Showing 78001 words to 81000 words out of 140483 words
hanya dake gidan can sai gashi tare da Faisal suna zuwa Mama ta nunawa Faisal wata dank'areriyar bak'ar mota ta ce "Zaka yi driving 'yan uku zamu je k'auye ne," ya ce "To madam,"
Bayan mota Abba ya bud'e Doctor ta shiga shima ya shiga sabi'u ya shiga ya ja motar.
Bud'e bayan mota Sameeha ta yi ta kalli Sabreen dake gefe tana waya ta ce "To dear sai kin taho dan mu mun tafi," da sauri Sabreen ta shige motar tana yiwa Sameeha hararar wasa yayin da Sabeeha ta shiga gaban mota tana yin chart da Maleek.
Jan motar Faisal ya yi yabi bayan motar su Abba sai k'auye.
Suna shiga k'auyen daidai lokacin gidan Kawu Bala ya kama da wuta sosai wutar ta fara ci ganga_ganga ba tare da sunsan dalilin kamawar ta ba rabon su da d'ora tukunya a gidan ba sun manta shekarar ballantana ace wutar murhu ce ta haddasa.
Dakyar suka fito daga gidan suna neman agaji tuni 'yan gari suka hallara aka fara k'ok'arin kashe wutar domin karta shafi mak'ota dakyar aka samu aka kashe wutar sai dai gidan ya yi k'urmus 'yan garin sai tausayin Kawu Bala suke ji domin duk wani Mai imani idan yasan halin da Kawu ke ciki sai ya tausaya masa ballantana yanzu da gidan nasa da shi kad'ai ya rage masa ya k'one.
Tun daga nesa suke hango tarin jama'a wajen gidan Kawu Bala Abba ya ce "Maryam duba kiga taron jama'a wajen gidan Yaya lafiya kuwa," Mama da itama mamakin hakan take yi ta ce "Insha Allah lafiya lau,"
"Dear Kinga mutanen garin a tare a gidan Kawu Allah yasa dai lafiya," Sameeha ta fad'a cikin Sabeeha da Sabreen babu wacce ta kulata domin su mugun haushin Kawu Bala suke ji.
'yan k'auyen ganin manyan motoci yasa su baza idanu suna kallon motocin daga nesa da mutanen kad'an suka yi parking sannan suka firfito daga motar.
Nan fa mamaki ya kuma kama mutanen saboda ganin wad'an da suka fito daga motar musamman wad'an da suka san Abba da Kuma sanin halin da yake ciki da amma yanzu gashi cikin tsadaddiyar mota ga wani canjawa da ya yi kamar ba shi ba haka ma 'yan uku sai kallon su ake yi ganin yadda suka zama bama a zancen Doctor domin ko gane ta 'yan garin basu yi ba zuwaira mai abinci dake lek'e ta katanga ce kad'ai ta gane ta.
Hanya mutanen wajen suka bud'a musu suka wuce zuwa k'ofar gidan turus suka tsaya suna kallon yadda gidan ya k'one saurin juyawa Abba ya yi ya kalli Malam Saleh ya ce "Malam Saleh ina Yaya?" Domin Abba Sam bai lura da Kawu Bala dake gefe ba.
Da hannu malam saleh ya yiwa Abba nuni da Kawu Bala dake gefe a durk'ufe idanunsa sai zubar da hawaye suke yi domin tausayawa rayuwar su halin da zasu shiga yake yi damuwar sa d'aya a Ina Lantana da Zainabu da d'anta zasu dinga zama shi bata kansa ma yake yi ba domin shi namiji ne.
Sai da Abba ya tsorata ganin wadda aka nuna masa a matsayin yayan sa yasan dai yayan sa dogo ne sannan yana da k'iba amma a nuna masa wannan siririn mutumin matsayin yayan sa su kansu 'yan uku da maman su sunyi mamakin hakan sosai ga Zainabu rik'e da d'anta sai kallon su take yi kamar ranar ta fara ganin su yayin da su ko gane ta ma basu yi ba.
A tsorace Abba ya nufi inda Kawu yake durk'ushe yana kukua ya dafa kafad'ar sa a hankali Kawu ya juya domin ganin Wanda ya dafa shi da sauri Abba ya cika shi tare da ja baya cikin rud'ani ganin yadda yayan nasa ya koma gaba d'aya fuskar sa sai k'ashi da fata.
Ganin Abba ne da sauri Kawu ke k'ok'arin tashi tsaye domin tabbatar da abinda ya gani amma ya kasa da sauri Abba ya k'arasa ya d'ago shi ya mik'e idanun kawu Bala na zubar da hawaye ya ce "Habu," Abba bai damu da yadda jikin Kawu yake tumu_tumu ba ga wani tsami da yake yi na rashin wanka da wanki ba ya rungume kawu shima yana hawayen ya ce "Yaya me yake faruwa da kai haka ne?" Rungume Doctor Sameeha ta yi itama tana kukan tausayin Kawu Bala su ma su Sabeeha ya basu tausayi sosai.
Kawu Bala ya bud'e baki ya ce "Habu kayi hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba," saurin rufe masa baki Abba ya yi ya ce "Ya isa Yaya a cikin mutane muke yanzu muje mu tafi," Zainabu ce ta taso da d'anta a hannu tana kukan haka ma Lantana.
Doctor kuwa ta kasa cewa uffan tana rungume da Sameeha dake aikin kuka wajen ta Lantana ta nufa tana kuka ta ce "Maryam kece," Doctor ta ce "Ni ce lantana," haka ma Zainabu ta k'arasa tana wani zare ido harara Sabeeha ta galla mata bawai bata tausaya mata bane a'a sai kawai tunawa da irin cin mutuncin da Zainabu tayi musu da ta yi Sabreen ma tsaki ta ja.
Tuni jikin Zainabu ya yi sanyi Doctor kuwa wani kallo ta yiwa Sabreen jin tsakin da ta ja Sabeeha kuwa mazewa ta yi ta fara danna wayar ta yayin da Sabreen ta kalli wani gefe daban.
Abba ne ya rik'o hannun Kawu ya k'arasa gaban su Doctor ya ce "Doctor Ina ga mu tafi gida kawai," juyawa suka yi suka nufi motor yayin da 'yan gari kowa ke jinjinawa Abba da abinda ya yi sanin yadda Kawu ke muzguna masa.
Doctor kuwa duk da haka sai da suka gaisa da zuwaira Mai abinci sannan suka wuce zuwa mota yayin da Sabeeha fafur tace bazata shiga mota d'aya da Zainabu ba duk da hararar da Doctor ke yi mata ganin tana neman tara musu jama'a kamar k'aramar yarinya yasa Abba cewa shikenan kuzo mu tafi a nan.
Gaban mota Sabeeha ta shige Sabreen ma ta shige bayan mota ta zauna Wai itama bazata zauna mota d'aya da su kawu ba Sameeha ce kawai ta shiga gaban motar yayinda Kawu Lantana da Zainabu ke bayan motar da su Sabeehan suka zo a ciki suka tafi.
Tun a mota Doctor ta fara yi musu fad'a baji ba gani Sabeeha sai tura baki take yi Sabreen kuwa shiru ta yi tana sauraren yadda Doctor taita fad'a kamar ta ari baki Abba dai shiru ya yi baice komai ba domin yasan cewa tabbas 'yan uku sun wahala sosai wajen kawu Bala dan haka da wuya sun karb'e su da wuri da haka suka k'arasa gida.
Idanu waje Kawu Lantana da Zainabu ke kallon gidan domin ganinsu suke yi kamar a k'asar turai suna gama parking Sabeeha ta bud'e mota ta fice ta shige cikin gidan da kallo Doctor ta bita ta girgiza kai kawai Sabreen ma kallo su Kawu basu ishe ta ba ta shige cikin gidan.
Doctor ta kalli Sameeha dake gefe a tsaye ta ce "Daughter shiga ki Kira mun Halima kuzo tare wad'an can 'yan uwan naki kuwa ni da su ne," Sameeha ta ce "Mama kiyi...,"
"Kinga ba abinda na saki kenan ba wuce ki tafi," shigewa falon Sameeha ta yi Mama ta waiga ta kalli Kawu ta ce "Amma Yaya kamar baka da lafiya ko?" Lantana ta ce "Eh Wallahi wajen sati biyu kenan,"
Doctor ta ce "Ayyah me yake damun ka?" Nan Kawu ya yi mata bayanin yadda yake ji take Doctor ta gane ulcer ce ke damun Kawu mai zafi Sameeha da Halima ne suka k'arasa wajen Doctor ta kalli Halima ta ce "Yawwa Halima ga bak'i munyi kije da su wancan k'aramun part d'in nasan a gyare yake ki nuna musu yadda ake amfani da kayan toilet d'in zasu yi wanka sannan ku basu abinci suci yanzu zan ba Faisal kud'i ya siyo musu kayan sawa kafin zuwa gobe mu fita shopping Faisal idan ka dawo kaba Halima kayan ta Kai musu sannan ke kuma idan zaki Kai musu abinci ki sanar dani na baki magani ki kaiwa Yaya yasha kafin gobe muje hospital," sannan ta kalli Kawu Bala ta ce "Yaya idan Kun kammala sai ku shigo ciki," Kawu Bala kuwa kasa magana yayi domin mamakin halin kirki irin na Maryam.
Kud'i Doctor ta zaro a jakar ta ta bawa Faisal ta ce "Ka dai ji bayani na ko?" Ya ce "Eh madam," Doctor ta ce "Ku je Halima," ta ce "To madam," suka tafi Doctor Kuma ta ja hannun Abba dake mamakin ta shima suka shige cikin falon.
[10/25, 8:46 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️
RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)
SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)
Page 22
Har d'aki ta ja Abba sannan ta shige bathroom ta had'a masa ruwan wanka ya shige domin yin wanka Doctor ma ta tafi d'akin ta tayi nata wankan.
Sabeeha kuwa tana shiga d'akin su cire kayan jikin ta tayi ta d'aura towel ta fad'a wanka tana fitowa ta samu Sabreen zaune tana danna waya wuce ta Sabeeha tayi zuwa gaban mirrow ta yi shafe_shafen ta ta zira wata doguwar riga marar hannu maroon tasa hula a kanta maroon tayi kyau kamar yar baby gashin gaban goshinta ya kwanta luf gwanin sha'awa ta kalli Sabreen ta ce "Dear wallahi zuciyata tak'i yin sanyi yau da naga Zainabu sai naji tsanar da nake mata tafi ta ko yaushe har tsanar da nake mata tafi ta Kawu saboda mun girme ta amma hakan baisa ta raga mana ba," ajiye wayar Sabreen ta yi a gefe ta ce "Wallahi kuwa nima haka amma ki duba yadda Sameeha dear ta kama kuka kamar ta manta sanda Zainabu taso kashe ta ba,"
Tashi Sabeeha ta yi ta ce "Ah to nima dai abinda nagani kenan ni bara na fita," daga haka ta fice daga d'akin Sabreen kuwa ta shige toilet don yin wanka.
Sabeeha na sauka down stairs lokacin Mama ta fito daga d'akin ta zata je na Abba "Ke zonan," Doctor ta fad'a wajen ta Sabeeha ta nufa ta ce "Gani Mama," hararar ta Doctor ta yi sannan ta ce "Kunsan Allah ku kiyayeni a cikin gidan nan ku abinda ku ke yi haka ku ka ga ya dace Yaya fa yayan mahaifin ku ne Zainabu yar uwar ku ce ku duba halin da suke ciki haka ya kamata kuyi musu?" Tura baki Sabeeha ta yi ta ce "Mama basu da mutuncin fa dukan su,"
"Rukayya Wallahi ki fita a idona na rufe matsa mun a nan ko yanzu ranki ya b'aci Wallahi," kitchen Sabeeha ta nufa tana buga k'afa ajiyar zuciya Doctor ta sauke tana bin Sabeeha da kallo a zuciyar ta ta ce yaran nan sai a hankali zasu sauko nasan dama za ayi haka ta nufi d'akin Abba.
Abinci Sabeeha ta zuba ta koma d'akin su ta ci sannan ta tashi ta yi alwala ta yi sallah ta kwanta saman gado take bacci ya d'auke ta.
Tana baccin ne ta ji ana tashin ta juyi ta yi ta bud'e idanunta ta sauke su akan Sameeha ta ce "Dear yadai?"
"Kizo inji Mama tana down stairs kuma yanzu fa," tana fad'ar haka ta juya ta fita tashi Sabeeha ta yi ta gyara zaman hular ta tabar d'akin.
Tunda ta fara sauka ta hango su Kawu Bala a falon d'an d'auke kai Sabeeha ta yi ta ja k'aramun tsaki ta k'arasa falon kusa da Sameeha ta zauna ta ce "Mama gani," shiru Doctor ta yi mata.
Abba ya kalli Kawu ya ce "Yaya lafiya kace duk mu taru anan bayan baka da lafiya ai kamata ya yi ka kwanta ka huta," Kawu Bala kuwa hawaye ne ya zubo a fuskar sa ya ce "Habu dan Allah ka gafarce ni kuyi mun aikin gafara nayi maka abubuwa da dama a rayuwa nasan ban cancanci yafiya a wajen ku ba tun muna yara nake k'untata maka har zuwa girman mu Habu duk farke maka shagon da ake yi nine nasa da hannuna a ciki," sai da Abba ya razana girgiza Kai kawai ya yi domin bai tab'a tunanin Kawu ne ya yi masa haka ba domin a tunanin sa d'an uwan sa ai sai dai yaso cigaban sa amma gashi d'an uwan nasa ne da hannu cikin kashe masa wajen sana'a.
Kawu ya cigaba da cewa "Sannan Maryam ki gafarceni neman Maryam da akayi aka rasa mune sila domin mune muka je wajen bokanya ta yi mana aiki akan a b'atar da ita sannan a mantar da ita k'auyen da duk mutanen k'auyen ballantana mijin ta da yaranta amma da Allah yaso asirin mu ya tonu sai rana d'aya bamu barbad'a maganin da ta bamu ba akan musa kullum ba daga nan bokan ya ta tabbatar mana cewa dole Maryam zata dawo sannan zamu d'and'ana talauci mai zafi haka kuwa aka yi abinci ma gagarar mu yake yi duk wata kadara ta mu sai da muka siyar ga Kuma Zainabu a gida saboda itama asirin da muka yiwa Sadam ya karye shine ya korata gida Dan Allah ku yafe mana munyi hakan ne saboda sharrin shaid'an da Kuma hassada saboda Sanin Maryam wacece da Kuma kud'in iyayen ta hakan ne yasa mana hassada da rashin son cigaban ku amma munyi nadama,"
Abba duk sanyi AC dake falon amma goge gumi yake yi jin aika aikar da yayan sa ya yi Doctor ma jikin ta duk ya yi sanyi a hankali hawaye suka zubo kan fuskar ta jin akan wani Abu na duniya ake neman hallaka ta ga rabata da 'ya'yan ta da aka yi da kuma mijin ta a lokacin da tafi buk'atar su a lokacin da ta rasa nata mahaifan gaskiya su Kawu sun cutar da ita a rayuwa.
Lantana ta ce "Duk abinda malam ya fad'a gaskiya ne amma Dan Allah ku yafe mana dan girman Allah munyi nadama tun ba yanzu ba," wata uwar harara Sabeeha ta zabga Mata domin wata sabuwar k'iyayyar su taji a ranta domin jin duk sune silar jefasu a wata rayuwar a baya wacce ba dan Allah ya tsare su ba da sun fad'a wata rayuwar daban.
Sameeha kuwa hawaye ta dinga gogewa Sabreen kuwa itama tsanar su ce ta ninku a ranta tab'e baki ta yi ta kauda kanta daga kallon su.
Zainabu ta ce "Dan Allah ku yafe mana ba dan halin mu ba mun aika ta laifi dukan mu ko Lantana?" Harara Sabeeha ta wurga mata taja wani dogon tsaki jin yadda 'ya ke gatsa sunan mahaifiyar ta kamar ta Kira sa'ar ta.
Da kallo mutanen wajen suka bita Zainabu kuwa sai wurga ido take yi tana k'arewa falon kallo domin yafi Wanda aka kaisu kyau tana ganin can d'in kamar ba a Nigeria ba sai ga Wanda ya fi shi gashi sunci abincin da basu tab'a cin mai dad'in sa ba ga kaji sai da suka bar su da lemuka.
Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Yaya tabbas kun cutar da rayuwar mu da ta yarana Amma bakomai Allah ma munayi masa laifi ya yafe mana mun yafe Allah ya yafe mana baki d'aya," suka amsa da "Ameen," Kawu Yana hawaye ya ce "Nagode Habu nagode," Doctor ma ta ce "Nima na yafe muku," godiya sosai suke yi sannan suka kalli 'yan uku tun kafin su yi magana Sameeha ta ce "Mun yafe,"
"Kin yafe dai," cewar Sabreen Sabeeha kuwa wayar k'arya ta fara ta mik'e tabar falon domin idan ta ce zata yi magana to maganar da zata fad'a baza ta yi dad'i ba.
Doctor kuwa ita kunya ma suka bata ta kalli Kawu ta ce "Yaya kayi hak'uri," Kawu ya ce "Bakomai Maryam yarana ne ai Kuma a abinda nayi musu a hakan ma ba k'aramun hak'uri suka yi ba," Doctor kuwa kallon Sabreen dake zaune ta yi kicin-kicin ta yi ta yi k'wafa.
Abba ya ce "Yaya kuje ku huta nasan kun gaji nima zan fita ne," tashi su Kawu suka yi zuwa part d'in da aka sauke su Abba Kuma ya hau mota ya fita.
Da daddare har d'aki Doctor ta samu su Sabeeha ta fara yi musu fad'a baji ba gani sai da ta gama fad'an ta sannan tabar d'akin.
Sameeha ta ce "Dan Allah ku fahimci Mama maganar ta gaskiya ne ku yafe musu ko mu muna yiwa Allah laifi Kuma ya yafe mana duk abinda suka yi mana ba gashi sunyi nadama ba Kuma da sunsan wannan ranar na tafe da baza su aika mana haka ba," tab'e baki Sabeeha ta yi ta fice daga d'akin domin ita tana da wani hali rik'o ne da ita sosai sannan idan tayi fushi akan abu to ana shan wuya kafin ta sauko.
Har Sabreen zata tashi Sameeha ta rik'o hannun ta tana hawaye da sauri Sabreen ta zauna ta ce "Subhanallah dear ki dena kuka please," cikin hawaye Sameeha ta ce "Haba dear kuna ganin ya dace Mama tayi fushi da ku laifin fa da su Kawu suka yi mata yafi namu girma rabata suka yi da duk wani farin cikin ta suka rabata da mu duk da kuwa soyayyar dake tsakanin uwa da yaran ta Amma ta yafe musu meyasa mu bazamu yafe musu ba bai kamata mu zama d'aya da su ba," ajiyar zuciya Sabreen ta yi ta ce "Nagane dear,"
"Yawwa sister me muje mu bawa Mama hak'uri," Sameeha ta fad'a tare da jan hannun Sabreen suka fita daga d'akin a falo suka samu Sabeeha nan itama suka kashe mata jiki da maganganun su tashi ta yi suka tafi bawa Doctor hak'uri amma ta k'udurta a zuciyar ta babu ruwan ta da su Zainabu.
A d'aki suka samu Doctor tana waya da Ummi sai da ta gama sannan ta kalle su ta kawar da kai tashi Sabeeha ta yi ta zauna gefen doctor ta yi Mata side hug ta ce "Kiyi hak'uri kinji Mamana baza mu k'ara ba," Sabreen ma ta rungume ta ta d'aya side d'in ta ce "Please Mama we promise that we will not do it again," ajiyar zuciya Doctor ta yi ta ce "Shikenan na hak'ura ku rungumi 'yar uwar ku ku koyar da ita abinda bata saniba idan tayi ba daidai ba ku nuna mata kuskuren ta bata da wad'an da suka fi ku Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen uwa ta gari," daga haka suka fita daga d'akin.
Washe gari da safe Doctor Abba da Kawu suka je