Showing 6001 words to 9000 words out of 140483 words
ya ce "To shi za ayi mun," Ware ido Umar ya yi ya ce "Kai haba dai amma you are joking?" Mtswww Maleek ya ja tsaki ya ce "Umar I'm not joking I'm serious Wai ko ka manta halin Uncle ne yanzu haka fa bikin bai fi 3 weeks ba," jinjina kai Umar ya yi tare da cewa "Kenan mu fara shiri?" Tsaki Maleek ya ja ya tashi ya fice.
Bin bayan sa Umar ya yi dan yasan haushi ya ji da sauri ya tarar da Maleek dake tafiya shi da Salman ya ce "Sorry MG amma dai ba Nasreen ba ce ko?" Ba tare da Maleek ya kalle shi ba ya ce "Ita mana," daga haka ya wuce ya yafi part d'in Ummi.
Salman ya kalli Umar ya ce "Amma Umar abinda ake yiwa MG Sam ba a kyauta masa Dan ma dai mai biyayya ne shiyasa," Umar ya dafa kafad'ar Salman ya ce "Captain Nima abin na damuna Wallahi Amma kawai mu taya shi da addu'a kawai," haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalar dake faruwa a gidan.
Da Sallama Maleek ya shiga falon Ummin sa ya zauna akan kujera ya jingina a jikin kujerar Yana tunanin damuwar da yake ciki ji yayi falon ya d'auka da "Fauwaz is open the door," har lokacin bai ko bud'e idanunsa ba.
Fauwaz ne ya shiga falon kunnen sa manne da ear piece yana rera wak'ar fire boy ta like I do har wani kad'a kai yake yi Yana bin wak'ar "e-sure for you baby I'm going no where your love is true I know you always be there no one can take my place bad energy stay fa...," Tsawar da Maleek ya yi masa ne yasa shi saurin cire ear piece d'in jikin sa har d'an rawa yake yi dan tsoro.
"Zo nan," Maleek ya ce Yana k'ara had'e fuska kamar bai tab'a dariya ba k'arasawa Fauwaz ya yi ya zauna k'asan carpet Dan yau ya ga ba wasa kallon sa Maleek ya yi ya ce "Kai Wai meyasa baka jin magana ka shigo waje babu ko sallama," Fauwaz ya ce "Sorry ya Maleek bazan sake ba," d'aga kafad'a Maleek ya yi ya ce "Is left for you," Rinaz ce ta k'arasa falon tana yiwa Fauwaz dariya k'asa k'asa.
Hararar ta Fauwaz ya yi sannan ya cije baki ya kalli Maleek ya ce "Yaya kasan kuwa me Rinaz ta yi da baka nan?" Duk da yana cikin damuwa sai da ya girgiza kai domin yana so ya ji halin da k'annen nasa ke ciki domin rayuwar yanzu sai a hankali musamman shi da ya san baya rasa mak'iya.
Fauwaz ya ce "Last week fa Rinaz ta fita unguwa tun around 5:00pm bata dawo ba sai wajen 10 Wai ta tafi birthday party d'in friend d'in ta," jinjina kai Maleek ya yi tare da kallon Rinaz da ta yi tsilli tsilli da ido ya ce "Haka ne?" Cikin rawar murya ta ce "Sorry ya...," Tsawa ya daka mata ya ce "Don't sorry me I just ask you haka ne!" Noding kanta ta yi sannan ta ce "Kuma wallahi yaya shima fa bro kullum sai cikin dare yake dawowa kuma kullum sai Ummi ta yi masa fad'a," Girgiza kai Maleek ya yi Yana binsu da ido sannan ya ce "Ok yanzu nagane wato duk ranar da bana nan duk abinda kuka ga dama shi kuke aikawata ko?" A tare suka girgiza kai kwafa ya yi ya ce "You really know bazan ce ku dena ba dan Allah ku cigaba da duk abinda ku ka ga dama," yana gama fad'in hakan ya ce "Kun isheni da zama da anan," da sauri suka bar wajen suna hararar juna.
Falon ne ya d'auka da "Ummi is open the door," k'ofar Nabil ya kalla sannan ya mik'e ya nufi inda take rungume ta ya yi ta yi masa kiss a for head d'insa ya ce "Sannu da dawowa Ummi," ya fad'a tare da karb'ar hand bag d'inta suka k'arasa falon ta zauna a gajiye tare da cire farin glass d'in dake idanun ta.
Ya ce "Ummi Sannu shiyasa nace ki hak'ura da aikin nan Ni Sam banga amfanin hakan ba," hararar wasa ta yi masa ta ce "Yanzu kai taimakon al'umma ne bai da amfani bayan kaima abinda ka ke yi kenan," murmusawa ya yi ya ce "Amma Ummi ai ni daban zuwa yanzu kamata ya yi ki zauna ki huta a gida zuwa asibitin ya isa haka," banza ta yi da shi ta k'wala Kiran "Hadiza," wata budurwa ce ta fito daga kitchen d'auke da wani had'adden tray mai d'auke da ruwa da drinks da glass cups ta ajiye akan center table ta ce "Sannu da dawowa Ummi," cikin fara'a Ummi ta ce "Yawwa Hadiza da fatan komai lafiya," Hadiza tana satar kallon Maleek ta ce "Lafiya lau Ummi,"
"Ok kun gama girki ne?" Cikin ladabi ta ce "Eh mun gama," gyad'a kai Ummi ta yi ta ce "Me ku ka girka?" Murya na rawa Hadiza ta ce "fried rice with coslow and papper chicken then white rice with fish soup and fruits salad an...," Tsakin da Maleek ya ja ne ya hanata k'arasa fad'in abinda zata fad'a dan mugun tsoron sa take ji gashi da kwarjini.
Kallon sa Ummi ta yi ta ce "Son me za a kawo ma?" Kallar tausayi ya yi ya ce "Ummi fa ni naki nake so dukan su ba abinda suka iya," girgiza kai Ummi ta yi ta ce "Ni yanzu Son na gaji amma ka fad'i wacce kake so ta yi ma girki cikin Hadiza,Salma,Halima,Yasira,Zainab,Hajara ko fati?" Kamar zai yi kuka ya ce "Ummi duka basu iya ba,"
D'aukar waya Ummi ta yi kira ana d'agawa ta yi sallama suka gaisa sannan ta ce "Yawwa Fulani ina so ki samo mun 'yan aiki wad'an da suka iya girki," tana gama fad'in haka ta kashe wayar tana yiwa MG hararar wasa ta ce "Wallahi na gaji da rigimar ka," tana gama fad'in haka ta yi stairs shi Kuma ya kalli Hadiza ya ce "kina jiran meye ne?" Da sauri tabar wajen har tana tuntub'e.
Sabeeha ce kwance a d'akin su da yamma wata 'yar aiki ta yi sallama ta ce "Kece Sabeeha?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi.
"Ki zo inji Yallab'ai," ba tare da tsoro ba ta ce "Gani nan," ta tashi sanye da dogon hijabin ta ta fita a hanya suka had'u da Sabreen dake komawa d'aki.
"Sabeeha dear ina zaki?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Wai Kamis ke kirana," zare ido Sabreen ta yi ta ce "Dafatan dai lafiya?"
"Nima bansani ba amma kije yanzu zan dawo," tana fad'in haka ta tafi Sabreen ta bita da kallo Dan gani take yi kamar za ace laifi Sabeehan ta yi.
A falo ta samu Yallab'ai shi da Habibu tana zuwa Kamis yabar wajen Yana binta da wani irin kallo ita kuma tana hararar sa.
Habibu ya ce "k'araso mana 'yan mata," k'arasawa ta yi ta zauna k'asan carpet ta ce "Gani," Nan fa Habibu ya zayyane mata dalilin kiran ta wani murmushin mugunta Sabeeha ta yi ta ce "Kace masa na amince zan aure shi," shi kansa Habibu ya yi mamakin saurin amsawar da ta yi Amma ya fuske ya ce "To ba damuwa mun gode," sannan ya d'auko kud'i wajen dubu hamsin ya bata karb'a ta yi har da godiya ta tafi.
Ko da Kamis ya ji yadda suka yi ba k'aramun dad'i ya ji ba Dan ranar har kyauta ya yiwa 'yan aikin gidan abinda bai tab'a ba su kansu mamaki suke yi.
Nan fa kusan kullum sai ya aika an kira ta sunyi fira ba tare da Farida ta saniba.
A haka aka yi sati d'aya Sabeeha da Kamis suna kwasar soyayya kamar gaske.
Yau ma firar suka gama ta nufi d'akin su tana farin ciki da sallama ta shiga d'akin Sabreen ta tare ta tana cewa "Ka ga ta Yallab'ai," dariya suka yi harda tafawa ta ce "Mu zauna Sabreen dear akwai labari," zama suka yi ta ce "kinsan mene yau nace da Kamis ya sanar da matar sa yana sona Kuma aurena zai yi," Sameeha ta ce "Shikenan mun shiga uku yanzu Sabeeha dear abinda ki ka jawo mana kenan," Sabreen ma a tsorace ta ce "Amma sister kina ganin hakan bazai jawo mana matsala ba?" Sabeeha ko a jikin ta ta tab'e baki ta ce "Manta ba abinda zai faru ba dai saura kwana hud'u ayi salary ba ranar zamu bar gidan nan sannan zuwa lokacin ku zuba ido ku ga abinda zai faru,"
"Son gobe nake so na tafi Dubai ni da Asiya da karimatu Amma ba dad'ewa zamu yi ba bai fi muyi 3 to 4 days ba," Maleek dake gefe yasha kyau cikin jajayen k'ananun kaya ya ce "Me zaku yi a can?" Ummi ta ce "ka manta bikin ka bai ma kai 2 weeks ba zamu je had'o lefe mana," take ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba.
"Haba yaron Ummi dan Allah ka saki ranka kasan auren nan ba fashi kayi hak'uri ayi a gama lafiya ka cigaba da yiwa mahaifin ka biyayya kaji?" Noding kansa ya yi cikin damuwa sannan ya ce "To Ammi maganar abinci fa?" Dariya ta yi ta ce "Yadda ka ke damuwa da maganar abinci da haka ka ke cinsa da kafi haka girma to ban da rigima irin taka Kai da zaka yi aure ai matar ka ce zata dinga girka ma," shiru kawai ya yi ba magana.
Washe gari Ummi da Maman Umar da Umman Salman suka tafi Dubai had'o lefen auren Maleeek.
B'angaren amarya Nasreen kuwa shiri suke yi ita da friends d'in ta sai shirya events take yi bata damu da yadda Maleek baya ko kiranta ta waya ba hidimar ta kawai take yi tana cin uwar kud'i kamar central bank a gidan yake sai rawar Kai take yi zata auri kyakkyawan jarumin namiji Mai dukiya ya yinda friends d'inta kowa burin sa ya ga MG Maleek.
Shi kuwa a nasa b'angaren ko a jikinsa har mantawa yake yi Wai aure zai yi idan ba zancen aka yi masa ba.
Kwanan su Ummi hud'u a Dubai suka koma tare da kayan lefe akwatuna ashirin da hud'u Maleek da kansa tare da sojojinsa da Kuma Salman da Umar suka je suka tari iyayen nasu.
Ko da suka koma gida ana nunawa Maleek kayan ko kallon basu ishe shi ba daga k'arshe ma tashi ya yi yabar wajen su Umar suka bi bayansa Dan suma jinin su bai had'u da amaryar ba Dan bata da kirki kwata kwata ga wulak'anci da girman kai da rashin girmama na gaba da ita.
A haka akai ta shagali ya yinda Rinaz itama Sam bata son Nasreen Dan tunda aka fara Shirin bikin bata wunin gidan.
Ballantana Fauwaz da ko kallo Nasreen bata ishe shi ba Dan da Yana da hali yayan sa bazai aure ta ba dan Sam bata da kamun Kai.
A b'angaren uwar amarya Umma shiri take yi sosai na aurar da tilon 'yar ta.
A haka aka fara gabatar da events ba tare da ango ya lek'a ko nan da can ba amarya ma bata damu ba domin gayyar maza abokan ta ta yi suka dinga shek'e ayar su duk abinda ke faruwa Maleek Yana sane sai dai shi ko a jikin sa.
Wuni yake yi a part d'in sa dan ko part d'in Ummi baya zuwa saboda yasan cike yake da bak'i kullum Yana tare da Umar da Salman idan ba a fad'a ma ba bazaka ce bikin sa ake yi ba dan uzurin gaban sa kawai yake yi.
A gobe d'aurin aure Daddy da Uncle suka dira a Nigeria.
Maleek ya fito kenan cikin Shirin masallaci kasancewar juma'a ce ya ga motocin su Daddy na shigowa gidan kallo d'aya ya yiwa motocin ya d'auke Kai ya kalli Salman ya ce "Salman muje ko?" Mota suka shiga suka tafi masallaci.
Daddy kuwa motocin su gama parking guards d'in su suka bud'e musu k'ofa suka fito manyan mutanene sannan kana kallon su kaga ya da k'ani saboda kamar da suke yi.
Sannan Daddy ya wuce part d'insa haka ma Uncle ya wuce part d'insa.
Da daddare Maleek na zaune a falon sa yana kallon news Nasreen ta shiga falon sai wani karairaya take yi tana iyayi kallo d'aya ya yi mata ya d'auke Kai domin tsoro ma ta bashi tayi wani fau kamar aljana dama fara ce ita sai Kuma ta k'ara da mai sai dai bata wani kyau ga ta da k'ananun idanu kamar 'yar China.
K'arasawa ta yi ta zauna a gefen sa ta ce "Sannu da hutawa husby," bai kalle ta ba ya ce "Kece da sannu ba Maleek ba," basarwa ta yi ta ce "yawwa Ya Maleek dama cewa nayi mai zai hana na zauna a nan part d'in ni bana son waccan part d'in," kallon banza ya you mata sannan ya ce "koh?" Wayar sa ce ta yi ringing d'auka ya yi ya ce "Ok gani nan zuwa," yana fad'ar haka ya yi hanyar fita ta ce "Yaya Maleek ina Kuma zaka muna magana?" Ba tare da ya juya ba ya ce "Kiran da ya fi naki muhimmanci zani Kuma a can zaki zauna kya iya fitar mun a part," Yana fad'ar haka yasa Kai ya fice itama ranta a b'ace ta fita.
[10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️
RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)
SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)
Page 3
Yana fita Kai tsaye part d'in Uncle ya shiga da sallama a bakin sa amsawa sukayi suna zaune akan kujera k'arsawa ya yi ya zauna k'asan carpet ya ce "Daddy uncle sannun ku da hutawa da fatan Kun dawo lafiya?" Daddyn say ya ce "Lafiya lau Son," Uncle baban Nasreen kallon banza ya yi masa ba tare da ya amsa ba shima Maleek bai sa akan sa ba ya kalli mahaifin sa ya ce "Daddy gani,"
"Son dafatan ka sanar da auren ka ga abokan ka da Kuma wajen aikin ka ko Dan naji har yanzu banji wata sanarwa daga radio ko jarida ko gidan televisions ba," ya ce "Daddy gaskiya ban sanar ba," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya fara zazzaga masifa "Ai dama Kai baka da tarbiyya baka daraja iyayen ka wato kai ba a isa da Kai ba ko to wallahi ka kiyayeni wawan yaro kawai wato saboda tsanar da ka yiwa daughter ne yasa baza ka sanar da auren ba kenan?" Shiru Maleek ya yi zuciyar sa na tafasa dan ji yake kamar ya shak'e Uncle ya kaisa har lahira Amma ba dama saboda wan mahaifinsa ne.
Kallo d'aya zaka yi masa kasan Yana cikin b'acin rai saboda idanunsa sunyi jajur kamar Wanda aka watsawa barkono a idanun jijiyoyin dantsen sa duk sun tashi dan a lokacin duk Wanda ya damk'a sai dai wani ba shi ba.
Daddy dai ko uffan be ce ba mik'ewa Maleek ya yi yayi hanyar waje Uncle na cewa "Ka gani ko Hamza ka ga rashin tarbiyyar ko ina magana Amma saboda ya rainani ya tashi zai fita wato ga mahaukaci na magana," har lokacin Daddy bai yi magana ba dan yasan idan har Maleek ya tsaya a wajen zai iya aikata abinda ba a tab'a tunani ba domin yana da zuciya sosai.
Haka Maleek ya fita yabar Daddy Sai Masifa yake yi Daddy dai bai ce komai ba shiru ya yi Yana sauraron yadda yayan sa ke k'arewa d'ansa zagi da tsine masa a gaban sa.
Maleek kuwa ko da ya fita part d'in sa ya wuce ya kwanta saman lallausan gadon sa sai sauke ajiyar zuciya yake yi kamar Wanda ya yi kuka ya k'oshi da abun ya dame shi ya tashi ya yi ta sallah ya yi karatun Qur'an sannan ya ji zuciyar sa ta yi sanyi.
Washe gari aka d'aura auren Fatima Aminu mai dala da MG Abdul-maleek Hamza mai dala akan sadaki dubu d'ari biyu d'aurin auren ya samu halartar abokan Daddy da Uncle daga k'asashe daban daban sai dai ango ba tawagar sa dan bai yi gayyata ba.
Ana gama d'aurin auren ya nufi gida part d'in sa ya nufa ya watsa ruwa ya kwanta bayan ya ba sojojin sa umarnin kar su bar kowa ya shiga inda yake.
A firgice su Sabeeha suka tashi daga baccin da suke yi sakamakon bugun da akewa k'ofar d'akin su gaba d'aya sun gama tsorata especially ma Sameeha Dan har ta fara hawaye ta b'oye a bayan Sabreen da itama jikin ta rawa yake yi Sabeeha kuwa tsaki ta ja tare da nufar k'ofar ta bud'e.
Farida ce ta shiga d'akin tare da cin kwalar Sabeeha ta ce "Ke har wacece ke da zaki aure mun miji to wallahi yau sai kin bar gidan nan tunda bana uban ki bane," yatsina fuska Sabeeha ta yi ta ce "Wanne mijin naki ki ke magana Wai?" Dak'uwa Farida ta yi mata ta ce "Dan uwar ki miji nawa gareni to wallahi daga ke har 'yan uwanki sai kun bar gidan nan shegu aljanu," k'arfi Sabeeha tasa ta fisge rigar ta ta ce "Dalla can malama cikani muje wajen mijin naki shine yace Miki akwai alak'a tsakanina da shi to bari kiji ko maza sun k'are bazan auri wannan wawan ba kawai dama danna had'a ku ne Kuma ko yanzu alhamdulillahi burina ya cika," Sabreen da Sameeha sakar ido suka yi suna kallon ikon Allah basu tab'a tunanin k'arfin halin Sabeeha ya kai haka ba.
Juyawa Farida ta yi ta fita tana cewa "Gara da ki ka tonawa kanki asiri," tana fita Sabeeha ta kyalkyale da dariya ta ce "Sabreen dear Sameeha sister ya ku ka ga wannan," to ku biyo ni ku ga wani salon ta d'auki hijabi ta d'ora saman hijabin jikin ta ta fita suma binta suka yi suma.
Falo suka fita suka samu Kamis zaune kan kujera Farida kuma na tsaye a kansa sai zabga masifa take yi kamar zata tsaga gidan saboda d'aga murya "To Wallahi sai dai idan ka sake ni ka rasa wacce zaka aura sai waccan yarinyar wacce ba son Allah da annabi take ma ba so take kawai ta ga ta rabamu," Sabeeha na zuwa falon ta fashe da kukan munafurci har da k'ak'alo hawayen k'arya tuni Kamis ya rikice ya yi wajen ta kamar zai rungume ta ya ce "Subhanallah