Showing 102001 words to 105000 words out of 411854 words

Chapter 35 - ADALILINTA Complete Hausa Novel

13 Jul 2025

25277

amina bayero nace mashkhur anya kana da imani a cikin zuciyar ka kuwa? In banda jiri ba abinda zahra take ga wani mahaukacin cikwan kai da mura da suke damunta, kwata-kwata ma dai bata cikin hayyacinta dan da qyar take iya bud'e ido komai dishi-dishi take ganinsa.

Haka ta miqe tana taga-taga kamar zata fad'i sai. dafe bango take, mashkhur kuwa cewa yayi wlh na futo baki gyara wajan ba sai kin gane baki da wayo, Ya qarasa fad'i tare da jan wani dogwan tsaki ya juyawa, ya wuce d'akinsa. Dakyar zahra ta iya qarasawa wajan da cup d'in ya fashe ALLAH ya taimaketa gida uku cup d'in ya fashe, dan haka hannu na rawa ta kwshe su domin kaiwa dozbin. Amma ina ta qasa miqewa, haka dai ta ringa jan qafafuwanta tana rararfe har ta qarasa wajan kwando dozbin d'in ta zubar.

Sai da ta tsaya a bakin sharar ta huta sosai sanan ta fara rarrafawa domin shiga bedroom d'inta. Dakyar ta iya qarasawa da rarrafe bedroom d'in ta, sanan ta shige. A bakin qofar bedroom d'in ta zauna wani mugun ciwan kai ne yake damunta ga zazza6i daya rufeta, ga mura ka kuma goshinta ya fashe, ga qafafuwa duk sun kunbura. Tafi rabin hours a haka sam ta kasa komai, can dai ta daure ta rufe qofar tana so ta sawa qofar key amma bazata iya tashi ba, haka dai zahra ta rarrafa har zuwa wajan bed d'inta, sai da tayi namijin qoqari kafin ta iya hawa kan gadon nan.

Da kyar ta iya sa bargo ta rufe jikinta, jikinta sai rawa yake sabi da tsabar sanyi da takeji. Kai ranar dai duk san sallar zahra bata iyaba ba, dama batayi sallar magriba da isha'i ba, da yake tun qarfe shida na yamma ya d'aure ta sai goman dare ya kwance ta, ita zahra ma ta manta da wasu salolin da ake binta, kai ai koni amina bayero sai da na zubarwa da zahra hawaye dan zahra ta bani tausayi sosai😢. A Haka dai baccin azaba ya kwashe zahra.
6anran mashkhur kuwa ranar bacci yayi harda munshari dan ko ba komai yasan yau ya quntatawa zahra.

Washegari.............

Ringing d'in wayarsa ne ya tashe shi daga bacci, har wayar ta katse mashkhur bai samu damar d'auka ba. Nan da nan wani ringing d'in ya sake shigowa, hannu ya miqa kan qaramar drowar kusa da bed d'in ya zaro wayar domin ganin wake kiran wayar. Sunan ahmad ya gani ya futo 6aro-6aro akan wayar, ajiyar zuciya ya sauke tare da d'aukar wayar ya kara a kunan sa. Okay kawai mashkhur yace sanan ya katse wayar, sai da ya shiga toilet yayi brush ya wanke face d'in sa sanan ya futo, yana futowa ya zira jallabiya, sanan ya fuce daga bedroom d'in gaba d'aya.

Yana futa falo ya nufi hanyar bud'e qofar gidan, yana fud'ewa yaga Ahmad a tsaye ya riqe ugu da alama ya dad'e da tsayuwa a wajan. Rai a had'e Ahmad yace gaskiya mashkhur ka cika iyayi, tun yaushe na cema, ina tsaye? na kira wayar takama da kyaur ka d'aga, nacema kazo ka bud'e amma sai da ka shanyani?. Haba Ahmad yanzu meye Na mitar tinda dai na bud'e ma, kawai ka shigo!! Da sauri Ahmad yace aa ai ni dama ba wajan ka nazo ba.

To idan ba wajena kazoba wajan wa kazo? Cewar mashkhur, wajan qanwata zahra nazo mana ko ka manta yau zan kaita school ne?. Mashkhur kuwa bai san santa murmushi mugunta ya kwace masa ba, sabida tinawa da yayi da abinda ya yiwa zahra jiya tambas yasan bazata iya moruwaba yau dan taji jiki. Mamaki ne ya kama Ahmad shi dai yasan mashkhur ko maganar zahra bayaso, amma shine yanxu yana jin ance zahra yake wani murmushi. Ahmad kawar da maganar yayi da cewa, yanzu dai kaje kace ta shirya ta futo in kai ta, makaranta kasan yau muma zamu koma school kuma muna da lectures.

mashkhur yama manta da wata makaranta da zasu koma, sai yanzu da ahmad ya tina mai. Shiru Ahmad yayi yana jiran amsar mashkhur, can mashkhur ya kalli ahmad fuska d'auke da murmushi yace kai yaufa bazata iya zuwa makarantar nan ba because she is not feeling fine ya qarasa maganar yana sakin Murmushi mugunta. Shima ahmad murmushi yayi tare da cewa mashkhur ko dai ko dai? Mashkhur ciki rashin gane inda magar ahmad ta daso yace ko dai me?.

Hmm mashkhur kenan ko dai ka angwance ne yau ban sani ba? Ahmad ya qarasa maganar fuska a sake. Nan da nan annurin fuskar mashkhur Ya 6ace 6at, wani dogwan tsaki mashkhur ya saki tare da cewa, look Ahmad bana san wanan iskanci, aikin banza aka gayama ni irin kane, to sam ni wannan bai dame ni ba, kai barima kaji, ko zanyi abinda kake tinani bazan ta6ayi da itaba barema bayi zanba, yana gama fad'ar hakan ya wuce yabar ahamd a tsaye.

Jinjina kai Ahmad yayi tana mamakin hali irin na mashkhur abin dai yana bashi mamaki sosai, Allah dai ya shirye ka Ahmad ya furta cikin zuciyar sa. Shiga ciki ahmad yayi ya fara jiran zahra ko ALLAH zai sa ta futo, sai da ahmad ya kai har qarfe tara na safe yana jiran zahra bata futo ba, yana shirin fita mashkhur ya futo da shirin zuwa makaranta ba 6ata lokaci suka wuce tare. Ahamd yanaso ya tambayi mashkhur mai yake damun zahra amma yasan ko ya tambaya mashkhur ba bashi amsa zaiyi ba, haka nan da ya ha qura suka tafi zuciyar ahma cike da tinanin zahra a wana hali take?.

ZAHRA.......

6anran zahra kuwa tinda ta kwanta ba ita ta tashi ba sai qarfe sha biyu na rana ta tashi. Da wani matsanancin ciwan kai da mura ta tashi ga zazza6i, jikinta duk yayi stami, hankalinta ya tashi sosai da ta tina batayi sallar magriba da isha'in jiya ba, ga kuma ta asuba d'in yau. Jiki ba kwari ta miqe, tare da sa hannu ta riqe kanta da yake mata barazanar rabewa. Toilet ta shiga, ta had'a ta gasa kanta da qafarta da ta kunbura suntum, da sauran jikinta da yake mata tsami.

Daga haka tai wanka ta da brush sanan ta d'ara alwala, ta futo jiki d'aure da towel. Sanan ta zura dogwan higab tayi sallar asubayi, sauran salolin da ake binta batayi ba, ta bari sai lokacin su na yau yazo sai ta had'a tayi. Bayan ta gama addu'o'i ta da lazumi miqewa tai ta cire hijab d'in sanan ta nufi mudubi. akan kujerar mudubi ta zauna, kalla fuskarta tayi, idanuwanta sun kunbura sosai goshinta ma haka. Hannu tasa ta fara mulmula goshin nata, duk da tanajin azaba haka ta daure. Ba yan ta gama mulmulawa ruwan zafi ta d'akko ta qara gasa goshin nata duk da kuwa tanajin azaba kawai daurewa take, ba laifi goshin nata ya sace sosai, kunburin ma saura kad'an.

Daga haka mai ta fara shafa sanan ta zura bayan taidar da gama ta nufi drowar kayan ta. Doguwar rigar mara nauyi ta saka.

Sai da da zahra ta gama leqawa falon ta tambatar mashkhur baya falon sana ta futo. A hankula ta nufi kicin, tanaso d'ora abinci amma tana tsoran ta fara mashkhur ya zo ya tarar da ita. Zahra bata shirya shan sabuwar muguntar mashkhur ba dan haka bedroom d'in ta ta koma, cikinta cike da yunwa. Ventilation d'in bedroom d'in ta ta shiga domin shan iska kamar yadda ta saba, kamar ance ta kalli qasa!! gani tai ba motar mashkhur hakan ne ya nuna mata cewa mashkhur fa ya fita,, cikin farin ciki, ta koma kicin ta dafa indomei da kwai, sanan ta d'ora t, bayan ta gama a kicin d'in ta zauna ta ci abinci sabida uwar yunwa da takeji.

Tana gamawa ta fita falo tare da bud'e firij, maganin mashkhur na mura da na shaye-shaye ta gani da yawa a ciki, Da sauri ta d'akko maganin mura tasha murfi d'aya, sanan ta d'auki ruwa ta koma bedroom d'in ta. Tana komawa ta bud'e qaramar drowar, ta samu maganin ciwan kai tasha, daga haka tayi sallar azahar ta kwanta bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita. ALLAH SARKI ZAHRA BAIWAR ALLAH.............

Abinda yasa kuga kwana biyu bana yi muku posting shine!! Inayi posting bakwamin LIKE 💗 , shiyasa kukaga banayi muku posting, in bakwa buqata ku fita daga group d'in mana amma sai ku bud'e ku karanta bakuyi min like ba. Wlh in dai bakwa like zan daina posting gaba d'aya na rufe group d'in, in kuma wasu daga cikinku sunayi zan cire wanda naga basiyi, nabar masuyi, daga yau duk wacca naga ta bud'e kuma ta karanta batayimin like ba sai na cire ta daga group tinda littafin free ne bana kud'i ba, dama na kud'i ne sai kuce biya kuke shiyasa bakwa like d'in..........

Amma in kunji ba dad'i kuyu haquri, gani nai Gwara na gaya muku gaskiyar karna cutar da kai na, ina yimuku fatan alkhairi kuma da fatam zaku gyara na barku lpy sai ku biyoni a next page........


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240

Typing............

*page 55*

Tana komawa ta bud'e qaramar drowar, ta samu maganin ciwan kai tasha, daga haka tayi sallar azahar ta kwanta bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita...............

Tunda zahra ta kwanta bata motsaba, sai wajan qarfe hud'u saura da akayi kiran sallar la'asar. Jikinta duk a mace ta tashi ga zazza6i da cuwan kai daya sake kamata, haka dai ta daure ta miqe ta shige toilet. Wanka tayi da ruwan sanyi sabida tsabar zafin da jikinta yake mata, tana gama wanka wata mura mai zafi ta qara rufe ta. Haka dai ta lala6a, ta d'aura alwala ta futo, tana fitowa jikinta ya fara rawa wani mugun sanyi taji ya rufeta.

Dakyar zahra ta iya sa kayanta ta gabatar da sallar la'asar, sallar ma a zaune tayi, sabida har yanzu qafafuwanta zafi suke mata. Bayan zahra ta gama lazumi miqewa tai zata koma kan gado dan kwanciya kawai taji ana knocking d'in qofar ta. Shiru zahra tayi tana tinanin waye yake kwankwasa mata qofa? Tasan dai mashkhur bazai ta6a kwankwasa qofar taba, haka dai ta wuce jiki ba kwari domin ta bud'e karma tace mashkhur ne yake bugawa ta jawowa kanta wasa masifar.

Zahra tana isa ba 6ata lokaci ta bud'e qofar, mamakine ya bayyana akan idon zahra sakamakwan wanda ta gani a bakin qofar, Ba kowa bace face zee wato qawar mashkhur. Yamutsa fuska zee tayi cikin yaran English tacewa zahra, dama pepper soup nake so ki dafamin yanzu, ki hanzarta ki dafamin banason ki6atamin lokaci. Daga haka zee tai wucewar ta tabar zahra a tsaye, cike da mamaki. Shiru zahra tayi tana tunanin taya zata dafawa zee pepper soup alhalin tana cikin wanan halin na rashin lafiya, ya sallam, abinda zahra ta furta a cikin zuciyar ta kenan.

Juyawa zahra tayi ta koma cikin bedroom d'in ta, tinanin ta farayi, bataso taje ta dafawa zee pepper soup, sabida batajin dad'i, amma tasan in bata yiwa zee abinda takeso ba sai jikinta ya gaya mata a wajan mashkhur. Tina hakan da zahra tai ne yasata sauri tashi ta nufi drowar. mayafinta ta zaro ta yafa tare da fucewa daga bedroom d'in. Tana tifa bata tsaya ko inaba sai falo, mashkhur ta gani zaune baje da kwayoyi maye a gabansa, ga zee a gefe tana kallo riqe da remote a hanunta.

Kawar da kai zahra tayi tare da shigewa kicin. Haka zahra ta fara aikin dafawa zee pepper soup duk da kuwa batajin dad'i, tanayi tana tinanin halin da mashkhur yasa kansa a ciki na shaye-shaye. Sai da zahra ta d'auki minti talatin tana dafawa zee papper soup, duk gidan ya karad'e da kamshin, papper soup d'in zahra. Har lokacin zahra batajin dad'i jikinta kawai daurewa takeyi. Bayan ta gama pepper soup d'in joye mata tai a flask sanan ta kama hanyar fala domin kai mata.

Lokacin da zahra ta isa falo wajan zee har qasa ta stuguna, ta ajiye mata, sanan ta miqe domib barin wajan. Dawo ai baki gama yimin aikin ba, zee ta fad'a cikin isa da gadara, zahra kuwa ji tayi kamar ta wuce ta gyaleta, amma da ta tina a gaban mashkhur ne, da sauri ta jiyo tare da komawa gaban zee d'in ta stuguna. Girgiza qafa zee ta farayi irin cikakun 'yan barikin nan, tare da mai da kanta kan tv, tafi minti goma batacewa zahra komai ba.

Zahra kuwa damo sarkin haquri bata cewa zee komai ba tana tsugune a wajan, mura da ciwan kai ga zazza6i duk sun addafeta. Can zee ta juyo tacewa zahra!! Kije ki dafamin chip's da chiken papper, kuma ki hanzarta banasan jira, sai yanzu na tinama bana shan pepper soup. Ji zahra tai kamar ta kwallara uwar qara sabida tsabar baqin ciki, sam qarfin ta ya qare, tinda uwarta ta haifeta ba'a ta6a bata wahala irin haka ba, in aka cere dukan da mashkhur ya ta6a yi mata akan ta fasamai laptop. Sai d'aure tan da yayi jiya a taga sanyi yayi mata duka qafafuwanta suka kunbura, sanan ta fasa goshi.

Muryar mashkhur ce ta dawo da zahra daga tinanin data tafi!! Kee ba magana akeyi miki ba ko sai jikinki ya sake gaya miki. Zahra tanajin haka ba shire ta miqe ta shige kicin da sauri. Ranar zahra tasha baqar wahala kafin ta kammalawa zee chip's da chiken papper, ni kai na amina bayero bazan iya rubuta muku wahalar da zahra ta shaba, zahra bata ta6a zatan tana da juriya ba sai yau duk da kuwa bata saba aikin wahala ba. Haka zahra ta d'ibi chip's da chiken papper ta nufi hanyar falo domin kaiwa zee abinci,, tafiyama da gyar zahra takeyi.

Zahra tana direwa zee chips d'in zee ta miqawa zahra key d'in motarta tacewa zahra jeki motata taqasa ki bud'e ki dakko min jakataa, haka zahra ta kar6i key d'in nan hannu na rawa, ta miqe da kyar ta nufi hanyar futa dag falon. Haka zahra ta fita da kyar, ta zubawa matatakalar benan ido tana tinanin taya zata fara sauka tana cikin wanna halin?. Sai da zahra tafi minti biyar a haka can tai ta maza ta fara sauka dafa kan step d'in benan, tana sauka tana hutawa, idan ta sauka daga kan step uku sai ta huta a haka ta qarasa sauka daga step d'in, ga benan da mugun tsayi.

Bayan ta sauka sai data sake wutawa kafin ta nufin inda motar zee d'in take. Duk da motocin ukune a wajan zahra batasha wahalar gane ta zee ba da yake tasan motar mashkhur kuma tasan ta ahmad. Haka zahra ta bud'e motar ta d'auki jakar zee d'in sanan ta juya. Da kyar zahra take iya tafiya sabida tsabar azabar da takeji a jikinta, tana zuwa bakin matatakalar ta zube wanwar ta zauna a wajan sabida tsabar azaba. Kamar daga sama zahra taji muryar Ahmad yana cewa qanwata lafiya dai koh? Da sauri zahra ta d'aga kai alamun ehh.

Girgiza kai Ahmad yayi tare da tsugunowa gaban zahra yana cewa haba qanwata karkimin qarya mana kalli yarda fuskarki ta kunbura goshin ki ya fashe jikinki duk yayu jajawur, tundaga nesa fa na hangoki kina layi kamar zaki fad'i kum kicemin kina lafiya. Murya a raunane kuma a dashe kamar zahra zatai kuka tace yaya ahmad bani da lafiya, kai na ciwo ga zazza6i ga kuma mura da take damuna yanzuma jiri nakeji. Innalilahi amma baki gayamin ba tun yaushe ne baki da lafiya? Murya na rawa zahra tace tun jiya.

Qanwata ki gayamin gaskiya mashkhur ne ya dakeki koh? Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa bai dakeni ba. Kallan tuhuma ahmad ya watsawa zahra tare da cewa haba qanwata kalli goshinki ya fashe ga hannayanki duk sunyi shati, kuma kice ba dukanki yayi ba, bari naje na same shi, wlh sai ya gayamain dalilin dukan ki da yayi, ai dady amana ya bani ke bazan zuba ido naga yana zalintar kiba, ya qarasa maganar yana qoqarin miqewa. Da sauri zahra ta riqe rigar ahamd cikin kuka take cewa dan Allah yaya ahmad ka rabu dashi wlh yanzu kayi mai magana dukana zai yi, kuma ni wlh ba dukana yayi ba pls yaya ahmad ka rabu da shi, karkai mai magana, sai yayi tinanin ni na gayama wani abun.

Dawowa Ahmad yayi, nan da nan tausayin zahra ya kamashi, cikin raunaniyar murya yace haba qanwata, taya zakice mashkhur bai dakeki ba alhalin ga alamun duka a jikinki, karfa shurunki da haquri ki su cutar da ke, Wlh in baki gayamin abinda mashkhur yayi miki ba yau zan gayawa dady abinda yake faruwa. Da sauri zahra ta d'ago tare da girgiza kai, tana cewa!! Aa yaya ahmad dan Allah karkai hakan sometimes yaya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login