Showing 3001 words to 6000 words out of 140483 words

Chapter 2 - 'YAN UKU COMPLETE

11 Jul 2025

19327

tsakiyar layin Wanda bishiyu suka yiwa titin runfa.



Wani had'adden gida ne unguwa guda a wajen suna k'arasawa sojojin dake tsaron gate d'in suka bud'e musu gate suka shiga basu tsaya ba sai da suka kai wajen wani dogon bene Mai kyawun gaske sannan suka yi parking.




Sojojin suka diddiro daga motar gaba d'ayan su suka zagaye army green d'in.

D'aya daga cikin sojojin ne ya bud'e bayan motar sannan ya ja gefe ya k'ame.



Mutumin dake cikin motar ya ziro k'afar sa mai d'auke da wani takalmi Mai matuk'ar kyau irin nasu na sojoji sannan a hankali ya fito.



Wayyo kuzo ku ga kyau iya kyau a wajen guy d'in nan kamar balarabe dogone sosai fari sol da shi har yellow yake yi gashin kansa kamar na indiyawa gashi bak'i wuluk yana shek'i sannan askin dake kansa ma abin kallo ne Yana da dogon siririn hanci ga pink lips abinda zaifi d'aukar hankalin mutum shine idanun sa farare ne kar k'wayar idon Kuma bak'i wuluk kamar yadda gashin kansa yake da Kuma gashin girarsa da ta kasance siririya mai shape kamar zata had'e ga zara-zaran eye lashes kamar mace.



Guy d'in ya had'u iya had'uwa kana kallon sa ka ga k'akk'arfan namiji Yana sanye cikin kak'in su na sojoji Wanda kamar dan shi kad'ai aka d'inka su saboda yadda suka yi masa matuk'ar kyau kamar ka sace shi ka gudu.



Wani b'angare ya kalla ya saki wani sassanyan murmushin da ya bayyana dimples d'insa dake gefe da gefen fuskar sa da Kuma fararen jerarrun hak'oran sa.



Sannan cikin k'asaita ya fara tafiya kan jan carpet d'in da aka shimfid'a masa Wanda a jiki aka rubuta da manyan bak'i WELCOME BACK TO HOME OUR HAPPINESS MG ABDUL MALEEK.



Wata kyakkyawar mata ce a tsaye tasha kyau cikin wani tsadadden less orange colour wuyan ta sanye da sark'ar gold da d'an kunne haka ma zobunan hannunta da warwaron ta duk na gold ne fara ce sol sannan suna kama sosai da MG wato major general.




Gefe da gefen ta wata budurwa ce da Kuma saurayi kyawawa kamar larabawa.


Yana k'arasawa budurwar ta ce "Welcome ya Maleek," cikin dakakkiyar muryar sa mai dad'in sauraro ya ce "Thank you Rinaz," saurayin Kuma ya yi huging d'insa ya ce "Sannu da zuwa ya Maleek," Nan ma ya ce "Thank you Fauwaz," daga haka ya nufi wajen mahaifiyar su wacce tun fitowar sa daga mota take sakin murmushi.




Yana k'arasa ya rungume ta ya ce "I really miss you Ummina," ta ce "mee too I miss you much more my son," sannan ta bashi kiss a goshi ta ja hannunsa zuwa cikin falon.



Falon ya tsaru iya tsaruwa babban falone na gaske Yana d'auke da kujera set uku ga wata tafkekiyar plasma a falon da home speakers ga wani lallausan carpet da wasu fulawoyi da aka k'awata falon da su ta kowacce kusurwa ga wasu show glass na jikin bango dake cike da kayan k'amshi da wata red da blue d'in haske a ciki can gefe kuma had'adden daining ne mai kujeru birjik da Kuma ba babban kitchen tsayawa fad'in had'uwar falon ma b'ata lokaci ne.



Zama suka yi dukan su a falon Ummi ta ce "Son ya hanya?" Ya ce "Ummi hanya lafiya," sannan ya mik'e ya ce "Ummi zanje part d'ina I want to have some rest," ta ce "Ok ga abinci yana jiran ka," yatsina fuska ya yi ya ce "Amma Ummi kinsan ni bazan ci abinci 'yan aikin ki ba?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "ai yau da kaina na girka maka saboda ban fita office ba amma kasan dole sune zasu dinga yin girki a gidan nan," shagwab'e fuska ya yi ya ce "Amma Ummi duka fa basu iya komai ba?" Ummi ta ce "ka ga ya isa zan canja ma Mai yi ma girki yanzu kaje idan ka shirya kazo dan Daddyn ka ya bayar da sak'o a fad'a maka sannan ka tabbatar kaje ka gaida Umman ku," tab'e baki ya yi sannan ya yi hanyar fita Yana cewa "To," yana fita Salman ya biyo bayan sa Wanda Salman ya kasance soja ne sannan amintaccen Maleek Kuma d'a a wajen k'awar Ummi.



Kai tsaye part d'insa ya nufa duk inda ka kalla 'yan aiki ne a gidan suna ta hidima duk wacce ta ganshi sai ta gaishe shi tun Yana amsawa har ya dena dan ya gaji da magana.



Tun kafin ya k'arasa sojojin dake wajen suka bud'e masa k'ofa ya shige falone na gani na fad'a ya yi kyau matuk'a komai na d'akin fari ne yasha ado kamar d'akin amarya stairs ya haye nan ma wani falon ne mai kyawun gaske bedroom d'in sa ya shige sannan ya fad'a bathroom sai da ya d'au lokaci sannan ya fito yana tsane sumar kansa da towel cikin k'ank'anin lokaci ya shirya cikin black jeans da red riga sai k'amshi yake zabgawa juyawa ya yi ya fita daga part d'in.


Ko da ya fito sojojin sa suka biyo bayan sa d'aga musu hannu ya yi suka tsaya shikuma ya cigaba da tafiya abinsa har sai da ya je wani b'angare shiga ya yi da sallama a bakinsa wata mata ce kashingid'e a kan carpet ga fruits a gaban ta 'yan aiki zagaye da ita wasu na yanka fruits wasu na mata tausa k'arasawa ya yi ya zauna ya ce "barka da rana Umma," kallon sa ta yi ba yabo ba fallasa ta ce "yawwa," shi kuma ganin yadda take amsa masa ne ya b'ata masa rai ya mik'e tare da fad'in na barki lafiya ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya jiyo muryar ta tana cemasa "Ya zaka Tafi baka tambayi Nasreen ba?" Ko kallon ta bai juya ya yi ba ya fice.
[10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 2


Maleek na fita daga part d'in na Ummi ya nufa a garden ya hangi Nasrin zaune kan wata kujera sai zabgawa wata 'yar aiki mari take yi kamar wata uwar ta tsaki ya ja kamar Nasrin tasan Yana tsaye a wajen ta waiga suna had'a ido ta tashi da gudu ta nufe shi rungume shi tayi niyyar yi ya tsayar da ita ya ce "Meye haka?" Ya fad'a a d'an tsawa ce had'e fuska ta yi ta ce "Haba ya Maleek murnar ganin ka ce fa sannan kasan wani Abu kuwa jiya Daddy yazo sannan anyi maganar auren mu," kallon banza Maleek ya yi mata ya ce "Bangane me ki ke son fad'a ba kinga idan ma kina wasa ne ki dena nifa ban tab'a cewa ina sonki ba kinga maganar aure it is impossible thing,"


"Haba MG bangane auren mu bazai yiwu ba Amma aini ina sonka Kuma wallahi ko baka sona sai ka aureni," wani murmushi Maleek ya yi ya ce "Idan kin gama zaki iya barin nan wajen if not Wallahi saina buge ki stupid kawai," da gudu ta yi part d'in Umma tana kuka shi Kuma ya ja tsaki ya tafi.



Bud'e masa k'ofar falon sojan sa ya yi ya shige ya samu su Ummi zaune a falo suna kallo zama ya yi ba tare da ya yi magana ba Ummi ta ce "Muje kaci abinci son," duka daining suka nufa suka fara cin abinci sai dai shi Sam ba wani cin abincin yake ba tashi ya yi kawai yabar daining d'in ya koma falo ya zauna fuskar sa babu alamun wasa.



Ba Wanda ya yi masa magana har suka gama cin abincin sannan suka koma falon dukansu shafa kansa Ummi ta yi ta ce "My son meye matsalar?" Kallon ta ya yi ya ce "Ummi dagaske ne maganar da Nasreen ta fad'amun wai za ayi mana aure ni da ita?" Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Hak'uri zaka yi son kasan halin yayan Daddyn ku Sam bashi da hak'uri jiya haka yazo nan ya dinga fad'ar maganganu har Daddyn ku ya kira dole ya baro Landon yazo aka yi maganar auren yanzu haka one month aka sa bikin shiyasa mahaifin ku ya kira ka ya ce lallai ka dawo a yau," cije leb'e MG ya yi sannan ya ce "Yanzu Ummi ina Daddy yake?"



"Ya koma Landon yau da safe," jinjina kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi Sam bansan meyasa Uncle yake son ganina a cikin damuwa ba sannan ni fa ba sonta nake ba," Ummi ta ce "nasani son amma kayi hak'uri wata rana sai labari," gyad'a kai ya yi ya mik'e ya fice.



Part d'in sa ya koma ya kwanta bacci ne ya d'auke shi.



Nasreen Kuma da kuka ta shiga falon ta fad'a jikin Umma a rikice Umman ta ce "Lafiya Nasreen mai ya faru?" Cikin kuka ta ce "Umma Wai kinji baya sona," tsaki Umman ta ja ta ce "kyale banza duk da baya sonki aure ke da shi babu fashi ya yi duk abinda ya ga dama amma sai ya aure ki Kuma mun kwashe dukiyar d'an iska," Nan dai Umma tai ta rarrashin ta.



B'angaren 'yan uku kuwa Sabeeha ce a kitchen tana yin girki Rashida ta shiga sai wani shan k'amshi take tana yatsina ko kallo bata ishi Sabeeha ba fridge ta bud'e ta d'auki ruwa ta juya zata fita Sabeeha ta ce "Rashida baki ji ba," waigawa Rashida ta yi ta ce "Lafiya kuwa?" K'arasawa gaban ta Sabeeha ta yi ta ce "Akwai maganar da nake son fad'a miki amma sirri ce bana so wani yaji,"



"Ina jinki," cewar Rashida murmushin mugunta Sabeeha ta yi sannan ta ce "Wai kuwa kinsan yallab'ai yana mutuwar sonki kuwa?" Zare ido Rashida ta yi kamar gaske ta ce "nidin Kuma?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "sosai ma domin jiya naji yana waya Yana sanarwa da abokin sa shi duk duniya ke yake so," tsalle Rashida ta yi ta ce "Nagodewa Allah dama Wallahi ina mutuwar son shi kamar raina amma dan Allah ki tayani rufe sirrina bana so Farida ta sani dan gaskiya ina tsoron hukuncin da zata yanke mun," tsaki Sabeeha ta yi ta ce "karki damu ni nan zan taimake ki karki damu tunda ai shima Yana son ki kinji?" Gyad'a kai Rashida ta yi cike da gamsuwa sannan ta ce "Amma aike d'in bangane ki ba a cikin 'yan ukun?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Manta kawai ni dai burina na taimake ki dan haka karki damu kanki wajen sanin wacece ni cikin 'yan uku," tana gama fad'in haka ta juya ta cigaba da abinda take yi Rashida Kuma ta fita zuciyar ta fal farin ciki.


Haka Sabeeha tai ta jan Rashida tana zugata akan cewar Yallab'ai na mahaukacin sonta ya yinda shi baima san wainar da ake toyawa ba.



Zaune Yallab'ai yake shida wani gabjejen abokinsa suna fira yallab'ai ya kalli abokin sa cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Gaskiya Habibu ina mutuwar son yarinyar nan dake yi mana girki a cikin gidan mu saboda gata doguwa kyakkyawa ga iya girki dan tunda nake a rayuwata ban tab'a cin girki mai dad'in na ta ba," jinjina kai Habibu ya yi ya ce "Yanzu kana nufin auren ta zaka yi ko me?" Gyad'a kai Yallab'ai ya yi ya ce "Sosai ma kuwa kawai abinda nake so da kai shine kai nake son aikawa wajen ta," Habibu ya ce "Haba dai ai gara kaje da kanka ka gaya mata," girgiza kai Yallab'ai Kamis ya yi ya ce "A'a gaskiya kamar ni da matsayina naje wajen ta bayan 'yar aikina ce," Habibu ya ce "Shikenan yanzu yaushe zan same ta d'in?"


"Ka bari zanyi ma magana kawai," Habibu ya ce "To Shikenan an gama," haka firar ta su ta tashi.



Sabeeha ce ita da Rashida a kitchen suna fira idan ka kalle su zaka d'auka k'awaye ne domin fira suke suna dariya kamar gaske Rashida ta ce "Yanzu kina ganin anjima ya yi daidai dana fad'a masa abinda ke zuciya ta?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "Sosai ma kuwa d'azu ya kirani yake ce mun Wai Yana son ki ya lura kwana biyu munfi kusa ni da ke shiyasa ya fad'a mun sannan anjima Yana neman ki a falon Farida," d'an zare ido Rashida ta yi ta ce "Amma kina ganin ba matsala?"


"Bawani matsala gani nake yi ya yi hakan ne dan ba k'aramun so yake Miki ba kuma son naki ne yasa yace kije har falon Farida dan da alama so yake ya nunawa Farida kalar son da yake Miki," wani wawan tsalle Rashida ta yi ta ce "Wayyo dad'i Amma nagode sosai," cikin murmushi Sabeeha ta ce "Karki damu," haka suka gama hirar su Sabeeha ta tafi tabar Rashida a kitchen domin dama kawai fira ce ta kai su kitchen d'in.



Da yamma Yallab'ai Kamis da Farida na zaune a falon Farida suna yin fira sai Sabeeha ta shiga falon d'auke da tray a hannunta da fruits a ciki har k'asa ta tsugunna ta gaishe su Yallab'ai Kamis ne kawai ya amsa yayin da Farida ta galla mata harara dan ita bata son ganin wacce ta fita kyau musamman idan mijin ta na wajen.



Sabeeha kuwa tana ajiyewa ta mik'e ta fita tana fita ta kalli Rashida dake tsaye tasha kwalliya ta ce "Yace ki shiga," cikin farin ciki Rashida tasa kai cikin falon ya yinda Sabeeha ta mak'ale tana lek'e tana dariyar mugunta.



Da sallama Rashida ta shiga sai wani yanga take tana lankw'asa jiki da kallon Mamaki suka bita ba tare da wani tunani ba Rashida ta k'arasa ta zauna d'ayan gefen Yallab'ai Kamis ta ce "Barka da hutawa masoyina a gaskiya naji dad'in cewar da kayi kana sona dama Kuma na dad'e ina mahaukacin sonka dama damuwata ka ce baka sona Amma tunda ka furta hakan da bakin ka cewar kana sona naji dad'i sosai sannan ina so asa bikin babu yawa saboda bana so abin ya yi nisa nafi so asa nan kusa domin na baka kulawar da ta dace ba irin ta wawiyar matar ka ba," duk abinda take da kallo suka bita sai da ta kai k'arshe sannan Yallab'ai ya mik'e ransa a matuk'ar b'ace saboda ba wacce ma bata kwanta masa a rai cikin 'yan aikin gidan ba kamar Rashida dan dai kawai Farida na sonta ne yasa bai kad'a keyar ta gidan su ba.



Ya ware zabgegen hannunsa ya zabgawa Rashida Marin da sai da ta fad'o daga kujera tana ganin stars bata gama wartsakewa ba ya Kuma k'ara mata wani Marin ya yi ball da ita har sai da ta buge da jikin kujera goshin ta ya fashe kuka ta fashe da shi tana ihu.



Cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Ke dan uwar ki ni sa'an ki ne da zaki zo kice kina sona shegiya munafuka so kike ki had'ani da sarauniya ta ko?" Farida ma cikin b'acin rai ta mik'e ta ce "Dama duk abinda ki ke yi dan ki aure mun mijine aikuwa Wallahi yau sai kinci uban ki a gidan nan sannan daga yau sai kinbar gidan nan munafuka kawai," duka suka rufe Rashida da shi sai ihu take yi gashi babu Mai ceto.



Sabeeha tana daga waje har rik'e ciki take yi saboda dariya sannan ta nufi d'akin su da gudu tana k'wala Kiran "Sabreen sister Sameeha dear kuzo ku yi kallo," da gudu suka fito suka bita ragowar 'yan aikin gidan jin ihun da 'yan uku ke yi suma suka fito suka nufi falon su ma.



Kowa tsayawa ya yi Yana kallon yadda Farida ke yawo Rashida daga bene sunyi mata jinajina sai ihu take yi tana bada hak'uri Amma ko sauraron ta basa yi har tsakiyar falon suka jawo ta suka yi wurgi da ita zabgegiyar dorinar hukunci Yallab'ai ya karb'a ya fara zabga mata sai ihu take yi har sai da ta kasa motsi sannan ya kyale ta ya koma gefe ya zauna.



Sabeeha kuwa har lokacin dariya take yi harda rik'e ciki wani farin ciki take yi Sabreen ma sai taya ta dariyar take yi Sameeha kuwa tun tana dariyar har ta koma kuka tsabar tausayin Rashida galala su Sabeeha suke kallon yadda take hawaye sannan suka cigaba da dariyar su.



Farida ta ce "Dan uban ki ki dena yi mana ihu a falo ki tashi ki bar mana gida ko insa a fitar dake daga cikin gidan nan," mik'ewa Rashida ta yi dakyar tana tafiya har wani layi take yi suna had'a ido da 'yan uku Sabeeha ta kashe mata ido d'aya.



Juyawa Rashida ta yi ta fita daga gidan ya yinda kowa ya watse.



Da murna su Sabeeha suka shiga d'akin su sai taka rawa suke yi ita da Sabreen ya yinda Sameeha ta zauna gefen gado tana kallon su.



Sabreen ta d'ebo shoky tana cewa "Sabeeha dear saura Kuma Farida itama ta gane kuren ta," Sabeeha rawa take yi kamar wata macijiya ta ce "Ai yanzu aka fara wasan," Sameeha ta ce "Ni dai please Sabeeha sister ki dena abun nan," ko kallon ta basu yi ba suka cigaba da rawar su sai da suka yi Mai isar su sannan ko wacce ta tafi wajen aikin ta.


Zaune Maleek yake a falon sa wasu takaddu yake dubawa wani soja ya shiga falon ya Sara masa sannan ya ce "Ranka ya dad'e kana da bak'o," sai da ya ajiye takardar hannun sa sannan ya kalli sojan ya ce "waye?" Cikin ladabi sojan ya ce "Umar ne ranka ya dad'e," cikin Mamaki Maleek ke kallon sojan sannan ya ce "Ok ya shigo mana," sanna ya cigaba da abinda yake yi.



Umar ne ya shiga falon ya k'arasa gaban Maleek ya Sara masa hararar sa MG yayi sannan ya ce "Yau Kuma me ka ke ji da sai an nema maka izinin ganina?" Zama gefen sa Umar ya yi ya ce "Wallahi Maleek baka da kirki yanzu ka shigo gari Amma ba labari yanzu ma fa sai da na je wajen Ummi ne Rinaz ke fad'amun ka dawo shiyasa ma yanzu nace a nema mun izini kar nazo a harbe ni tunda haushina ake ji," kad'an Maleek ya yi murmushin gefen baki sannan ya kalli Umar idanun sa sunyi jajur ya ce "Umar kasan auren dole?" Dariya Umar ya yi ya ce "Yeah I know it but for what reason ka tambaye ni?" Tab'e baki Maleek ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login