Showing 351001 words to 354000 words out of 411854 words
tom naji amma ki canza maya fin nan ni yayi min qanqanta.
Turo baki zahra tai tare da cewa to ni ai ba kai na sawa ba. Zaro ido mashkhur yayi cikin mamaki yace oh to wa kika sawa?. Hmm ni ba ina nufin wani na sawa ba my hero, I mean ba kai nai wa kwalliyar ba fita fa zamuyi. Qarasowa mashkhur yayi tare da cewa to in bani ba wa kikayiwa to yanzu, ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa kai na nayiwa mana.
Hmmm to ban yarda kiyiwa kan naki ba da dai a gida kike ke kad'ai ko dagani sai ke sai na yarda amma wanan kinga mutane zasu ganki sosai. Cikin jin haushi zahra tace to ni wa zai ganni bayan a mota muke. Oh gidan da zamuje ba mutane?. Cikin mamaki zahra tace kai gidan mu fa zani wa kake nufin karya ganni ammi ko kuwa su ilham d'in da sun riga da sun san komai a jiki na.
Oh su kad'ai ne a gidan ba maza kenan?. Cikin mamaki zahra ta sake cewa to su mazan mai zasuyimin in sun gannu, yaya abdul kake nufi ko haidar da faruq ko kuwa ameer. Wata harara mai cike da salon qauna mashkhur ya jefawa zahra tare da cewa dukan su mana bana so su kalle mun ke. Oh tinda da suke kallo na ba abinda ya same ni sai yanzu?.
To da kikace ai ba matata ce ba ke a time d'in, ba wani nan ko da muka dawo russia sun gani sosai har ba mayafi sun ganni. Cikin 6acin rai da kishi mashkhur yace kwarai kuwa na sani tinda har hugg d'in abdul kike da auran ki, abinda kikayi a baya bazan sake bari ki mai mai tashi ba sabida yanzu nasan darajar ki kuma nasan wacece ke?.
Kamar zahra za tai kuka ta juya ba tare da tace komai ba ido tab cike da kwalla ta fara qoqarin d'aukar trolley d'in kayan ta. Muryar mashkhur taji ta ratsa kunan ta da cewa! Ki ajiye trolley d'in nan dan ba kwana zaki ba. Sabida tsabar baqain ciki zahra bata son sanda ta tsuguna ta fashe da kukan mai cin rai ba.
Mashkhur kuwa dawowa bakin gado yayi ya zauna ya zubawa zahra ido, son ta da tausayin ta lokaci guda suka rufe shi. Zahra kuka take mai sauti hawaye sha6e-sha6e harda majina. Zahra ta d'auki kimanin 5 minutes tana kuka kafin mashkhur ya taso ya qaraso inda take jiki a mace. A hankula ya tsuguna a gaban zahra tare da zuba mata mayun idanuwan nan nasa.
Zahra kuwa har time d'in bata dena kuka ba inma banda d'aga muryar da ta sake yi. Mashkhur bayajin dad'in kukan da zahra take har zuciyar sa, dan haka hannu yasa ya shafa gefan fuskar ta cikin muryar rarrashi yace sorry my wife cool down pls. Zahra kuwa mai makwan tai shiru sake fasa wani uban iwun tai. Wani irin haushi da dariya ne suka kama mashkhur lokacin guda dan shi sam baya san hayaniya ko iwu.
Amma yanayin yadda take kukan ya bashi nishad'i sosai. Sake kwantar da murya mashkhur yayi tare da cewa haba teadyna meye na d'aga murya kuma sai kace wanda ake duka ai ko dukan ki nai bai kamata ace kina kukan nan ba bare ma maganar baki. Cikin kuka zahra tace bazanyi shirun ba tinda ka dena sona ai sai ka sake ni naje na auri wanda yake sona.
Mashkhur zubawa zahra ido yayi cikin mamaki yace saki kuma zahra mai ya kawo maganar saki mai nai miki kuma?. Share majina zahra tai tare da cewa ee sai ka sake ni d'in au bama kasan mai kai min ba, kace nayi hugg d'in yaya abdul d'ina sanan kuma kace bazaka barni naje na kwana ba zahra ta qarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya.
Oh sorry my teady nifa wasa nake miki banyi hakan dan na 6ata miki rai ba, ai nasan yaunzu kin dena hugg d'in kowane namiji sai ni, dama can saboni da shine da shaquwa da kuma rashin sanin darajar auran mu da bamayi ne yake sawa ki haka amma yanzu ai kin dena koh?. Ido sha6e-sha6e da hawaye zahra ta d'aga kai alamun ee.
Yauwa my teadyna shi yasa nake son ki, cikin muryar kuka zahra tace to in kana sona ka barni naje na kwana mana. Haba my teady barin ki kije ki kwana bashi yake nuna cewa ina son ki ba, hasalima son ki ne da shaquwar ki ya hana ni barin ki kije ki kwana pls ki fahimce ni matata. Kuka zahra ta saki mai qarfi wanda yafi nada ma sauti. Rarrashin duniya mashkhur yakewa zahra amma zahra taqi kula mashkhur.
Kuka take mai sauti lokaci guda sai da zahra ta rikirkita mashkhur ta canza mai mood sabida tsabar rashin son hayaniya irin nasa. Wata lafiyayyar tsawa da mashkhur ya dakawa zahra! Da cewa pls ya isa haka kimin shiru! nan da nan zahra ta rufe bakin ta gam. Kafin kace kwabo kamar mashkhur ta bayyana tacan baya nan da nan zahra ta shiga hankalin ta sabida gani tai ya dawo mata mashkhur d'in da mugun nan.
Cikin kausassar murya mashkhur yace wlh ko kwakwaran nunfashi kika qarayi a nan sai na baki mamaki so nawa zan baki haqurin ne, kuma ya kike so nasa kai na ne ke bazaki iya fahimtar mutun ba sai an had'a miki da fad'a koh?. Da sauri zahra ta miqe tare da komawa kan bed ta kwanta ta shige cikin blanket abinta jikin nan nata sai rawa yake dama dai kunsan zahra da tsoro musamman ma na mashkhur.
Mashkhur kifa kan sa yayi a guiwa yana ladamar tsawar da yayiwa zahra, yana son zahra sosai bayaso tayi nesa da shi amma ta kasa ganewa ya rasa ta yarda zai ganar da ita. Tinani mashkhur ya fara tayarda ya shawo kan zahra da wahala amma gashi yanzu yazo yana yi mata tsawa sai ta fara jin tsoron sa kamar da ta dena saki jiki da shi kuma.
Cikin damuwa mashkhur ya miqe ya nufi kan bed d'in jiki a sanyaye. Wani irin mugun tausayi zahra ta sake bawa mashkhur ganin yarda jikin ta yake rawa a blanket. A hankula mashkhur ya janye blanket d'in, yana janyewa zahra ta rufe idon ta gam tare da duqunqune jikin ta alamun tsoro. Cikin sanyayiyar murya mashkhur yace my teady?.
Baki na rawa zahra tace dan Allah kayi haquri karka dake ni, ni kawai ka kai ni gida tinda ka dena sona zahra ta qarasa maganar zafafan hawaye suna zobowa daga idanuwan ta. Da sauri mashkhur ya qara matsawa kusa da zahra cikin tausayawa ya kifa fuskar sa a fuskar zahra tare da cewa i'm so sorry teady na, wallahi ban dena sonki ba ina qaunar ki teady na.
Zahra bana so kiyi nisa dani ko kad'an na saba rayuwa da ke zahra ta, shi yasa kikaga bana son ki tafi ki barni. Pls ki yafemin wlh bada son rai na nayi miki shouting ba, kin san dai bana son hayaniya kuma bana son naga kina zubar da hawaye yana ta6amin zuciya ta, kuma gashi na rarrashe ki kinqi haqura shi yasa nai miki shouting, nima kai na ban san nai miki hakan ba.
Cikin muryar tsoro zahra oh yanzu yaya mashkhur baka ganina a matsayin mata kana nufin zaka iya cigaba da duka na, in na 6atama rai?. No my teady waya gaya miki haka, ni ai ba jahili bane, sam bazan daki matata ba ko a russian ban ta6a dukan ki ba har muka qare zaman mu bare ma yanzu da kika zama jinin jikina. Da sauri zahra ta bud'e ido cikin mamki tace anya kuwa baka ta6a duka na a russian ba.
Kwarai my wife ni ban ta6a dukan ki ba ki tina sai dai na baki punishment koh?. Jim zahra tai tana tinanin tabbas haka zanca mashkhur yake ko a russian bai ta6a dukan ta ba sai dai ya bata punishment mai wahala sosai sai kuma time d'in daya shaqeta dan yaga ahmad yana mulmula mata kai. Mashkhur sumar sa ya goga a kumatun zahra sanan yace, shikenan my wife tinda kin za6i kibar mijinki a mawuya cin hali ki tafi baki har one week hakan shine farin cikin ki na amince miki kije.
Mashkhur ya qarasa maganar cikin murya mai ban tausayi jiki ba kwari ya d'auke fuskar sa daga ta zahra sanan ya miqe yasa hularsa yana cewa tashi ki wanke fuskar ki na kai ki. Itama zahra tashi tai zaune mashkhur duk ya gama kashe mata jiki da kalamai nan da nan ya mashkhur ya sawa zahra kokwantan ta tafi ko kuma ta tsaya wajan mijin ta.
Zahra zubawa mashkhur ido tai cikin tausayawa tabbs tasan mashkhur in bai damu da kasuwa ba ko sauti baya bayarwa, tabbas zahra tasan mashkhur yana son ta sosai in ta tafi ta barshi zai shiga damuwa. Nan da nan zahra tausayin mashkhur ya kamata dama dai kunsan zuciyar mata tana da sauri karyewa musamman ma irin ta zahra mai tausayi.
Jiki a sali6e zahra ta fad'a kan qirjin mashkhur fuska cike da hawaye da majina cikin kuka tace dan Allah yaya mashkhur kayi haquri na haqura da zuwa zan zauna tare da kai zahra ta qarasa maganar tana qanqame shi. Shima mashkhur rungume ta yayi cikin farin ciki yace yauwa my wife ALLAH yayi miki albarka, shi yasa nake qara qaunar ki sabida kina da tausayi ga haquri.
Dai dai kunan ta mashkhur ya fara yi mata magana kamar mai rad'a. Hmmmm tofa nima amina bayero naso naji mai mashkhur yakecewa zahra dan har kasa kunne nayi amma banji ba, wayyo da naji dana gaya muku. Mashkhur yana gama yiwa zahra rad'a zahra ta saki mashkhur daga hugg d'in da tai mai ta d'ago fuska cike da farin ciki tana sakin dariyar jin dad'i.
Bayan zahra ta gama dariyar cewa tai hmmm ina qaunar ka mijina soyayya mai qarfi har muddin rai na. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmm nima ina qaunar ki matata uwar 'yaya na mai d'aki na yi sauri kije ki wanke fuskar taki kizo mu tafi. Ba musu zahra ta shiga toilet ta wanko fuskar ta sanan ta d'auki babban mayafi ta yafa ta rufe jikinta ta ko ina.
Miqewa mashkhur yayi tare da cewa yauwa matata wanda tasan ya kamata. Dariya zahra tai tare da rufe fuskarta da tafikan hanun ta. Hanun ta mashkhur ya jawo tare da cewa tawo muje kar yamma tayi. Murmushi zahra tai sannan ta kalli qirjin rigar mashkhur tare da cewa kallifa rigar ka ta 6ace da majina ta da hawaye na mazakaje ka canza ba?.
Murmushi mashkhur yayi tare da shafa qirjin sa yace na gani mana, amma dai ki barni a haka tinda dai nasan zanyi missing d'in ki kafin nazo na d'auke ki kinga ai sai na ringa ganin jirwayan hawayan naki ko ya d'ebe min kewa. Murmushi jin dad'i zahra tai tare da cewa gaskiya ne my hero daga haka ta juya ta d'auko wayar ta wanda ilham ta cika ta da miss call yafi goma.
Bayan zahra ta d'auko wayar ta mashkhur kama hanun ta yayi suka sauka kan bene suna hirar su ta masoya. Daga haka suka nufi wajan parking space, sai da zahra ta za6i motar da take so su fita aciki, sanan mashkhur ya koma cikin gida ya d'auko key d'in motar, bayan ya fito ya bud'ewa zahra mufin mota ta shige,. Bayan ta shiga ya rufe murfin shima ya shige sanna ya tayar da motar mai gadi ya bud'e musu get suka fuce zuciyoyin su cike da qaunar juna.
Oh mata da miji kenan ba mai shiga tsakanin su sai Allah wato har sun jone sun barmu baki sake.😂😂😂
To fa mu had'e a next page my fan's.
ADALILINTA💜❤💜
BY AMINA BAYERO
TYPING.........
*page 134*
Bayan ta shiga ya rufe murfin shima ya shige sanna ya tayar da motar mai gadi ya bud'e musu get suka fuce zuciyoyin su cike da qaunar juna.
Bayan sun qarasa gidan su suna shiga gidan mashkhur yayi parking zahra ta fara qoqarin bud'e murfin motar amma gam. Wata doguwar ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa meye haka yaya mashkhur ka bud'e min qofar mana. Cikin muryar mai sace zuciya mashkhur yace to sai ki tafi ki barni ba sai ki jira mu tafi tare ba. Oh dole sai mun jera kowa yasan tare mukazo gidan kenan?.
Zahra ta qarasa maganar tana gyara mayafin ta wanda ya zamar mata kaya. Uhmmm kowa sai ya sani mashkhur ya qarasa maganar yana ruqo hanun zahra. Zahra bata sake cewa komai ba tai shiru, mashkhur kuwa hanun zahra ya cigaba da shafawa cike da soyayah dan sun d'au wajan 5 minutes a haka ba wanda yacewa d'an uwan sa qala.
Can zahra ta fizge hanun ta tare da cewa wai kai baka son zuru ba, dan ALLAH ka bud'e min na shiga ciki tin dazu sai jamin rai kake. Murmushi masoya mashkhur ya zubawa zahra tare da cewa ki bari mana nifa ban qoshi da ke ba mashkhur ya qarasa maganar cikin kasalaliyar murya. Cikin 6acin rai zahra tace to tinda baka gaji dani ba sai ka cinye ni ka wuta.
Oh haka kikace mashkhur ya qarasa maganar yana lashe kyayawan lips d'in shi. Hararsa zahra tai tare da cewa ee haka nace, to ta ina zan fara cinye kin? Mashkhur yayiwa zahra tambayar cike da shauqi da tsokana. Rai a had'e zahra tace ta inda zai fi maka sauqi, juyowa mashkhur yayi sosai yana kallan zahra.
Sanan ya d'orawa dugwan kyakyawan dan yatasan sa a kan le6an zahra na qasa tare da cewa tanan zan fara nasan kema zaki so hakan koh?. Ya qarasa maganar yana mata wasa da dogwan yatsan sa a le6an ta, kamar dai tafiyar tsutsa. Zahra da ta gama qulewa sai da ta bari mashkhur ya shagala da wasa da le6an nata ta bud'e bakin ta tare da gantsara mai cizo.
On expand mashkhur yaji cizon zahra wani siririn iwu dad'i ya saki, dan shi cizon ma dad'i yayi mai da yake ba can sosai ta cije shi ba. Zahra kuwa bata saki yatsan mashkhur ba haka tai tabi tana ciza a hankula a hankula. Mashkhur kuwa lumshe ido yayi lokaci qanqani ya tafi wata duniyar shauqi. Ya lumshe ido kamar mai bacci.
Zahra da ta shagala tana cizon yatsan mashkhur kamar ance ta d'ago tana d'agowa taga mashkhur ya lumshe ido kamar mai bacci. Da sauri ta saki hanunsa ta dena cizo, sanan ta daki qirjinsa a hankula da hanunta tana cewa wai bazaka bud'e min qofar na fita bane?. A hankula mashkhur ya bud'e kyawawan idanuwan sa ya zuba su akan zahra.
Lokaci guda idanuwan mashkhur suka canza suka komai kamar na mai jin bacci. Hanunsa zahra ta riqe cikin muryar rarrashi tace dan Allah hero na ka bud'e kaji kasan ina qaunar ka fa sosai. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa tom shikenan teadyna tinda kina so zan bud'e amma da sharad'i fa. Kamar zahra zatai kuka tace namenene kuma?.
Kawo kunan ki kiji, a hankula zahra ta matsarwa da mashkhur kunan ta. Shima a nitse ya sai ta bakinsa saitin kunanta ya fara yi mata rad'a. Sautin voice d'in rad'an mashkhur ma kad'ai ya isa ya shagalar da mutum sabida dad'i murya,. Naso naji abinda mashkhur yake cewa amma sabida sautin dad'in murya sa danaji bacci ne kawai yayi awan gaba dani amina bayero a wajan. 😢
Bayan mashkhur ya gama yiwa zahra rad'a dagowa zahra tai sanan tasa tafin hannuta ta rufe fuskar ta alamun kunya. Wani kallo mai cike da fassarori kala-kala mashkhur ya watsawa zahra tare da cewa kin yarda koh?. Cikin kunya zahra ta d'aga kai sanan tace hmmm na yarda, cikin farin ciki mashkhur yace yauwa my wife i love you to the extent of my life
Mashkhur ya raqasa maganar yana bud'e qofar motar. Yana bud'ewa zahra ta fuce a hanzarce, shima mashkhur zahra tana fita ya futo ya rufe murfin motar yana kiran ta amma ina ko jiyowa batayi. Wani siririn murmushi mashkhur ya saki yabi bayan zahra a zuciyar shi yace hmmm zamu had'u ne dama nasan ladabin muzuru kikeyi min.
Zahra tana shiga babban falon gidan ta saki doguwar ajiyar zuciya alamun tasha, zahra idon ta yana sauka akan yaya abdul da yake zaune akan kujera yana danna waya ta saki wani qasaitaccan murmushi, tare da cewa oyoyo my yaya abdul zahra ta qarasa maganar tana qarasawa inda.
Da sauri abdul ya dago yana ganin zahra ya saki wani tattausan murmushi tare da cewa your welcome my sister yana qarasa maganar yana kashewa zahra ido d'aya alamun yaji dad'in ganin ta. Zahra taso dai tai hugg d'in abdul kamar yarda ta saba amma taga bai bata fuskar hakan ba kuma ita taji ta kasa hakan bugu da qarima tasan mashkhur yana nan tafe a bayan ta.
Dan haka qoqarin zama ta farayi a kusa da shi, a dede lokacin mashkhur ya shigo baki d'auke da sallama. Mashkhur yana shigowa ya fara jifan zahra da wani kallo wanda ita ka d'ai tasan mai yake nufi. Da sauri zahra ta matsa can qarshan kujerar da abdul yake a zaune ta zauna. Mashkhur yana qarasowa ya saki fuskar shi tare da miqawa abdul hannu suka gaisa.
Bayan sun gama gaisawa zama mashkhur yayi a tsakiyar zahra da abdul. Zahra kuwa lokaci guda ta canza fuska dan sam batajin dad'in abinda mashkhur yake mata yanzu yana nufin zai rabata da yaya abdul d'in ne ko kuwa?. Haka mashkhur yayiwa zahra fin qarfi tana son magana da yaya abdul amma ya hana ta sai wani jansa da hira yake kuma in tayi qoqarin magana sai ya take mata qafa ta gefe.
Zahra kuwa sai zafgawa mashkhur harara take amma mashkhur sam bai masan tanayi ba. Can mashkhur ya juyo ya kalli zahra tare da cewa taso muje mu gai da ammi,