Showing 24001 words to 27000 words out of 146191 words

Chapter 9 - KYALKYALIN KAUNA BOOK2 COMPLETE

M shakur   

23 Oct 2026

321

bata karashe maganan ba luuuu kawai ta zube itama Nanah haka dasauri yakira Wike yace  Oga operation successful gamu nan mun dauki hanyar palace dasauri yace  muma yanzun nan zamuyi grabbing babban.
Wannan kenan.


Wani kalan shan gaban Keken Van din yayi saida keken yaci bala in burki dudda haka saida suka daki van din.  Subhanallahi Yasmeen dake cikin keken tai ihu daidai Wike yabude gaban motan yafito yace  kasha wiwi ne baka ganin gabanka shima azuciye Mai keken yafito yace  kaine kasha wiwi dan kaine baka ganin gabanka Yasmeen zaro idanu kawai take ita kadai acikin keke tana kallonsu, dayan mutumin dake tareda Wike ne yasauko daga motan yana kallon mai Keken da Wike yace  dan Allah kuyakuri bari na duba passenger ko taji ciwo yabar mai keke da Wike na chachan baki, baya yaje inda Yasmeen ke zaune kallo daya tamai tasauke kanta kasa tana kara kankame jakan school nata ahankali yace  sannu baiwan Allah kinji ciwo ne girgizamai kai Yasmeen tayi batare data kalleshi ba, dan jujjuyawa yayi ganin babu mutane wajen yasa yakai hannu aljihun shi yazaro wani handky yace  to ga handky kishare fuskanki kinata zufa yay kaman zai bata hanky hakan yasa Yasmeen tadago kanta danna mata hanky yayi ahanci tana mitsi mitsi yana kokarin magana da ihu hango haka yasa Wike yawani fizgo mai keken ya matseshi jikin mota yaciro bindiga yadannamai aciki yace  kawai ka tsaya ahaka kona harbeka wacce ka dauko nake bukata bakaiba zaro idanu mai keken yayi fitsari na gangaromai jin bindiga acikinshi, Wike yajuyo yana kallon keken daidai Yasmeen takarasa passing out, chak Guy din yadauketa yafito da ita Mai keken na kallonsu van din yabude yasata aciki sanna yarufe yazaga da gudu yadhiga gaba yace  come on Wike wani kalan wurga mai keken Wike yayi bayan ya fizge key keken sannan yashiga mota sukaja motan da mugun gudu sukabar wajen.

('KYALKYALIN KAUNA('




'
EPISODE 1?? 2??

Maryam Eygpt abaya gidane na abayoyi daban daban na Egypt da sauransu, tana bada sari tana saida daidai abayanta are damn affordable, click on this link and join her group.
 Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj





Yana zaune kishingide acikin office dinshi ya lumshe idanu kaman wanda ke bacci akai knocking, batare daya bude idanunshi ba hannunshi ya mika ya danna wata botur hakan yasa aka bude kofan office din aka shigo, anatse Dan ya maida kofan yarufe yajuyo yataho zuwa gaban table din, cikeda girmamawa yace  Sir Wike yakawo girls din shiru yayi still idanunshi a lumshe batare dayay motsi ba, kusan 2min yayi ahaka sannan yabude idanunshi ahankali sundanyi ja kadan ya zubasu akan Dan, sauke kanshi Dan yayi kasa, ahankali yace  kayi abinda nace kama dakin? Gyadamai kai Dan yayi yace  yes sir tashi yayi ahankali dagakan kujeran yadauki kwalin tabanshi dake kan table yazaro daya yasa abaki yadauki lighter ya kunna sannan yafara tafiya kadan kadan yana busan taban yatafi zuwa wajen babban window dake dakin dakenan da wasu hadaddun plain design milk curtains, wani dan remote dake gefen labulen dake makale a bango yakai hannu yataba hakan yasa window yabude, garden ne lafiyayye abayan window da flowers but daga window kana iya hango wani separate building again wanda yakenan ta bayan gidan, ga yaran Wike tsaye gaban flat din rike da bindigogi suna gadi, taban yakai bakinshi ya zuka ya busar idanunshi kyar akan building din kaman mai tunanin wani abu, hannunshi daya yakai yatura a aljihun wando dayan hannun kuma rikeda karan taba yana zuka yana kallon building din chan yace  take that phone kamini snapping nasu all 3 together dasauri Dan yace  sir the girls are unconscious batare daya juyoba yace  that s how I want the pics dasauri Dan yace  yes sir yawuce gaban table din wannan special phone din daya kira Baba dashi yadauka yawuce yafita daga office din, Maheer na tsaye yana shan taban yana kallon Dan yawuce yaje building din yashiga ciki ko 1min baiyiba acikin dakin ba yafito duk Maheer na kallonshi ta window yadawo, kai tsaye wannan karan yashigo office din har inda Maheer yake tsaye gaban window yazo yamikamai wayan yace  gashinan nayi hotunan ko juyowa baiyiba balle yayi alamun karban wayan saida yakarashe shanye taban tass sannan yamikamai hannu batare daya juyoba, samai wayan yayi a hannu hakan yasa yadawo da wayan gabanshi ya danna screen din tai haske saiga Yasmeen, Farida dakuma Nanah, dukansu zazzaune akan wasu kujeru irin na kulle mutanen nan, kujerun nada belt tawajen hannu da wajen kafafu duk an kulle hannuwansu da kafaffuwansu da belt, dukansu idanunsu lumshe suna bacci kansu ya lankwashe babu wacce tamasan inda kanta yake, kusan 1min yabata yana kallon hoton sannan yasa fingers dinshi yashiga scrolling yana kallon 5 different pics da Dan ya dauka nasu checking and rechecking dan tabbatar babu wani abu dazai incriminating ko sanar da komi game da inda suke, sannan yajuya ahankali yakoma kan kujeranshi hoto daya ya zaba cikin hotunan yay sending nashi as MMS ma CP tareda kashe wayan dip sannan ya ijiye agogon hannunshi ya kalla yace  today is Friday yeah ? Dasauri Dan yace  yes Sir tashi yayi yadauki wayanshi kadai dagakan table din yawuce batare daya jira Dan yabudemai kofa ba yabude da kanshi yafice yawuce sama dakinshi yashiga lafiyayyen wanka yayi yafito ya goge jikinshi yawuce closet yana tsane kanshi wani Riga da wando yadauko na jean dark blue da farin riga yadawo ya shirya tsaf bayan yagama wankan turare, dadduma yadauka ya shimfida sai alokacin yay sallan asubahi sannan yatashi yafito Dan na falo ganinshi yasa yay wajen kofa budemai yayi yana zuwa yafice yace  take me to mosque .



Wuraren 12:30 Baba na cikin wani kurkuku da ake dukan criminals idan anaso su bada information yana kallon yanda akecin uban direban kan sunada information akan Pablo Escobar amman sai cewa suke su basu sanshi ba basuma taba ganinshi ba iya kansu dauko kaya daga lagos zuwa nan shikenan, address na border ma sunki badawa har lokacin dan kowannensu naji no matter what zasu fito, Baba dake tsaye daga ta waje yana kallon abinda ke faruwa aciki wayanshi ne na office yay karan shigowan sako, dasauri yakai hannunshi aljihun wandonshi yaciro wayan, messege yagani from no number, kawai just sako, hakanan yaji kirjinshi kawai ya buga shi kanshi baisan dalili ba, ahankali yabude message din idanunshi suka sauka kan Yasmeen, Farida da Nanah dukansu basa hayyacinsu an daddaure musu hannu da kafafu, wani kalan wawan bugawa zuciyanshi yayi baisan lokacin da wayan tafadi daga hannunshi zuwa kasa ba, hakan yasa dasauri yakira sunan Allah.  La ilaha illallah still kirjin nashi na dukan uku uku amman yadaure yaduka ahankali yadauki wayan yakara kallo gashi nan yaranshi ne tabbas dudda duk suna bacci basa hayyacinsu, ga Nanah da Uniform, Farida ma sanye da uniform na school nasu, dasauri yajuya yafita daga dakin yaciro dayan wayanshi yashiga dialing number Ammi yana tafiya da sauri da sauri kaman mahaukaci, ringing daya biyu Ammi ta daga kafin tama gamamai sallama yace  Nanah taje school yau ne ? Ammi fushi takedashi sosai but jin yanayin muryanshi yasa tace  eh taje meya faru ? Shiru yayi yakasa magana saikuma ya katse wayan da sauri tunawa da yanada number principal din school nasu dasauri yanemo number ta yayi dialing, wayan na gab da katsewa tadauka tace  yallabai congratulations naga karin girman da aka maka, nasan hala kana kirane dan kaji ko su dawo an gama musu interview ko, Farida zata iya dawowa ita sai 3:30 dama, Nana ko kawai kawuce da ita gida Baba ji yayi magana na neman gagaranshi ga Ammi sai kira take yana shigowa as call waiting, da kyar Baba ya tattaro natsuwa shi yace  ban gane abinda kike fadi ba, ina sukaje Farida da Nanah? Baki principal tasaki tace  a a, dazun nan ba ka aiko wani dan sandaba yasa Uniform sunanshi Aliyu SS nagani a tag nashi wai kace yazo ya kawo maka Farida da Nanah station za amusu interview, namaso nakira ka yace kana meeting Baba ji yayi kaman iska na dibanshi Aliyu natare dashi a station tun jiya har yanzu, yanzu da gaske an dauke yaranshi, katse wayan yayi dasauri daidai wayan Ammi nasake shigowa hakan yasa yadauka yakai wayan kunnenshi yay shiru yakasa magana, anatse Mama tace  Baban Nanah meke faruwa wai? My mind is telling me something, tun safe yau natashi gabana sai faduwa yake yanzu kuma yadadu meke faruwa? Kasa magana Baba yayi saida Ammi tamai ihu.  Baban Nanah! Firgigit ya farka daga nisan tunanin dayayi ahankali yace  don t worry I will handle everything gani nan zuwa baijira mezata ce ba ya katse wayan daidai Aliyu na fitowa duk yay zufa ganin Baba shikadai tsaye a filin station din rana na dukanshi zufa na ketomai yasa yay wajenshi da sauri yace  Yallabai lafiya ka tsaya kai daya arana haka juyowa yayi yakalli Aliyu, kafin anatse yace  come with me .
('SPARKLES OF AFFECTION ('




'

EPISODE 1?? 3??


KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;
wa.me/+2347012181461


Office din IG suka wuce wannan karan baima jira secretary yabashi izinin shiga ba Baba ko kallonshi baiyiba yatura kofan kawai yabude yashiga cikin office din, IG natare da mutane but ayanda yaga fuskan Baba yasa yasallamesu yakalli Baba yace  CP lafiya kuwa? Why are you looking somehow ? Karasowa Baba yayi gabanshi ahankali yamikama IG wayan cikin wani kalan yanayi yace  y ay ana Oga dasauri IG yaduba hoton yace  Innalillahi wa innailaihi raji un, ya kwashe maka yara ? Dasauri Aliyu yataho leka hoton yayi sanan yakalli Baba, anatse IG yakalli Aliyu yace  daukomai ruwa daga fridge dina yasha dasauri Aliyu yay wajen fridge dake office din yabude goran ruwa yadauka karami mai sanyi yakawo ma Baba tareda bude marfin, karba Baba yayi saida ya tada ruwan duka sannan ya ijiye goran, anatse IG yace  calm down gyadamai kai kawai Baba yayi yay shiru shi kadai yasan yanda yakeji, IG yakalli Aliyu yace  yanzu a ina kuke any progress ? Anatse Aliyu yace  babu so far so good su karan kansu basusan waye Pablo ba i believe them, ire iren mutanen nan dama kananun workers irin direbobi haka basu sansu ba, sannan basu bamu address na inda zasukai kwayoyin nan ba, shikuma Pablo yaba CP dama awa daya dazu dasukai waya kan yasaki kayanshi da yaranshi inba hakaba zai aiko mai sako, I guess wannan ne sakon ijiyan zuciya IG yasauke yakalli Baba dayay shiru kawai yana kallonsu yace  Ibrahim ahankali Baba yadago kai yakalleshi, IG yace  kai kasan I have only kyaykyawan niyya akanka, nasan cewa daka kawomini case din nan nina baka go ahead akan eh go for it, banyi kuma bantaba tunanin cewa shi wannan Pablo Escobar din kwararren criminal bane dazai iya kidnapping family naka ba sai yanzu, kalleni da kyau Ibrahim Baba yakalli IG, yace  yaranka are involve in this whole thing now, yaranka ma bawai anyhow yara ba ana maganan yara mata anan kuma kanana karaman chan ma banjin takai 5yrs ba dan haka inaso kasaki kayan nan da dirobobin nan yasakin maka yaranka kafin wani abu yazo yasamesu, tunda yanzu munsan waye Pablo Escobar din, munsan how he operate, munsan how notorious yake zamu shirya mishi da kyau kafin muce zamu kamashi ko jam iyyan shi muyi case dasu tunda yafara maganan Baba ke kallonshi baice tak ba, IG yace  your children are mine, I can t imagine wani kasurgumin dan ta adda ya sacemini kananun yarana yammata ko aure basuyi ba kasan risk na hakan kuwa Ibrahim? Kasan me this abun nan will do to their future idan duniya tasan Pablo Escobar ya kwashe maka yara, babu wanda zaiso yahada zuri a da matan da Pablo Escobar yay kidnapping. No no no banmaso nayi wannan tunanin nan Allah ya tsare, dama this whole operation is black operation mu kadai ne muka san dashi muka san abinmu, ko mun sakesu babu abinda zai faru ko wani abu yafaru ma you have me, da sanina akayi komi I can stand for you, kayanshi da direbobin shi yakeso kabashi ka karbi yaranka, family before everything kada kasaka rayukan the only yaran da Allah yabaka aduniya in danger in the name of kanason ka kama Pablo Escobar kanajina Ibrahim, idan baka kamashi ba an kama criminals dubu kuma duka duk kauda mugun daga doron kasa ne kusan minti daya Baba yayi yana kallon IG kafin ahankali yasauke ijiyan zuciya cikeda damuwa yace  naji yallabai amman ina neman alfarma wajenka gyadamai kai IG yayi yace  ina jinka shiru Baba yayi kaman mai tsoron abinda zai fadi kafin cikeda dakewan zuciya yace  dan Allah Yallabai kabarni nan handling this issue in my own way Dan Allah Yallabai kada kabada umurnin asaki kayan nan ko direbobin nan dakanka kabarni nayi decision din idan nagama tunani baki IG yabude yana kallon Baba kawai, sai chan yace  shikenan Ibrahim daman shawara ce nabaka duk yanda kai handling case din is fine but remember family comes first karkace ban fadamaka ba gyadamai kai Baba yayi sannan ahankali Baba yatashi yawuce yafita Aliyu yabishi abaya IG ya girgiza kai kawai Ibrahim nada taurin kai na gidi komadai menene Allah ubangiji ya karemai yaranshi.



Office Baba yakoma ya zauna ganin Ammi taki daina kira yasa ya kashe wayan gabaki daya, yakalli Aliyu yace  hoto kawai yatura mini baice wani abu game da hoton ba, na gwada kiran number da yakirani da ita dazu kaman number bata kan network ahankali Aliyu yace  Yallabai can I say something? Batare da Baba yakalli fuskanshi ba yace  you can ijiyan zuciya yasauke, ahankali yace  abinda IG yafada gaskiya ne, yallabai koda ace yau bomabomai yake sakawa akasan nan bama kayan shaye shaye ba, gaskiya da kamashi gwara ka hakura ka bashi kayanshi yasaki yaran nan cikeda masifa Baba yace  did you look at me kaman mai tsoron wani lowlife stupid drug kingpin eh? Bakasan dama wannan tsoron da shakkanshi shine dalilin dayasa ya kwashe su Yasmeen ba sabida na tsorata nasaki kayanshi da gudu, he can t do anything to them jikina yabani hakan, he s a druglord not girl trafficker, babu abinda zai sami yarana I am sure, yes yes yanda Baba ke magana kaman ya zare hakan yasa Aliyu bai kara fadin komiba, tashi Baba yayi yakwashe duka wayoyin incase Pablo yakira sannan yadauki key motanshi yace  zanje masallaci daganan zanje gida yawuce fuuu yafita.

KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;
wa.me/+2347012181461


('KYALKYALIN KAUNA('



'


EPISODE 1?? 4??




Saida yay sallan juma a wanda shidai yasan yay salla ne amman baida natsuwa sanan yashiga mota yatuko kanshi zuwa gida, duk wanda zai kalli Baba yasan ba lafiya ba, yayi dialing number da Pablo yakirashi dashi yau da safe yafi sau dari but number bayama connecting kaman babu number a network, parking yayi a kofar gida yadade zaune a motan sannan yabude mota yafito yashiga cikin gida ahankali, Ammi yagani zaune atsakar gida idanunta sun jajir kaman kuka tagamayi gasu Kaka da Hajjo akanta da duka yaran gidan harda Sa a kowa yay zuru zuru, ana ganin Baba Hajjo tace  yauwa ga Baban Nanan nan yadawo dasauri Ammi ta mike tsaye jin ance ga Baba kafin ma yakarasa idasowa wajensu tayi wajenshi dasauri tace  ina suke, su Hassana kowa yadawo daga makaranta banda Farida da Nanah, naje makarantan principal tace ka aiko a daukesu amman kuma wai kasake kiranta kaman dawani matsala, and yanzu danaga fuskanka nasan da matsalan dagaske ina suke, ina Farida da Nanah? Kallon fuskan Ammi yayi wato uwa uwace she is feeling something, jikinta yabata ba lafiya, daidai nan aka bude gate, Baffa ne dakuma Baba Karami suka shigo dan dama duk Friday bayan masallaci suna dawowa gida aci abinci kafin akara fita, ganin Baba yasa yace  Ibrahim meke faruwa Maman Sa a takirani wai ba aga su Farida ba yay maganan yana karasowa gaban Baba, fuskan Baba kadai yagani yagane da wani abu babba ma ba karami ba, ganin Baba yayi shiru har lokacin yaki magana yasa Ammi dake kallon fuskan Baba all this while takai hannayenta tadaura saman kanta saikawai tafashe da kuka sosai tace  Baban Nanah ina yarana? Kayakuri ka taimaka kafadamini inda yarana suke zanje dakaina in dauko su, jikina nafadamini they re in trouble, tunda natashi yau I ve been feeling somehow ina yarana eh, kafadamini ina yaran& &   an kwashesu! Baba yay maganan da ihu ranshi abace cikin wani kalan zafin zuciya, kowa na gidan tsayawa yayi kikam yana kallonshi babu wanda ya iya yay magana, Ammi daura duka hannayen ta tayi saman kirjinta dake wani kalan mahaukacin bugu, Baffa ne yay namijin kokarin iya magana yace  ban gane an kwashesu ba Ibrahima dan lumshe idanu Baba yayi dan yakasa jure kallon da Ammi kemai kaman wacce ta zare, kafin ahankali yabude su cikin wata kalan raunanniyan murya yakalli Yayan shi yace  Yaya akwai wani case danakeyi da wannan dan kwayan Pablo Escobar& .! Ganin kalan kallon da Ammi kemai yasa yakalli Baffa yace  Yaya na kwace motan kayanshi dasuka shigo na kwayoyi guda biyar da direbobin shi nakama shine yay kidnapping, Nanah, Farida dakuma Yasme& & . luuuuuu kawai Ammi ta tafi a asume dayasa su Hajjo tareta, azafaffe Baba ya karbeta daga hannunsu yana kiran sunanta, Baffa yace  kwantar da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login