Showing 30001 words to 33000 words out of 52458 words
ta soma ganin bacin Ransa Jikinta na soma kyarma,
'Baxan sake Ki ba Nainah, Idan bakyasona Ki kasheni?
'Friend.... Kafin tayi magana tuni Ya juya a fusace yabar dakin, yana fitowa Ya same su suna hira cikin farinciki Harda dariya, ya dauki jakarsa Ya rataya xai fice cikin bacin rai,
Bahijja da majeed suka tashi, ya riqo sa
'yallabai me Ya faru ina xakaje yanxu?
Nainah dake daki tanajin abinda majeed Ya fada tayi saurin fitowa tana kallonsu,
'sakeni pls, xan koma gidanmu inda ake Sona aka san darajata,
'nan ma ana sonka kayi haquri pls acewar bahijja,
'umma lotee ta Matso, fuskarta da damuwa (Dan zaman da sukayi dashi ta fahimci Yanda yake son Nainah tun daga Yanda yake roqonta, ta ganshi kyakkyawa yana da mutunci, shida majeed ta lura basu da rawar kai irin na masu kudi, bataga dalilin Nainah na tsanar Shiba tunda shi yana sonta)ta riqo hannunsa fuskarta da damuwa
'tace Wannan yaro menene, Shin meyasha xakaje ka Barmu kana fushi kanaso Nima Naji ba dadi baqonmu baiji dadi ba, me Nainah yayi ma ?
Cikin muryar damuwa ya soma mgn
Umma, Nainah bata Sona, rashin qaunar da take min har yakai Nainah bata son Ganina tana cewa na kyaleta, ni kuma na kasa rabuwa da ita, na kasa jure rashin Nainah shiyasa na biyota take wulaqantani馃槳, Inma Nainah bata Sona tabani damar tabbatar mata da cewa ina sonta ina qaunarta,
Umma tace na sani ynxu na fahimci kana so yarona da kyau kana damuwa dashi shi kuma yaxo ya gayamin qarya akanka harnace xan raba aurenku, tunda kana sonta haka baxan rabaka da matarka ba kuma zan Baka daki ka xauna har Ayi Bikin bahijja, Karka damu da munafikin yarona ai naganshi Jiya baiyi barci ba, su bahijja suka soma dariya, Nainah na bakin qofa tana kallonsu, Lotee taja hannunsa takaishi wani daki, ba komai aciki sai gadon karfe irin Wannan mai rumfar sama, a qasa an malalen wurin da Tabarma ga jere irin nasu na buxayen nijar, sunyi ado da kwarya mai xane mai kyau anjera an Qawata dakin, jeren dakin har sama yayi tsawo, dakin Ya birgeshi in his life bai taba xaton akwai daki irin haka da mutane xasu iya rayuwa acikin Saba, hassalima bai taba xaton xai iya shigowa acikinsa Ballantana ya kwana aciki ba.....
Kaxauna har Ayi Biki sai ka koma da matarka ko bata so.
Yayi murmushi kawai ta juya ta fice, shima majeed tabashi nashi daki,
[9/14, 10:40 PM] Pherty 馃帳馃懐: Ganin bahijja ta dage tana gyara dakin da aka bawa majeed, itama ta dauki tsintsiya bakinta a tunxure ta nufi dakin da aka bawa Mus'ab, umma lotee na xaune tana kallonta,
Mus'ab na tsaye dakin yana kallon yanayinsa,da jakarsa a hannu fuskarsa da damuwa alamar Yanda xaiyi rayuwa a dakin yake tunani,
Jin motsin mutum ya sanya shi juyawa, tana tsaye Sanye da hijab hanunta da tsintsiya, ya tsuke fuskarsa, ya rataya jakarsa Yabi ta gefenta Ya fice batare daya sake kallonta ba, ta bisa da kallo har ya fice kafin ta soma gyaran dakin.
Ta gama ta fito Ta sami bahijja na Jan ruwa a rijiya, Mus'ab na xaune gefe da Lotee suna hira sama sama,
Majeed Ya dauki ruwan Ya shiga bayi, Mus'ab yaji yana son wanka sai ya shiga dakin da Nainah ta gyara masa ba laifi yayi haske da kyau, ya cire kayan jikinsa ya daura towel dinsa dayaxo dashi a qugunsa ya fito馃檮
Anyi sa'a ba kowa a tsakar gidan sai Nainah itama zaman jiransa take ya fito tana ganinsa Ta saki baki cike da mamaki, hade da xaro idanuwanta a waje,
Da Sauri ta taso ta tsaya gabansa tana kallonsa a fusace, sai ta koma yar ficika da ita馃憣馃徎Dan kuwa yafita nesa ba kusa ba, namijin gaske ne jiki ne dashi irin na jarumai,duk jiki a mur膹e,
Change friend you know,nan ba bathroom din gidan ku bane, Baa dakin ka kake ba, nan ba gidan ka bane, umma fa mahaifiyatace Idan taganka Ahaka fa, ka manta Anty Bahijja...... Ya xura mata ido yana kallon Yanda bakinta Ke motsi,
Sai a lokacin ya tuna bafa a gida yake ba Ya juya fuskarsa ba Walwala Ya sanyo jallabiya ya fito, bai sake kallonta ba yaje rijiya ya soma Kokowar janyo ruwa ya kasa, a rayuwarsa bai taba ba, bai san Yanda ake a janyo ruwa ba,
Kusan minti biyar ya dauka ya rasa ta Yanda xai dibo ruwan Nainah na daga gefe tana kallonsa tana dariya, kafin taje kusa dashi
'let me help you friend, a fusace yace
'leave me alone Nainah?
'please friend, baxaka iyaba then allow me....ya katseta
'Ki kyaleni, Kince na kyaleki ina ruwanki da nine?
'Am sorry Friend let's bygones be bygones, ya sakarmata harara kana Ya fisge abin 膹iban ruwan Ya maida rijiya馃槀,umma lotee dake kallonsu tuntuni taxo ta Karba ta 膹ibo masa tana rarrashinsa akan Nainah, tasa Nainah ta kai masa bayi kana ta dawo ta sami guri ta xauna a sanyaye, bataji dadin sauyawar Mus'ab ba ko Ya daina sonta ne? Nan da nan kwallah na taru a idanuwanta.
*馃吙herty novels馃摑*
[22:03, 9/15/2016] ameerouq: *Nainah ....馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah 馃挒*
*47*
Tun bayan farfadowar Baffa daya sanarda Yasir abinda Ke ciki Ransa yake a bace,
Duk inda yake sa ran ganinta yaje batanan, a Wannan lokacin ynda xuciyarsa Ke masa xafi Duk ya ganta xai iya kasheta a hasashensa ma gunduwa gunduwa xai mata da Naman jikinta,
Wannan cin amana dame tayi Kama a ina xasu xauna ynxu shi baya ta kansa kamar baffa, yanada frnds xai iya xuwa Ya xauna tare da su, baffa fa?
Ya furxar da Iska mai xafi har lokacin xuciyarsa Bata kwantaba ko a mafarki yaganta baxai kyaleta ba, shine ajalinta Wlhy baxai bar inna ba sai ya kasheta... Ya goge guntuwar kwallar dana xubo masa, fuskarsa har tayi Ja saboda bacin rai,abinka da farin mutum.
Dabara ta fado masa daga xaunen da yake ya juya yana kallon baffa da tuni barci yayi awon gaba dashi, a fusace yabar asibitin ya nufi unguwarsu kai tsaye gidan limamin unguwar ya nufa,
Nan Ya Roqesa alfarmar baffa ya xauna anan gidan hr lokacin da xasu sami nasu gidan, ni xan nemi wani gu na xauna,
'a'ah Yasir xaka iya xama da baffa a gidana xan Baku daki daya, musulmi Dan uwan musulmi ne, duk inda musulmi yake xuciyarsa tasha banban data Arne,
Godiya sosai Yasir yayi kafin ya koma asibiti, Kwanan baffa biyu asibiti aka sallamoshi sai dai sun tabbatarwa da Yasir jininsa Ya hau sosai.
*
Sanda ya fito wanka tana xaune zaman jiransa, fuskarsa a yatsine take da toilet din sai wani kyama yake, bata damu da halin da yake ciki ba ta karbi bucket din Ta ajiye,
Tana biye dashi har dakinsa, ta qarasa wurin travelling bag dinsa Ta bude ta soma ciro masa kayansa, yana tsaye ko kallonta baiyi ba
Ta dube shi a sanyaye,
Friend kayi haquri, it seems like I hurt you,
Ya tabe bakinsa batare daya tanka ba, ta tashi ta fita Dan bashi wuri ya shirya, sai da ta tabbatar Ya gama shirin ta nufi dakin da madarar Shanu,
Friend gashi kasha nasan kana jin yunwa,
Thank you kawai ya fada yana cigaba da maida kayansa a jaka, idanunta suka yi raurau
'Ina xakaje,
'Gidan mu, ya tashi
Ta riqo hannunsa tana kallonsa
'Dan Allah kayi haquri, baxan sake ba ai umma ta Baka haquri Tace ka xauna,
'so kike na cigaba da xama anan ne, inda Baa sona? Ana korata,
'Ai Nace baxan qara ba, Karka tafi kabari Ayi auren Anty bahijja sai kaje,
'Au Nima xanje Ke baxaki Je bane?
Ta gyada kai tana kallonsa
'ni baxan koma ba,
'Why Nainah, nine bakyaso ko xama danine bakyaso,
Tayi shiru hade da sunkuyarda kanta qasa,
'Talk Nainah, kigayamin gskyr xuciyarki Idan bakya Sona ne xan sauwaqe maki a ynxu nayi tfyta Allah xai baki irin wanda kike so,
Ta riqo hannunsa idanunta akansa cike da hawaye, bakinta sai motsi yake alamar tana son mgn amma ta kasa, ya xura ido kawai yana kallonta Yanda ta riqo hannunsa kamar mai neman yafiya,
Umma lotee Ya tsinkayo dauke da kwarya a hannunta da Alama dakin xata xo, sai ya janyo Nainah da karfi xuwa jikinsa
A hankali Ya furta
'I love you Nainah, kafin yakai bakinsa cikin nata dai dai da shigowar lotee, idanunta na sauka akansu, da Sauri taja baya hade da dafe qirjinta
Amma Wannan yaro munafikine,yace baya sonshi shine kuma suke Wannan? Bari ya xo Yace bayason mijinshi in bige mashi baki, kuma dole xaije gidan mijinshi, ta fice da Sauri tana waiwayen dakin.
Kusan minti goma suna tsaye a hakan, jikinta sai kyarma yake tana kiciniyar raba Jikinta da nasa, da kyar ya cikata yana kallonta qasa qasa, ta Ja baya da Sauri tana maida numfashi da kyar, suna hada ido ya sakar mata wani malalacin murmushi tayi saurin dauke idanuwanta daga garesa hade da rufe idanuwanta da Tafin hannuwanta cikin jin kunyarsa......
*馃吙herty novesl馃摑*
[11:00, 9/17/2016] 鈥�+234 803 888 6036鈥�: [9/16, 7:38 PM] 馃吙herty馃帳馃懐: *Nainah......馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah 馃挒*
*48*
Kafin yayi magana tuni ta juya ta fice da Sauri.
Shi da Majeed da bahijja suka fita xagaya garin, yanayinsu Ya birgeshi sosai ya ciro wayarsa yana daukansu video, wani gu kuma ya dauki pictures al'adarsu akwai Birgewa,
Qauyen Baida girma sosai haka mutanen cikinsa basu da yawa, buxaye ne kawai anan garin,
Suna Tafiya su uku sai gashi Ya dawo tfy shi Kadai kasancewar Ya barsu baya sunyi Nisa a soyayyarsu shi Kadai ke tafiyarsa, Ya juya yana kallonsu sunyi matuqar birgeshi sun bashi sha'awa,
Inama shi da Nainah ne ahaka, Idan bahijja tayi dariya sak Nainah yake ganinta, murmushi kawai yayi Duk xuciyarsa ba dadi daya tuna Nainah bata sonshi,
Ya sami guri ya xauna yana kallon wasu samari dake xaune akan qatuwar bujukura (tabarma) suna ta shan jabra suna caca sunfi su goma, gasu a qauye cikin gidajen Katako da katangar qaya, wasu a gidajen laka masu kudine keda na suminti irin nasu Nainah, Suturar jikinsu baqin yadi ne mai layi layin fari wacce suke dinka yar Shara da wando iyaka gwiwa fuskarsu rufe da kyalle idanunsa ne kawai a waje da ka gansu Kaga buxayen nijar, amma koda Yaushe sai ka gansu suna farin ciki ko Meyasa? Bahijja ta kallesa
'ko xakaxo muje gida saboda hadari?
'Yace kuje kawai ai ni ba yaro bane, xn iya maida kaina gida, ya dubi majeed, Abdul Ya kamata ka koma abuja hakanan saboda aikinka, banason sunanka Ya shiga cikin mutanen da Dad xai Kora saboda suna wasa da aikinsu,
Yace Insha Allah yallabai, dama munyi mgn da umma lotee ta maida aurenmu nan da Sati daya saboda da bahijja xan wuce Abuja.
'Alhamdulillah Allah ya nuna mana ranar Ya sanya albarka,
Duk suka ce Amin, kana suka fice.
Yana nan xaune Iska mai qarfi ta taso hadari gadan gadan yayi baqi Ya 膹aga kansa sama yana kallon giragixai,
Duk hankalin Nainah a tashe yake ganin su majeed sun dawo ba Mus'ab, ya hadari da magrib sun kusanto lokaci daya sannan baisan gari ba, kusan sau hudu tana leqa waje ko xata tsinkayosa amma babu sa babu alamarsa, ta dawo da Sauri tana tmbyr bahijja fuska a daure,
'Ai Yace xai dawo yanxu Ki kwantar da hankalinki,
'bakiga an soma ruwa bane bai dawo ba kigayamin inda kuka barsa, nan bahijja tayi mata kwatance gurin ta fita da Sauri dai dai lokacin aka soma ruwa masu qarfin gaske
[9/16, 10:35 PM] 馃吙herty馃帳馃懐: Ga kuma duhun dare, kafin ta iso gurin duk ta jiqe sharkaf da ruwa, duk iya dube duben ta bata ganshi ba nan fa hankalinta Ya qara tashi ta soma Tafiya a hankali tana waige waige,
馃棧Mus'ab ......karo na farko da ta soma Kiran sunansa, ko ina wayam ba kowa sai Qarar ruwa dake sauka,
馃棧Mus'ab ta sake kiransa idanunta taf da hawaye bata ankaraba ta buga uban tuntube da dutse
'Ya Allah.. Ta fada a hankali bayan ta sunkuya tana duba babban yatsanta har ya soma Jini, takalminta daya Yabi ruwa tana kallonsa baxata iya bi ba saboda axaba da qafarta Ke mata zogi ta tashi da kyar tana dingirsa kamar daga sama ta tsinkayosa can qarqashin wata bishiya Ya jingina da itaciyar yana Sanye da rigar sanyi baqa Ya lumshe idanuwansa, da Sauri ta qarasa bayan ta cillar da takalminta daya,
'Friend ta kirasa a hankali, ya bude idanunsa yana kallonta jikinsa na rawar sanyi, inaji tun da yake ruwa basu taba dukansa haka ba,
'Meyasa bakaje gida ba ka tsaya ruwa sukayi maka duka haka, ya riqo hannunta
'Nainah sanyi!! Sanyi pls help me.
Taya xan taimakeka kaida kake da rigar sanyi, I don't know what to do friend, ruwan basu tsaigata ba, me kake so nayima? duk a rude take wadannan maganganun, ya jawota xuwa jikinsa hade da cire baqar rigar sanyi Ya lulluba masu akai ta xama kamar umbrella 鈽�, take taji ta qara tsanar majeed da bahijja tunda suka tafi suka barshi ruwa nayi masa duka, ta saqalo hannuwanta ta bayansa tana kallonsa shima ita yake kallo,sun dau fiye da minti talatin a haka har ana batun isha'i ma,
'friend kaxo mutafi gida Kaga ruwan sunqi su tsaya Anyi sallah fa.
'Aa mu tsaya anan ni ina tsoron dukan ruwa Nainah.
'nan ma ai suna dukanka kayi haquri muje, ta ciro rigar ta maida masa ajikinsa ta riqo hannunsa suka fice. Suna tafe duk ya qanqameta jikinsa sai rawa yake,
'Nainah qafana ,takalmina Ya shige a qasa,ta sunkuya qasa tana lalabe da hannunta tunda ba haske da kyar ta lalabo takalmin tabashi Ya sanya, taja hannunsa da Sauri kamar wani yaro, sanda suka iso gidan umma lotee na bakin qofar dakinta tsaye hankalinta Duk a tashe, da yare ta soma yiwa Nainah fada Dan me xata barshi ruwa su dakesa,
'umma ba laifina bane ai kinga tare dasu Anty bahijja suka fita shine suka dawo batare da shi ba, lotee ta riqo hannunsa sanyi sosai,
'Nainah xo taimaka masa yayi arwalla yayi sallah gashi isha'i ma tayi ta canxa Wannan kayan kixo na baki mantaleta馃檮Ya shafa a jikinsa,
Da kyar Nainah ta samu yayi arwallah ,suka Je dakin jikinsa sai kyarma yake ta ciro masa Kayan barci masu Kauri ta bashi hade da shimfida masa darduma, Taje ta karbo mantaleta ta samesa wando kawai ya sanya sai faman qoqarin cire botiran rigar yake hannunsa na rawa,
Da kanta taxo ta cire masa, sanda taxo cire masa shimi ta rumtse idanunta ita batason kallonsa ba riga馃槀,idanunta a rufe ta sanya mishi rigar yana kallonta taja hannuwansa inda darduma,
'pray, Idan ka gama ka shafa mantaletar sai ka kwanta kaji, ya gyada kai yana kallonta,
'Gudnyt.... Ta juya ta fice, ya bita da kallo kafin ya tada sallar.
Bayan ya gama shafa mantaleta, Karo na farko a rayuwar sa馃槀da Ya soma shafawa, cikin kyankyami, ya hau gadon ya takure guri daya tuni Ya fara rawar 膹ari, kansa ya Sara Ya fara ciwo xaxxabi mai tsanani ya lullubeshi tsoro da fargaba da tsananin kadaici suka dinga shigarsa, son Nainah da tunaninta suka cika masa xuciya, bakinsa sai bari yake saboda tsabar sanyi, a hankali yake Kiran Hajiya! Hajiya!!! Sister!! Sister!!! Xo ki tafi dani Karna mutum ruwa sun min duka,
A Wannan lokacin saboda sanyin garin tuni majeed Ya nufi dakinsa, bahijja da lotee sun qudundune a gado, sai Nainah kawai da idanunta a bude suke ta kasa barci saboda tunanin Mus'ab, Qila Ma baiyi barci ba, bai lulluba ba, qilama ko addu'a baiyi ba saboda tasan Yanda ta barshi xaune akan darduma, Mus'ab komai sai Anyi masa taga ynda mufeedah keyi dashi, da Wannan tunanin ta fita ta nufi dakin,
A hankali ta tura qofar dakin ta shiga tana haskawa da wayarta, can ta tsinkayosa qudundune haqoransa na Kadawa, xuciyarta na tsinke da Sauri ta nufesa ta riqo sa
'Friend..., ganinta yasa yayi saurin fadawa jikinta, tsananin xafin jikinsa yasanyata rudewa ta rasa abinyi sai sunansa da take kira
'friend meya same ka?
'sanyi Nainah, lullubeni.
Ta miqe da Sauri taje ta rufe window, ta riqo Tafin hannuwansa tana gogawa da qarfi haka Tafin qafafuwansa, gaba daya ta rude ta rasa abinyi, har lokacin bai daina fadin
'Nainah sanyi help me pls,
Ta fashe da kuka mai tsanani,
'me xanyi ma ne, ruwan sama yama duka ga Iska ga sanyi ina tsoron wani abu ya sameka ,ta sauka daga saman gadon taje ta bude jakarsa kakakaf ba wata rigar sanyi kenan da daya yaxo, ta fita dakin ta nufi nasu, rigar sanyinta ta Dauko da kyar ta iya sanya masa, ta janyo qaton blanket ta rufa masa, ta sake fita ta Dauko nata ta qara dora masa akai馃檮,
Ya jawota Ya shigar da ita cikin blanket din Ya rungumeta sosai, ta soma kiciniyar kwace jikinta
'Nainah karki tafi Ki Barni pls, Idan kika tsaya a haka sanyin xai tafi.
Bata da xabi a Wannan lokacin daya wuce wanda xata taimaka masa, ta qara shigewa jikinsa tana goga jikinta acikin nashi, sunyi gogayyar jiki sosai (body contact )duk ilahirin jikinsu sai da ya hade tun daga kan fuska har qafafuwansu, dumin jikinta yayi matuqar taimakama sa ya dawo ha每yacinsa Ya daina rawar 膹ari kafin kace me har ya fara xufa, ta cire blanket daya, ta tashi tasoma daddanna masa jikinsa har barci mai nauyi Ya daukesa, itama ta raba ta gefensa ta kwanta tana kallon kyakkyawar fuskarsa , bata jima ba barci Ya dauketa.
Dukkansu basu farka ba sai da gari yayi haske, Mus'ab Ya fara bude idanuwansa Ya ganta kwance a jikinsa gashin kanta ya rufe mata fuska, ta dora hannuwanta a jikinsa ta rungumeshi sosai, yasa hannu Ya Yaye gashin ya xuba mata idanu lokaci daya Ya saki murmushi Ya qara shigewa jikinta hade da kaimata sumbata a lips dinta,
'Nainah Meyasa baxaki bari mu rayu tare a haka ba, in kasance tare dake har abada, ya zamana ko wane motsi xanyi in jiki a jikina?
Suna haka ta bude idanuwanta taci Karo da fuskarsa idanunsa akanta, nan take taji