta fad'a tana mik'ewa baba uwani ta k'araso suka kama gimbiya Aysha da dabara da komai kamar yadda suka Saba suka shigarta toilet d'in...Bayan Wani lokaci suka fito da gimbiya Aysha suka zaunar ta nan Saman wata kujerarta Dake nan d'akin Wacce idan ta gaji da kwanciyar suke dawo da ita Kai ta huta.baba uwani tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e Adama mata kunun yanzu ko sai anjima". Anty Amina tace. "A'a ki bari zuwa anjima da Rana ko Kuma da yamma sai adama matan tunda Kinga yanzu ta gama cin abincin". Baba uwani tace. "To to Shikenan babu damuwa bari naje na k'arasa aikin da nakeyi"..anty Amina ta kalleta tace. "Allah ya saka Miki da Alkhairi baba muna godiya sosai da d'awai niyar da kike tayani Yi da Yayata Allah ya bar zumunci". Ta fad'a cikin Jin dad'in yadda baba uwani Bata Wani damuwa ko nunawa afuska alamar gajiyawar d'awainiyar da take da gimbiya Aysha.baba uwani da har ta juya ta juyo tana kallon anty Amina tai saurin cewa. "Haba haba ranki Dad'e yanzu duk abinda naiwa Fulani Aysha kina ganin na Fad'i ne? Ai ko kad'an ban biyata kan abubuwan datai min ba,idan ban tsaya kan duk Wani Abu da ya sameta na farin ciki ko na Bak'in ciki ba Mai Zanyi ni uwani?ashema na zama butulu indai ban tsaya tsayin daka na kula da ita halin da take ciki ba , saboda haka Dan Allah ranki Dad'e karki K'ara min godiya akan wannan D'an abinda nake Yi , wallahi Ranki Dad'e Ina Jin gimbiya Aysha ne araina kamar 'yar data fito daga cikina.damuwar ta damuwa tace ,Haka samun lafiyar ta Nima shine farin cikina a kullum muna addu'a da Allah ya tashi kafad'unta Allah ya Bata lafiya". Tafad'a cikin rauni.anty Amina ta sauke numfashi tace. "Shikenan baba mungode Allah ya bar zumunci". Baba uwani tace. "Ameen thumma Ameen bari naje" daga haka ta nufi k'ofar fita daga d'akin..Anty Amina Kuma ta d'auki lotion ta fara Shafawa gimbiya Aysha kafin ta gama ta shiryata cikin wata doguwar rigar tsaddan material d'inkin doguwar riga wanda dai bazai takura taba. bayan ta gama tai parking d'in doguwar kitson kalbar datai mata two days ago da rinbbom tana Kallon gimbiya Aysha tai k'asa da murya tace. "Na barki kan kujerar ko Kuma na kaiki saman gadon?..." Tafad'a tana kallanta Dan jiran ansarta. Gyad'a mata kai gimbiya Aysha tai kamar da wasa.take Anty Amina ta saki murmushi tace cikin Wani irin shaukin farin ciki Daya shigeta lokaci D'aya ganin yadda yau dai gimbiya Aysha ta gyad'a kai da kanta da da ko d'aga kan nata batayi Amma yau itace tai nudding kanta ai da Wani Irin farin tace. "Yaya gimbiya yanzu kece kika gyad'a mini Kai haka?.."ta fad'a har sannan murmushi ne a saman fuskarta.Lumshe idonta gimbiya Aysha tai,anty Amina ta d'aga hannunta sama tace.
cikin Wani irin farin ciki. "Alhamdulillah ya Allah! Allah mun gode Maka da wannan ni'ima da kafara mana ,ya Allah ka bawa wannan baiwa taka lafiya Mai d'orewa ta har abada gabad'aya da ita duk Wasu masu fama da jinya" sai Kuma ta Sauke hannunta k'asa nan ta fara gyara mata zamanta akan kujerar. Bud'e k'ofar d'akin akayi Hajiya inna ce ta shigo.Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar Jin anbud'e taga Hajiya inna ce take ta saki murmushi tana kallanta .Hajiya inna ta ta rufo k'ofar tana kallan anty Amina tace. Haya niyar me nake ji Ina falo lafiya dai ko?.." Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi inna yanzu Ina tambayar yay gimbiya akan na barta nan Saman kujera ko Kuma na kaita kan gado kawai naga ta gyad'a mini kanta abinda ban tab'a Gani ba ko tunani tunda ta fara jinyar nan.." Ta fad'a tana no kasa b'oye farin cikinta. Mamaki ya bayyana sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?man fuskar Hajiya inna itama Batasan lokacin data k'arasa shigowa cikin d'akin ba tana kallon Anty Amina tace. "Ke da Gaske Dan Allah Amina ko dai wasa kikeyi?.Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi Hajiya". Hajiya Inna itama ta d'aga hannayenta sama tace cikin farin ciki. " Allah mun gode Maka,ya Allah yadda ka nuna mana wannan Rana ya Allah ka nuna mana ranar da Aysha zata samu Lafiya gabad'aya". Anty Amina na murmushi ta ansa mata da "Ameen ya Allah inna". Hajiya Inna ta shafa addu'ar ta Kalli gimbiya Aysha Dake Kallansu itama tace. "Aysha Allah ya cigaba da Baki lafiya Kinji?.." this time around lumshe idonta tai sai Kuma ta gyad'a musu kan ahankali". Inna tace. " Wallahi kuwa Nima na gani Allah mun gode maka". Sai Kuma ta kalli Anty Amina tace. "Ina fatan Babu Wanda kika fad'awa wannan maganar dai ko? Anty Amina da har lokacin murmushi ne with surprised a fuskarta ta gyad'a ma inna kai tace. "Babu Wanda na fad'awa inna". Hajiya inna tai k'asa da murya tace. ",to banaso kowa yaji wannan maganar dagani saike Amina Dan ko Mai martaba bazan fad'awa ba gudun sub'utar Baki wannan abun yazama sirrin da har sai munga komai Yana tafiya da cigaba sosai Dan bamu sani ba ko akwai Wad'anda suke da sa hannu a cikin jinyar Aysha suke mana zagon k'asa ba.idan suka ji Kuma Kinga ai sai su Bat'a Mana aiki" anty Amina na murmushi tace. "In Sha Allah inna babu Wanda zan fad'awa".Dan da harta yanke hukuncin zata k'ira can gidansu ta fad'a harma ta fad'awa gimbiya Bilkisu Amma yanzu ta fasa tunda Hajiya inna tace Kar a fad'awa kowa Dan ita Kanta batai wannan tunanin ba sai a yanzu da Hajiya inna tai maganar.maganar da Hajiya inna take yasa ta maida hankalinta Kanta. hajiya Inna tace. "D'azu uwani ta kawo maganin da nace idan zakuyi mata wanka kudinga sawa acikin ruwan kuna amfani dashi?. Anty Amina tace. "Eh ta kawo dashima muka mata wankan". Hajiya inna tace. "To shikenan Dan Allah ki cigaba da mata Wankan dashi harya k'are, sanna ki cigaba da Bata ruwan mananin Dan antabbatar min Mai kyau ne". Anty Amina tace. "In Sha Allah inna Allah ya Saka da Alkhairi"..inna tace. "Zamu koma Egypt d'in ma dai dole saboda lokacin komawar tamu ya kusa fa".anty Amina tace . "Eh hakane Allah ya kaimu". Hajiya inna tace. "Ameen" daga Haka tace. "bari zan dawo anjima ta Kalli gimbiya Aysha tace. "Allah ya K'ara lafiya Fulani".daga haka ta bar d'akin bayan anty Amina tai mata fatan sauka lafiya.....


___________?&


Da yamma wajen k'arfe 5pm shakundum ce tai sallama anan k'ofar main falorn b'angaren gimbiya Aysha tareda rakiyar hadimanta harda amintacciyar hadimar ta wato safara .basu shigo falon ba suka tsaya daga nan Bakin k'ofar bisa ga umar nin uwar d'akin nasu.iya safara ce kawai ta tabiyo bayan shakundum danyin sallama a uwar d'akin nata ta k'arasa falon da sauri ta tsaya nan tsakiyar k'aton falon ta shiga yin sallama. shakundum ta Shiga falon cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali take da tashin k'amshi babu kuwa a falon sai K'arar AC data fan Dake Kad'awa a hankali.baba uwani ce ta fito Daga kitchen d'in downstairs jin yadda.hadimar shakundum ke k'wada sallama da cewa ga sarauniyar masarutar zazzzu ta k'araso.k'arasowa cikin falon baba uwani tai ta zube har k'asa nan ta hau gaishe da gimbiya Hajara cikin salon gaisuwa Irin ta gidan sarauta.da ka kawai Shakundum ta iya ansa mata tana Wani hararar ta kafin baba uwani tace. "bari aje ayi miki iso ranki Dad'e". Daga haka ta Mik'e ta haura sama zuwa b'angaren gimbiya Aysha.bayan tafiyar baba uwani Shakudum ta shiga k'arewa falon kallo tana nan tsaye sultan ya fito daga cikin d'akinsa yasha Wani rantsatstsan yadi na Maza Mai bala'in tsada fari K'al sai baza k'amshi yakeyi ga yayi Wani fresh dashi kallo D'aya yay mata ya d'auke kansa kamar zai juya ya koma Cikin d'akin nasa sai Kuma kawai ya fasa ya fara takowa zuwa cikin falon cikin nutsuwa a hankali dama kitchen zashi Haka ya k'araso ya wuce ta gaban shakundum da ko gaisheta baiyi ba Haka nan yashige kitchen d'in,ko minti D'aya baiyi da shiga ba ya fito dama cup ya shiga ya d'auka hayan ya d'auka ko ya fito nan ma ya K'ara wucewa ta gabanta ya koma d'akin nasa ya kulllo k'ofar da k'arfi.har Saida falon ya ansa . Mamaki ne kawai ya kashe shakundum anan inda take tsaye Tama rasa wani yanayi take ciki,mamakin yadda taga sultan lafiya lau kamar Babu abinda yake damunsa ko Kuma mamakin yadda ko gaisheta baiyi ba haka yazo ya wuce ta gabanta ya sake dawo wa ya wuce ta d'in? ita data d'auka yauma zata shigo ta ganshi Yana kulle a d'aki Yana hauka tuburan kamar yadda ya saba Amma shine yau ta shigo ta sameshi lafiya lau lallai ashe ko zama Bai kama taba me yake shirin faruwa ne? Lallai dole sultan ya koma yadda yake ada dole sultan ya koma haukansa da yakeyi ada .tsabar shock d'in da take ciki Batama san har baba uwani ta dawo tana mata magana ba".dai dai kanta kawai tai tana sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ta Kalli baba uwani tace. "Yauwa na..nagode" ta fad'a Cikin inda inda abinka da Marar gaskiya" daga haka ta nufi stairs d'in da zai kai ta b'angaren gimbiya Aysha tana kalle kalle.da kallo kawai baba uwani ta bita ganin yadda shakundum take a figice bayan ta tafi ta barta lafiya lau. sauke numfashi tai ta wuce kitchen d'in Dan cigaba da aikin da takeyi.tunani da mamakin Maiya samu gimbiya Hajara fal ranta....


Anty Amina ce tsaye tana kallon shakundum Dake tsaye bakin k'ofar bayan ta Bud'e mata k'ofar.kafin ta Bata hanya akan ta wuce.shiga ciki shakundum tai tana k'arewa d'akin kallo kafin ta tsaida idanuwanta kan gimbiya Aysha sannan ta k'arasa cikin d'akin ta zauna nan saman kujera Dake d'akin tana murmushin da take Yi a kullum idan tazo duba gimbiya Aysha.Kallan Anty Amina tai Dake gaida ta .ansa mata tai tana tambayar ta Mai Jiki Anty Amina tace. "Da sauk'i" Sha kundum data Ari fuskar tausayi lokaci D'aya tace. "Allah ya K'ara mata lafiya yasa kaffarane". Anty Amina ta ansa da Ameen .Anam ce Dake Zaune kusa da gimbiya Aysha nan Saman Gadon ta gaida Shakundum.gimbiya Hajara ta ansa mata da kulawa tana tambayar ta school..nan Anam ta ansa mata tana d'auke kanta daga kallanta.bud'e k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama baba uwani ce ta kawo wa shakundum ruwa da drink's sai fruits a k'aton tray ta duk'a har k'asa ta ajiye mata anan gabanta cikin girmamawa sannan ta mik'e ta Bar d'akin.shakundum ta jima a d'akin kamar Wacce tazo dubiyar da Gaske.nan Kuma ba komai ne ya kawota taba iyaka kawai yadda zata aiwatar da aikin cikin sauk'i ne kawai take tunani bayan Wani lokaci ta mik'e taiwa gimbiya Aysha Allah ya sawak'e sannan taiwa anty Amina sallama ta bar d'akin gabad'aya..a falon downstairs ta Had'u da Hajiya inna ta fito daga cikin d'akinta shakundum ta duk'a har k'asa ta gaida ta .ita dai Hajiya inna kallanta Kawai takeyi kafin ta ansa mata tana kallanta da mamakin Maiya kawo ta.mik'ewa gimbiya Hajara tai taiwa Hajiya inna sallama sannan ta bar falon gabad'aya cikin sauri.Hajiya inna ta bita da kallo harta bar falon kafin ta sauke numfashi ta haura sama Dan zuwa d'akin gimbiya Aysha ta tambayi anty Amina Mai ya kawo Hajara wannan b'angaren Kuma duk da tasan bazai wuce dubiyar data Saba zuwa bane ya kawo taba.....



K'arfe 8 da mintuna na dare Ammie ce ta sauko downstairs tana waya. su ya Zarah ma Dake zaune a falon downstairs d'in suka juya suna Kallan Ammein data shigo falon tana waya harta zauna nan Saman kujera tana cewa. "Khadija ki bari dai zan fad'awa Mai martaba idan ya amince in Sha Allah zasuzo ko one week ne sai suyi miki".ta fad'a tana murmushi.Daga can b'angaren Anty khadija tace. "Indai Mai martaba ne Koda kaina nai Masa magana bazai hana su Huyaam zuwa wajen hutu ba Anty! ,kawai dai k'ila kece bakyason Rabuwa da yaranki". Ammie tai murmushi tace. "To ki k'irashi mana ni wallahi da kin hutashsheni ma". Anty khadija tace. "A'a ki Dai tambayar min kawai Anty" Ammie tace. "To shikenan in Sha Allah zuwa gobe zakiji feedback". Anty khadija tace. "To shikenan nagode sosai Anty ki Gaida min da yarana". Ammie tace. "Zasuji in Sha Allah Nima ki Gaida min da nawa yaran" anty khadija ta ansa mata nan dai sukai sallama Ammie ta kashe wayar tana kallon su Huda Dake kallanta. Huyaam tace. Ammie dawa kike waya?." Ammie na murmushi tace. "Da mamanku Khadija Mana wai ta dage sai an kawo ku kunyi hutu ni Kuma ba bawai banason kuje bane islamiya ce banason kuyi missing".Huda tace. "Ammie gobe fa asabar zamu fara exam kuma one week kawai zamu kai muna exam d'in Kuma fa hutun 3 weeks za'a bamu Dan Allah Ammie idan muka gama ki barmu muje?."ta fad'a tana kallan Ammie.Huyaam kan da Murna ce ta kamata Jin zasuje Abuja tana kallan Ammie tace. "Dan Allah Ammie ki barmu muje idan mun gama". Ammie ta Sauke numfashi tace "to bari dai Mai martaba ya shigo idan na tambayeshi idan ya barku to sai kuje d'in" nan suka ce in Sha Allah ma zai barsu ya Zarah dai kallansu kawai take Amma Batace komai ba haka ma muneefa. suna zaune a falon har Wajen k'arfe Tara sukaji an Bud'e k'ofar falon tareda shigowa lokaci D'aya bakinsa d'auke da sallama. gabad'aya suka d'aga kai suna kallan Mai shigowar Afeef ne yashigo sai dogarin Daya rakoshi da kayansa.mamaki ne ya kamasu ganin shi a wannan lokacin.Amma Banda Ammie Dan dama ita ya fad'a mata cewa in Sha Allah ayau zai dawo dogarin gidan ne ya k'araso ciki ya ajiye akwatun kayan nasa Anan tsakiyar falon ya duk'a Yana gaida Ammien cikin girmamawa Ammie ta ansa masa kafin ya Mik'e ya juya ya bar falon gabad'aya.sannu da zuwa suka shiga Yi masa Yana ansa musu Batare da ya Kallesu ba.harya k'araso gaban Ammie ya duk'a Ammie ta kai hannu ta shafa kansa tana murmushi tace. "Ka dawo Lafiya?..." Ya d'ago Yana kallanta Yace cikin deep voice d'insa. "Lafiya lau Alhamdulillah Ammie". Ammie tai murmushi tace. "Masha Allah! sannu da zuwa". Mik'ewa yayi Yana kallon Ammie yace. "bari na je ciki" Ammie tace. "Ya kamata kan kaje kai wanka ma huta". Barin falon yayi ya nufi stairs muneeb kuma ya bishi da akwatun kayansa zuwa b'angarensa su ya Zarah suka bishi da kallo.....




# # # #


*mutanan MRS SARAKIES =??? Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =?G?*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank


Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376



Niger 07066508376



Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =???=??? mutanan arziki.





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =???)__*


PAGE 3?? 1??



____________?&


*Bayan kwana biyar*



Da yamman Ranar Alhamis wajen k'arfe biyar da Rabi su Huyaam sun dawo daga b'angaren su safna ita da huda. tun daga nesa suka hango wata rantsatstsiyar mota ta shigo cikin palace bayan an wangale mata gate d'in.motar da danno kai ta shigo cikin harabar palace d'in.tun daga nesa su Huda ke kallan motar Dan Basu San waye aciki ba. Har motar isa tai parking a parking lot suna tafiya suna kallon motar. Aziz chiroma ne ya fito daga cikin motar sanye yake cikin k'ananun kayan da sukai masa bala'in kyau riga da Wando rigar blue black sai Wandon Daya kasance blue jeans ba k'aramin kyau kayan sukai masa ba tafiya yake cikin nutsuwa kamar ance ya d'aga kansa sukai ido hud'u da Huyaam tareda da Huda wacce tai saurin d'auke kanta Dan har ya kusan cimma masu basu farga ba,ya fara takowa zuwa harabar gidan Cikin saurin da shi kansa Bai San Yana Yi ba saboda yadda zuciyar sa ta harba da ganin Wacce idan ya kalleta a Koda yaushe ko Kuma ya tuna ta Hakan ke faruwa dashi.ganin direct gunsu yake nufowa yasa Huyaam ta damk'e hannun Huda da k'arfi tana K'ara saurin tafiyar ta itama .Huda na Jin yadda HUYAAM ke janta yasa ta kalleta da mamakin Irin wannan saurin da takeyi tace. "Ke saurin me kike haka ne? ki tsaya mugaisa da ya chiroma shine fa yazo kinganshi can". Ta fad'a tana juyawa tana K'ara kallan Aziz chiroma Wanda har ya kusan cimmasu . batareda da Huyaam ta kalleta ba tace suna cigaba da tafiya. "Kinga fa dare nayi kuma kinsan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login