Showing 99001 words to 102000 words out of 140150 words

Chapter 34 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

218

Allah" ya ce "to naji, Amma Dan Allah zan rok'i wata Alfarma agunki, Dan Allah idan na k'iraki ki d'inga d'agawa Koda Baza kiyi magana" cikin k'osawa Huyaam ta ce "eh naji Dan Allah ka rabu Dani" tana Jin buguwar Zuciyasa . Cikin Mamakin abunda ta fad'a ya ce "da gaske kike my sweet" Bata ansa masa ba cikin sauri ta ce "please leave a lone" daga haka ta kashe wayar tana sauke numfashi kafin ta jefar nan saman gadon ta kifa kanta cikin filo tana sheshshek'ar kuka Saida tai Mai isarta sannan ta hak'ura ta koma sauke numfashi a jejere anan bacci ya d'auketa.....the Same da magrib Huyaam tana kwance saman gado har bacci ya fara d'aukar ta saboda Kukan da tai tayi d'azu da Rana yasa ciwon kai ya saukar mata Mai zafi da k'yar dai ta samu ya sauka bayan tasha magani. wayar ta Dake gefen ta ce tai ringing alamar shigowar k'ira,jawo wayar tai tana duba Mai K'iran take ranta ya B'aci taja tsaki tana K'un K'uni, wannan Mai K'iran ba Aziz bane ba wannan Wanda ya ce d'in sun Had'u a park ne Ranar shine ya K'iratan.kallan Huda tai Ganin tana kallanta yasa ta kauda kanta kamar bazatai picking ba sai Kuma tai ta kai kunne tai shiru batai magana ba "Assalamualaikum warahmatullah. barka da dare ko harma kin fara bacci ne na tasheki?" shiru tai batai magana ba yasan dama bayin zatai ba ya ce tun ya Saba ya cigaba ya ce "wai har yau Baki shirya sanin waye ni da suna na ba?" Ya fad'a Yana sauraran Mai zata ce .nan ma dai Shur6un ne ya biyo Baya kamar bazatai magana sai Kuma can ta sauke numfashi ta ce cikin k'osawa "Dan Allah waye kai mai Kuma kake buk'ata daga gareni da kuka takura min?" Ta fad'a Tana Hararar wayar.murmushi yayi har tana Jin sautinsa daga can ya ce "sanin wane ne ni abun bamai Wahala bane sarauniya ta, sannan sanin Mai nake buk'ata daga wajenki Kuma ai na fad'a miki tun tuni sai dai ko kina so na K'ara Mai Mai ta Miki ne sai nayi" ya cigaba ya ce "suna Abdullah shattima nida iyayena muna Zaune a garin Abuja kuma Ina Son HUYAAM so Mai tsananin Gaske, Kuma idan har ta bani dama zan iya zuwa har Inda take na gabatar mata da kaina a gidansu sannan ki ganni Tunda Dama kince Baki sanni ba"ya fad'a cikin sassanyar muryarsa. Huyaam ta murgud'a Baki kamar Yana kallanta ta ce "bana buk'ata" yay Wani killer smile ya ce "Mai yasa"? Ta ce "saboda mu agida ba'a barinmu kula samari tunda bamu isa ba" ya ce "okay naji Amma zaki bani dama nazo na samu Abba zan jira har lokacin da zakin fara kulasamarin nayi ALKawarin zan iya jiranki" cikin tsoro da fargaba Huyaam ta ce "a'a nidai Babu ruwana sai anjima" ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar yay saurin cewa"Dan Allah to ki barni na dinga k'iranki Ina Jin Jin daddad'ar Muryar ki Koda Baza ki barni Nazo gida ba?" Girgiza masa kai tai tana kashe wayar lokaci D'aya ta juya ta kwanta tai rufda ciki tana sheshshek'ar kuka...siyama Dake zaune kan gado kusa da Huda tana sauraran duk conversation d'insu ta d'aga kanta ta Kalli HUYAAM ta ce "ke wallahi wannan mutumin daga Jin muryarsa ma ko Baki ganshi ba kinsan kyakkawane wai Dan Allah waye shi? Huda ta ce "ina Wanda ya taremu ranar a park har yake cewa Huyaam ta bashi Aran lokacinta? Siyama tai Jimm alamar tunani sai Kuma can tace "tabbas na gane shi" Huda tace "to shine fa" ai tuni siyama ta mik'e Zaune da sauri tana kallan Huyaam ta ce "wallahi Huyaam Wannan mutumin ya Had'u kinsan Allah karkiyi wasa da damarki ki saurareshi Koda Baza ki bari yazo gidan bane ba ko iya waya kuke yima ai ta isa,ko Huda?" ta fad'a tana kallan Huda.Huda ta gyad'a mata kai tana murmushi Amma batai magana.can Kuma Siyama ta ce "to abin mamakin ayina ya samu contact D'inki nan ma banza tai ta k'yaleta. Huda tace "Nima Abinda nake tunani kenan Amma haryan na kasa samun ansa ta" Siyama ta ce "ita Huyaam d'in ta tambaya shi ne?" Huda ta ce "inama ma ta saurara shi da har zata sani? Siyama ta ce "uhmm to bari Idan ta huce na tambayeta".Ita dai Huyaam tana Jin su batai magana ba Dan Bata jin ko uwar had'uwa yayi zata tab'a kula shi ba, ita su barta ma da abinda yake damunta.tana wannan tunanin har bacci ya d'auketa tana jinsu suna ta hirar had'uwar da yayi sama sama...


__________?&


Da daddare misalin k'arfe biyu Saura na dare a cikin masarautar zazzau, lokacin idanuwa sun rufe ma'ana kowa yayi bacci,shiru babu motsin ko wanne Maha luk'i a Cikin wannan dare,Dan ko Kukan tsuntsu bakyaji sai daddad'ar iska Dake Kad'awa tana kad'a bishiyun Dake shuke a cikin palace d'in.a Kuma wannan lokacin a Wani sashe Dake nan cikin masarautar cikin Wani d'aki mai bala'in duhu Wanda bakya tab'a ganin komai aciki ko da hannun Kane.daga tsakiyar d'akin na hango wasu mutane su biyu mace da namiji suna tsaye da dukan alamu magana sukeyi. muryar ta namijin da naji ta doki dodon kunnuwana Yana cewa macen Dake kusa dashi a tsaye "bazai yuba Razik'a,bazai yuba,Dan ko Bazan tab'a kashe sultan a yanzu ba har sai lokacin dana tsara yayi,ai ni ba sultan ne yamin Laifi ba da zan kashe shi? ni ubansa ne yamin Kuma Kinsan fansa nake d'auka akan sultan ba akan ubansa ba,saboda haka sultan Babu abinda yamin kawai dai so nake na k'unta tawa ubansa akan sarautar sarki da aka bashi Mai makon ni shiyasa nake so ciwon zuciya ya kashe shi lokaci D'aya zuciyar sa tai bundaga ya Fad'i ya mutu ta hanyar jinyar ciwon haukan da muka sawa sultan yakeyi shiyasa kikaga nake bin Komai a hankali bana gaggawa kema Kuma nake goya Miki baya kike duk abinda kika ga dama" ya fad'a Yana zare ido. Sauke numfashi wacce aka k'ira da Razik'a tai ta ce "Amma maina Bai kamata nazo Maka da buk'ata ta kace ba haka ba" maina yay Wata iriyar dariya ya ce "Razik'a Kenan kin manta waye ni? Ki Fad'i wata buk'atar nai Miki Amma ba wannan ba" harararsa tai acikin duhun d'akin tana Jin Kamar ta shak'e shi ya mutu haka take ji ta ce "so nake na cika aikina akan gimbiya Ayush" maina ya kalleta ya ce "eh Nima nazo da Wani abun Amma Mai kike buk'ata akan nata?" gyara tsayuwarta tai ta ce "so nake nayi aikin da boka na yabani nayi amma na rasa ta wacce hanya zanbi maina?" Maina yay jimmm alamar alamar tunina sai kuma can ya ce "ayina zaki aiwatar da aikin naki?" Razik'a ta ce "acikin d'akin tane maina Amma nasara ta Ina zan fara gabad'aya wannan k'anwar tata ta Yi bak'e bak'e a d'akin na rasa ta Ina zan shiga har na aiwatar da aikin ga itama jara babbiyar tsohuwar nan Hajiya inna taje ta tare a part d'in ta kasa ta tsare na rasa ta Ina ma zan fara" ta fad'a cikin damuwa.Jin jina kai maina yayi ya ce "wannan Mai sauk'i ne" Razik'a ta ce "Taya ya ya zama Mai sauk'i?" Maina ya ce "kamar yadda mukai a wancan Karan a wannan ma haka zamuyi "ni zanji da komai ke Kuma ke zaki je ki aiwatar da aikin" ta ce "na fahimta ya ce "shikenan ke dai kisa lokaci kawai Ina jiranki" sauke numfashin salama Razik'a tai Jin abinda maina ya fad'a take murmushi ya bayyana a Saman fuskarta ta ce "godiya nake sarkin masarautar zazzau na gobe"wata iriyar dariyar farin ciki maina yayi kafin ya ce "an gaisheki sarauniyar masarutar zazzzu ta gobe" sai Kuma ya ce "Nima akwai abinda nazo dashi Wanda duk zaki had'a kiyi Aikin tare" kallansa Razik'a tai kafin tace"menene maina?" Mik'a mata Wata jarka yayi Yana kallanta, karb'a Razik'a tai tana jiran K'arin bayaninsa ya ce "duk ranar da zakiyi wannan aikin naki ki zuba mata ajikinta kafin ki fara naki aikin" Razik'a ta kalleshi cikin rashin fahimcita tace "shikuma na miye?" Ya kauda da kansa gefe yace "ke idan zakiyi naki aikin Ina tambayar ki na miye?" Girgiza masa kai tayi.ya ce "to Nima wannan nawa aikin ne na Daban" ita dai Razik'a kallansa kawai take . Ya ce "mu bar gunnan lokaci fa Yana tafiya kar wasu su fito su ganmu" Jin jina e kai Razik'a tai kafin ta ce "hakane Maina bari na tafi idan na shirya yin aikin zan maka magana" ya ce "saikin shirya d'in Ina sauraranki" daga haka yabi bayan Razik'a ganin ta nufi hanyar k'ofar suka fita daga d'akin gabad'aya bayan sun kullo k'ofar a Hankali,suna fita daga d'akin kowa ya nufi b'angarensa ta boyayyiyar hanyar da suke biyo wa a duk lokacin da zasu had'u d'in.....




# # # # #


Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =?G?

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =?G?
07066508376



*Yan Niger 07066508376



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*

*NA*


*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*


*Bismillahirrahmanirrahim*


My channel link =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y

PAGE 3?? 7??


___________?&


Tun daga wannan ranar Aziz chiroma da Abdallah shattima suka Saka Huyaam agaba da yawan k'iran waya Babu dare babu Rana kullum ne idan garin Allah ya waye sai sun K'irata Koda Baza tai picking ba basa tab'a hak'ura, gefe guda kuma wannan d'aya number data rage da har yau Batasan kowa ye ba Kuma dayak'i bayyana mata kansa shima sai yayi mata sms da barka da safiya da Kuma good night.yanzu shi kad'ai ne kawai Daya rage da Bata San ko waye shiba,and thank God ma da yak'i bayyana Mata kan nasa a gareta ita Hakan ma shine dai dai Dan Bata son a k'ara Bata Wani mamakin Wanda yafi na Aziz chiroma Kuma, Wanda har yau ta kasa daina Mamakinsa wai shine ya furta mata Kalmar so, yake sonta.bai tsaya iya nan ba gefe guda kuma ke mata kalaman soyayya ko kunya bayaji. Abu D'aya ne a yanzu yake damunta na yadda zata dak'ile Yi mata message d'in da akeyi Dan harta gaji da goge Wanda yake mata kullum. Ga suma kansu su Aziz da Abdallah shattima Banda Anty khadija ta ce Babu kyau walak'anta Wanda ya ke sonka ta dinga Sauraransu har su Gane Batason nasu su hak'ura su k'yaleta su Rabu lafiya da wallahi ba abunda sai Hana ta blocking dinsu tun tuni.,Ita gabad'aya zuwanta Abuja ma ba hutune ya kawota ba Damuwa ce kawai aka Sakata aciki. yo inba haka ba Mai zaisa kace baka Son mutum Amma ya nace Maka dole saika so shi.gashi har yau satin su biyu da Kwana biyu a Abuja har suna shirye shiryen komawa kano... yanzu haka da misalin k'arfe hud'u da Rabi na yamma zauna take agefen gado tana saka igiyar ta kalminta, Dan Anty khadija ta ce su shirya zasu fita unguwa su Huda har sun shirya sun fita can main falor ita kawai suke jira.bud'e k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama d'agowa tai daga duk'en da take bayan ta gama Saka igiyar ta kalmin ta Mik'e tana kallan Siyama data shigo d'akin tun kafin tai magana Huyaam ta ce "Gani nan na gama" daga haka ta d'auki hand bag d'inta da wayarta tabi bayan siyama Data fita daga d'akin ta kullo k'ofar gabad'aya ta sauka downstairs.acan ta Tarar da Anty khadija tana tsaye tare dasu Huda iya Hassan da Hussain ne kawai banda su za'a, sai imaan wacce da ita za'a tafi da dukan alamu ita kawai suke jira.sauke numfashi Anty khadija tai tana kallansu ta ce "ku wuce mu tafi ko? Driver na jiranmu" k'ofar falon suka nufa Anty khadija tabi bayansu har zuwa compound inda driver ke jiransu.siyama ce agaban motar sai Anty khadija da imaan sai Huda da Huyaam ne a bayan motar, ahaka driver Yaja Motar suka bar gidan gabad'aya ya nufi inda aka bashi instruction d'in zuwa....

Awani k'aton mall Dake garin Abuja driver yay parking suka fito gabad'ayansu suka tsaya suna jiran Anty khadija Dake magana da driver.kallansu tai bayan ta k'araso gunnasu ta ce "muje" gaba sukai tana binsu a Baya Saida suka shiga ciki sannan ta ce su fara zuwa wajen gown kowa ya zab'i irin wacce yake so da takalma da hand bag da dai duk abinda suka Gani indai suna so su d'auka, godiya sukai mata nan suka wuce b'angaren dogayen riguna ita Kuma ta kama hannun imaan suka wuce b'angaren jewelleris...sunyi siyayya ba kad'an ba Dan su da farko kad'an suka d'auka kayan Saida Anty khadija ta k'ara musu komai da kanta ganin 'yar siyayyar da Sukayi Bai taka Kara ya karya ba.bayan ta gama tai musu magana nan suka bar wajen suka nufi wajen cashier.kayane ta Siya musu ba kad'an ba masu bala'in kyau da tsada. fitowa sukai daga cikin Mall d'in gabad'aya bayan Anty khadija ta biya kud'in, D'aya d'aga cikin workers d'in Mall na biye dasu da kayan siyayyar da Sukayi har zuwa wajen motar su driver ya Bud'e masa boot d'in motar ya zube kayan gabad'aya aciki sannan ya koma cikin mall d'in bayan Anty khadija ta sallameshi.. fitowar sa Daga cikin motar sa kenan bayan ya kulle Motar, tafiya ya farayi a hankali zuwa interance d'in Mall d'in, tsayawa yayi cikin fad'uwar gaba Yana kallan Wacce har yau fuskarta ta kasa goguwa a kwanyar kansa ko a mafarki idan ya ganta saiya Gane ta Saboda Irin yadda ya haddace kamanninta Kamar karatun sallahr sa. tunda suka fito daga cikin Mall d'in nan yake kallansu daga nan inda yake tsayen baya ko kiftawa har suka k'araso wajen motar ta su, zuwansa kenan shima cikin mall d'in zaiyi siyayya kallanta Kawai yake Wanda ita batama San Yana Yi ba suna tsaye kusa da motar suna k'ok'arin shiga ciki Dan gabad'aya hankalinta da nutsuwarta Yana tare da 'yan uwanta, har su Huda dasu ma Basu lura dashi ba. shiko yayi nisa a shagalar da yayi da kallanta har suka shiga cikin motar driver Yaja suka bar wajen.sai alokacin ya dawo sense d'insa cikin Sauri ya juya zuwa inda yayi parking motarsa ya shiga yabi bayansu da sauri......


Tafiya sukai Mai D'an tsayi kafin yaga sun isa unguwar tasu har zuwa k'ofar gate d'in gidan, inda yake Kyau tata zaton nanne gidan nasu.gidan ne dai Wanda kwanaki ya biyosu ranar da suka had'u a park shine dai suka zo driver ke k'ok'arin shigar da motar ciki. sauke numfashi yay Yana Zaune a cikin motar sa inda yayi parking a can bakin titin shigowa layin nasu daga can gefe yadda baza su tab'a ganin Saba ko Kuma Wani ya farga da cewar binsu yake ba.Saida yaga sun shiga har cikin gidan security sun rufe gate d'in sannan yay zooming up ya bar wajen ya wuce Wani masallaci Dake nan cikin unguwar ganin ana k'ok'arin shiga sallahn magrib....


Wajen k'arfe 9 Saura na dare suna zaune a d'akinsu Tun bayan da sukai dinner suka hauro sama Suka mak'ale a d'akin shine basu koma downstairs d'in ba.hira kawai suke suna dariya gabad'ayansu harda rik'e ciki HUYAAM ta ce tana dariya "Dan Allah ya isa haka siyama karkisa cikina ya k'ulle aini kece kike ban dariyar ma bawai Shi Wanda kike bamu labarin ba, dan yadda kike acting kad'ai zai sa mutum ya sume saboda dariya" siyama zatai magana wayar Huyaam tai ringing alamar shigowar k'ira.juyawa tai tana kallan Mai K'iran take ta daina dariyar da take Yi ganin number Aziz ne,nan ta had'e Rai siyama Dake kallanta ta ce "waye" Huyaam ta ya Mutsa fuska kamar zatai kuka ta ce "wa kika sani?" Huda ta ce "ya Aziz ne ko Abdallahn? Juya musu secreen d'in wayar tai tana nuna musu.kallan screen d'in siyama tai kafin ta rik'e hab'a ta ce "iKon Allah wai Yaya Aziz da soyayya da Huyaam! nifa har Yanzu ganin abun nake kamar a mafarki wallahi,badan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login