Showing 114001 words to 117000 words out of 411854 words

Chapter 39 - ADALILINTA Complete Hausa Novel

13 Jul 2025

25301

kina bacci?. Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa nayi bacci mana mai ka gani? Naga kin futo da sanyi safiya kin zsuna a kan step kina bacci.

Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa ba bacci nake ba kawai dai ina jiran kane. Gaskiya qanwata ki dena tinanin kina qarama kina tinani? Sunkuyar da kanta qasa zahra tai, batare da cewa komai ba. Ahmad kuwa ci gaa da magana yayi da cewa kinga ke qaramace soosai bai kamata kina qarama ki ringa tinani barkatai ba karfa ki d'orawa kanki wani ciwan kina qarama, komai yayi zafi maganinsa ALLAH. Murya a raunane zahra tace in sha ALLAH yaya ahmad zanyi qoqarin kiyaye hakan, yauwa qanwata haka akeso, pls ki dena tunanin kamar haka? Tom shikenan yaya ahmad na dena.

Kawarda maganar Ahmad yayi da cewa tom taso mu tafi koh? Ba musu zahra ta miqe, suka fara tafiya. Harga Allah zahra ta yiwa Ahmad kyau sosai kuma ta birgeshi sabida uniform d'in sunyi mata kyau sosai, amma sam ba nuna mata hakan ba yana mata kallo d'aya ma ya d'auke kansa daga gareta sabida yasan ita matar aure ce, kuma a'addini haramun ne ya cigaba da kallonta.

Suna isah wajan motar Ahmad ya bud'ewa zahra qofar mota ta gaba ta shiga,, sanan shima ya zagaya gefe ya shiga motar ya tayar, suka fuce daga gidan. Tunda suka fara tafiya ba wanda ya cewa kowa komai kawai dai tafiya suke. Can zahra ta d'ago ta kalli ahmad, amma sai taga sam baya cikin tunaninsa ya tafi wata duniyar tunanin ta daban, da yake an tsayar da danja. Murrya a sanyaye zahra tace yaya ahmad!! yaya ahmad!! Da sauri yadawo daga cikin tunanin daya tafi tare da juyowa ya kalli zahra.

Yana kallata ya kawar da kansa tare da cigaba da tuqi yana cewa qanwata lafiya? Itama zahra kawar da kai tai tare da cewa yanzufa kafin mu futo ka gayamin cewa ba'a so mutum ya ringa yawan tunani amma shine kai yanzu kakeyi?. Ajiyar zuciya Ahmad yayi tare da cewa hmm wlh qanwata wani abune yake damuna shiyasa kikaga na tafi tinanin kullum bana iya isashan bacci da abinnan nake kwana a zuciyata. Allah sarki yaya ahmad ALLAH ya yayema abinda yake damunka amma kai ma kasan ai yawan tinanin baya kawo mafita koh?.

Ehh qanwata hakane in sha ALLAH zan dena, kuma watarana zan gaya miki koma menene, murmushi zahra tai tare da cewa to yaya abdul Allah ya kaimu kaimu lokacin, murya a raunane Ahmad yace ameen ya Allah. Daga haka ba wanda ya sake cewa komai har suka isa makarantar. Ai suna isa makarantar zahra ta saki baki tana kallan ikwan ALLAH. Makarantace ta had'u ta ko ina ta tsaru ta qeru, abinka da makarantar turawa, turawan ma 'yan rasha. Sukana shiga ciki tun kafin su futu daga motar zahra ta fara ganin studen d'in tutawa kala-kala, wasu da guntun hijab irin nata wasu kuma ba hijab d'in mah gaba d'aya a jikin su.


Student d'in Farare ne tasss masu blue eyes, haka Ahmad da zahra suka fita, nan. Mah suna fita zahra ta saki baki sabida yarda take ganin yaran kamar ba a gaske take ganun suba, ji take kamar a tv take ganinsu. Nan da nan hankali ya dawo kan zahra da ahmad kallansu ake sosai musamman ma Ahmad da yake bashi da hasken fata sosai, amma kyakyawa ne na ajin farko kana ganinsa gaya cikakyan d'in Nigeria kuma kyakyawa. Haka Ahmad da zahra suka ringa ratse student har suka wuce office. Ahmad yana kai zahra office akace sai na mata interview, Ahmad kuwa bai jira ba da yake yau suna da lectures, sallama yayiwa zahra yace mata zuwa qarfe biyu zai dawo ya d'auke ta, daga haka yayi tafiyarsa.

Ahmad yana fita zahra tai jugum abinta, sam ta kasa sakewa ga teacher duk tura mata ido sai wani faman kallanta suke, itama zahra d'ai-d'ai take bunsu da idanuwanta. Can kuma wata baturiya tazo ta zauna a kusa da zahra domin yi mata interview. Ba wasu abubuwa masu wahala aka tambayeta ba, kuma duk abinda aka tambayeta tana iya bada amsa duk da ba wani sosai take gane turancin nasuba, dan ma tana yawan kallan tashar MBC 2️⃣ ne shiyasa take gane wani turanci da yake kusan irin turanci d'aya suke a america.

Bayan an gama yi mata interview tambayar ta sunanta matar tai. Lokacin da zahra ta fad'i sunanta duk teachers d'in gurin murmushi sukayi kowa yana qoqarin fad'ar sunan duk da kuwa ba iyawa sukayi ba. Fatima zahra suke qoqar fad'a wasun sun fad'a dai-dai wasu kuma akasin haka. Sai da suka tsare zahra da tambayoyi iri ri, kowa cewa yake ita 'yar Nigeria ce? Koma wana yare takeji a Nigeria harda masu cewa sai ta yimu hausa. Haka dai tai zahra ta ringa bin teacher d'in nata tana amsa musu duk tambayar da sukayi mata.........


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240


Typing............

*pqge 59*

Sai da suka tsare zahra da tambayoyi iri ri, kowa cewa yake ita 'yar Nigeria ce? Koma wana yare takeji a Nigeria harda masu cewa sai ta yimu hausa. Haka dai tai zahra ta ringa bin teacher d'in nata tana amsa musu duk tambayar da sukayi mata.........

Bayan sun gama yiwa zahra tambayoyi direct ss 2 suka kai ta. Har sit d'in zamanta teacher d'in ta raka zahra, a sit d'in farko ta zaunar da ita sanan ta gabatarwa da 'yan class zahra, da sunanta, sanan tace su ringa kiranta da zahra dan sunan yafi musu sauqin fad'a, daga haka ta koma office. Zo kaga yarda 'yan class suke kallan zahra kamar su cunyeta. Ma dai-dai cin class ne student d'in ajin duk mata ne, kuma basufi su ashirin ba, ga A. C da fanka sai hurowa take duk 'yan ajin kowa da laptop d'in sa a kan dsk d'in shi.

Cikin lala6awa uncle d'in su yake teacher d'in su, ba hantara ba duka bare zagi, suma d'aliban ba laifi suna mayar da hankalinsu kan karatu sam basa yawan surutu a ajiki in dai uncle ko aunty tana nan. Kai ranar zahra taga yarda ake teacher ba irin Nigeria ba, duk da kuwa itama zahra babban makaranta suke a Nigeria amma sam bata kai tsaruwar wanan ba. After 30 mints sai an kawowa kowana dalibi abin da zai ci, irin suke cake, biscuit, spring roll ki, pizza, juice da dai sauran sun.

Lokacin da akan fita break kuwa student d'in school har d'in har layi suke wajan kallan zahra, zahra kuwa a zuciyarta tace ai ba nice abin kallo ba kune abin kallo. 😂 haka dai sukai ta kallon zahra wasu daga cikin 'yan class d'in su zahra kuwa sai maqale mata suke, wasu kuwa ko kallo bata ishe suba, dama kunsan su tura suna da kishi kuma basaso ace wani ya fiso ko kuma su ringa zubar da mutunci, su. Ranar fa zahra taga gift sosai daga wajan 'yan class d'in su, irin su coculet da alawowyi da dai sauran su.

Sam zahra bamai san surutu bace da mutane amma haka ta ringa daurewa, tana kulasu, duk dan karsuce tayi musu rashin mutuncin. Lokacin da aka tashi daga school yaya ahmad bai zoba, haka class meant d'in zahra har office suka rakata. Wasu kuwa in iyayansu sukazo d'aukar su har kawosu suke wajan zahra wai sai sunzo sunga 'yar Nigeria. Kai a ranar zahra tayi farin jini ba laifi, nikuwa amina bayero nace inama nice. 😂🙈

Yaya ahmad bashi yazo d'aukar zahra ba har sai wajan qarfe uku na rana yazo ya d'auki ta, Haka yay ta bata haquri a hanya yana cewa fasu futo lectures da wuri bane shi yasa, har sai da ya tsaya ya siya mata abinci a reswerrens. Suna isa gida zahra ta wuce sama Ahmad kuwa ya wuce part d'in shi, lokacin da zahra ta bud'e qofar fallon a garqame ta jita zuciya na bugun uku-uku zahra ta fara biga qofar a hankula, bama taso ta danna qararawar sabida kar tayiwa mashkhur laifi.

Tafi 10 minti a tsaye tana bugun, ba'a bud'e mata, ba, sai can taji ana qoqarin bud'e qofar, da sauri zahra taja baya, domin kar yaya mashkhur ya kai mata mari. Amma da mamakin zahra sai taga zee ce ta bud'e mata. Tana sanye da riga pink mai kamar singlet, sai wani mini skirt shima pink wanda ko guiwar ta bai gama qarasawaba, kan nan nata yasha gyara sai kyalli yake gashinta a baje har gadan bayanta, ga uban farace data tara a hanunta zaqo-zaqo yashan kala pick.

Zahra kuwa batace komai ba ta ra6e ta shige ta gefan zee d'in, tana shiga bata tsaya ko ina ba sai bedroom d'in ta. Ajiye ledar abincin tai da jakarta wanda class meant d'in ta suka ciko mata ita tab da kayan zaqi, da sauri ta wuce toilet tai alwala, sanan ta zura hijab d'in ta har qas ta shinfid'a dadduma ta fara gabatar da sallar la'asar bayan ta idar tayi addu'o'i ta., ledar takeaway d'in abincin da yaya ahmad ya suyo mata ta janyo, sabida wata baqar yunwa takeji.

Pride rice ce wanda taji had'in salat, carbage, bama, carrot, green biens, da meal d'in gwangwani, sai dankalin turawa a kai, d'ayan takeaway d'in kuwa ckching papper ne a ciki, sunsha had'a ba wai, d'a yar ledar kuwa lemukane masu sanyi, d'ayar ledar abincin ma zahra bata samu damar bud'ewa ba, sabida wanda ta bud'e ma sun mata yawa ba iya cinyewa zatai ba. Sai da zahra taci abincin ta qoshin sosai sanan ta rufe ragowar ta mayar kan table ta ajiye, tana qoqarin cire uniform tai wanka taji ana knocking d'in qofar ta.

Da sauri zahra ta shiga toilet ta wanke hanunta sanan ta futo, ta nufi hanyar qofar bedroom d'in. Tana bud'ewa taga zee tsaye, hannu riqe da ugu, zee tana ganin zahra ta fara binta da wani irin kallo wanda ita kanta zahra batasan wana irin kallo bane. Zee tafi minti biyar tana qarewa zahra kallo tin daga kan lips d'in ta ta dawo kallan Breast d'in zahra, sanan ta zubawa hips d'inta ido, sam zee ta kasa cire ido daga kallon ugun zahra. Zahra kuwa mamaki ne ya kamata ganin irin yadda zee ta shagala da kallonta, kamar taga wata sabuwar halittar, dan da namijine yakewa mace irin kallon da zee takewa zahra da haka za'a cemai d'an iskane so yake ya lalata ta.

Murya zahra ce ta dawo da zee daga duniyar kallanta data tafi? Cikin yaran English zahra tace aunty zee lpy?. Da sauri zee tai firgigid ta kalli zahra cikin sarqewar murya tace noo ba komai kawai dai inaso ki futo ki dafamin abinci ne, yunwa nake ji. Okay aunty bari na cire kaya makaranta nai wanka. Nan da nan zee ta had'e rai tace aa ni yanzu zaki futo ki dafamin kina house girl wato 'yar aiki, kina wani iyayi, to ba wani wanka da zakiyi a haka zaki dafamin abinci. Tom zahra kawai tace, sanan ta koma ta d'auki mayafinta ta rufe jikinta, haka zee ta tusata a gaba har qofar kicin, sanan tace ta dafa mata coffee da cake.

Zahra ba musu ta shiga ta fara dafawa zee abinda tace, kwa6a cake d'in ta farayi, bayan ta kwa6a ta dora coffee, tana zauke coffee d'in ta zuba kwa6in cake d'in a oven sai da ta saita hutar oven d'in sanan ta rufe. Har zahra taza futo taji muryar mashkhur, yana cewa sorry my zee abu mai mahimmanci nake a Ciki shiyasa kikaga na dad'e. Cikin shagwa6a zee tace ai honey sai da nace zan tayaka kace aa, wai sabida mai bakaso mu ringa kasancewa tare ne?. Shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba.

Can kuma zee ta sake cewa honey ya kamata fa ka bani tariyinka? Gigiza kai mashkhur yayi tare da cewa no zee ki barshi kawai ba yanzu ba. Okay honey tinda bazaka gayamin kai waye ba yau ni zan gayama koni wace, mashkhur kuwa shiru yayi nan ma bai ce mata komai ba, zahra kuwa tanajin haka ta sake la6ewa a bakin cikin d'in domin jin mai zee zatace, duk da kuwa bata gane wani turanciin zee d'in inta fad'a.

Gyara zama zee tai cikin yaran English ta fara bawa mashkhur tarihinta kamar haka! Mahaifiyata haifarfiyar rasha ce, mahaifin mamana kuwa babban mutum ne yana da kud'i sosai, duk yaransa mazane, maza uku mahaifiyata ce kawai mace, kuma itace 'yar autar cikinsu. Mahaifina kuwa haifafan d'an NIGERIA ne kuma musulmin, mashkhur kuwa yana jin haka ya d'ago da sauri tare da firta Nigeria kuma musulmi? Gyad'a kai zee tai alamun eee. Ba iya mashkhur ba har zahra da take la6e a kicin sai da mamaki ya kamata.

Zee kuwa cigaba da magana tai kamar haka!! Mahaifina yace min iyayansu su biyu suka haifa shida qanwarsa zainab. Kuma iyayan su talakawa ne sosai basu da komai da kyar suke iya cin abinci a rana, kuma duk 'yan uwan mahaifin babana suna da kud'in sosai, kawai taimaka mai ne bazasuyi ba. a haka dai har mahaifinsa ya rasu, bayan ya rasu zuciyar mahaifiyarsu ta biga itama ta mutu. A lokacin mahaifina da qanwarsa sunga tashin hankali sosai, akan nan dai suka cigaba da cikin qonci da talauci, gashi duk 'yan uwansu basa tai maka musu. Bayan shekara uku da mutuwar iyayan mahaifina qanwarsa zainab ta fara cuta, ciwan hantane yake damunta haka mahaifina yay ta jinyar ta cikin talauci har ciwan hanta ya kasheta.

Hankali mahifina ya tashi sosai dan a lokacin ma yayi qoqari komawa Christian da yake a tsakiyar yarabawa suke, kuma duk kafirai ne, musulman kad'an ne suma su mahaifin nawa yarabawa ne, suna zaune a state d'in shiru zee tai tana qoqarin tuno sunan state d'in da mahaifiyata yake, can kuma tace Lagos. Bayan qanwar mahaifina zainab tayi wata uku da rasuwa mahaifina ya samu ofer d'in tafiya rasha karatu. To a lokacin dayazo karatu suka had'u da mahifiya a school, mahaifiyata taso mahaifina sosai, duk da kuwa musulmi ne.

A sannu a hankali suka fara soyayya da mahaifina, soyayyar su tayi qarfi sosai, hakan ne yasa mamana ta samu mahaifiyata da magar aure su. Mahaifin mamana ya amince mahaifiyar mamana kuwa bata amince ba. Amma mahaifin mamana yayi watsu da maganar mahaifiyar mamana da yake 'yan uwanta maza sun goya mata baya akan haka. Lokacin da mamana tazowa da mahaifina maganar bai yi gaddama ba ya amince da hakan, daga haka kuwa aka d'aurawa musu aure. Lokacin qanqani mahifina ya zama mai kud'i gaske da tai makwan dukiyar mamana.

Bayan iyayena sunyi aure da shekara biyar mamana ta haifeni, A lokacin babana ya roqi mamana alfarma akan ta amince na zama musulma a sa mun sunan qanwarsa zainab da yake babana yana qaunar qanwar tasa zainab. Mahaifiyata kuwa cewa tai aa sai na girma zan za6i wana addi ni nake so, amma ta amince a samun zainab d'in, haka kuwa kayi aka samun suna zaiba sukuwa dangin mahaifiyata suke kirana da zee. Daga haka zee tai shiru alamun labari ya qare, mashkhur kuwa duk sai yaji jikinsa yayi sanyi, dajin labarin zee musamman ma yarda yaji mahaifina ya tsinci kasanta a halin rayuwa, kuma ba wanda ya iya tai maka mai.

Tunatarwa........

Gaskiya mutane ya kamata mu ringa tausayawa talakawa da marayu, ko dai wani na qasa damu, yanzu a zamanin nan tai mako yayi qaranci, sam masu kud'i basa san tai makawa na qasa da su komai dukiyar su. Ta kusani cewa abinda ka bayar shine rabanka, kuma rashin tausayawa na qasa da kai yana jawo musifu a qasa. Karku manta manzan Allah S A W, shine shugaban duniya yafi kowa muqami da sarauta da daja, Allah wanda ya halice kowa yafi san shi fiye da ko wana bawa, amma manzan Allah da yafi kowa arziki, baya kwana da ko kwallin dabino, sabida kulluma akaci abinci a gidansa sadakar ragowar ake komun yawansa, bai yarda ya kwana da wani ba a gidan saba wasu kuma a waje suna jin yunwa, baya tanadin na gabe, duk arzikinsa na mutane ne.

To ku duba kugani, d'an gatan Allah ma yake temako bare kai wani bawa, qarshema duk abinda ka tara tafiya zakai ka barshi a duniya bazaka tafi da komai ba sai da aikin na alkhairi . In kana taimakawa na qasa da kai kaga da kyau in kuma bakayi hmmmmmmmm Allah dai ya kyauta kawai dan sai kayi nadamar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login