Showing 18001 words to 21000 words out of 140150 words

Chapter 7 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

180

tafi..... Ranar Wednesday Basu da paper sai ranar Friday itace last paper kenan aranar kuma zasuyi candy.da yamman Ranar su Huda suka shirya ya haidar zai kaisu suyi siyayyar kayan graduation d'in da zasuyi Mai martaba ne da kansa yace akaisu kowa ya zab'i abinda yake so duka su biyar d'in harsu ikleema tunda dama sune zasuyi graduation d'in a duka gidan ,Shine a matsayin gift d'in Da Mai martaba zai Basu . kuma ko Wacce dama uwarta tayi mata gift na graduation . itama Ammie tayiwa su Huyaam d'in Kuna musu bala'in tsada kala hur hud'u less da atamfa.dama tun jiya su Huda suka fad'awa su ikleema akan cewa yau za'a kaisu shopping....yanzu haka k'arfe biyar ne Saura na yamman ranar su ikleema already sun fito daga part d'insu suna tsaye nan harabar gidan itada safna ko Wacce cikin shiri sunyi kyau ba kad'an ba suna tsaye suna k'ok'arin zuwa part d'in su Huyaam Aziza ta fito daga part d'insu ta k'araso har wurinsu tana kallansu tace.


"Ina su ishashshu mulkakku Daman suke basu fito ba koh?..."Ta fad'a tana kallon hanyar part d'in su Huyaam.


ikleema ta Kalli Aziza wacce ta Wani had'e Rai tace .


"Haba Aziza Dan Allah ki daina abinda kikeyi Babu Dad'i,yanzu me zaisa ki Fad'i Irin wannan maganar yanzu idan agabansu kikayi fa? Ai kema kinsan fad'a kika takalo ko?..."Aziza zatai magana ya Haidar ya fito daga part d'insu sanye yake cikin shigar k'ana nun kaya Wanda sukai masa bala'in kyau sai baza k'amshi yake hannunsa Kuma rik'e da key d'in motarsa su Huyaam Kuma suna bayansa .tun daga nesa Aziza take kallansu Huyaam Ganin yadda sukai bala'in kyau ba kad'an .gabad'ayansu sanye suke cikin shigar doguwar rigar abaya maroon color wacce ta fito da ainihin kyansu sai Wani d'aukar ido kayan suke saboda duwatsun da akai adon rigunan dasu sai kawo haske suke ta ko Ina.Ai take Aziza ta d'auke kanta tare da tsuke fuska ta Maida gefe ganin yadda kallo ya koma kansu HUYAAM Dan hadiman gidan nan sai kallansu suke suna musu kirari,har suka k'araso wajen motar. ya haidar ya danna remote d'in Dake jikin key d'in motar take motar ta Bud'e da Kanta ganin haka yasa Aziza tai saurin shiga can bayan motar Dan Bata so ma su hadu dasu HUYAAM bare tai musu magana, ikleema da safna suka shiga suma suka zauna kan seat d'in Dake gaban Aziza su Huyaam ne suka karaso Suma suka shiga inda su ikleema ke zaune HUYAAM ce k'arshen shiga tana Zaune daga bakin murfin motar.


Ya haidar ya juyo Yana kallansu fuska d'aure yace.


"Nine driver ku da duk zaku shige baya?wa kuka barwa front seat d'in?...". Sukai shiru basuyi magana ba suna sunkuyar da kai k'asa.yace.


"ba magana nake muku ba?..."ya fad'a a D'an tsawace.


Huda ce tai k'arfin halin kallan Huyaam Wacce ta tura Baki gaba tai k'asa da murya tace.


"Kije tunda kece a farko HUYAAM"...HUYAAM ta d'ago zata harari Huda sukai ido hud'u da ya haidar Wanda shima kallanta yake yay mata Wani kallo take ta Bud'e Murfin motar ta fito daga wajen ta koma gaba ta zauna tana K'ara tura Baki gaba .ya haidar ya juya ya ta-da motar suka fice daga gidan bayan an wangale musu gate fadawan nan sai kirari suke musu.


Awani K'aton mall Wanda ake ji dashi a garin kano ya haidar yay parking motar ya fito Suma suka fito ya rufe motarsa yay gaba suka bishi a Baya Huda da ikleema sune a gaba sun jera suna tafiya Huyaam kuma da safna wacce ke ke tai mata surutu itadai sai dai ta bita da uhmm ko a'a sai Aziza wacce ta ware kanta ita kad'ai tana tafiya cikin Isa da tak'ama sai Wani Shan k'amshi take .tun kafin su shiga cikin Mall d'in nan kallo ya koma kansu saboda Babu k'arya ko Wacce tayi kyau Kuma keda kin gansu kinsan hutu Had'i da Jin Dad'i sun samu muhalli ajikinsu.Ahaka suka shiga cikin Mall d'in ya haidar ya Kallesu bayan sun shiga yace.

"kuje ku zab'i duk abinda kuke so".yana fad'ar haka samu waje ya zauna ya zaro wayarsa. ikleema da Huda suka tafi wajen trollories d'in Dan d'aukar musu.D'aya ikleema da safnah Huda Kuma ta d'aukar musu itada HUYAAM Aziza kuwa dama sun San halinta itama haka ta K'arasa ta d'auki nata trolling tai nata wurin HUYAAM ta k'araso kusa da ya haidar tai k'asa da murya tace.

"Yaya! ya ka zauna Kuma?..." Ta fad'a tana tura Baki gaba.


Batare da ya haidar ya d'ago ba Yana duba wayarsa yace.

"Da kukai Sa'a ma na rakoku shine kike tambayar ya na zauna ko? to ki zauna tambayata Karki bisu kuyi abinda zakuyi nidai ina gajiya tafiya ta Zanyi "ya fad'a Yana cigaba da kallan wayarsa.


HUYAAM ta tab'e Baki tabi bayan su Huda. B'angaren dogayen riguna suka fara zuwa nan suka fara zab'a kowa biyu biyu kafin su d'auki Wasu iri D'aya Guda biyar suka ce anko zasuyi gabad'ayansu .duka su biyar d'in harda Aziza suka d'aukawa da tai nata wurin,daga wajen dogayen riguna Kuma wajen hands bag da takalma suka nufa nanma kowa ya d'auki biyu biyu sai Kuma sukai wajen cosmetics suka d'auki turaruka masu bala'in kyau da tsada da kayan kwalliya,bayan sun gama da nan Kuma sai sukai wajen kayan graduation d'in da zasu d'auka nan ma dai sun d'auki abubuwa sosai daga nan Kuma sukai wajen payments. A cikin Mall d'in nan inbanda Kallansu Babu abinda akeyi ganin sun gama yasa ya haidar ya mik'e ya karasa wajen payments d'in shima bayan anyi counting kud'in ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in sannan aka zuba musu cikin Manyan bags ma'aikatan wajen suka rakosu dashi har boots ya haidar ya Bud'e musu suka sa kayan ya zaga driver seat ya shiga ganin su Huda har sun shiga ya ta-da motar suka nufi palace.


K'arfe shida Saura suka shiga palace bayan ya haidar yay parking motar nan harabar gidan ya Bud'e musu boots kowa ya d'auki ledarsa Dan dama tun a wajen payments aka sawa kowa nata unlike su Huyaam da nasu ke had'e sai bayan kowa ya d'auki ledarsa Sukai wa ya Haidar godiya kowa ya nufi part d'insu bayan sunyiwa juna sallama.Amma Banda Aziza data Saka kayan a gaba tana K'iran Wani dogari Mai suna bala akan yazo ya kai mata nata kayan b'angarensu.


Gabad'aya su ikleema sai da suka juya suna kallan Aziza saboda mamakin abinda tai, Amma sai basuyi magana ba Suka juya suka cigaba da tafiya ganin ya haidar ya juya Yana kallanta alamar zai mata magana suko su Huyaam tuni sun shige part d'insu.


Ya haidar Yana kallan Aziza da bala yazo ya zube agabanta cikin rawar jiki Yana cewa.


"Gani ranki Dad'e" ya fad'a cikin girmamawa.

Aziza ta juya masa ido tace.

"Kayan nan zaka biyoni dasu". tana fad'ar haka ta juya zatai gaba ya haidar ya k'ira sunan bala da k'arfi wanda ya juyo da sauri Yana zare ido ya haidar yace.


"Kai bala karka sake ka d'auki kayannan idan ba zata iya d'auka ba ta barshi " ya fad'a Yana kallan Aziza data juyo da sauri tana kallansa Jin abinda ya fad'a.


Aziza ta Marai raice tace.

"Yaya haidar da nauyi fa kayan,Dan Allah ka barshi ya tayani d'auka mana".ta fad'a kamar zatai kuka.


Ya haidar yay mata Wani kallo yace.


"Su sauran 'yan uwanki da suka d'auki nasu kayan kin fisu ne? ba Kai D'aya kuka Siyo ba nawa kayan yake da Dan Rashin tausayi zakisa mutumin Daya kusan haifarki d'aukar miki kaya?..." ya fad'a atsawa ce.sai Kuma ya juya Yana kallan bala Daya k'asa tafiya yace.


"Bala ko baza ka tafi bane?..." Bala ya mik'e da sauri yace.


"A'a rankai Dad'e wane ni,Allah ya huci Zuciyarka".Yana fad'ar haka ya tashi ya bar wajen.Aziza ta fashe da Kuka ta d'auki kayan tai part d'insu tana rusa uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.ya haidar yay tsaki yabi bayan su HUYAAM......






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*



*PAID BOOK =???*



*FREE PAGES*





*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zo muku har inda kuke=???=????.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=?G?*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=?I?08135305790

*Sai mun jiku =???=???=???*





*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 1?? 0??



__________?&


Da kuka Aziza ta k'arasa b'angaren su.Ramla da walida ta rara a falon suna Zauna suna kallo Baki Bud'e suka bi Aziza da kallo ganin yadda ta shigo cikin falon tana zunduma uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.tun daga sama Fulani Salamatu Dake cikin d'akinta ta d'auro alwala ta fito daga toilet kenan zata ta-da sallah tajiyo kamar kuka d'aukarta ma ko walida ce yasa babu shiri ta fito daga d'akinta cikin tashin hankali ta sauko downstairs.


Mamaki ne ya kamata ganin yadda Aziza take kuka ta k'araso Gaban Aziza tana kallanta tai k'asa da murya tace.


"Aziza meyasa meki kike wannan uban kukan haka? Ina daga shopping kuke?...."ta fad'a Tana kallan Aziza tare da k'arewa falon kallo da mamaki.


Aziza da tun shigowarta ta dire kayan nan kan tiles tana kallan Fulani Salamatu tace tana sheshshek'ar kuka.


"Mummy ba ya haidar bane Dan nasa bala dogari ya d'aukar min kayan nan ya tayani shigowa dasu ciki Shine ya Haidar ya hanashi wai bazai kawo ba idan hazan d'auka ba na barshi. kuma Bai tsaya nan ba Saida ya wulak'anta ni a gaban gabad'aya bayin gidannan sai kallo na suke Dan dai kawai su Raina ni".ta k'arasa fad'a tana K'ara sautin Kukanta.


Fulani Salamatu da tunda Aziza ta fara magana take kallanta da mamakin abinda haidar yay mata . gabad'aya ranta ya gama B'aci tace cikin D'aga murya da b'acin Rai.


"Shi Haidar d'inne ya hana Wani bawa Irin dogari ya d'aukar miki kaya sannan Bai tsaya iya nan ba ya wulak'antaki agaban su saboda shi ya isa yake nufi kome?...." Ta fad'a da k'arfi har Saida hadimanta biyu Dake kitchen suna mata girki suka lek'o suna kallan iKon Allah.


Aziza ta gyad'a mata kai tana cigaba da murza idonta tana Kuma sheshshek'ar kuka.Fulani Salamatu ta gyad'a kai kafin cigaban tace .


"Wato tunda yayansa baya nan shine shi Kuma zai D'ora daga inda ya tsaya ko me yake nufi? To wallahi Bai isa ba bazai yuba yace sai takurawa Yara na agidan nan ba, ko yayansa alokacin da yake kan ganinyar Rashin mutuncinsa Baya min haka bare Kuma shi ki K'yaleni dashi Dan wallahi bazan zuba ido ana tsangwamarku ana wulak'anta Kuba kuda gidan ubanku bari Mai martaba ya shigo zan fad'a masa idan zai d'auki mataki gara ya d'auka idan kuma bazai iya d'auka ba toni zan d'auka da kaina sai dai ayi duk wacce za'ayi agidan nan Dan bazan d'auka ba". ta k'arasa fad'a tana huci Aziza dai sai share hawayen idonta take Yi Ramla koh da walida sun nan Zaune kan kujera sun zuba musu ido kawai suna kallansu .


Fulani Salamatu ta kalli Aziza tace. " ki wuce ciki ki wanke fuskarki ki barni dashi ai zai K'ara idan halin sane dama can shima ba mutunci ne dashi ba,ki dai na kukan nan haka Aziza". ta fad'a tana kamo hannun Aziza ta kaita har d'akinta ta cigaba da lallashinta kafin tace tai alwala tai sallah . Aziza ta gyad'a mata kai bayan ta goge hawayen fuskarta Fulani Salamatu ta fita daga d'akin ta koma nata danyin sallah.



Suko su Huyaam suna shiga part d'insu suka nunawa Ammie kayan da suka Siyo.Ammie tai godiya tace idan Mai martaba ma yashigo anjima suje suyi masa godiya suka ansa mata da to sannan suka shige D'aki Dan d'auro alwala suma suyi sallah.


Wajen k'arfe na daren ranar Mai martaba yana Zauna a falonsa tare da ya haidar suna magana su Huyaam suka shigo bakinsu d'auke da sallama suka k'arasa suka d'urkusa har kusa Mai suna suka had'a Baki wajen gaida shi.

Mai martaba Yana kishin gid'e jikin tuntun sarautan dake falon ya ansa musu da kulawa Yana gyara zamansa.


Sannan suka juya suka gaida ya haidar.ya haidar ya ansa musu . Suka juya Suka fuskanci Mai martaba huyaam tai murmushi tace .


"Abba munga Sak'o munje munyi shopping d'in d'azu mungode Sosai Allah ya K'ara Bud'i Allah ya K'ara girma". ta fad'a tana murmushi.itama Huda ma tai masa nata godiyar.mai marataba ya Jin jina kai Yana kallan su Yace.


"Babu komai Allah ya Bada good results". Ya fad'a Yana kallansu .sukai murmushi gabad'ayansu suna sunkuyar da kansu k'asa Basu Dad'e a falon ba sukai masa sallama suka tafi Dan zasu suje suyi karatu ne Saboda exam d'in gobe.....


Bayan fitar su Nan Mai martaba ya cigaba da maganar da yakeyiwa ya haidar....



____________?&



*Graduation day*



Washe gari Friday ranar data zamto the best Rana awajen su Huda more especially ma Huyaam. wannan ranar ta zamto D'aya daga cikin ranakun da Huyaam take ganin bazata ta tab'a iya mantawa da ita ba saboda ayau idan Allah ya yarda zatai graduation na SSCE...karfe 8:30am dai dai a makarantar taiwa su Huyaam Dan exam d'in ta k'arfe 9 ce suna zuwa hole d'in exam d'in suka Wuce direct suka zauna nan zaman jiran a fara exam d'in.


K'arfe 11 dai dai su Huyaam suka gama paper su ta k'arshe.gabad'ayansu suka fito kowa sai murna yake gwanin ban sha'awa Babu Dede'wa Kuma suka wuce assembly ground Dan za'a Bada gifts d'in the Best students na this year Wanda suka fi cin maki tun daga first term har zuwa second term dama haka suke ko wanni year sukan bada gifts ga best students d'insu to wannan Karan ma hakace ta kasance.A cikin subjects d'in da sukeyi aka ware 3 sciences subjects including English wanda a shine za'a Bada gifts d'in.Assembly ground d'in ya cika mak'il da students kowa ka kalla fuskarsa tana bayyanar da farin ciki Yana yin da yake ciki... SS 3A fannin Biology HUYAAM M BELLO itace over role student wacce making ta yafi na kowa a b'angaren biology take wajen nan ya kaure da tafi da ihu haka ana congratulations Huyaam m Bello.Huyaam ta fito cikin jin kunya har gaban assembly ta tsaya ta sunkuyar da kanta k'asa.sai a fannin physics kuma aka K'ira Huda M BELLO sai wata 'yar SS 3B itace tai over role a fanning chemistry wacce k'awar su Huyaam ce itama Mai suna jidda . A fannin English ma dai Huyaam ce dai still over role nan ga akai ta tafi ana mata congratulations. take a wajen aka hau yi musu pictures Had'i da malamai sannan aka basu gifts d'in bayan anyi raping d'insu D'aya text book ne aciki wanda a kai rapping d'insa Wanda zasu musu amfani daga nan har jami'a sai agogon bangon da graduation gown da aka Basu sai enlargement pictures da akai musu tun tuni Wanda ke d'auke da pictures d'in ko wanne students a cikinsu haka aka bawa kowa nasa sannan aka K'ara Yi musu pictures kowa rik'e da gifts d'insu bayan an gama akaiwa graduate d'in addu'ar samun kyakkyawan saka mako daga k'arshe akai addu'a gabad'aya students d'in aka sallamesu..tunda suka baro assembly ground d'in ikleema da safna suka karb'i gitfs d'in suna Gani sai kace su aka bawa gifts d'in nan dai sai Wani murna suke suna Taya su Huyaam murna Amma Banda Aziza data had'e Rai Dan ita ba'a Bata ba k'iras ya rage ta saki Kuka kai tama Yi a b'oye Bata bari bane sun Gani ba,suko su Huyaam Basu ma San tana Yi ba har aka zo d'aukar su Aziza Bata Bud'e Baki tai musu magana ba bare Kuma tai musu murna Sukuwa Basu damu ba saboda sun riga da sun San halinta..


Driver Yana yin parking bayan an Bud'e musu motar duk suka fito fuskokinsu d'auke da mad'aukakin farin ciki saboda yau Rana ce ta musamman agaresu da suka Dad'e suna fatan Gani .safna da ikleema sukaiwa su Huyaam Sallama Suma sukai musu sannan kowa ya wuce part d'insu farin ciki bayyane a saman afuskarsu, na suma sun zama graduate, Amma Banda Aziza da ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe saboda haushi.



Aziza tana shiga part d'insu ko sallama batai ba su Ramlat suna zaune falon suna jiran dawowar Aziza su tayata murnar gama exam d'inta da kuma Murnar zama candidate da tai .ganin ta shigo falon yasa su walida duk suka mik'e sukai kanta suna K'iran sunanta tareda cewa.


"congratulations ya Aziza".suka fad'a suna k'ok'arin zuwa su rungumeta fuskokinsu d'auke da murmushi,Bayin Allah Basu kula da yadda Aziza ta shigo falon ba.... Aziza data daka musu wata uwar tsawa muryarta na rawa Basu San lokacin da suka tsaya a inda suke ba kowa ya k'ame ya kasa motsawa kusa da ita ..


Fulani Salamatu da itama da fuskarta take d'auke da farin cikin yau 'yarta ta zama candidate Amma sai fuskar ta Disha she ta maye gurbin farin ciki da damuwa ta tsaya tana kallan Aziza da Kuma tunanin Mai yasa meta haka da ita dai a saninta d'azu da safe da farin ciki Aziza ta bar gidan tana Murna tana komai Amma Shine yanzu Kuma ta dawo da b'acin Rai.fulani salamatu ta Mike ganin Aziza nata masifa ita kad'ai ta k'araso har gabanta ta kamo hannun Aziza ta zaunar ta kan kujera itama ta zauna kusa da ita tana kallanta tai k'asa da murya tace cikin lallashi...


"Meyasa meki Aziza?....", ta fad'a tana kallan Aziza.


Aziza ta fashe da Kukan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login