Showing 72001 words to 75000 words out of 146191 words

Chapter 25 - KYALKYALIN KAUNA BOOK2 COMPLETE

M shakur   

23 Oct 2026

332

so sweet yanda yakeyi mantawa tayi dakomi dasauri tasa hannunta tadauki glass cup da cold pineapple juice datamai keciki tabashi batare datai magana ba tsabagen yanda yakejin zafi cup din yakarba hannunshi ya gogi nata dasauri yakai bakinshi yahausha da sauri da sauri wani kalan mugun dariya abin yabata, murmushi tayi tareda daukekai zuwa one side cikin kukkuni chan kasa tace  rago kawai  me kikace? Taji muryanshi ahankali yay maganan dasauri takalleshi suka hada ido har lips nashi sun kara pink sabida yanda tuwon ya konasu, dan hararanshi kadan tayi cikeda tsiwa tace  ni badakai nake ba dan murmushi kadan yayi yasauke cup din kasa yakalleta yace  ni kika cema rago ? Sake dauke kanta tayi cikin kunkuni tace  kunne kaman na maciji  nine maciji ? Juyowa tayi tadan kalleshi tana zaro idanu takasa magana idanunta yabi da kallo dasukaji kwallin Ammi batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace  you have the most beautiful eyes I ve ever seen in my entire life Fateema dasauri Yasmeen tasauke kanta gabanta nafaduwa yatsunta tashiga wasa dashi bata kara dago kanta ba, tass yacinye abincin ya shanye juice din tareda lumshe idanu wlh yakoshi kaman cikinshi zai fashe, wannan tuwon yamafi na rannan daya sayo dadi, she is such a talented cook, duk yawace yawacen dayayi aduniya bai tabacin abinci Mai dadin abincinta ba.
Zaro kudi yayi daga aljihunshi 20k ya ijiye a gefen tray din kafin yamike tsaye ahankali yana kallonta, yace  kicema Anty natafi dagokai tayi anoke ta kalleshi, glasses na idanunshi yamaida kan idanunshi anatse yace  by 4 kibar nan and go back home banson ki kai 5 dan juyamai idanu tayi azuciyanta tace  sannu ubana anatse yawuce yafita daga shagon adan sace tabishi da kallo kaman tace yadawo batamasan mesa ba, sai alokacin taga kudin daya ajiye dasauri tadauka duka duka abincin dayaci 7k ne wannan plenty money fa, daidai nan Maman Intee tafito ganin kudi yasa da sauri takarba tace  badai kudin abincin yabiya ba akan mene yana surukina to be turo baki Yasmeen tayi ta kwashi tray tawuce ciki abinta.
Karasa taya Maman Intee ayyukanta tayi jin ana kiran la asar haka nan maganan shi yafado mata arai, dudda tana gayama kanta bazatabi umarnin shi ba samin kanta tayi da saka hijabi tama Maman Intee sallama kan zata tafi tatafi, tana fita Keke tagani already pake agaban shagon, Mai keke yace  Hajiya kece Yasmeen ko wani bawan Allah yabiyani na ijiyeki agida yabani ledan nan kuma nabaki Keken yajuya yadauko wani cute leda mai kyau daga bayan keken yamikama Yasmeen dake tsaye tana kallonshi, ledan ta kalla takasa amsa mai keken yace  amshi mana Hajiya ahankali tasa hannu ta amsa, Mai keke yace  yauwa to shigo mutafi kalle kalle tashigayi awajen saikuma ahankali tai bismillah tashiga tariga ta sadakar ita wannan mutumin tasan ko kasheta yay niyyan yi yanzu zai iya gwara tabishi ahankali kawai surabu lpy Baba ya tsokano shi.
Saida taga hanyar da akebi aje anguwansu akabi hankalinta yadan kwanta, ahankali tabude ledan dake hannunta chocholates ne ciki dayawa irin expensive cute chocolates din nan dasauri ta maida ledan tarufe tacigaba da kallon hanya, nunamai har anguwansu tayi har kofar gidansu mai keken yakaita sai alokacin tasauke ijiyan zuciya tasauka mai keken yatada kekenshi yatafi abinshi itakuma tabude jakanta ta wurga ledan chocholate din sannan ta rataya jakanta tai sallama tashiga gidansu daidai Ammi na fitowa da kitchen rikeda kula tace  ba biyar zaki dawo ba incedai lafiya ? Murmushi ta kakalo tace  Ammi lecturer 4-5 wai bazata zo ba Gyadamata kai Ammi tayi tace  to jeki rage kayan jikinki kizo kici abinci murmushi tayi tawuce dakinsu su Farida ne kadai aciki jefar da jakanta tayi kasa tana kokarin cire hijabi chocholate din suka watso daga jakan dawani kalan sauri da Farida da Sa a suka kwasa tareda daukan jakan, Farida tahau bude chocholate zatakai baki tace  waya baki hadaddun chocholates din nan Anty Yasmeen ? Dasauri Yasmeen dabama tasan Chocolate din sun watse ba kokarin cire kaya take takallesu dawani kalan sauri ta yarda rigan nata tazo wajensu ta fizge jakanta da chocholate dake hannun Farida tazuba ajakan back tarike jakan gam tace  wayace ki budemin jaka ? Dasauri Farida tace  laaaa Ya Sa a dan Allah ba ita ta jefar da jaka ba suka zubo ? Dan dariya Sa a tayi dan ita harta karanta wata yar karaman takardan ciki tace  wlh saurayi ne yabata ai harna karanta takardan saisa dukta tsure dasauri Yasmeen takalli Sa a ahankali tace  wace takarda? Dariya Sa a tayi tace  duba jakan ki dasauri Yasmeen tabude jakan wata yar karaman takarda ne da note jiki da akayi da byro handwriting din so fine.
Take Care
MMd'?

Aka rubuta dawani kalan sauri taboye takardan abayanta daga Sa a har Farida suka kwace da dariya ganin yanda tayi tana zaro ido, Sa a tace  dalla chill bazamu fadama Baba ba mudai kibamu chocholate muci hararan Sa a tayi tace  baram bayarba zata juya Sa a ta fizge jakan tabude ta kwashi chocolate son ranta taraba biyu ta watsama Farida rabi tace  Allah sanya alheri first boyfriend din Yasmeen, her first love, nasan yanzu duk afirgice kike sabida Baba kika natsu kya bamu labarin shi ko Farida kasa magana Faridan tayi tana danne dariyanta bakinta cikeda chocholate yarda jakan kawai Yasmeen tayi tajuya tafita daga dakin dan zuwa dakin Ammi cus she s loosing her mind.

EPISODE 4?? 7??



Kusan atare dagashi har Hamad sukakai gida, Hamad yafara isowa sai shi daga baya, wucewa ciki yayi Dan biyeda shi, afalo yasami Baba da Hamad zaune suna magana, kafin ma yayi magana Baba yace  Maheer anatse Maheer yace  Na am Baba  taho nan dan juyowa Maheer yayi yakalli Dan da idanu yamai alamu yatafi sama yahuta wucewa wurin Baba yayi waje yasamu yazauna kusada Hamad yasauke kanshi kasa dan yasan maganan shi Hamad yama Baba, shiru dukansu sukayi chan Baba yace  kalleni Maheer dago kanshi ahankali Maheer yayi yakalli Baba dake da bakin glass kaman Baba yanagani yace  Maheer zan maka tambayoyi biyu kagayamin tsakaninka da Allah dan Hamad yafada mini komi daga farko zuwa karshe, baka tabamini karyaba Maheer tunda kake yaro kawowa yau dan haka ka amsani tsakaninka ga Allah Baba yadanyi shiru sai chan yace  kanaso ka auri yarinyar nan dan kaci mata mutunci ne ka wulakantata kodan ka kara tozarta mahaifinta sabida yataba kayanka??? Kaa gayamin gaskiya Maheer shiru Maheer yayi kafin chan yace  a a Baba shiru Baba yayi tun yana karami Allah yabashi baiwan gane idan mutum yana karya ajikinshi kodan sabida shi makaho ne Allah yabashi baiwan oho, cikin kwantacciyan murya Baba yace  sai tambaya tabiyu kanason yarinyar ne Maheer ? Hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi, wannan karan yakusan kai 5min yakasa amsa maganan kafin chan cikin murya mai taushin gaske tsakanin shi ga Allah dakuma zuciya daya yace  nima bansani ba Baba dan shiru Baba yayi yana kallonshi sunnar da kanshi kasa Maheer yayi kusan 10min suka bata ahaka kafin Baba yasauke ijiyan zuciya yace  tashi katafi zan kira Malam Sani yau zaije yama Baban ta magana yaneman mana izini idan ya yarda cikin satin nan zamuje sai ayi magana kutashi kutafi cute smile Maheer yasaki yatashi ahankali yawuce sama shikuma Hamad ya tsaya batare daya tashi dagakan wajen ba yana kallon Baba cikeda mamaki dan baiyi tunani Baba will accept maganan nan dawuri haka ba, dan murmushi Baba yasaki dan yasan Hamad na zaune awajen har yanzu, anatse yace  hanyar shiriya Maheer ya dauko Hamad I have to support him dudda nasan kalubale na gabanshi, akasin hakan zai iya jefashi yaje yayi wani babban kuskuren dayafi komi muni, tashi kaje soon u will understand abinda nayi dakuma abinda hukunci na ke nufi harya tashi Baba yadauki wayanshi yamikamai yace  gashi kiramini Malam Sani, idan kaje sama ka karbi address na gidan su yarinyar saika turama Malam Sani ta wayanka ijiyan zuciya Hamad yasauke yayi ma Baba dialing number sannan yawuce yatafi sama yana tunanin kiran telanshi dan dinkama Maheer manyan kaya dan bazasu neman aure yana sanye da kananun kaya ba.


As usual wuraren 6 na yamma Baba yadawo gidan saida yafara duba yaran dan yau babu islamiyya sannan yawuce daki, wanka yayi agurguje ya chanza kaya zuwa shadda yasa hula yafito dan tafiya masallaci atare suka fita da Baffa da Baba Karami dan suma sun dawo daga kasuwa.

Ana idar da salla andanyi jawabi suka fito suna gangarowa Baffa namusu magana kan kayan gonna da aka samu a gonan Baban su, wani magidancin mutum suka gani akofar gidansu tsaye jikin wata yar mota corolla tsaf tsaf dashi yaci manyan kaya harda Malum malum suna karasowa cikeda girmamawa yabasu hannu yace  Assalamu Alaykum barkanmu dai dasauri Baffa dan yafisu raha yace  barkanmu bismillah naga kaman mu kake nema ko ? Atsanake yace  kwarai kuwa nazo naganku ne gaskiya kam ni ina matsayin kaman dan aike ne, wajen Malam Ibrahim nazo

Yay magana yana kallon Baffa, Baba dashi kadaine babu wata fara a akan fuskanshi bawai kuma ko wulakanci bane no he s just a serious person, sanin halin Baba yasa dasauri Baffa yace  incedai bawata matsala bane, ga kanina nan shine Ibrahim Meya faru ? Dan dariyan dattawa mutumin yayi yace  to dafarko dai sunana Malam Sani nine babban aminin Malam Maheer Makaho wanda a gaskiya shiya aikoni nan na nemi izini wajenku anatse Baba da sai alokacin yah magana yace  izinin mene ? Ahankali yace  Kunsan dayake makaho ne baya iya fita sosai ya aikoni ne nazo na nemi izini awajenku yanaso yazo axauna ya nemawa danshi Maheer izinin neman auren diyarku Fateema wani kalan gyara tsayuwa Baba yayi dan maganan ta saukanmai kaman aradu, baki yabude zaiyi magana Baffa sanin halinshi yadagamai hannu yace  waye dan nashi a ina yasan Fateema? Sannan ita tasan shi ? Anatse Malam Sani yace  ehh to kusan zan iya cewa Fateema tasanshi amman bawai irin sannin dakuke tunani ba dan banjin wata magana ma yataba hadasu ba danshi Maheer lecturer ne a makarantan su yana koyar da English ma duka department dake makarantan, yasami Baban shi yau kan yanaso afara sanarda iyayenta idan sun bashi izini sai afara neman aurenta gaskiya banjin suntaba magana bama kusan Baba zai iya cewa ya yarda dan wayanta akai akia yake bincika wa kuma da aka dauketa wayan all through na hannunshi ba a taba kiranta daidai da 1 miss call ba anatse Baba yace  ba yanzu zan aurar d& &  tareshi Baffa yayi da sauri ta hanyar sakin ma Malam Sani murmushi yace  gobe juma a zaku iya zuwa bayan juma a dan bayan salla bama komawa kasuwa agida muke yini murmushi Malam Sani yayi yace  Masha Allah to too Allah ya zabamana abinda yafi alkhairi, bari na barku ku shiga gida to saida safenku yasake babbasu hannu suka gaisa, motanshi ya shiga yaja yabar wajen Baffa yakalli Baba da bacin rai dan dama baiwani huce sosai ba dudda Baba yabashi hakuri yace  kana kokarin gayamusu baka shirya aurar da Yasmeen ba kasan alamomin gidan mutunci kuwa ? Baffa yanuna motan mutumin daya wuce yace  gidan mutunci ne da yaron kwarai awannan zamanin zasuzo sufara tambayan izinin iyaye kafin dansu yama yima diyarka magana, kadaisan bazan taba bayarda Yasmeen banyi bincike ba kabar ganin kanka kaine dan sanda kaine ka iya bincike kasan abubuwa nafika sanin rayuwa Ibrahim, kabari gobe suzo muga yaron idan natsuwanshi yayi zamu bashi izini ya nemi Yasmeen inyaso saina hada bikinta dana Sa a dan iyayen yaron sunzo kasuwa sun samen, kuam iyayen yaron sun damen sunaso asa rana nan da wata daya kanajina badan yasoba Baba yace  eh Baffa yakalli Baba karami yace  koba hakaba anatse yace  hakan yayi Yaya, Yasmeen ta isa aure ai jinjina kai Baffa yayi jin ana kiran isha i yace  mutafi muyi isha i kawai gabadaya duk suka juya suka wuce mosque, koda suka dawo sama sama Baba yaci abincin yawuce dakinsu Yasmeen dukansu na zaune adakin harda Nana suna hira suna dariya ganin Baba yasa sukai tsit, binsu yayi da kallo one bye one sannan yasaki labulen yawuce yashiga dakinsu, direct kan kujera yayi yazauna Ammi dake zaune ganinshi haka yasa tace  lafiya Baban Nanah kanka ciwo yake ne ? Girgixa mata kai yayi baice komi ba yawuce yatafi uwarka da kawai.

Har wajajen dayan dare Baba yakasa bacci juye juye yake hakan yasa cikeda damuwa Ammi ta kunna wutan dakin takalleshi shima kallonta yayi saikuma yatashi yazauna tareda folding hannu akirji cikeda damuwa Ammi tace  wai menene Baban Nanah am getting worried? Meke troubling naka haka ka kasa bacci sai juye juye kake shiru yayi yana kallon Ammi kasa dannewa yayi yace  wani mutumi dazu yazo tambayan neman Auren Yasmeen shine Baffa yace suzo gobe wani kalan murmushi Ammi tayi da abin harsaida yasa Baba sakin baki dasauri tace  waye shi ? Cikeda dan bacin rai Baba yace  nima bansani ba sai gobe idan sunzo amman ance yaron lecturer ne a school nasu wani kalan murmushi Ammi tayi kaman anmata albishir da kujeran makka hannu ta daga sama tace  Ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kabawa Yasmeen miji mai sonta sama da yanda Baban ta ke sona dan tsaki Baba yayi kawai yakoma ya kwanta tareda juyamata baya dariya Ammi tayi da shewa tace  wlh Baffa Yamin daidai aka biyemaka bazaka taba aurar da yaran nan ba kashe wutan tayi tadawo rungume Baba tayi tace  zonan wlh saikai farin ciki daganan salon labarin ya chanza.

('KK('



'

EPISODE 4?? 8??



EPISODE 48



To Jama a anan nakawo karshen FREE EPISODES na wannan littafin nawa Mai suna KYALKYALIN KAUNA wato SPARKLES OF AFFECTION('


Wannan aure zai yu kuwa??
Yaya Baba zaiyi idan yagano Maheer shine Pablo Escobar??
Kuna ganin kafin aure ko bayan aure ne Baba zai gano gaskiya???
Hajiya zata taba barin Maheer da Yasmeen suyi zaman aure???
Hmmmm!!! Kubiyoni.

Idan kinason cigaba da karanta littafin nan all you have to do is pay ko 1k or 500 into 3107021073 Aisha Muhammad first bank.

Zakimin magana a WhatsApp wa.me/+7012181461 sainai adding naki a paid group.

Group na 1k is 2updates daily banda alhamis da juma a.

Group na 500 is 1update daily banda alhamis da juma a.

And inada EXCLUSIVE shi a Email nake musu update yanzu haka sun wuce ku is 5k.
4episode dailyd'?


Please patronize my little work, and appreciate my talent, show me support ta hanyar subscribing ki shiga paid group.


Thank you I love you alld'?

https://vm.tiktok.com/ZM2U8NPMo/
Kusan duka yaran gidan babu wanda yasan akwai wani abu dazai faru yau Baffa dai yasa Baba karami yasayo drinks harda su Maltina da ruwan gora, matan gidan kuma harda Ammi aka hau girki yaran gidan kuma duk suka tafi school, Baba sabida haushi tun 6 yatafi aiki Baffa dai saida yakirashi ya jaddadamai biyu tamai agida, Yasmeen 9 ta tafi school abinta yau har 6 takeda lectures.


Ana idar da sallan juma a Baba yadawo gida gidan an gyara yay kal kal an shimfida manya manyan tabarmai a compound kasan bishiya girgixa kai kawai yayi yawuce ciki wanka yayi ya shirya cikin babban kaya harda Malum Malum da hula ya fesa turare yafito waje daidai ana sallama Baffa ya kalleshi yace  muje mu shigo dasu baiyi musu ba suka fita atare, Hamad ne ke tuki sai Maheer agefenshi Maheer yasaka wata faran shadda jumper da hulan Hamad akai wlh kaga Mageer zaka dauka ango ne, Malam Sani da Baba sai limamun anguwan su wanda yake abokin Baba ne sosai, duk suna tsaitsaye Baba yafara fitowa daga gidan kallo daya Maheer yamai yasauke kanshi kasa sabida yanda Baba yamai wani kalan kwarjini a ido gaisawa su Baba sukayi dasu Malam Sani hakan yasa Hamad yataho tareda dan jan Maheer daya kasa motsi Malam Sani yace  surukin naku akwai bala in kunya, wannan shine yayan shi Hamad yanuna Hamad dake bama Baffa hannu Baffa yakarba cikeda murmushi yace  ina gajiya sannan yanuna Maheer da kanshi ke kasa yace  wannan shine Maheer ahankali Maheer yabama Baba dake kallonshi hannu karban hannun Baba yayi mury??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a chan kasa Maheer yace  ina yini ba yabo ba fallasa Baba yace  lpy lau tareda karbe hannunshi, Baffa yace  bismillan ku kushigo shiga ciki sukayi Ammi dasu Yaya ta window suke lekawa kaman yara dukansu are so excited Ammi tace  waye surukin nawa naga samari biyu Yaya tai pointing Maheer dake sunnar dakai tace  daga ganin mai kunyan chan shine mai neman Yasmeen wani kalan murmushi Ammi tayi tace  surukina badai kyau ba kaman bakin balarabe Masha Allah tubarkallah shewa sukayi, jin Baffa na kwala musu kira yasa duk suka saka hijaban su suka daddauki su drinks da ruwan gora suka fita dashi, anatse Baffa yace  ga iyayen Fateema nan gaggaishe su sukayi Maheer yakasa dagokai suka wuce suka koma daki sannan Baffa yace  to bismillan ku .

Gyaran murya Baba Makaho yayi yace  to godiya ya tabbata ga Allah ubangiji daya hallice mu ya raya mu sa an nan ya nuna mana wannan rana, dafarko dai sunana Alhaji Maheer Makaho, haka aka haifeni da makanta, gaskiya dana taso iyayena basu da shi ahaka ahaka dai nasamu wata makauniya irina marigayiyi mukai aure Allah yamata rasuwa yanzu atare kowa yace  Allah gafarta mata ahankali yace  Ameen sannan yace  bazan muku karyaba dalilin d ana ne nazo gidan nan yau, yarana biyu da Hamad wanda shi likita ne saikuma Maheer pharmacy yakaranta amman bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login