Showing 330001 words to 333000 words out of 411854 words
fine how was your night?. Alhamdulilah yaya mashkhur. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa ya jikin naki da fatan dai kin samu sauqi, jim zahra tai na wasu lokutan kafin tace ee to jiki dai an gode ALLAH amma ban gama samun sauqi ba. Jinjina kai mashkhur yayi sarai yanzu ya gane zahra lafiyar ta qalau kawai rainin hankali ne.
Jawo ta yayi wace tare da cewa okay zo muje muyi breakfast in baki samu sauqi ba sai muje hospital a duba min ke. Jim zahra tai batace komai ba tana tafiya da kyar kamar wanda kwai ya fashewa a jiki. Teady naga kina tafiya da kyar in bakyason tafiyar bari na goyaki na goyaki?. Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aaa bana buqata zan iya tafiya. Haba my love ki bari na goya ki bana so kina wahalar min da kanki.
Aaa ka bari zan iya tafiya ai gwara na taga da qafafuwa na ko na samu naji gwarin jiki na. Mashkhur a zuciyar shi cewa yayi zakiga kwarin jiki ni zaki rai nawa wayo wlh yau ko kukan jini zaki sai na sadu dake, amma a fili murmushi yayi tare da cewa to shikenan tawo mu tafi. Haka mashkhur ya riqe hanun zahra cike da soyaya suka sauko qasa domin yin breakfast.
Ko da suka qarasa wajan draining d'in mashkhur ne ya jawa zahra kujera ta zauna sanan ya saving d'in su. Bayan ya gama suka faracin abinci a plate d'aya kowa da abinda yake saqawa a ranshi. Mashkhur yana tinanin taya zai sadu da zahra yau cikin sauqi, zahra tana tinanin taya zata gudarwa mashkhur yau?. My teady naga bakyacin abinci ko na baki a baki ne?.
Girgiza kai zahra tai tare da cewa aa zanci da kai na, haba masoyiya kin san dai duk wani aikin wahala bana so ki ringa yi ki bari mana na baki. Ya qarasa maganar yana kai mata airish d'in bakin ta. A hankula zahra ta bud'e bakin ta fara ci. Haka mashkhur yayi ta bawa zahra a baki harta qoshi sanan shima yaci ragowar. Bayan sun gama breakfast d'in kallon zahra mashkhur yayi cike da sha'awa yace teady ya maganar mu ta jiya kuwa?.
Tana nan mana yaya mashkhur, murmushi mashkhur ya saki tare da cewa yauwa my wife taso mu tafi d'aki mana. Aaa yaya mashkhur ai ba yanzu ba ka bari sai da daddare yanzu kawai kai fitar ka. Ni zahra ba inda zani daga nan har one week ina tare da ke. Gaban zahra sake fad'uwa yayi amma sai ta dake tace ka bari ba yanzu ba sai dare yayi.
Jinjina kai mashkhur yayi zuciya cike da zumud'i yace okay ALLAH ya kai mu daran ai kamar yanzu ne. Wunin ranar mashkhur yana manne da zahra komai shi yake mata sam baya bari ta wahalar da kan ta, amma dai baya yawan ta6a jikin ta ko nuna mata maitarshi a fili duk dan karta tsorata da shi in daran yayi taqi amincewa.
Bayan mashkhur ya dawo daga sallah isha'i bedroom d'in zahra ya nufa zuciya cike fall da qaunar ta. A kan dadduma ya same ta tana sallah, zama yayi har ta idar da sallah sanan ya miqe ya qarasa kusa da ita ya zauna. shiru zahra tai batace komai ba, cikin tattausar murya mashkhur yace teady na ki taso haka nan kinga dare yayi kuma kin sa ni a matse nake.
Jim zahra tai batace komai ba, haba my wife karki kasance a cikin masu sa6a alqawari jiya fa kikayimin promise akan yau zaki amince dani a matsayin mijin ki. Cikin sanyayiyar murya zahra tace to yaya mashkhur ai bazan sa6a alqawari ba alqawarin mu yana nan amma gaskiya ni bazan yadda ba har sai ka siyomin kaza amarya kamar yadda ake suyowa ko wace amarya, zahra ta qarasa maganar cikin sigar shagwa6a.
Ajiyar zuciya mashkhur ya saki cikin murya lallashi yace oh karki damu baby na da kai na zan gasa miki, in mun gama. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aa ni yanzu nake so, to shikenan bari naje nai miki yanzu tinda kina so, qafad'a zahra ta noqe tare da cewa aaa ni ba taka nake so ba ta waje nake so. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke sanan yace karki damu ai giram kine my wife bari na fita na siyo miki yanzu, mashkhur ya qarasa maganar yana miqewa.
A hanzarce mashkhur ya shirya sanan ya d'auki mukullin muto ya fuce domin siyowa zahra kazar amarci kamar yadda ta buqata. Mashkhur yana fita zahra ta fara wasu wasi har ga ALLAH tana so ta bawa mashkhur kanta ko dan ta cika mai alqawari sa na jiya ta sauke haqqin sa na kanta, amma tana matuqar jin tsoro. Haka dai zahra ta dake yau ta d'au alwashin ko mai zai faruwa sai ta amince mashkhur ya sadu da ita.
Bayan fitar mashkhur rabin awa kawai yayi zahra taji qarar shigowar motar shi alamun ya dawo. Hmmm zo kaga tashin hankali wajan zahra duk tabi ta rud'e. Amma duk da haka daurewa tai sabida tana tausayawa yaya mashkhur sosai, kuma bata son sa6a alqawari. Zahra abu kamar wasa har ta fara jin sautin takun matattakala, alamun mashkhur yana gab da hawa sama ya shigo d'akin.
Ai zahra a guje ta miqe batasan sanda ta turo qofar d'akin da qarfi tasa mata key ba cikin tashin hankali. Mashkhur dai yaji qarar rufe qofa amma duk da haka guiwar shi batai sanyi ba ya cigaba da hawa benan da niqi-niqin ledojin da yayiwa zahra shopping. Yana qarasawa ya ajiye su a qofar d'akin ya fara knocking d'in qofar tare da cewa amarya ta ki fito ga angon ki ya kawo miki kazar amarci.
Wayyo naji dad'i typing har na wuce qa'ida. πππππ
Ya kuke ganin za'a kwashe tsakanin zahra da mashkhur kuwa?.
Mu had'e a next page dan jin ya zata kaya.
[23/04, 8:29 pm] Oum Farhanβ€οΈπ©·: ADALILINTA πβ€π
BY AMINA BAYERO πβ€π
TYPING...........
*page 124*
Yana qarasawa ya ajiye su a qofar d'akin ya fara knocking d'in qofar tare da cewa amarya ta ki fito ga angon ki ya kawo miki kazar amarci.
Nan da nan zahra da take tsaye a bakin qofa ta fara gumi, mashkhur kuwa daya ji shiru sake bibbaga qofar yayi yana kwallarawa zahra kira me sauti. Na shiga uku ALLAH gani gareka zahra ta fad'a a zuciyar ta bata son sa6awa mashkhur alqawari amma ya zama dole wanan karan ta sa6a sabida mugun tsoran da take ji. Haba my wife haka mukayi dake mai kike nufi da hakan ne?.
Mashkhur ya fad'a a sare, gyara tsayuwa zahra tai cikin tsoro tace aaa yaya mashkhur nifa gaskiya hmmmmmm, rai 6ace mashkhur yace kefa gaskiya mai wai ni zaki rai nawa hankali mai kika mayar dani bazaki bud'e qofar nan ba. Kuka zahra tasa tare da cewa aaa gaskiya ni bani da lpy ka bari sai gobe.
Wani irin 6acin rai ne da haushin zahra suka lilli6e mashkhur ko ta ina, cikin 6acin rai yace oh yah ALLAH. Sassauta murya mashkhur yayi cikin sigar rarrashi yace pls zahra ta dan ALLAH ki bud'e kinji ki dena jin tsoro bafa wani zafin da kike tunani zakiji ba nan da 20 minutes anyi an wuce wajan,. Kuka zahra ta sake saki tace 20 minutes fa kace yaya mashkhur kawai kace kashe ni zakayi.
No zahra ba haka nake nufi ba taya zan kashe ki ina qaunar ki fa sosai my wife kin san bazan miki abinda zai cutar da ke ba ki bud'e qofar nan dan ALLAH naji na rage tinda bakyaso ko 10 minutes ne kinji. Aaa gaskiya yaya mashkhur bazan iya ba bani da lafiya ka rabu dani. Ke zahra ni kike rai nawa hankali ko? to wlh kika shigo hannuna sai kin gane baki da wayo.
Kuka zahra ta saki tace dama ni nasan ba sona kake ba kawai jikina kake buqata, dama na dad'e ina wanam tunanin, ama yau kashi na tabbatar. Da qarfi mashkhur yasa hannu ya kai wa qofar wani naushin baqin cikin wanda sautin naushin sai da yayi mugun razana zahra da take bakin qofar rai ba dad'i ya wuce a fusace d'akin sa.
Zahra kuwa kuka ta saki tare da komawa kan bed ta kwanta. Bayan tasha kukanta ta gama ta shiga toilet ta wanke fuskar ta sanan ta dawo tasa kayan bacci ta kwanta akan bed. Zuciya cike da so da qaunar mashkhur, ga wani irin tausayin sa da take ji, har ga ALLAH tasan batayiwa mashkhur adalci ba amma da zata iya da ta amince an wuce wajan amma tsoro ya hana ta.
6angaran mashkhur kuwa yana komawa bedroom d'in shi rai a 6ace ya cire kayan sa sanan ya wuce toilet yayi wanka da ruwan sanyi ko ya samu salama. Bayan ya futo ta daga toilwt zira kayan baccin sa yayi sannan ya kwanta akan gado zuciya cike fall da haushin zahra,. Sai a lokacin yake tinanin yayi ragwan azanci da tun farkon tarewar su a gidan bai afkawa zahra ba da ya samu dama. Ranar dai haka mashkhur ya kwana da baqin cikin zahra da kyar ya iya bacci.
Washe gari.
Washe gari mashkhur da sassafe ya shirya tsaf ya fuce yabar gidan. Zahra da take tsaye a bakin window d'in bedroom d'in a tsaye tana ganin motar mashkhur ta fita ta saki wata doguwar ajiyar zuciya. Lokaci guda wani mugun tausayin sa da son sa ya sake lili6e ta ko ta ina amma duk da hakan batajin zata iya amince mai a halin yanzu.
Bayan mashkhur yayi kamar 20 minutes da fita, zahra wanka ta shiga sanan ta futo ta shirya tsaf ta bud'e qofar d'akin. Tana bud'ewa taci karo da ledojin da mashkhur ya kawo mata su a baje a wajan, da sauri zahra ta durqusa ta d'ebe ledojin duk da kuwa suna da nauyi. Tana d'auka ta koma hanyar sauka daga kan step d'in benan. Bayan ta gama sauka bata tsaya ko ina ba sai bakin qofar babban falon.
Da sauri tasa key ta kulle d'akin sanan ta juya ta d'auki ledojin ta koma kicin. Tana shiga ta bud'e ledojin dan ganin menene a ciki. Kaza ce tasha jan gashi ba wai, d'ayar ledar kuma gashashan balango ne da gurasa, d'ayan kuma lemuka ne da yogurt. Zahra ba 6ata lokaci ta kunna oven ta gasa naman ta sanan ta dafa tea mai zafi ta koma falo za zauna akan gujera ta hard'e qafa d'ayan kam d'aya tana ci.
Hmmm ni kuwa amina bayero nace lallai zahra kin rainawa mashkhur hankali, baki bada had'in kai ba amma kinzo kina cinye mai kazar amarci. ππππ
Bayan zahra ta gama cin kazar ta da tea d'in ta qofa ta bud'e sanan ta haye sama ta shige bedroom d'inta ta rufe shi gam. Har wajan qarfe hudu ba labarin mashkhur bai dawo ba, zahra kuwa bayan ta idar da sallah la'asar bud'e qofar tai ta sauka qasa sanan ta kulle qofar babban falon,.
Bayan ta kulle ta shige kicin ta d'ora abinci. Zahra ta d'au kimanin awa d'aya tana dafa abinci, bayan ta gama ta shiryawa mashkhur nasa akan draining sanan ta d'auki nata ta bud'e qofar babban falo ta haye sama ta shige bedroom d'inta ta kulle abin ta. Bayan zahra ta gama cin abincin ta toilet ta shiga tai wanka sanan ta d'auro alwala sabida an kusan kiran sallah magriba.
Bayan ta futo daga toilet d'in ta gama shafa mai ta shirya, dadduma ta shinfid'a ta tayar da sallah magriba. Bayan zahra ta idar da sallah magriba ta gama lazimi, miqewa tai ta d'auko qur'ani sanan ta dawo kan dadduma ta fara maraji'a. Zahra bata tsaya da maraji'ar ba har sai da aka fara kiran sallah isha'i. Ajiye qur'an d'in zahra tai sananta tayar da hiqama ta fara sallah.
Bayan ta idar kan godo ta nufa sanan ta dauki wayar ta. Kewar yaya abdul zahra take dan haka ba 6ata lokaci number shi ta kamo ta kira shi. Ringing 3 wayar tai yaya abdul ya d'auka, cikin murya mai cike da farin ciki abdul ya d'auka tare da cewa hello aunty zahra. Had'e rai zahra tai kamar yaya abdul yana ganin ta tace aunty kuma.
Sorry qanwata wai dai gani nai ya kamata na ringa ce miki aunty tinda kinga ke matar yayana ce. Oh yaya abdul yanzu kana nufin na tashi daga qanwar ka kenan?. No my zahra kina nan daram kin fi ko wace qanwa a waje na kina rai na ina son ki a matsayin qanwa ta. Murmushi zahra tai sanan tace yauwa, yaya abdul ya nake jin muryar mace sama-sama wace wanan dai ba muryar ilham bace.
Oh kai karfa kice baki gane muryar ta ba?, aa gaskiya ban gane ba. Hmmm nana ce fa, cikin mamaki zahra tace nana kuma eee mana gata nan ku gaisa, aunty zahra ina wuni, lpy lau qalau nana dama har yau baki koma ba. Eee na dawo nan har sai munyi aure ni da yaya abdul. Murmushi zahra tai tare da cewa kai nana bakiji kunya wlh to ALLAH ya nuna mana lokacin.
Amen ya rabbi, daga haka dai nana da zahra sukayi sallama, sanan zahra ta qara gaisawa da yaya abdul. Bayan sun d'an gama hira sukai sallama zahra ta kashe wayar. Zahra mamaki ne ya kamata ganin har tara saura mashkhur bai dawo ba shi da ya fita tun safe, waya zahra ta dauko ta kamo number yaya mashkhur wanda tai safe d'in ta da MALLAKINA.
Zahra ta dad'e sosai tana tinanin ta kira ko kuwa?. Tana cikin wanan halin taji qarar zugewar get, alamun mashkhur ya dawo. A jiyar zuciya zahra ta saki tare da ajiye wayar tana gyara kwanciya. Dama bedroom d'in a rufe yake qam.
6angaran mashkhur kuwa yana parking d'in motar ya futo zuciyar shi cike da kewar zahra.
Ya d'auki alwashin share zahra zai yi gaba d'aya na d'an wani lokacin,. Mashkhur yana shigowa cikin gidan ji yayi sam bazai iya ba dole sai yaje wajan zahra. Dan haka ba 6ata lokaci ya hau benan bai tsaya ko ina ba sai qofar bedroom d'in zahra. Cikin nutsuwa mashkhur yake knocking, zahra kuwa tanajin mashkhur yana knocking kimanin 5 minutes amma ko tari batai ba tai shiru gum kamar dai ba mutum a ciki.
Mashkhur dayaga zahra bata da niyar bud'ewa juyawa yayi ya koma qasa, can ya hango filasan da zahra ta jera mai abinci. Wani dogwan tsaki yaja tare da cewa lallai 'yar nan zaki gane baki da wayo Allah ya had'a mu, rai ba dad'i mashkhur ya juya ya koma bedroom d'in shi. Ranar ma haka mashkhur ya kwana zuciya cike da baqin ciki.
To fa abu kamar wasa har zahra da mashkhur sun d'au kwana 3 suna wasan 6uya mashkhur in ya fita tun safe baya dawowa sai tara ko goma, ita kuma zahra sai ta dai-dai ci mashkhur yana gab da dawowa sai ta shige bedroom d'inta ta rufe. Mashkhur duk abinda zahra take yana ganint ta cctv camera, dan haka shima ya gama had'a mata target d'in shi ya d'ana mata tarko mai kyau.
Yau mashkhur misalin qarfe 7:30 na dare ya dawo gidan yana dawowa yayi parking d'in motar sa awaje. Yaga gama parking ba 6ata lokaci ya bud'e laptop d'in da take nuna d'aukar da acct camera d'in gidan tai. Yana bud'ewa ya fara bi daki-daki har ya shiga ta d'akin zahra.
A dai-dai lokacin zahra ta shige toilet qirji d'aure da towel, ga dukkan alamu wanka za tai. Mashkhur zubawa zahra ido yayi kamar wani maye har ta shige toilet d'in. Zahra ta shigewa mashkhur ya mayar da kallan sa qofar bedroom d'in, ya zuba mata ido sosai.
Wata uwar ajiyar zuciya mashkhur ya saki ganin qofar a kulle take amma bata kai da sa key d'in ba. A hanzarce mashkhur ya futo daga motar ya kulle sanan ya nufi qofar gida. Mashkhur baya so ya shiga da motar cikin gidan sabida zahra karta ji sautin bed'e get ko qarar motar shi ta futo ta rufe qofar bedroom d'in ta, kafin ya qarasa shigowa. Bayan mashkhur ya kwankwasa get d'in mai gadi ya bud'e mai, ba 6ata lokaci ya shige cikin gidan.
A hankula mashkhur ya bud'e qofar babban falon duk dama ba lallai zahra taji qarar ba. Yana shiga ya rufo qofar a hankula tare da murd'a mata key. bayan mashkhur ya gama rufe qofar a hankula ya fara hawa steps d'in benan, yana gama hawa ko kallan d'akin sa bai ba ya nufi hanyar d'akin zahra. Dama mashkhur daga gida yake yayi wanka acan kafin ya tawo.
Shi yasa ma bai yi tinanin wanka ba ya nufi d'akin zahra. A hankula mashkhur yake tafiya sai sand'a yake kamar wani 6arawo ba mai gida ba. Yana zuwa ya murd'a handel d'in qofar a hankula, ai kuwa cikin sa'a har time d'in zahra bata rufe qofar ba dama haka mashkhur yake tsammani.
A hankula mashkhur yasa kai ya shiga bedroom d'in sanan ya turo qofar a hankula yadda zahra bazataji ba. Qarar ruwa mashkhur yaji a toilet alamun har lokacin zahra wanka take. Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya fara murd'a key d'in d'akin a hankula, bayan ya kulle d'akin ciki ya qarasa shiga sai