Showing 9001 words to 12000 words out of 20656 words
abinda yake karama
hanna banda takaici.Abu daya ya gano lagonta in
har yana so tayidariya a duk halin bacin ran da
take shine yacemata haisam. Haka yake sakata a
gaba yace dolesai ta bashi labarin haisam. A koda
yaushe hanna na kirga kwanikin y
aushe bello zai
dawo dagawaje aiki saboda dashine kawai take
hira mai dadihar tayi dariya hirar ita ce hirar
haisam.. Hanna daindo ne suke surfe a yau, inna
haule ta fita unguwashine ma suka samu suna
yar hira. Duk da indo tagirmewa hanna amma
duk da haka
bata fi shekaru ashirin da shida ba a
matsayin suruka take a wajenhanna tunda matar
baban mijinta ce. Amma doletasa suka zama
kawaye. Hanna na bakace dusar,indo tana tikar
dawa a turmi. Indo ta tsagaita dadakan tace''
hanna sai dai hakuri ni harna saba daw
annan
bauta haka Allah ya rubuto mana rayuwarmu.
Hanna tayi ajiyar zuciya tace '' Allahyana barin
bawanshi a halin daya so ya ganshi.Amma duk
abubuwan da inna kemun bayadamuna irin duk
abunda muke yi mata bata ganidubi fa irin aikin
da mukeyi kamar zamu mu
tuyanzu idan tazo
cewa zatayi munyi ha'inci bata surfu ba. Ga zagin
da take yimin akan gara ni narasa yadda zanyi da
rayuwata. Indo ta ajiye tabaryatace'' ai waike
kina nufin duk abinda ake baki saniba a gidan
nan yau? Hanna ta ajiye faifan dakehannunta ta
tattara hankalinta gaba daya a wajenindo tana
jiran taji me yake faruwa. Indo tace '' ko da yake
kin tafi debo ruwa dazu da sassafe ni innahaule
tasa na shifa dakinki na miko mataakwatinan
aurenki guda biyu wadanda baki dinkakayan ciki
ba tasa almajiri ya
daukar mata wai zatakai wani
gida ajiya tunda ba.ayi mii gara ba sumabaza ki
daura lefansu ba. Daman wata uku ta daukar
miki a kawo gara gashi yanzu kin shigawata hudu
da aure . Don haka da zarar bello yadawo zata sa
ya sakeki, lefen kuma ta kaiwa watayar
inyar a
daura masa aure da wacce zata kawomata gara.
Kuma kinsan bello babu yadda zaiyiidan ta sashi
a gaba tace '' ya sake ki . Hawaye ne sur yake
zuba daga idanuwanta hanna ta mike dagudu ta
shiga daki ta tara wayan an kwasheakwatina sai
kwaya daya 'yar
karamar kaya kalauku ne ta
dinka a lefen su suka rage sai saurantsofaffain
kayanta nada gasunan a kasa an watsarmata. Sai
ta kwanta a kan gado ta fara rusar kuka hanna ta
kware wajen iya kuka dan ko gasar masuiya kuka
akaje ta duniya ina ganin ita zata zo
tadaya. Can
ba dadewwa inna haule ta dawo ta tarada indo
ce kadai take aikin abincin rana tace'' inahanna?
Indo tace'' ciwan ciki take tana daki. Taleka ta
tarar da hanna sharkaf cikin kuka sai tace.'' babu
wani ciwan ciki ba ciwan cikiba ko ciwannakuda
ki
ke kin bar gidan nan bazan iya ba harkartalauci
anyi biki ko gara babu lefan dana dauke neshine
yasa bakin ciki ya kwantar dake. Haka hannata
yini cur a kwance babu ci babu sha sai kukaAllah
cikin ikonsa sai ya jeho mata Bello da yamma
kwanansa biyu ral da
tafiya ba zato ba
tsammanihanna taji sallamansa ya shigo, furgigit
tayi ta tashizaune kallo daya yayi mata yasan
akwai abindaaka yi mata har tasha kuka. Yaje da
sauri ya zaunaa kusa da ita ya jawota jikinsa ya
tambayeta mekedamunta take kuka. Ta amsa
masa
da ba komai . Ya ce yasan dole da wani
abu kar ta boye masa ta fadamasa gaskiya, sai
tace cikin tane ke ciwo, yayi shirushi dai ya jita ne
kawai amma bai gamsu ba. Sai canaka jima
hankalinsa yakai wajen akwatina yagabasa nan
yace hanna ina akwatinanki suk
e? Tayishiru can
tace inna ta kwashe takai ajiya wai tunda
ba'yimin gara ba wata zata kaiwa ta aura maka
itani ka sakeni. Sai ta rushe da kuka. Bello ya cije
bakidon tsananin bakin ciki yayi shiru ya kasa
maganasai yasa hannu yana goge mata hawaye
ya nisay
ace. Daina kuka kece baki sani ba na baw
ahmedkudin da zai saya mika gata kakaf yanzu
ma cikon kudin da zai karasa sayyar na kawo
masa. Damanyanzu zan koma wajen aiki tunda
ina da aikin dare.Daman inna bata ganni ba ance
tana makwabtabari inyi sauri in taf
i baza ta san
nazo garin bamaballe tayi min maganar sai ince
Ahmed suyi kokarisu kawo garar gobe kinga an
kashe bakinta kafin in dawo. Ya rungumeta
hanna ya sambacikumatunta yace '' bazan sake
kiba hanna ina sonkida yawa ki kwantar da
hankalinki kinji ko,
sannanya fice yana sauri ya
tafi. Hanna ta bishi da kalloyayin da zuciya kece
mata'' ba haisam kadai ba bello madu ma
maisonki ne hanna ki kaunace shi.'' haka kuwa
akayiwashe gari da misalin karfe uku na yamma
saihanna taji an doso cikin gidan kamar a
mafa
rkitaga kartan maza suna ta ajiye
buhunhuna a kofar dakin inna haule . Mata suna
ta shigowa dafantekun alkaki, nakiya dibulan da
sauransu.Wannan al.amari ya bawa inna haule
mamaki,nauyi da kunya saboda sunyi mata ba
zata duk tabigari tana fadin ba.ayiwa ha
nna gara
ba kuma bazasu iya yiba kwatsam sai ga gara
wacce ko 'yayan attajiran garin ba'a taba yi musu
gara mai yawanbuhunhunan haka ba. Nan dai
inna haule ta haufara.ar borin kunya tana cewa
ashe kuna tafe ku kaki sanar min nima in gayyato
yan uwana suxo
sutayani karbar irin wannan abin
alhairi sannunku dazuwa ku shigo daki mana ya
zaku zauna a waje. Hanna dibo tabarminki dana
indo a shinfida baki.Ai da kun sanarmin zaku zo
da nasa anyi mukugirke girke da soye soye irin
wannan abin arzikihaka'' yan uwan ha
nna suka
ce'' babu komai ai bazama muka zo yi ba mun
kawo gara gata nan,zamu koma don yarmu ta
sami salama a zamanta na aure da mijinta''
suma suka yaba mata ba dadi.Washe gari inna
haule da sassafe taje ta debowahanna
akwatinanta ta kawo mata amma ankwash
e wasu
kayan da yawa babu ta kumagargadi hanna kada
ta sake ta fadawa danginta komijinta tayi shiru da
bakinta. Da bello madu ya dawo faran faran inna
haule ta kira shi ta nunamasa gara har tana
cewa'' allah sarki ashe bakaramin shiri suke yiba
shi yasa ba
su kawo dawuri ba irin wannan yawan
gara sai kace yarsarkin noma ka auro '' bello yayi
dariya ya ce'' Allahya sanya alheri ya bamu
zaman lafiya'' ya nufi dakin hanna, bayan tayi
masa sannu da zuwa ta kawomasa abinci da
ruwa yasha sai ya jawo akwatinanya bu
de kamar
yadda ya zarga tabbas mahaifiyarsazata kwashe
wasu kayan haka kuwa ya gani takwashe kaya da
yawa. Ya waiga ya kalli hanna saita sunkuyar da
kanta kasa bata ce masa komai ba...
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
GANGARJIKINSA NA AURA 2
Part 2
Posted by ANaM Dorayi on 03:14 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
Yace '' hanna an kwashe miki lefenki ko?
Kiyihakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan
muka yialbashi wani watan'' hanna ta dago cikin
ladabi datattausar murya tace'' ni na y
afe duniya
da lahira basai ka biyani ba wahalar zata yi maka
yawa. Kawubello babu abinda zance maka sai
godiya da wannan gara daka yimin Allah ya saka
da alheridomin ka kwatar min yancina tun daga
ranar daaka kawo inna bata sake yimin gori ba.
Yanzu zanyiz
aman farin ciki a gidan aurena: yayai
murmushiyace'' farin cikin ki shine nawa Hanna,
Allah ya karasanya ki a farin ciki fiye dana yanzu''
tace amin na gode. Karshen wata nayi da bello ya
dau albashi saida ya sisiyawa hanna kayayyakinta
damahaifiyarsa ta k
washe cikin dare ya
kawowahanna a boye yace ai hakkintane dole ya
biya ta.Hanna tayi godiya ta karba haka hanna
da bellosuka kasance yana kyautata mata a boye
komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya
suyo mata dadaddare ya shigo mata dashi ya
bata a boy
e ba taredaya bari mahaifiyarsa ta gani
ba. Bello yana karason hanna saboda ladabinta
hankali da nutsuwada uwa uba tsananin
hakurinta da tawakkali itakuwa hanna har yau
har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin
haisam ta mayar da bello zuciyarta.Idan bacci
t
ake yi tana kwance da bello ammamafarkin
haisam take. Idan tunani take yi haisamkawai
take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin tamayar
da soyayyar da take yiwa haisam kan bellosaboda
ita ma ta saka masa da soyayyar, sabida irin
kyautata mata da yake amma abu
ya faskara
hakadai take dagewa tana nunawa bello tana
sonsawanda a zuciyarta ba haka bane. Wasu
lokuta dayawa idan suka tashi da safe. Bello
yakan ce matayaya haisam? Don jiya kina kiransa
a mafarki.Hakika hanna duk sanda ta kwanta
mafarkin haisam take yi
ashe har ambatonsa
take a fili.Saboda tsananin son da bello yake yi
mata ya yardaya amince kuma zai zauna da ita a
haka. Bai tabanuna mata bacin ransa ba. Ita
kuma hanna sai tajitausayinsa ya kama ta nauyi
da kunyarsa talullubeta. Amma yaya zata yi
tunda
GANGAR JIKINTA YA AURA ZUCIYARTA na
wajen haisam.Matsalar gara ta wuce tsakaninta
da surukarta saikuma matsalar da inna haule ta
dakko ta dorawahanna ita ce har yanzu hanna ko
batan wata batayiba balle ta samu ciki fada da
gori a wajen innahaule babu dare
babu rana.
Bello yayi kokari ya wayar mata dakai akan cewa
ba laifin hanna baneciki Allah ke badawa amma
abu yaci tura inna hauletaki ta saurarawa hanna
cewa take ga sa'anninaurenta nan dukka ciki
garesu wata bakwaibakwai tunda yanzu watan
hanna bakwai da
aure.Yau hanna tun karfe biyun
dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari
idanuwanta. Duk budeidon da bello zayyi sai yaga
hanna tana fita ko tanashigowa cikin dakin
kaman a mafarki yake ganinta. Can yaji ana
kiraye kirayen sallar asuba tayi. Yasahan
nu ta
laluba gefensa yaji hann bata nan. Yayifirgigit ya
tashi ya fito tsakar gida ya hango hanna a gaban
murhu tana hura wuta ya karasa inda takeyace.'
Hanna yau lafiyarkikalau kuwa tun dare kike
shige da fice kinki kikwanta yanxu da asubar nan
wutar me k
ikehurawa? Hanna ta danyi murmushi
tace'' kawu kamanta yau da duku duku oganka
yace zai aiko damota za kuje Agadas shine nake
dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi
sanyi''Yayi murmushiya ce'' Ai jinsa nayi kawai
meye abun turo mota daduku duku sai
kace
zamubar kasar'' Hanna tace''Agadas ai da nisa
shi yasa kuma wata kila bakwana zakuyiba ko ?
Yace' Gaskiya agadas da nisaba kuma cikin garin
zamu shiga ba local government zamu je ina
ganin wajen 450 Km nekuma bana jin zamu
kwana ziyarar aiki zai kaimu
can mu kuma yan
rakiya'' Hanna tace '' Allah ya kaiku lafiya ya
dawo daku lafiya. Ina jin kiran assalatukafin
ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin yin Sallah ?Ta
mika masa buta ta durkusa har kasa. Bello ya
tsaya yana kallonta kawai saboda wata
tsantsarsoya
yyarta ce take kara sarke masa
zuciya.Musamman wannan kulawa da ladabi da
Hannatake masa, ya karbi butar ya shiga
bandaki, kafinya idar da sallar Hanna ta hada
masa ruwa wanka .Ya tashi ya shiga wanka. Kafin
ya fito ta debo wankakkaun kayansa data wanke
ta
goge masa tadora akan gado ta goge masa
takalmin da zai sakamar yadda tasaba masa
kullum. Bayan yakammala yana goge gogensa da
yan shafe shafesai ya dauko kayan da Hanna ta
fitar masa ya saka.Tazo tana balle masa maballin
wuyan rigarsa. Yayi murmushi yace
'' Hanna na
gode da irin wannahidima da kulawa da kike
nunamin wannan yasaina kara sonki dari bisa
dari, idan akwai soyyya datafi dari bisa dari ina
miki Hanna sai dai ni anyakuwa na sami kwaya
dayan nan kacal da nake so asanmin a cikin darin
da ake yiwa h
aisam ?Cikin kunya hanna tace''
Haba daya kacal ai kafiguda daya'' yace '' a.a
zancen gaskiya muke, nawaaka karamin ? Tayi
dariya tace'' kawu ka wucegoma ma zaka kai sha
biyar'' su duka suka tuntsireda dariya. Yace '' to
tunda a wata bakwai na samigoma sha
biyar nan
da shekara bakwai zan iya tadda haisam'' suka
sake tuntsirewa da dariya.Muryar inna haule ce
ta katse musu dariyar da sukeyi tana bakin kofar
dakinsu tana cewa'' tun dazumagana nake muku
baku jini ba kun shige dakikuna tuntsira dariya
da duku du
kun safiyar nan tomotar ofishinku ce
tazo suna ta kwankwasa gida . Daman Hanna
abinda kika sani kenan ki shiga dakida miji kina
dariya aikin kenan ciki fal kashi, babugurbin
kwanciyar Da sai gurbin tarin kashi'' Hannatayi
kasake yayi sanyi fara.ar da take
yi ta koma
cikiranta ya baci damin da ana siyar da ciki da ta
suyohaka kuma da a wani waje ake nemoshi da
taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu
ne. Ko tahuta da zagin da gorin da ake yi mata.
Bello yayiajiyar zuciya yace'' inna gani nan zuwa
shiryawa
nake'' ta wuce ta tafi tana tsaki tana
cewa'' Kaje kadawo dai daga tafiyar kazo mu
zauna muyimaganar saboda bazai yuba, in zuba
muku ido haka kawai aure wata bakwai kenan
babu ciki baalamarsa kaina da kafafuwana
turawa yarinyaabinci nake sai dai taci tayi
kashi
kawai. Ai ba dantazo ta cika mana shadda muka
aurota ba mumamuna so muga dan jariri a
gidanmu. Tunda tashanye ka ta asurce ka baka
ganin lefinta to ni bata asurceni ba dole ka karo
aure idan ma baza kasake taba, kai dole ma ka
sake ta ka auro maihaih
uwa don daki daya
garemu a gidan nan'' Harinna haule tayi nisa ta
juyo ta dawo ta tsaya a kofardakinsu Hanna tace''
Hanna kiyi ki fito daga dakinnan yau duk ke zaki
yi aikin gidan nan shara wanke wanke surfe da
girki ki fara debo ruwatukunna idan kin cika
randunan gidan kakaf sai kifara aikin gida da
yamma kuma kije gona ki tsinkowake da gyada
dan sun nuna. Yau wacce kukeaikin tare indo
aikenta zanyi magarya wajenkawata. Tunda ba
ciki garekiba ba goyo ba ai wannan aikin bazai
gagarekiba, sai dai idan kinjik
ashi sai kiyi a gonar
tunda cikinki sai kashi babuhaihuwa. Kinga kuwa
kashin naki ya zamar mintaki a gonar kinga kin
taimaka kema'' Bello maduya fisata baisan sanda
yace'' Haba inna ki dainayiwa hanna gorin
haihuwa ba laifinta bane rashin haihuwa Allah ne
yake bayarwa inna dama haryanzu Hanna ce take
debo ruwa a rafi ina almajiriindana dauko aiki
nace zan dinga biyansa. Ita taji daaikin gidan su
kuna almajiran suje gonar. Hannatasa hannu ta
toshe masa baki tace '' yi shiru karkasa taji
haushina, mahaifiyark
a ce babu komai duk zanyi
aikin. Inna Haule ta rike baki tace'' inyedannan
ka fara fada in fada dani akan matarkalallai abun
babba ne jeka ka dawo ka sameni donwallahi ina
ganin zamanka ya kare da wannanyarinyar mai
kama da tumatir ina ganin rabaka takesot
ayi da
kowa a duniya har dani dana haifeka . Ba'a
haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Tatafi
tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana
zubashar daga idon Hanna. Bello yasa hannu ya
gogemata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta
ammayafi jin tausayin ka
nsa da kansa. Saboda
zaifi hannashiga wani hali,idanmahaifiyarsa tasa
ya saketa don shine yafi sontafiye da yadda take
sinsa idan ya rabu da hanna yarabu da farin cikin
rayuwarsa. Kalma daya ce yasanidan yafadawa
Hanna duk irin bacin ran da takezata yi dar
iya
idan ya ambaci sunan Haisam . Yayi dan
murmushi ya kalleta yace'' Hanna dama ace
ayanzu kina da ciki ki haifanmun da namiji in
sakamasa suna haisam. Hanna ta dago ta
dubeshiidanuwanta a cike da hawaye sunyi jawur
donkuka amma saida murmushi ya subuce m
ata
a taketaji zuciyarta ta fara dan hucewa daga
tsananin tafasar da take yi saboda kunar
maganganun dainna Haule ta fada mata. Hanna
taji wani dan sanyi aranta wani abu ya dasu a
zuciyarta da bello yace ''dama ace ana da ciki ta
haifi da namiji ya saka ma
sasuna Haisam taji
dama ace hakan faru mana. Ammadata tuna
yanxu ma haka al'ada take don haka zancen ciki
ma babu shi sai ta sake rushewa dakuka. Bello
ya jawota ya rungumeta akirjinsa yanashafa
lallausan gashinta yace'' Hanna lallai yauranki ya
baci sosai
har in kira miki Haisam ammakici gaba
da kuka kiyi hakuri ki yafewa innata mucigaba da
yi mata addu'a Allah yasa ta gane gaskiya Allah
ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannatayiajiyar
zuciya tace amin'' amma ka tayani addu'aAllah ya
bani ciki kafin karshe
n watan nan inaganin haka
zai saka soyayyata a zuciyar inna. Belloyace amin
ya Allah, zan dukufa da addu'a kema kiyiAllah ya
amsa mana. Ya goge matahawayen idanuwanta
ya sumbaci kumtunta yace'' Haisamsunan danmu
fa. Hanna ta kyalkyale da dariya tarufe ido
sai taji
wani farin ciki ya lullubeta. Tatsugunna ta jawo
takalminsa ta fara saka masa akafa tana sake
goge masa da tsumma. Ta feshemasa jikinsa da
turare tace'' Kawu bello Allah ya kiyaye hanya
kuje lafiya ku dawo lafiya. Yace aminHanna Allah
yasa nazo na
sameki lafiya cikin farinciki'' yana
tafiya yana waiwayan hanna, itama ta fitohar
bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masahannu
har ya shiga dakin mahaifiyarsa sannanhanna ta
koma daki. A zaune a gefen gado Bello ya iske
mahaifiyarsa tana tunani tana gay
da kai
yadurkusa ya gaisheta ta amsa a fusace ta fara
masfada tace'' to dannan abunda nake so dakai
shinekarka yadda kayimin musu akan duk
hukuncindana yanke akanka ina nemar maka
aure a gidandagacin garinnan yar sarauta ka dace
ka aura tubda ka makalewa H
anna baza ka iya
sakinta bato ta zauna anan gidan tare dani ita
kuma waccamidan anyi aure sai a kaita gidan ka.
Bello ya dagakai ya kalleta zuciyarsa cike da bakin
ciki.Gidan da yasha magiya ta yarda akai Hanna
takiyau gata da bakinta tana cewa yayi aure
y
akaimatarsa can amma banda Hanna ba. To
ashe hannadin ta tsana kawai . Ya nisa yace inna
me zai hanamu tare mu duka da amarya da
hanna duk inhadasu acan din'' Ta girgiza kaia
tace '' nace maka karka yimin musu ko? Haka
naga dama, tashi kajeka dawo din mu k
arasa