Showing 39001 words to 42000 words out of 42552 words
kasance yaranta uku jal, ita kuma amaryar take da yara hud'u, maza biyu mata biyu, yayin da na uwar gidan suka kasance mata biyu sai namiji d'aya.
A yaran uwar gidan akwai Rayyan Rayyan Muhammad RM² da ya kasance shi ne Babba kuma M
ahaifin nasu sai ya yi ma kansa takwara, sai kuma 'yar uwansa mai bi masa Layan sunanta kuma ita ce mahaifiya ga jaruminmu Ryan wato Aaron Nikolai Denzel.
Sai mun ci gaba da tsunduma cikin labarin zamu gano dukkan abin da ya k'unsa a kuma warware zare d
a abawa.
Matan Alhaji Rayyan Muhammad ana kiran uwargidan ne da Hajja Babba sai kuma amaryar 'ya'ya da jikokinta ke kiranta da Mammu.
Yaron Alhaji Rayyan Muhammad RM Barde na uku kuma shi ne Babban d'an amaryarsa wato Nuraddin Rayyan Muhammad sai kuma
ƙ
anwarsa Salaha Rayyan Muhammad da kuma Ahmad Rayyan Muhammad sai kuma Autar d'akinsu Zuwaira Rayyan Muhammad sannan sai Autar gidan gaba d'aya kuma 'yar gaban goshin Barde Family ita ce Rimas Rayyan Muhammad.
Dukkanin ahalin sun had'e kansu ne wuri d'a
ya cikin wannan had'ad'd'en ginin Mansion da yake jinsa kamar masarauta guda ne tare da iyalansu kuma kamar yadda na fad'a ne akwai sirrika da yawa baibaye da wannan ahali kuma ta cikin wannan ahalin komai ya fara duk wata k'ulla-k'ulla ta nan ta samo aini
hin asali.
Sannan wani abu mai girma game da wannan ahalin shi ne, su d'in sam koda wasa basu auren bare kuma suna da tsatstsauran hukunci akan wannan ra'ayi nasu. Abu na biyu kuma shi ne basa tab'a zama da mace d'aya, a k'aidar familyn shi ne aure mata
biyu kuma dukka su kasance 'yan ahalin.
**
Habib...
7 Year's Back
Shekaru Bakwai Baya
Lagos State, Nigeria.
Mak'ale hannayensa suke cikin aljihun slim Black trouser dake jikinsa, yayin da kunnuwansa suke sanye da earpiece, kana iya hango f
arar t-shirt d'in jikinsa sakamakon zip d'in gaban rigar sanyi ta Hoodie dake saman rigar da ya kasance ba'a zage ba, k'afafunsa rufe cikin sneakers, yayin da ya d'aura hular rigar Hoodie d'in jikinsa ya rufe lallausar gashin kansa, a hankali yake takawa c
ikin had'ad'd'en club d'in da aka zubar da dukiya wurin k'erasa, ta ko'ina 'yan mata da samari ne daga masu rawa sai kuma wad'an da suke zazzaune tare da 'yan matansu, yana taka sawayensa jike da karsashi da zafin jini irin na matashin saurayi d'an shekara
ashirin da Bakwai da yake a ganiyar k'uruciyarsa ta ko'ina ya b'ulla daga masu d'aga masa hannu sai masu k'ariso wa su cafke kasancewarsa ba b'oyayyen mutum ba cikin club d'in, 'yan mata kuwa kowacce sai k'ok'arin kai masa hari take, amma bai kula kowacc
e cikinsu ba, domin ba wacce idanunsa suka hango masa a kaf wurin sai ita, ita d'in dai, ita kad'ai yake iya hangowa cikin ayarin 'yan matan dake wurin ba kuma dan ta fisu kyau ba duk da nata kyan ba irin wanda ake gane wa bane a tashi guda wani irin sanyi
n kyau gareta wanda sai an nutsu ake iya ganesa.
Tun wancan ranar wato kwanaki biyar ke nan da ya d'aura idanunsa a kanta, a take salon bugun zuciyarsa ya sauya kuma bai sake samun nutsuwa ba sai a yau da idanun nasa suka sake arba da ita, ita d'in dai
ita da har zuwa yanzu da k'afafunsa ke jan ragamar gangar jikinsa yana k'ok'arin k'arisar da shi gareta bai san ko sunanta ba.
Tsugunne ta ke gaban wani glass table tana d'auka tare da tsince fasassun glasses d'in da wasu 'yan mata da suka fasa a wurin
bayan sun yi tatul, tana sanye cikin shiga irinta ma'aikatan wurin Black fitted top With Black tailored leggings, k'afafunta sanye da Black low-heeled shoes, bata ankara ba sakamakon aikin da take yi ta bawa nutsuwarta hakan ya sa delicate necklace d'in wu
yanta zarewa a daidai lokacin da ta mik'e ta bar wurin, hannunta d'auke da bar dustbin da ta zuba fasassun glass cup d'in.
Habib ya nisa yana mai danne zuciyarsa ganin yadda wasu samari suka bita da kallo kamar sa had'iyeta sannan ya taka ya k'arisa wur
in da ta bari ya tsugunna tare da d'aukar necklace d'in nata ya jimk'e a hannunsa daga nan kuma bai k'ara sakata a idanunsa ba sai washegari.
Kamar kullum ranar ma tana sanye cikin uniform sai dai wannan karon tana tsaye ne daga waje wurin wasu flowers ge
fe kad'an da inda ake parking cikin club d'in, a hankali take fesar da hayak'in sigarin da take zuk'a cike da kwarewa.
“Am really disappointed...”
Ta tsinkayi muryarsa daga gefen ta cikin wani irin sauti, da sauri ta juya idanunta tare da zubasu akan
sa, gabanta ya d'an fad'i ganin yadda launin idanunsa suka birkice sun koma jaja ba kamar yadda ta sansu farare k'alk'al ba kuma suke d'aukar hankalinta.
Kamar bata fahimci abin da yake nufi ba ta ce.
“For what?”
Sai ya kasa magana illa iyaka d'ag
a hannunsa da ya yi ya nuna ma ta abin da ke hannunta, wanda ganinsa bai saka ta yar ba, ganin hakan sai ta yi 'yar dariya, yayin da shi kuma ya ci gaba.
“Amma me ya sa shin baki son lafiyarki ne da kike shaya-shaye da k'ananun shekarunki?”
Bai yi ts
amannin samun amsa daga gare ta ba, amma sai ji ya yi ta ce.
“Babu wanda ya damu dani ko lafiyata a gaba d'aya rayuwata, so leave me alone wannan rayuwata ce.”
Sai ya yi d'an shiru yana dubanta kafin kuma ya nisa.
“Idan wannan ne hujjar da ta saka
kike k'ok'arin kashemini kanki ta hanyar bankawa cikinki hayak'i to please ki dakata domin daga yanzu ni na damu da ke da lafiyarki.”
Dubansa ta yi sai kuma ta jefar da tsinken da ta zuk'e tare da murjewa da k'afarta sannan ta sake dubansa.
“Baka sa
n koni wacece ba, shi ya sa zaka fad'i hakan amma da kasan koni wacece, ta kanka zakayi ba zaka tab'a rab'ar inda nake ba.”
“Okay, so tell me, who are you.”
Ya fad'a da sauri tare da bin bayanta cikin sassarfa ganin ta juya zata koma ciki.
“I'm a
witch!”
Ta bashi amsa kai tsaye domin bata da zarafin denying d'in abin da yake k'addararta, a baya ta yi kuma hakan ba abin da ya sauya.
Sak Habib ya yi idanunsa a kanta cikin tsananin shock da jin abin da ta fad'a, bai san lokacin ma da ta shige ci
ki ba ta barsa nan.
Tsawon kwanakin da suka biyo baya wannan kalma nata ita ke amsakowa tana sake k'ara yi masa amo a cikin kunnuwa, ta hanasa sukuni kuma daga ranar bai sake dawowa club d'in ba sakamakon tafiya na gaggawa da ta samesa zuwa Abuja Momman
sa ce ba lafiya, shi ya sa tafiyar tazo masa ba shiri kuma koda yaje can tunanin ta da na kalamanta basu kyale kwakwalwarsa ta huta ba sam, satinsa d'aya a can ya juyo zuwa Lagos kuma kai tsaye club d'in ya yo wurinta Kasancewar shigowar dare ya yi.
S
ai dai ko mai kama da ita bai gani ba, abin kuma ya bashi mamaki haka ya dingi zagaye amma babu ko mai kama da ita bai gani ba.
Abin haushin kuma shi ne ko sunanta bai sani ba.
Haka dai ya dinga yi ma ma'aikatan wurin kwatacenta da kyar ma ya samu su
ka gane ta daga nan suka sanar da shi ai sati guda ke nan bata zuwa aiki wurin daga baya ma sai Resignation letter ta turo musu ta bar aiki a wurin.
“Hannah”
Habib ya maimaita sunanta da yaji ma'aikacin ya fad'a.
“Ina kika shige ne, me ya faru k
ika bar aiki, ko'ina zan sameki?”
Ya sake fad'a a hankali kamar wani zai basa amsa.
Daga haka shima ya bar wurin bayan ya basu kud'ad'e da kuma card nasa akan idan ta dawo su sanar da shi.
One Week Later...
Wani irin birki yaja da sauri yana ma
i kifa kansa saman hannayensa dake kan steering wheel, a hankali ya furta.
“Yah Rabb. Habib, meke damunka ne tunani ya saka kana neman burkicewa gashi ka kad'e 'yar mutane.”
Da sauri kuma ya bud'e motar ya fito tare da k'ari sawa wurin yarinyar da ya
kad'e tana kwance da alama ma suma ta yi ga mutane har sun fara taruwa.
K'irjinsa ne ya buga da k'arfi sakamakon arba da ya yi da fuskar da bai tab'a tsamannin gani a irin yanayin ba, cikin sauri ya k'ari sa yana mai tabbatar da gaske ita d'in ce ya ka
d'e da mota.
Ai da wani irin sauri ya d'auke ta calak ya yi mota bai tsaya wata-wata ba ya nufa asibiti mafi kusa.
Cikin taimakon Allah bayan ya k'ari sa likitoci suka karb'e ta da yake ma bata sama rauni sosai ba, kawai dai ta firgita ne sai abin ya
had'e da halin da take ciki ya haddasa ma ta suma na wucin gadi.
Habib bashi ya sama nutsuwa ba har sai da ya tabbatar an mayar da ita zuwa d'akin hutu tare kuma da bayanan da likita ya masa ko barin asibitin bai yi ba har sai da ya tabbatar da ta farf
ad'o.
Tura k'ofar room d'in ya yi tare da shiga cikin nutsuwa yana furta.
“Excuse...”
Ta amsa masa da.
“Yes, come in...”
Tana d'an murmushi ta dubesa tare da furta.
“You’re my savior? Thanks for pulling me back from the edge…”
“But I’
m the one who ran you over.”
Sai ta yi d'an murmushi tare da fad'in.
“I know.”
Kallonta kawai Habib ya yi yama kasa k'ara wata maganar.
“I'm Hannah.”
Ta sake fad'a feeling despair ganin yadda ya yi d'an shiru.
“Me ya sa kika aje aikin ki
?”
Muryarsa ta ziyarci kunnuwanta ba tare da ta yi tsammanin tambayar zai yi ma ta ba, hakan ya sa ta yi saurin dubansa jin tambayar da ya yi ma ta cikin harshen English.
“I don't know.”
Kallon da ya yi ma ta ne ya sa ta yi d'an murmushin da bashi
da akak'a da nishad'i.
“Nima ban san me ya sa ba, kawai naji aikin ya fita kaina ne, shi ya sa kawai na barshi.”
Ta sake fad'a.
Bai sake cewa komai ba ya mik'e tsaye tare da d'an dubanta kad'an.
“I’d say you should probably call your family by
now, right?”
“I don't have any...”
Habib ya yi ma ta duba irin na neman k'arin bayani kafin ya furta wani abu ta sake cewa.
“Bani da kowa ni k'adai nake rayuwata.”
“Daga sama kika fad'o ke nan...,”
Ya fad'a cikin gatse kuma da Hausa.
“Ma
i kace?.”
Ta tambaya jin ya yi magana da yaren da bata iya ba duk da ta kan had'u da mutane da yawa wad'an da suke yaren.
“Cewa nayi ban yarda ba.”
Sai ta sake murmushi mai sanyi duk da bata yarda hakan d'in ya fad'a ba amma sai ta share.
Sake
tsinkayo muryarsa ta yi ya ce.
“Well dama aiki a wurare irin can had'ari ne a gareki saboda haka gwara ma da kika dena.”
Shiru ta yi bata ce komai ba.
“Take it...”
Ta fad'a yana mai mik'a ma ta necklace d'in da ta 'yar a wancan ranar.
A ha
nkali ta d'ago fararen idanunta da kwalla suka cika su tab, saura kad'an suka d'iga.
Zaro ido ta yi tana kuma sakin murmushi mai bayyana hak'ora, lokaci guda kwallar da suka cika idanunta suka d'iga, tsantsar farin ciki ya bayyana a saman fuskarta da g
anin sark'ar.
“Oh My God, gaskiya na gode, na gode, na gode sosai a ina ka samu?, oh nayi tunanin ma shikenan ta b'ata sark'ar da ita kad'ai ce nake gani na tuna da mahaifiyata.”
Da sauri ta sakko daga gadon tare da k'arisawa gabansa tana wannan maga
nganun ne cike da farin ciki yayin da take k'ok'arin k'arb'ar sark'ar, sai dai Habib ya yi hanzarin mayar da sark'ar cikin hannunsa ya damk'e.
Rau rau ta yi da idanunta tana dubansa kamar mai shirin fashe masa da kuka.
“Ka bani mana kaji please...”
“Zan baki amma sai kin amsa min...”
“Mene?”
Ta yi saurin tambaya cike da zak'uwa.
A bazata taji ya furta.
“Will You Marry Me?”
Ai sai ta daskare a wurin tana mai kallonsa da tsananin mamaki.
D'aga ma ta gira ya yi alamar ita yake jira.
“Uhm... you don’t really know me. Don’t waste your energy on someone like me, I’m not worth it.”
“Me ya sa?”
“Saboda ni d'in ba kowa ba ce.”
“Ni ban damu da sai kin kasance wata ba a hakan ma ina son ki.”
“Hmmm shin ka shirya auren wannan ya
rinyar da fyad'e aka yi wa mahaifiyarta har hakan ya zama silar zuwan ta duniya, kuma sanadin hakan 'yan uwan Mahaifiyar nata suka juya ma ta baya, a maimakon so da kulawa sai ma tsana da kuma tsangwama ne suka biyo baya, shin ka shirye auren yarinyar da m
utane ke kira da Witch akan laifin da ba nata ba?, shin mene ne laifina dan wani mara imani da k'addara ta saka ya zama sila na zuwa ta Duniya ya yi ma mahaifiyata fyad'e, mene laifina anan? Tun tasowa ta ban tab'a samun farin ciki daga wurin kowa ba fa ce
mahaifiyata yanzu kuma she's no more ta mutu ta barni a sakamakon ciwon zuciya mai tsanani, shi ya sa nima rayuwata ba ta da sauran amfani, I’m broke, dealing with pain, and stuck in darkness, do you still see her as your future wife?”
“I do.”
Wan
nan karon kallonsa ta yi jikinta sanyi qlau da jin amsar da ya bata.
“Tabbas na shirya na aureki muddun kin amince dani, domin ni bana ganinki da duk aibin da kika lissafo don kuwa k'addararki ne kuma shi bawa baya tab'a kauce wa k'addararsa...”
“Ki
yarda dani zan zama mai bada kariya a gareki da duk mai neman wulak'anta ki domin ina son ki, ina k'aunarki tun daga ganin farko kuma kishin ki...”
“Am... Amma ba addinin mu d'aya ba, haka ma yaren mu, sannan ya ya ahalinka zasu d'auki alak'ar, karfa ka
manta ni d'in nan Christian ce kuma nasan yadda 'yan Arewa basu son kiristoci...”
“Karki damu da wannan kuma ki cire batun 'yan Arewa basu son kiristoci a ranki domin ba duka ne aka taru aka zama d'aya ba, kuma karki damu da batun addini domin ba zan t
akura miki akan sai kin bi addini na ba...”
Shiru ta yi domin Habib ya gama d'aureta da jijjiyoyin jikinta.
Sai dai a zahirin gaskiya tuntuni koma a ce tun ranar da ta fara ganin Habib ta fara son sa, sai dai sanin da ta yi hanyar jirgi daban na mota
daban, haka zalika bakin rijiya ba wurin wasa yaro ba, ya sa ta kama kanta har take ganin wautar da ta yi domin ita kanta ta san sama tayima yaro nisa, duniyarsu mabanbanta ne, saboda haka bata tab'a hasaso kanta a tare da shi ba, sai dai da yake shi d'in
shi ne k'addara ta zab'a ma ta ba tare da neman shawarar ta ba.
Bata sake yi masa musu ba, kuma a washegari aka sallame ta daga asibitin da yake tun kafin mutuwar mahaifiyarta 'yan uwan mahaifiyar nata suka koresu shi ya sa kafin shigowar Habib cikin r
ayuwarta haya take a wani department tana rayuwa ita kad'ai.
Ta bawa Habib labarinta da irin gwagwarmaya da fad'i tashi da suka yi ita da mahaifiyarta kafin ta mutu duk da Rayuwar Lagos kowa harkarsa yake, ba ruwan wani da wani, kuma su kiristoci basu
cika damuwa dan ya kasance ba ta hanyar aure aka haifi d'a ba, amma suka kan kyamaci abin idan ya kasance ta hanyar fyad'e ne shi ya sa mutane da yawa suka kyamace Hannah da mahaifiyarta.
Sosai Habib ya tausaya ma ta kuma ya d'aukarwa kansa alk'awarin k
ulawa da ita tsawon rayuwa zai zama bango majingina a gareta da yardar Allah.
Habib bai nuna Hannah ga ahalinsa ba har sai da ya tabbatar tana son kuma ta shirya aurensa da gaske duk da har lokacin bata musulunta ba, kuma koda ya kai ta Abuja ga ahalins
a sosai Momma ta fahimce shi kuma taji dad'in jahadin da zai yi na auren Hannah, sannan bata kyamaci Hannah ba, ta karb'e ta hannu bibbiyu, sai dai ita kad'ai ne taso auren domin shi Alhaji Bashaar One¹ abin dai ta wurinsa ba yabo ba fallasa, haka ya karb'
i zancen bai hana Habib auren Hannah ba kamar yadda bai cusa kansa a lamarin ba, abin yaso damun Habib amma sai Momma ta nuna masa kar ya damu ta kuma yi masa nasiha sosai a matsayin ta na uwa bayan ya sanar da ita gaba d'aya labarin Hannah.
Ba'a d'auki
lokaci ba suka yi aure kuma har lokacin Hannah bata musulunta ba, sannan Habib bai nuna ma ta ya damu da hakan ba, kuma cikin ikon
Allah basu rufe shekara da aure ba Hannah ta haihu a ranar da ta haihu a ranar ta karb'i Muslunci tsabar farin ciki a lokaci
n Habib rasa inda zai sa kansa ya yi sosai ya yi murna haka ita ma Momma kuma sai a lokacin ne 'yan uwansa suka d'an saki jiki da ita dama shi Affan na hannun damanta ne, tana gama wanka Habib ya d'auki matarsa da 'yarsa suka bar k'asar, basu dawo ba har s
ai da 'yar nasu da ta ci suna Siyam ta shekara uku sannan suka dawo k'asar a lokacin ne kuma mai afkuwa ta afku basu rufe watanni biyar da dawowa ba Hannah ta rasu a sakamakon hatsarin mota, ba Habib ba hatta Momma da sauran ahali sun ji mutuwarta abin mam
aki ma har da Alhaji Bashaar One¹ haka ya nuna damuwa sosai.
Za'a iya cewa kusan sai da Habib ya jima sosai bai dawo daidai ba sakamakon mutuwar Hannah kafin daga bisani ya fawwalawa Ubangiji, ya kuma