Showing 75001 words to 78000 words out of 140150 words

Chapter 26 - HUYAAM by MRS SARAKIes

07 Aug 2026

201

mata kai Huyaam tai tace. "Babu komai". Baba magajiya tace. "Allah ya K'ara lafiya ranki Dad'e". Huyaam ta ansa mata da Ameen.mik'ewa Baba magjiya tai ta bar falon ta koma kitchen d'in.huyaam ta d'auki cup d'in ta tsiyayi kunun ta kai Baki ta fara Sha sai taji yayi mata Dad'i sosai abakinta.bayan Kamar mintuna 15 suna Zaune afalon akai Sallama a k'ofar falon, safnah ce da mamansu Hajiya Aysha.Huda da Huyaam suka ansa musu sallamar tasu har suka k'araso falon. Huda da Huyaam suka had'a Baki Wajen gaida Hajiya Aysha.hajiya Aysha ta ansa musu da kulawa tana tambayar Huyaam jikinta.huyaam ta ansa mata a Kun yace.huda ta Mik'e tace. "Ummi ki zauna bari naiwa Ammien Magana tana sama".Daga haka Huda ta nufi stairs d'in.Hajiya Aysha tai murmushi ta zauna nan saman kujera . safnah ta k'arasa ta zauna kusa da Huyaam tana kallanta da kulawa tace. "Huyaam ya jikin?..." Huyaam na D'anyi murmushi tace. "Da sauk'i". Safna tace. "Allah ya K'ara lafiya". Huyaam ta ansa mata da Ameen k'asa k'asa.d'aya daga cikin hadiman Ammie ce tai sallama a falon hannunta d'auke da tray data D'ora ruwa da drink's akai ta ajiye saman table Dake nan gaban Hajiya Aysha sannan ta tsugunna har k'asa ta gaida Hajiya Aysha. Ansa mata Hajiya Aysha tai da kulawa sannan ta mik'e ta koma kitchen d'in.Huda ce ta sauko downstairs d'in tana kallan Hajiya Aysha tace. "Ummi Ammien tace kije falon sama" Mik'ewa Hajiya Aysha tai tana ansa mata da to daga haka ta nufi stairs Wanda zai sadan ta b'angaren Ammien..


Fulani Salamatu ce zaune a cikin d'akin Aziza tana kallan Aziza Dake zaune a falon tun d'azu sai chatting takeyi.Aziza ta d'ago tana kallan mummyn nasu Dake tai mata magana tun d'azu akaro na Babu adadi Amma Kuma batai mata magana ba yanzun ma gajiya tai tace. "wai mommy yanzu Dan Allah Mai kikeso nace miki ne? nifa wallahi banasanshi ko kad'an kuma kinsan ma Karatu Zanyi ba wai soyayya ba ni gaskiya kark'i k'aramin zancensa banaso". Ta fad'a a fusace tana Wani tura Baki gaba.fulani Salamatu kallan Aziza kawai take da mamakin abinda ta fad'a yanzu Aziza so take ta Bat'a mata duk Wani shiri da buri akan abinda take ganin shine kad'ai mafitar ta kome? Ita fa a yanzu babban burinta bai wuce ace 'yarta ta auri D'an sarki mai jiran gado ba tunda ita Bata haifi D'a namijin da zai gaji sarautar gidan ba ai gara ace 'yarta na Auren D'an sarki Koba komai wata Rana 'yar tace matar sarki harma ta haifi yarima .sauke numfashi tai ta k'ara gyara zamanta tana kallan Aziza tai k'asa da murya tace. "Haba Aziza Yanzu ni kenan ban isa na fad'a miki magana Kiji ba? Haba Aziza komai fa da kikaga Inaya danke nakeyi fa badan Komai ba, Amma yanzu ni zaki kunyata ko yaya?.." Aziza tai shiru batai magana tana cigaba da danna wayarta.fulani Salamatu ta cigaba tace. "To Yanzu da kike cewa bakyason sa Dan Allah meye laifinsa da zakice bakyason nasa sai kace bakisan Shiba Aziza? Ga kyau ga kud'i ga Aji to Dan Allah Kiko Aziza me kikeso awurin D'a namiji Wanda shi ba shida shi?..bana tunanin koke zaki fad'a masa kyau.
"Aziza ta Kalli mommyn nasu Jin abinda ta fad'a tace. "Wai mommy Dan Allah shine yace Yana Sona ko Kuma kece dai kike son ni na so shin?.ta fad'a tana jiran ansar mommyn nasu.Fulani Salamatu ta K'ara gyara zamanta tai k'asa da murya tace. "Waya ce Miki baya sanki Aziza? Kema kinsan babu Wani d'a namiji da zai ganki baiji kin masa ba". Aziza ta tura Baki gaba tace .
"To Dan Allah mommy abar zancen nan kawai yanzu AURE za'a min ko Kuma karatu Zanyi?. Falani salamatu tace. "Karatu zakiyi Aziza, Amma Kuma inaso ne na ga kin amince da maganar nan tawa yadda ko zuwa gaba ne nasan bani da matsala akan wannan Abu Da nakeso ya k'ullu". Aziza ta Bat'a Rai tace. "To Dan Allah tunda sai nayi karatu ki K'yaleni da wannan maganar ki bari har sai lokaci yayi".fulani Salamatu tai shiru tana kallan Aziza tana tunanin ta yadda zata b'ullo mata Dan Kada ta watsa mata k'asa a ido ta Bat'a mata duk Wani shirin ta,Dan Aziza ce kad'ai take tunanin zata had'a ta da shi Wanda take wannan burin akan nasa. Sauke numfashi tai tace. "Shikenan tunda kince haka Amma inaso kiyi tunnani akai". Da k'yar Aziza ta iya ansa mata da to sannan fulani Salamatu ta mik'e ta fita daga d'akin gabad'aya.......


_____________?&


Tun bayan da su Huyaam sukai sallahn magrib suka d'auko Al'qur'ani suke karatu anan falon kamar yadda suka Saba,har yanzu da ake K'iran sallahn isha'i kafin su tsaya da karatun bayan sunkai Aya sannan suka rufe Al'qur'anin .Addu'o'i sukai Sosai kafin su shafa suka Mik'e Jin anshiga Sallahn, jam'i sukabi suka bi sallahn.....k'arfe 8:30pm suna Zaune a falon downstairs bayan sunyi dinner ko Wacce rik'e da wayarta a hannunta daga Huyaam har Huda ya Zarah ce bata a falon tana d'akinta tun bayan da sukai dinner ta shige d'akin Bata fito ba har yanzu.muneefa da muneefa kuma suna zaune a falon suna game. Knocking k'ofar falon akai Tareda Sallama lokaci D'aya a aka turo k'ofar aka shigo.kallan k'ofar sukai Huda na ansa sallamar tasa harya k'arasa shigo falonwa falon bakinsa d'auke da sallama.huda na murmushi tace. "Ya chiroma sannu da zuwa". Ta fad'a tana kallansa har lokacin murmushi ne a saman fuskarta.Aziz chiroma ya zauna anan saman kujera Yana kallan Huda."yace.yauwa Huda." Muneeb da muneefa ne suka juyo suna gaida shi ,ansa musu yayi Yana murmushi Yana tambayar su school suka ansa masa da Alhamdulillah. Yace. "Good,Masha Allah! Ya Fad'a Yana kallan Huyaam ta gefen ido data sunkuyar da kanta idonta na kan screen d'in wayar ta kamar Batasan Yana wajen ba.Huda tana kallansa tace. "Ya chiroma Ina wuni?" Yana murmushi yace. "Lafiya lau Alhamdulillah ya huta?. Huda tace. "Lafiya lau". Huyaam ta d'ago da kanta tana kallansa ta D'an saki fuskarta kad'an tace. "Ya chiroma Ina wuni". Ya juya ya kalleta ya ansa mata da kulawa har lokacin idonsa yana Kanta yace. "Ashe Kuma anyi waya shine ko fad'amin?...." Huyaam ta sauke idonta batai magana ba sai Huda ce tana Murmushi tace. "To muma mun Dad'e bamu gankaba ai shiyasa bamu nuna Maka ba". Ya shafa kansa Yace. "Eh wallahi two days bana zama idan na fita tun safe sai bayan 8 nake dawowa". Huda tace. "Ayya". Ta mik'a masa wayar Hannunta tace. "To gatawa ka Gani " yasa hannu ya karb'a Yana juya wayar a hannunsa yace. "Wow Masha Allah! lallai yarima Yana ji daku irin haka wannan latest phone". Huda tai murmushi Amma batai Magana ba ya d'ago ya Kalleta yace. "To abani contact ko ba'a badawa?..." Huda tace. "Mai zai Hana kuwa ya Aziz bari na Karanto Maka". Yana murmushi ya Mik'a mata wayarsa yace ungo kisamin taki". karb'ar wayar tasa Huda tai.itako Huyaam na jin haka ta Mik'e ta Kara wayar ta a kunnenta kamar wacce zatai answering call sannan ta haye sama da sauri.Aziz ya bita da kallon gefen ido. ita ko Huda hankalinta gabad'aya na kan wayar AZIZ da take sa masa contract d'inta.mik'a masa wayar tayi bayan ta gama tace. "Gashi ya chiroma". kallanta yayi yace. "Kinyi serving tace. "Nayi, da suna na nai serving". Yace "okay Samun ta Huyaam". Huda ta Kalli inda Huyaam ta zauna ganin wayan Bata nan yasa ta Kalli Aziz chiroma tace. "Yaushe ta tashi kuwa?. Aziz yayi murmushi yace. "Now ,Not long ago may be ko ansa waya zatai". Huda tai shiru sai Kuma tace. "To bari nasa Maka natan". nan tasa masa contract d'in Huyaam sannan ta mik'a masa wayar, karb'a yayi zaiyi serving adai dai lokacin da Ammie ta sauko falon Aziz ya tsugunna har k'asa ya Gaida ta. ansa masa Ammie tai da kulawa sannan tace. " Yaushe Kashigo kwa Aziz?..". Aziz na shafa kansa yana murmushi yace. "Not long ago Ammie". Ammie tai murmushi sannan ta tambaye shi aiki yace mata Alhamdulillah nan Ammie tace. "Allah ya taimaka" yace. "Ameen" Yana mik'ewa sannan yaywa Ammie sallama. Ammie tace. "Tafiya Kuma zakai Aziz?..." Aziz Chiroma na murmushi ya ansa mata da eh sannan ya fita daga falon gabad'aya......


K'arfe 12:30am na dare shakundum ce tsaye a cikin toilet d'in d'akinta waya ce kare a kunnenta.magana take k'asa k'asa wadda koda kana kusa da ita idan ba Mai k'arfin jiba bazaka tab'a sanin Mai take cewa ba.tace Cikin k'asa da murya "barzuk Ina cikin tashin hankali na rasa ta Ina zan fara? wannan kakartasu ta dawo part d'in da zama gabad'aya bansani ba ko ta fara fahimtara Wani abunne?..." Ta Fad'a cikin tashin hankali. Daga can b'angaren Barzuk yace da wata iriyar murya marar dad'in saurare "ita tsohuwar ce Mai wannan aikin". Cikin tashin hankali shakundum tace. "Itace mana barzuk! Ga tsabar masifa sai ta kai har kusan k'arfe d'ayan dare tana falon Bata shiga d'aki ta kwanta da wuri bare na samu na aiwatar da aikin nawa ba". Ta fad'a cikin damuwa.barzuk yay Wani wata mahaukaciyar dariya kafin ya tsagaita yace da bu d'add'iyar muryarsa. "Ai wannan tsohuwar da kike ganinta NEMA take Taga ta karya mana aikinmu". cikin damuwa shakundum tace. "Kamar Yaya barzuk'! na shiga uku Dan Allah kada ai mun haka kada ka Bata dama barzuk". Ta fad'a tana share zufar data karyo mata lokaci D'aya. Barzuk ya K'ara shekewa da wata uwar Dariya kafin ya tsagaita yace. "To idan ba kyason haka gara ki zama jaruma kema ki Hana idonki bacci kibi duk wata hanyar daya kamata kibi wajen aiwatar da aikin naki batare da kin Bat'a aikin ba,ko Kuma kina an kamaki ba". Shakundum tace. "Barzuk duk Wani Abu da kace nayi nayi na bunne komai a B'angarena yanzu haka b'angaren Ayshan ne kawai banjeba kullum idan zanje sai na ga bayin b'angaren nata suna nan basa tab'a, matsawa ko kad'an Amma kuma barzuk nasan yadda Zanyi dasu akwai mafita ta yadda babu Wanda zai tab'a ganina bare Kuma har a zargeni kamar yadda nai a waccen Karan ma". Ta fad'a cikin k'warin gwiwar Daya shigeta lokaci D'aya.barzuk yace. "Ko kefa haka ya kamata kiyi,Dan Inaso ne kina gamawa idan kika dawo a sannan ne mu Kuma zamu cika miki aikin". Shakundum tace. "Godiya nake uban gidan su faisak". barzuk yace. "Angaisheki baragurbin masarautar zazzau" tai murmushi tace. "Sai munyi waya saurin katse wayar tai Jin kamar motsi daga cikin d'akin duk da tasan ta kulle k'ofar kafin ta shigo nan ta damk'e wayar a hannunta k'irjin ta na bugawa da sauri da sauri Sannan ta Murd'a key d'in k'ofar ta fito tana sauke numfashi kamar wacce tai gudun tsere tareda da kallon k'ofar Lokaci D'aya......



# # # #


*mutanan MRS SARAKIES =??? Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =?G?*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank


'yan Niger kuma kumin magana ta phone number na chart only.=?G?

07066508376


Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376


*'Yan Niger 07066508376


Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =???=??? mutanan arziki.





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*

*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =???)__*



PAGE3?? 0??


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =??=???=???? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >??? da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=???=??? wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire
*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire
*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire
*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =?I?+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=???=???*




*Bismillahirrahmanirrahim*


____________?&


Da k'yar shakundum ta iya d'aga k'afarta daga nan Bakin toilet d'in ta fara Takawa zuwa cikin d'akin nata a hankali fargaba da tsoron waye yake mata knocking a wannan tsohon daren kawai ke mata kai kawo a cikin zuciyarta .dai ta Dai daita kanta ta fara k'ok'arin Yi saboda yadda jikinta yake Wani Irin rawa kamar mazari jiki a Sanyaye da k'yar ta iya Bud'e Baki tace. "Waye?..." A tsorace. Safara ce Dake Bakin k'ofar tai saurin cewa k'asa k'asa . "Nice ranki Dad'e". Ta fad'a kamar wata munafuka .Take shakundum ta Sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama Jin muryar safara Dan duk d'aukarta ko Mai martaba ne Dan tasan Babu Mai zuwa mata b'angaren a wannan dare in ba Shiba, Amma Kuma ko shi d'inma Bai tab'a zuwa mata b'angare a Irin wannan lokacin ba,kawai dai abunka da Marar gaskiya shiyasa ta firgita Lokaci D'aya.d'aga murya tai tace. "Meya faru zaki zomin b'angarena a Irin wannan lokacin?..." Ta fad'a a fusace.safara tace cikin ladabi. "Ranki Dad'e sak'on da kika ce na kawo Miki k'arfe D'aya na dare saboda kada kowa ya ganni shine na kawo mikin".ta fad'a tana jiran ansar shakundum.Ajiyar zuciya shakundum ta sauke Dan shaf ta manta da maganar da sukai da safara d'azu wajen k'arfe goma na dare akan zata kawo mata Sak'o.Batace komai ba illa Bud'e k'ofar da tai tana kalle kallen Dan kada Wani ya gansu kafin ta mik'awa safara hannunta akan ta Bata . cikin girmamawa safara ta fito da Hannunta Dake cikin k'aton hijab d'in data Saka ta fito da abun data kawo matan ta mik'a mata Wani Abu Wanda ni kaina bansan menene ba ke d'aure acikin Leda an nannad'e shi da kusan linki biyar na Leda wanda yasha Nad'i bana wasa ba.karb'a shakundum tai tai k'asa da murya tana kallan safara tace. "Kin tabbata Babu Wanda yaga fito warki?. Tafad'a da sigar gargad'i.Jin Jina mata kai safara tai kafin tace cikin k'asa da murya. "Eh! Babu kowa ranki Dad'e". Sha kundum ta Jin jina kai kafin tace. "Shikenan jeki".daga haka tai saurin kulle k'ofar ta koma ciki.barin bakin k'ofar safara tai tana kalle kalle itama ta bar b'angaren gabad'aya ta koma nasu...Koda wasa shakundum batai gigin Bud'e wannan abu da safara ta kawo mata ba, iyaka kawai tsayawa tai a tsakiyar d'akin ta zuba masa ido tana kallansa Bata ko kiftawa tana sakin murmushi lokacin D'aya ga Wani Irin farin ciki na shigarta tana ganin kamar tana gab da Samun nasarsa ta ne. jujjuya shi ta fara yi a hannunta kafin ta K'ara sakin Wani shu'umin murmushin tana Ganin burinta na gab da cika .Sauke numfashi tai tareda takawa a hankali ta k'arasa inda duk take aje kayan k'ulle k'ullenta irin wannan tai masa mazauni Mai kyau Wanda Babu Wanda ya isa ya Gano inda yake inba ita data ajiye ba.barin wurin tai ta Koma saman gadonta ta kwanta tana lumshe ido.koda ta kwanta d'in ba bawai baccin tai ba duniyar tunani kawai ta fad'a tana tsare tsaren yadda zata samu mafitar samun gudanar da aikinta yadda zai tafi successful batareda an samu wata matsala ba haka ta dinga sak'awa da kwancewa Wanda da k'yar bacci b'arawo ya iya saceta a wannan dare Dan zamu iya cewa ma sai kusan asuba ta samu baccin yay awan gaba da ita........


Washe gari wajen k'arfe goma da Rabi na safe.Anty Amina ce Zauna a d'akin gimbiya Aysha tana Bata tea. Bayan gimbiya Aysha ta gama sha ta fara goge mata bakinta da duk inda ta Bat'a da tissue sannan ta d'auko maganinta ta Bata Tasha.knocking k'ofar d'akin akayi Hakan yasa Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar kafin tace.

"waye?.."


Muryar baba uwani taji tace itace Hakan yasa Anty Amina ta Bata iznin shigowa.turo k'ofar baba uwani tai tashigo d'akin hannunta rik'e da Wani kullin magani a farar leda ta k'arasa inda anty Amina take tana kallanta tai murmushi ganin yadda anty Amina ta zubawa hannun nata Ido.tun kafin Anty Amina tai magana baba uwani tace. "Ranki Dad'e Mai babban d'aki ce tace idan za'a yiwa fulani wanka mudinga d'iba kad'an kad'an muna zuba wannan maganin a cikin ruwan wankan". Ta fad'a tana kallan yanayin Anty Amina. "Anty Amina ta sauke numfashi kafin ta Kalli baba uwani tace. "to shi wannan d'in maganin meye?. Baba uwani tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login