Showing 18001 words to 21000 words out of 140483 words

Chapter 7 - 'YAN UKU COMPLETE

11 Jul 2025

19344

tabbata ba k'aramun budiri zata had'a ba.



Maleek kuwa yana fita ya ga Nasreen cikin motar ta ta figo ta da gudu kallo d'aya ya yiwa motar ya d'auke Kai yana yiwa Salman magana.


Gurin ta k'arasa ta ce "Ya Maleek," waigawa ya yi ya kalle ta tasha kwalliya cikin wata doguwar riga Mai k'aramun mayafi ta wani d'aura shi a ka sai kace ba matar aure ba yatsina fuska kawai ya yi ta ce "Dama bikin friend d'ita ce ko zamu je tare?" Kallon Mamaki ya yi mata domin bai ma san zata fitan ba ya ce "No jeki abinki," ta juya ta tafi tana wani karairaya shi kuwa ko kula da abinda take ma bai yi ba dan hankalin sa na gun Salman Yana fad'in "Ina so ku bincika mun garin ina so nasan komai a kanta," Salman ya ce "angama ranka ya dad'e," shi Kuma ya wuce part d'insa Salman kuwa mota ya shiga tare da wasu sojoji suka bar gidan.
[10/25, 7:35 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 5

Sabeeha kuwa mota suka samu suka tafi gida suna sauka a bakin titi suka tafi a k'afa har zuwa k'auyen su hango mota suka yi a k'ofar gidan su Sabeeha ta da fa goshi ta ce "Na shiga uku waccan mayen ya zo kenan?" Sameeha ta ce "Anya ba wani abu Kawu ke k'ullawa ba?" Zare ido Sabreen ta yi ta ce "Kai kunga fa mai gari can har ma da d'ansa waccan Mai k'aton Kai lallai akwai abinda kawu ke k'ullawa," tunawa da wani Abu da Sabeeha ta yi ne yasa ta ja da baya su ka ce "Meya faru?" Sabeeha ta ce "Kun manta da maganar kawu ne da ya ce nan da sati d'aya zai yi mana aure?" Ai take dukan su suka tsure Sabreen ta ce "Anya kuwa ma je gida kuwa dear Dan Wallahi aka aura mun Dauda mutuwa zanyi," Sameeha ta dafe k'irji ta ce "Wallahi da na auri faruk gara na mutu banyi aure ba," Sabeeha ta ce "Ku kwantar da hankalin ku ba Wanda zamu aura cikin su ku zo ku ji wata magana," rad'a tayi musu aikuwa suka shek'e da dariya suka nufi gidan kamar basu da wata damuwa.



Da sallama suka shiga gidan turus suka tsaya ganin akwatuna da cofee guda shida sai bak'ake guda biyu.



K'arfin hali Sabeeha ta yi ta k'arasa tana kallon Sadam dake zaune kan tabarma sai wani hura hanci yake yi yana wani karkad'e jiki da hanky shi lallai ga d'an gayu gashi bak'i k'irin da shi da jajayen idanu gefen sa kuma Kawu ne shi da D'ansa faruk wanda Sam shi ba halinsa d'aya da Kawu ba kawai dai Sameeha bata son shi da aure ne amma shi ba ruwan sa da takura musu.



Daga d'aya gefen Kuma Mai gari ne tare da Dauda d'ansa daga can Kuma Abba ne ya yi jugum kamar Wanda aka yiwa mutuwa yana kallon ikon Allah Wai a matsayin sa na mahaifi sai dai kawai ya ga an kawo kayan lefen 'ya'yan sa ba tare da ko izinin zance ba Wanda ya zo ya nema wajensa.



Sabeeha na k'arasawa ta d'urk'usa ta gaishe su tana washe bakin da iyakar sa bakinta amsawa suka yi banda Kawu Bala da ya aika mata harara bata damu ba ta mik'e sannan ta kalli su Sabreen da suka yi mutuwar tsaye ta kanne musu ido d'aya take suma suka baje hak'ora suka k'arasa suka kwashi gaisuwa.



Kawu ya ce "Naji dad'i da ku ka zo domin ayi komai a gaban ku wad'an nan akwatunan da ku ka gani naku ne," ya nuna guda shida ya ce "wannan sune naki ki godewa Allah ki samu mai dukiya," ya fad'a yana nuna Sabeeha sannan ya ce "ku Kuma ko wacce d'ai d'ai," Mai makon ya ga sun had'e rai ko su tubure kawai sai ya ga suna ta washe baki Sabeeha ta ce "Wayyo murna yau nice da kayan aure har haka amma naji dad'i yanzu yaushe ne auren?" Shi kansa Abba mamakin su yake yi Sabreen ta ce "Nima murna nake yi," Kawu Bala kuwa had'e rai ya yi domin ba haka yaso ba domin shi burinsa ya k'untata musu amma sai ya ga sai rawar Kai suke yi ya ce "Jibi ne d'aurin auren," Sabeeha ta ce "Dan Allah Kawu a k'ara mana ko kwana biyu ne saboda mu shirya," har Kawu zai yi magana Sadam ya ce "A k'ara musu," Kawu ya ce "Shikenan nan da kwana hud'u za a d'aura auren," ana haka Lantana da Zainabu suka shiga gidan kayan suka fara bud'ewa suna kallo sai da suka gama sannan suka kalli su Sabeeha suka yi dariya suka ce "Amaren kwana hud'u," ga mamakin su suka ji 'yan uku sunce "Na'am," had'e rai Lantana ta yi bata Kuma magana ba.



Kud'i Sadam ya zaro sun Kai dubu goma ya ajiyewa Sabeeha a gaba ya ce "Ga wannan kiyi amfani dasu a shagalin biki gobe zan dawo," Sabeeha ta yi far da ido ta ce "To sai ka dawo my love," ya fita yana dashare baki.


Haka ma Dauda ya ajiyewa Sabreen dubu biyar tai ta godiya har da raka shi zaure sannan ta dawo Sameeha ma Faruk ya bata tana ta fara'a wanda faruk bai tab'a ganin ta yi ba.



Ta tafi raka shi sai da ta raka shi waje har zata koma cikin gida ya ce "Sameeha," tsayawa ta yi ya k'arasa har inda take ya ce "ki yi hak'uri nasan bakya sona nayi duk yadda zanyi Baba ya janye maganar auren nan amma yak'i," ta ce "Ya faruk kenan karka damu da kanmu zamu d'au mataki," jinjina kai ya yi ya ce "Nasan kuna hak'uri da Baba amma ku cigaba da hak'uri wata rana sai labari amma yanzu me ku ka yanke yi?" Kasancewar sun yadda da shi Sameeha ta fad'a masa ya ce "Hakan yayi yanzu bari na baku number ta duk sanda ku ke buk'atar taimakona ku samu waya ku kirani domin ni gobe zan koma makaranta," number d'insa ya bata sannan ya tafi.


Dama shi ba mazaunin k'auyen bane karatu yake yi a birni.



Komawa cikin gidan Sameeha ta yi tana shiga ta samu su Kawu sun mik'e suka fice suna fita Zainabu ta sa kuka ta ce "Baba sai da nace karka bari Waccan ta Auri Sadam ni zai aura amma kak'i yadda wallahi Kuma ni shi nake so," Kawu Bala ya ce "Haba 'yar lelena ki kwantar da hankalin ki zaki aure shi domin na riga na gama shirya hakan so nake yi sai anyi auren sannan zan k'ulla mata tugun da sai ya sake ta daga nan kuma saina ba shi auren ki Kuma Kinga munci riba biyu saboda ko ba komai kin auri Mai kud'i ita Kuma mun mayar da ita bazawara," Lantana ta ce "Gaskiya Malam kana da basira Wallahi aida na d'auka haka zaka zuba ido ta Auri mai kud'i 'yar mu kuwa ko oho," Kawu ya ce "Kema kinsan hakan bazai yuwu ba kawai yanzu lallama shi nake yi saboda yanzu naga ya gama makancewa akan waccan d'in," Haka suka yi ta kitsa yadda zasu mayar da Sabeeha bazawara.

Su kuwa bayan su Kawu sun tafi su Sabeeha suka bubbud'e kayan suka gani suna dariyar da su kad'ai suka san ma'anar ta Abba kuwa kallon su kawai yake yi ba tare da ya ce musu komai ba suma Kuma basu ce komai ba suka had'a kud'aden da aka basu suka had'a da kud'in salary d'insu da aka basu Wanda ko rabi basu tab'a ba ga kuma dubu hamsin d'in da Habibu abokin kamis ya bata.



Shigar da akwatunan d'aki suka yi sannan suka d'ora girki suka ci suka k'oshi.



Da daddare suka samu Abban su a d'aki ya yi jugum zama suka yi a gaban sa Abba ya ce "Aminaina yadda ku ka nuna farin cikin kawu lefen ku hakan ya nuna kuna son auren ko?" Sabeeha ta ce "A'a Abba dama mun yanke wata shawara ne," ya ce "Ta me?" Sabreen ta ce "Abba gaskiya ba ma son auren nan shiyasa muka yanke shawarar mubar garin har sai komai ya nitsa," Sabeeha ta ce "Eh Abba dan wallahi na tsani Sadam," Sabreen ta ce "Ai gara ke Sabeeha Wallahi," hararar wasa Sabeeha ta yi mata ta ce "Ai Wallahi da na auri Sadam gara na auri Kamis," Sameeha ta ce "Ai ni kuwa bani da case domin ya Faruk ya hak'ura," Abba ya ce "Ni yanzu damuwata ina zaku je?" Sabeeha ta ce "Abba ka kwantar da hankalin ka zamu kula da kanmu," ya ce "Na yadda daku sai dai Dan Allah karku wuce Kaduna saboda tafi kowacce state kusa damu sannan ku rik'e mutuncin ku kula da kanku," Suka ce "To Abba insha Allah,"



"To yanzu yaushe zaku tafi?" Sameeha ta ce "Zuwa jibi Abba," ya ce "Allah ya kaimu Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen Abba,"




Washe gari da yamma suka shirya duka su Uku suka fita Kai tsaye gidan wata Mai abinci a unguwar su bayan sun gaisa suka bata dubu ashirin suka ce ta ajiye a wajen ta kullum ta dinga aikawa da Abban su abinci tunda da safe tana yi tayi da rana da daddare ma tayi.


Rok'on ta suka yi akan karta fad'awa Kawu matar ta ce "Kar ku damu zan b'oye muku sirrin ku ko dan mahaifiyar ku saboda mutuniyar kirki ce," godiya suka yi mata sannan suka tafi.


Suna fita kuwa tasha suka je suka samu mai wata mota golf suka yi magana akan gobe da asubar fari zai je ya d'auke su ya kaisu har kaduna domin basa so wani ya ga sanda zasu bar garin balle a kaiwa Kawu Bala munafunci.



Sai yamma lik'is suka koma gida girki suka yi sannan suka shiga d'akin su suka harhad'a kayansu tass suka ajiye.




Tun dare suka yi wanka suka ajiye kayan da zasu sa ranar raba dare suka yi suna fira da Abban su sannan suka sanar da shi duk abinda suka yi da suka fita yai ta sa musu albarka sannan suka tafi d'akin su suka kwanta.


Da asuba kuwa suna yin sallah suka zira dogayen rigunan su blue iri d'aya sannan suka fita waje suka samu mai motar zuwan sa kenan trolleys d'in su suka d'auka suka fita da su akasa a mota sannan suka shiga gidan d'akin Abban su suka nufa yana zaune akan sallaya yana addu'a gefen sa suka zauna suka shafa tare sannan cikin tausayin yaran nasa ya ce "Kun gama shiryawa mai motar ya zo?" Suka ce "Eh Abba," Nan ya fara yi musu Nasiha kuka kawai suke yi domin gani suke yi idan suka tafi bazasu dawo ba shima Abban hawaye yake yi ya ce "Ku tashi kuje Allah ya yi muku albarka ku yi ta addu'a nima zan taya ku Allah ya karemun ku ya d'aukaka ku," suna kuka suka ce "Ameen Abba," sannan suka rungume shi suna kuka har wajen ya raka su sannan ya ce "Ku tafi kar wani ya ganku Allah ya kiyaye," suka amsa da "Ameen," sannan Suka shiga mota Sabeeha na gaba da magen ta a hannunta Sameeha da Sabreen na bayan mota.


Haka suka tafi suna d'agawa Abba hannu kowaccen su na sharar hawaye.



Lokacin da suka isa Kaduna karfe Goma na safe tunda driver ya ajiye su suka rasa inda zasu yi ga yunwa na damunsu magen Sabeeha ma kukan yunwa take yi kifi ta siya mata ta bata taci ta k'oshi Sameeha ta ce "Sabeeha dear nifa yunwa nake ji," Sabreen ta ce "Nima haka wallahi," tashi Sabeeha ta yi ta tari Mai keke napep ya ce "Ina za a kaiku?" Sabeeha ta ce "Wallahi yayana mu ba 'yan gari bane dan Allah so muke ka kaimu wajen cin abinci mafi kusa," ya ce "To ba damuwa ku shigo," trolleys d'insu suka d'auka suka shiga ya jasu suna tafe suna fira kasancewar Mai napep d'in akwai surutu sai mamakin kamar su yake yi su Kuma suna amsa masa sama-sama saboda yunwar dake damun su.


Ya ce "Yawwa 'yan uku ga wani wajen cin abinci gaban mu kad'an sai dai na hajiyoyi ne domin wajen akwai tsadar abinci sai dai sun iya girki," Sabeeha ta ce "Bakomai mu tsaya a nan d'in," suna k'arasawa ya tsaya suka biya shi kud'in sa suka shige wajen janye da trolleys d'in su Sameeha na rik'e da magen Sabeeha wacce suke kira da pretty.



Motoci ne da yawa a harabar wajen suna shiga kuwa kallo ya dawo kansu saboda ganinsu janye da trolleys su kuwa basu damu da kallon da ake yi musu ba saboda damuwar su bata wuce cikin su ya d'auka ba guri suka samu can nesa da mutane suka zauna saboda ba sabawa da cin abinci suka yi cikin mutane ba.


Waiter ce ta je wajen ta ce "Me za a kawo muku?" Kallon Sameeha Sabeeha ta yi ta ce "Sameeha dear me za a kawo miki?" Sameeha ta ce "Jallop rice please with mirinda," Sabreen Kuma ta ce "Nima jallop rice amma da hollandia Mai sanyi," Sabeeha ta ce "Ni kuma fried rice with coslow sai maltina," juyawa waiter d'in ta yi ta tafi ba dad'ewa ta dawo ita da 'yar uwar ta d'ayar ta ce "Wow identical triple," murmushi kawai Sabeeha ta yi ta ce "Sunana Aysha," Sabreen ta ce "Nice name I'm Sabreen and here is my sister's Sabeeha and Sameeha," Aysha ta ce "Nice names nice to meet you," cikin gajiya da surutun ta Sabeeha ta ce "Nice to meet you too," tana fad'ar haka suka fara cin abincin.



Aysha ganin sun fara cin abinci ta tafi tana waigen su hakan ne ya janyo hankalin yawancin mutanen kansu sai kallon su ake yi saboda ganin su su uku iri d'aya.


Su kuwa sai cin abincin su suke yi Sabeeha ta ce "Kusan wani abu?" Sabreen ta ce "Meya faru?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da alama wata zata daku a wajen nan," Sameeha ta ce "Wato Sabeeha dear kin fara ko ni na rasa irin ki yanzu sai ki fad'i magana kuma sai ta tabbata wai to meyasa hakan?" Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Bansani ba nima amma Ni kaina Ina mamakin kaina haka kawai zanji wai abu kaza zai faru kuma ya faru wani bana ganin alamun abun zai faru amma wani lokacin kuma ina ganin alamun faruwar hakan kamar dai yanzu ku kalli waccan guy d'in Mai siffar 'yan daba magana yake yiwa waccan siririn abokin nasa tare da nuna masa waccan budurwar mai shan ice cream kuma alamu sun nuna magana yake cikin fushi har k'wafa yake yi," ta fad'a tana nunawa su Sabreen mutum da Kuma yarinyar.



Tunani suke yi anya Sabeeha bata da aljanu kuwa domin tunda suka taso take hakan sai dai ta dad'e hakan bai faru ba sai yau ko dan basa shiga mutanene oho basu gama tunani ba suka ga guy d'in ya shiga wajen direct ya yi wajen budurwar itama tana ganinsa ta mik'e tana zare ido Yana zuwa bai jira wata-wata ba ya fara zabgawa budurwar mari ita kuma tana zaginsa har mutane sun fara taruwa.



Mik'ewa Sabreen ta yi ta ce "Lallai ma waccan guy d'in d'an iska ne bari naje tsabar baisan darajar mata ba shine zai wani kama Marin ta?" Rik'e ta Sabeeha ta yi ta ce "Karki je babu ruwan ki domin ita ce bata da gaskiya," a tare su Sabreen suka had'a baki wajen cewa "Ta ya kika sani?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da kan ku ya kamata ku gane hakan ku duba lokacin da guy d'in ya shigo nan a firgice ta mik'e tsaye Kinga da alamau akwai abinda ya had'asu sannan ki duba mulki irin na mace da shine ya yi mata laifi baza ku ga ta tsure haka ba," aikuwa nan suka ji yo guy d'in na cewa "Ke dan kin raina mun hankali saboda bana kula ki shine zaki je har gurin mom d'ina kice kina d'auke da cikina to Wallahi kotu ce zata raba mu," duk mutanen dake wajen domin raba fad'an suka tafi jin maganar ta fi k'arfin su.



Sabreen ma zama ta yi tana cewa "Ahhab ai gara da yaci uban shegiya," Sabeeha kuwa waiter ta yafito da hannu zuwa waiter d'in ta yi Sabeeha ta ce "How much your money?" Ta ce "Six thousands eight hundred," bud'e jaka Sabeeha ta yi ta fito da kud'in ta biya.



Aysha ce ta k'arasa wajen ta ce "Sai tafiya?" Sabeeha ta ce "Eh,"


"A wanne unguwa ku ke ku bani address d'in ku wataran nazo," Sabeeha ta ce "Mu ba 'yan gari bane Kuma bamu san kowa nan ba yanzu ma zamu je mu nemi masauki ne," jinjina kai Aysha ta yi ta ce "Zan iya taimakon ku?" Sameeha ta ce "Haba Aysha waye yak'i taimako," Aysha ta ce "Kun ga rayuwar garin nan Yana da tsada mai zai hana ku zauna a nan ku dinga aiki," Sabreen ta yi caraf ta ce "Eh Kuma Sabeeha dear ta iya girki sosai," ta fad'a tana nuna Sabeeha.



Aysha ta ce "Ok ba damuwa bari naje wajen madam naji," tana fad'ar haka ta juya ta shige wani d'aki da alama Office ne.



Tana shiga ta samu ogar tasu a zaune kan kujera da glass fari manne a fuskar ta durk'usawa Aysha ta yi ta ce "Madam dama wasu bak'i ne a garin nan suka zo nan cin abinci sunce mun basu da masauki shine nayi musu tayin aikin mu tunda naji kina neman ma'aikata shine nazo na sanar Miki sannan d'aya a cikin su ta iya girki sosai," jinjina kai madam ta yi ta ce "Zo mun dasu," fita Aysha ta yi suka koma tare.



Kallon su Madam ta yi bayan sun gaisa ta ce "Amma 'yan uku ne ko?" Suka amsa mata da "Eh," ta ce "Masha Allah meye sunan ku?" Nan suka fad'a mata sunayen su ta jinjina kai sannan ta ce"Zan d'auke ku aiki sai dai naji ance akwai wacce ta iya girki sosai a cikin ku Kuma akwai wata Hajiya da ta bani cigiyar wacce ta iya girki sosai saboda yaron ta da duk Mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login