Showing 126001 words to 129000 words out of 411854 words
sanan ta cire takalminta ta hau kan bed d'in, har lokacin mashkhur bai d'aga ido ya kalli zee ba kamar ma bai san da zuwan taba.
Da zee taga shariyar tayi yawa a hankula ta fara matsawa kusa da mashkhur, takai gab da shikenan tana qoqarin ta6a guskar sa, mashkhur ya bige hanunta tare da watsa mata wani irin banza kallon. Nan da idon zee yaja ruwa kamar zatai kuwa tace wai honey sabida mai kake min haka ne? Ni yau bazan ta6a iya jurewa ba wlh, ta qarasa maganar tare da fashewa da kuka. Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba, zee kuwa cigaba da cewa, tai wai honey sabida mai duk abinda nake bana birge kana ne?.
Honey nifa yau bazan iya jurewa ba pls ka bani dama ko sau d'aya ne wlh ji nake kamar zan mutu bakaji yarda nakejin fleeing d'in kaba a jikina, da sauri mashkhur ya d'ago tare da cewa wai zee me kike nufi ne, mai kike buqata ne?. Cikin muryar kuka zee tace SEX nakeso muyi yau-yau d'in nan, da sauri mashkhur ya zaro idanunshi tare da cewa SEX kuma Zee?, ehh mana honey, da sauri mashkhur ya girgiza kan shi tare da cewa! No zee bazan ta6a iya hakan ba, a gigice zahra ta d'ago tare da cewa sabida mai honey.
Zee addinina bai yarda da hakan ba, sam ba kyau haramun ne ka kusanci wata in dai matar kaba, idanuwa cike da hawa zee tace honey na sani mana amma ai babana ya cemin in kukayiwa ALLAH laifi zaku iya roqanshi ya yafe muku, to mai zai hana bayan munyi ka roqe shi ya yafema?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ai ba haka abin yake ba zee, abinda dadyn ki yake nufi shine!! In mukayiwa ALLAH lefi a rashin sani ko kuma bayan munyi laifin sai mukayi nadama kuma mukasawa zuciyarmu bazamu qaraba har a bada, tom in muka qori ALLAH gafara zai iya yafe mana, shine abinda dadyn ki ya gaya miki baki gane ba.
Amma yanzu in nayi ai ina sane kenan nayi zina , kuma hukuncin zina a wajan ALLAH yana da tsauri sosai, kuma ALLAH bayasan mu aikata zina sabida babban lefi ne, kai zee nifa kwata-kwata bana sha'awar hakan ma, dan duk abin zai sa na sa6awa uban gijina ina qoqarin kuje mai. Zee tana gama jin bayanin mashkhur ta fashe da matsanan cin kuka tare da kifa kanta akan guiwar ta, mashkhur kuwa zuba mata ido yayi, yana kallan ikwan ALLAH. Can kuma yace haba zee ki dena kukan nan kinga dai ke maca ce, kuma aure zakiya, yanzu in mukazo mukayi sex dake in kikayi aure mai zaki cewa mijinki in ya gane ke ba budurwa bace kin ta6a ma'a mala da wani namijin na daban ba shi ba?.
Da sauri zee ta d'ago tare da cewa! No honey karka damu da wanan, nifa a halin yanzu ba budurwa bace, zaro ido mashkhur yayi dacewa what? Gyad'a kai zee tayi alamun ehh, mashkhur bai masan sanda yace tayaya?, zan gayama amma sai ka yarda inna gayama zaka amince da ni, shiru mashkhur yayi yana nazari da tinani, yana cikin tinanin nan yaji zee tace, dama ni tunda ina bin maza da dama, mamana tace bazatai min aure da wuri ba sai na gama karatu hakanne yasa na zama karauwa, bama iya maza kad'ai nake biba harda LESBIAN inayi...........
Koyi haquri jiya banyi muku posting ba, ban gama typing d'in da wuri ba shiyasa.
ADALILINTA 💜❤💜
BY AMINA BAYERO 💜❤💜
Typing................
*page 63*
Mamaki ya kama mashkhur sosai, sabida tinda yake bai ta6a tinanin zee karuwa bace kuma 'yar lesbian. Nan da nan kyakyamim zee ya cika mashkhur, Sam mashkhur bazai ta6a iya saduwa da zee ba, sabida shi mutumne mai kyakyami, bazai ta6a iya kusantar macan da taje tayi ma'a mala da maza daban-daban ba kuma ga mata, kai bama zee ba ko mace data ta6a saduwa da wani namijin ne sau d'aya sam mashkhur bazai iya ma'a mala da itaba, shi mashkhur ma in zai sadu da wato, to yafi san wanda bata taba ma'a mala da wani namijin ba kuma matarsa wanda yake tsananin so, tom shine mashkhur yake ganin zai iya aikata hakan da ita.
Tinani mashkhur ya tafiyi taya zai sha'wo kan zee ta haqura da abinda takeso ta ai kata da shi? Wani siririn tsaki yaja, nan da nan yaji haushin zee ya cika shi, dama tinda ba amincewa yayi da qudirinta ba kawai dai yace mata taje zai yi shawara ne, dan ta rabu da shi ya huta, jiki a sanyaye mashkhur ya ja bargo ya lulu6e jikin sa, zuciya cike da kyamar zee...
ZAHRA.
Yauma Ahmad yazo da wuri d'aukar zahra daga school, zahra tana futowa daga school Ahmad ya d'auke ta suka kama hanyar gida. Suna cikin tafiya Yaya Ahmad ya kalli zahra yace qanwata, in ba damuwa inaso na tambaye ki?, tom shikenan yaya Ahmad inajin ka?, shiru ahamd yayi bai ce komai ba, zahra dataga shirun yayi yawa cewa tai! Yaya Ahmad inajinka fa, oh sorry qanwata dama inaso na tambaye ki ya sunan wanan qanwar jinki mashkhur?.
Nan da nan zahra ta had'e rai tare da cewa haba yaya Ahmad, ya zakace qanwar mijina, nima ai 'yar uwata ce, Au ya haquri qanwata! Dama abinda yasa nace qanwarsa! Kinga ai gidan su d'aya da shi kuma sai kin fi ganewa. Kwa6e fuska zahra tai tare da cewa hmm tom gaskiya ba haka zancan yake ba kuma nima ai 'yar gidan ce, tunfa ina jaririyata nake gidan to kaga nima ai 'yar uwata ce Ko so kake ka cireni daga cikin 'yan uwana? . Ohh sorry qanwata wlh bansani ba, murmushi Ahmad ya saki tare da cewa shikenan kinga fad'uwa tazo dai-dai da zama.
Kallansa zahra tai tare da ce yaya Ahmad ban gane abinda kake nufi ba, haba qanwata sai kace ba bahaushiya ba?, murmushi zahra tai tare da cewa eh ina yawan jin kalmar amma bansan mai take nufi ba shiyasa. Tom bari in miki gwari-gwari ina nufi komai zai zomin cikin sauqi, jinjina kai zahra tai tare da cewa tom wacce daga ciki kake nufi, husaina tawa ko ruma ko kuma aunty rukee?, Dan zaro ido Ahmad yayi tare da cewa ohh shema da yawan su, ni dai guda d'aya na sani ita nake nufi ikhram ko ilham take da suna? Ahmad Ya qarasa maganar cikin kokwanto.
Wata siririyar dariya zahra tai tare da cewa kace husaina ta kake nufi, ilham sunan ta. Husainar ki kuma taya akai ta zama husaina taki?, hmm yaya Ahmad kenan bakasan ya muke da ilham bane kawai dan tabbas nasan da ina Nigeria bana boka bana malam muna tare da ita ai ko bacci ma baya rabamu komai tare mukeyi da ita. Murmushi Ahmad yayi tare da cewa alhmdllah!! Wlh zahra najin dad'in hakan kinga komai zai zomin cikin sauqi, qanwata kin san mene? Girgiza kai zahra tai tare da aa yaya Ahmad sai ka fada'a ina jinka.
Kin tina ranarnan da nace miki wata rana zan gaya miki abinda yake damuna kinta ko qanwata ?. Da sauri zahra ta tace qarai yaya Ahmad na tina, yauwa qanwata, wlh ba komai ne yake damuna ba face SON ILHAM. Zaro ido zahra tai tare da dafa qirjinta tace ilham kuma yaya Ahmad? Kwarai qanwata wlh kullum da ita nake kwana nake tashi tun sanda na d'ora idona a kanta naji ina sonta, wlh kullum a cikin tinaninta nake ko baccin kirki bana iya yi, koma da nayi tinanin na samu mashkhur da zancan amma dai kinsan halin mashkhur da shariya ba lallai ne ya d'auki maganar serious ba.
Shiru zahra tai dan ita tama rasa mai zata ce, shi kuma Ahmad cigaba da cewa yayi! Ina fatan dai bata da wani saurayi koh? Wani siririn murmushi zahra ta saki tare da cewa aa gaskiya a iya sanina bata kula samari sabida ko zance dady baya barinta fita ma. Ajiyar zuciya Ahmad ya saki tare da cewa amma a ganinki zata so ni kuwa? Jim zahra tai na wasu daqiqu chan kuma tace gaskiya yaya Ahmad ban sani ba ko zata soka ko akasin haka tinda kaka yanzu bama tare da ita. Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa hakane qanwata, amma dai da fatan zaki tayani nema ko ya qarasa maganar ciki da zaulaya.
Gyad'a kai zahra tai tare da cewa mai zai hana yaya Ahmad in dai na had'u da ita zan taya ka. Tom qanwata kimin addu'a ALLAH yasa dady ya bani ita, tom shikenan yaya Ameen. Suna kawo qarshan nan Ahmad yana kusa hancin motar sa cikin gida, yana gama parking zahra ta bud'e murfin muta ta fuce, shima Ahmad d'in zare key d'in motar yayi tare da fucewa daga motar, zahra ta wuce hanyar bene, shi kuma Ahmad ya kama hanyar part d'in shi.
Zahra tana gama hawa kan step d'in benan, ta qarasa bakin qofar a han zarce, har zahra zata fara kwankwasawa sai tai tinanin qilama qofar a bud'e take, a hankula zahra tasa hannu ta murda Handel d'in qofar, ai kuwa cikin sa'a taga qofar ta bud'e, a hankula zahra ta qarasa tura qofar sanan ta shige ciki. Tana ba 6ata lokaci ta juya domin rufe qofar, muryar mashkhur taji yana cewa! Ki sawa qofar key, da sauri zahra ta juya bayan ta, a zaune akan sofa ta ganshi yana ta danna laptop d'in shi, kamar ma bashi yayi magar ba.
Juyawa zahra tai ta sawa qofar key, sanan ta juyo ta kama hanyar bedroom d'in ta, a zuciyarta tana cewa kai dai wlh ka fiya san laptop, akan laptop ma sai da ka kusan kasheni. Zahra tana gifta mashkhur taji yace! In kikaji ana bugu karki sake ki bud'e qofar?, sunkuyar da kai zahra tai tare da cewa in sha ALLAH zan kiyaye, muryar mashkhur zahra taji yana cewa karma ki kiyaye jikinki ne zai gaya miki, zahra bata sake cewa komai ba ta juya ta cigaba da tafiya, tana isa bedroom d'inta, ta shige.
Zahra tana shiga ta fara qoqarin cire uniform d'in ta tana gama cirewa ta saka wasu kayan nata, bayan ta gama sa kayan, toilet ta shiga ta d'auro alwala sanan ta futo tana futowa, ta shinfid'a dadduma ta fara gabatar da sallah, bayan zahra ta idar da sallah ta gama lazimin, cire hijab d'inta tayi sanan ta d'auko mayafi ta yafa. Yunwa zahra takeji sosai hakan ne yasa ta kama hanyar fita fallo, a hankula zahra take takawa har ta qarasa fallon.
Har lokacin mashkhur yana zaune akan sofa, amma sai dai yanzu ba laptop d'in yake dannawa ba ga dukkan alamu karatu yake ko dai wani abu makamancin hakan da yake littafine a hanunsa, kuma hankalinsa ya karkata akan littafin. Kamar mai sand'a haka zahra ta shige kicin d'in, ba 6ata lokaci ta fara dafa indomei, bayan ta gama ko kwai bata tsaya soyawa ba ta juyeta a plate sanan ta d'auki ruwa, ta fuce daga fallon, zahra tana futowa ruwan jarkar hanunta ya fad'i, da sauri ta tsuguna ta d'auka tana d'agowa ta kalli mashkhur.
Wata uwar harara taga yana watsa mata wanda sai da zahra tasaha jinin jikinta, murya a kausashe mashkhur yace! Kee naga kanki yana miki rawa to wlh ki shiga hankalin ki dama jikinki ya dad'e bai yi tsami ba! Daga dawowarki zakizo ki ishi mutane, to wlh ko da wasa on mistake naga yau kin qara futowa fallon nan sai jikinki ya gaya miki, murya na rawa zahra tace kayi haquri, zaro mata manyan idanunsa mashkhur yayi tare da cewa keee wlh watarana in inagana kina magana sai na zubar miki da haquran rashin kunyar taki zaki bar nan wajan KO sai nazo na taka wuyanki?.
Ai zahra batai wata-wata ba tai sauri ta kama hanyar bedroom d'in ta, tana qarasawa ta shige a hanzarce, tana shiga murya qasa-qasa tace! MUGU kawai komai nai laifi. Daga haka zama zahra tai ta fara cin abincin ta, bayan ta gamaci tasha ruwa sanan ta ajiye plate d'in a gefan bed tana so ta fita ta kai kicin tana tsoran mashkhur a ala dole zahra ta haqura. Hawa kan bed tayi ta zauna, ai zahra tana zama zancan da sukayi da yaya Ahmad akan ILHAM ya fad'o mata, wani tatausan murmushi zahra ta saki.
Tinani zahra tai da yau ilham zataji yaya Ahmad yana sonta tofa sai ta kwana tana zaginsa, dan ita ilham ma in da akwai abinda ta a duniya to wani namijin yace yana son ta, in kace inason ilham tofa ranar basa bacci dare dan sai ta kwana tana mita tana qarewa wanda yace yana son ta tsiya, ita kuwa zahra duk wanda yace yana son ta tana dawowa gida take sa kuka ranar dai ko abinci bazata iya ciba haka dai ammi da hajiya kaka harma da yaya abdul zasu sha rarrashi.
A taqaice dai sam zahra da ilham basa so ace ana son su. Haka zahra ta zauna tana ta tinanin yadda suke rayuwa ita da ilham, tabbas zahra tasan tayi missing d'in ilham sosai, wata dariya zahra ta saki saka makwan tunawa tai da wata rana da suka sha dambe da ilham. Ranar sun tashi a makara zasu makaranta basuyi wanka ba! To ranar zahra ta riga ilham tashi daga bacci, zahra tana tashi ta cire kayanta ta d'aura toilet, tana shirin shiga towel ilham ta tashi ilham tana tashi itama ta cire kayan ta sanan tace wanka zata shiga itama.
Zahra tacewa ilham itama wanka zatai a toilet d'in ta tafi wani towel d'in a gidan tayi, nan fa ilham tai tsalle ta dire tace wlh zahra bata isaba itafa a toilet d'in bedroom d'in su zatai sai dai ita zahra ta tafi wani, a lokacin zahra tajin haushin ilham sosai, duk da zahra tana da haquri a lokacin ta kasan dan haka itama tacewa ilham bata isa ba, daga haka zahra ta banka qofar toilet ta fara qoqarin shinewa, da sauri ilham ta ruqota tace wlh zahra baki isa ni zan fara shiga, itama zahra tace wlh baki isaba in zan shiga, kuma bazanyi kaffara ba, sai dai ke kiyi azumun kaffara.
Ai itama ilham cewa tai wlh nima bazanyi ba sai dai kuwa mu shiga wankan nan tare, tsaki zahra tai ta shige toilet, ai zahra tana shiga ilham ta biyo bayanta ta banko qofar toilet d'in, ko kallan ilham zahra batai ba ta cire towel d'in ta tafara wanka. Itama ilham d'in towel d'inta ta cire, tana cirewa sabida nema tsokana ga soso guda biyu a cikin toilet d'in amma ilham tace dole sai zahra ta bata na hannunta, shiru zahra tai wa ilham ta cigaba da wanka ta.
Ilham kuwa da sauri tazo ta warce soson da zahra take wanka, zahra fa taji haushin hakan sosai, dan haka a zociye ta miqe ta kifawa ilham mari, ai zahra bata d'auke hanunta daga fuskar ilham ba itama ilham ta mayarwa da zahra mari, ai kafin kace kwabo dambe ya kaceme tsakanin zahra da ilham, ko kaya babu a jikinsu haka suke damban. Da yake zahra ba wani qarfin arziki ne da itaba sai da ilham ta zane zahra a cikin toilet d'in nan! Haka zahra ta zauna ta ringa rai-rai kuka a toilet d'in nan, itam ilham jikinta yayi sanyi sosai da ganin zahra duk haquri tana kuka.
Itama ilham d'in zama tayi suka ringa rafsa kuka abinsu, daga qarshe kuma ilham tazo ta rarrashi zahra, da yake zahra tana ba haquri a ala dole ta haqura, tunma kafin su futo daga toilet d'in suka shirya. Tun daga ranar in dai suka tashi a makare kuma ranar zasu makaranta tare suke shiga wanka, ko ranar da sukayi sauka wato ranar da aka d'aura auran mashkhur tare sukayi shiga wanka, suna kwanka suna hira abin nasu dai kwanin sha'awa kamar ta gawayan gaske.
Zahra ji tayi kamar tai kuka data tuno hakan, da tini yanzu maraici bazai ishetaba tana zaune tana hira da 'yan uwanta. Zahra tana cikin tinanin nan taji ana nocking d'in qofar gida, shiru zahra tai tana tinanin waye? Can kuma zahra da taji bugun yayi yawa sai tai tinanin mashkhur ne, dan haka ba 6ata lokaci ta kama hanyar fita daga d'akin nata. Lokacin da zahra ta futa falo bata kula da mashkhur yana nan ba da yake ya sauka daga kan sofa yana can carpet a zaune.
Da sauri zahra ta nufi hanyar bud'e qofar tana hawa tsakiyar cafpet d'in tai kici bus da mashkhur yana watasa mata wani mugun kallo. Nan da nan jikin zahra ya fara rawa ita tama manta da kashe din da mashkhur yayi mata kan in taji bugu karta bud'e!! Kuma yace mata karta sake yau ta qara futuwa fallon nan ai duk zahra ta manta da wanan sai yanzu,