Showing 27001 words to 30000 words out of 140483 words
abinda Sabeeha ta fad'a mata dangane da rayuwar su.
Ummi har hawaye ta yi gaba d'aya tausayin su ya kama su Maleek kuwa tunda Rinaz ta fara magana yake kallon ta saboda ya tausaya musu jin za ayi musu auren dole a zuciyar sa yace kamar dai ni da Uncle ya yi mun amma nasu daban ne domin ko uwar da zata rarrashe su bata kusa.
A hankali ya ce "Ummi dan Allah kuyi hak'uri duk bansan da haka ba amma insha Allah zansa a nemo su Ina son hoton su," Ummi ta ce "Mamana akwai hoton su?" D'aukar wayar ta ta yi ta ce "Eh akwai video d'in da nayiwa Sabeeha tana yin girki," ta fad'a tana mik'awa Maleek wayar.
Karb'a ya yi ya Kai idanunsa kan wayar saurin mik'ewa ya yi Yana k'urawa wayar ido gani yake ko dai gizo idanunsa ke masa murza idon ya yi Yana kallon ta tana girki tana murmushi saurin juyawa ya yi da sauri yabar falon da kallo su Ummi suka bishi har ya fice.
Yana fita ya k'walawa Salman kira yana zuwa ya ce "Ku kawo motoci," motocin aka kawo aka bud'e masa ya shiga sannan suka bar gidan sai jiniya ke tashi wajen mota ashirin suka fita neman 'yan uku.
Ya yinda Maleek ta lumshe idanunsa hoton fuskar ta kawai yake gani yana jin meyasa ya aikata hakan ashe dama ita ce a gidan su take masa daddad'an girki bai saniba bud'e idanunsa ya yi Yana k'ara kallon videon sannan ya nunawa Salman ya ce "ita zamu nemo,"
Nan suka fara zagaye garin kaduna suna duba inda zasu hango su Sabeeha amma shiru babu su ba alamun su.
Basu suka koma gida ba sai dare a gajiye Maleek ya shiga falon Ummi domin tunanin ta da yake yi ne ya saukar masa da wani irin ciwon kai Wanda bai tab'a tunaninsa ba domin Maleek yana d'aya daga cikin masu barin abu a rai abu kad'an sai ya hana shi sukuni.
Yana shiga falon Rinaz ta mik'e da sauri ta ce "Yaya an same su?" Girgiza Kai ya yi sannan ya zauna kusa da Ummi gaba d'aya ya rasa nutsuwar sa ganin halin da ya shiga Ummi ta ce "Son lafiya kuwa?" Kallon Ummi ya yi da idanuwan sa da suka yi jajir ya ce "Ummi bamu same ta ba Ummi ita ce ita ce Wacce zuciya ta take so ita ce Wacce tunanin ta ya hanani sakewa," ya fad'a kamar zai yi kuka.
Ummi ta ce "Ita ce wa?" Ya ce "Ummi ita ce Wacce nagani waccan lokacin a waccan k'auyen yanzu a Ina zan ganta sonta ya yi mun kamun da ban tab'a tunani ba," cikin Mamaki da tausayin d'an nata ta shafa kansa ta ce "Nasan kana sonta tunda har ka iya furtamun domin nafi kowa sanin yarona idan har ya furta Yana son abu to ba k'aramun so yake wa abun ba dan haka ka kwantar da hankalin ka har zuwa lokacin da za a gansu," noding kansa ya yi yana jin idan ba a ganta ba zai shiga wani hali.
Har Rinaz ta bud'e baki da niyyar fad'in inda suke sai Kuma ta yi shiru a zuciyar ta tana fad'in ashe dama ita Yaya ke matuk'ar so aikuwa sai na wana shi kafin yasan inda suke.
Karb'ar wayar ta ta yi ta haye stairs ta kira dija a waya daga can Dija ta ce "Beb yane nagode da kyautar k'awaye masu shiga rai," dariya Rinaz ta yi ta ce "Ya suke to?" Dija ta ce "Normal ga Sabeeha a nan Sabreen da Sameeha na tare da aunty a kitchen," jinjina kai Rinaz ta yi ta ce "Yawwa ba Sabeeha wayar," karb'a Sabeeha ta yi ta ce "Hello Rinaz dear," Rinaz ta ce "Yes kina jina ba Ummi ta dawo taji mai Yaya ya yi sannan bata ji dad'i ba haka ma yaya Fauwaz amma kinsan me sharri Nasreen ta yi mana wajen yaya sannan na fad'a masa abinda ya faru yanzu haka baki ga damuwar da ya shiga ba bai dad'e da dawowa daga neman ku ba amma ban sanar da kowa nasan inda ku ke ba Dan haka ku zauna a nan har saina wana Yaya," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "To ba damuwa ya Ummi fa?" Rinaz ta ce "Tana lafiya sai dai tana cikin damuwar rashin ku," murmushi Sabeeha ta yi tabbas tasan Ummi Mai k'aunar su ce.
Da haka suka yi sallama Rinaz kuwa ba ta fad'a wa Sabeeha komai akan budurwar da yake so ba saboda tasan zuciyar Sabeeha cike take da haushin Maleek idan ta fad'a mata ma ba lallai su koma gidan domin zata iya tunanin dan yana sonta ne shiyasa ya matsu su koma sannan Kuma ba ta da tabbacin Sabeeha ya gani a k'auyen may be Sabreen ce ko Sameeha domin tasan Yaya Maleek bai tab'a ganin ko d'aya a cikin su ba.
Ranar Ummi da Fauwaz basu rintsa ba balle Kuma oga Maleek domin tunda ya yi wanka ya yi sallah ya kwanta saman gadon sa ya fad'a tunanin yanzu idan ba a ganta ba ya zai yi haka ya yi ta tunani gashi Nasreen ta dame shi da kira Amma ya k'i d'agawa domin wani mugun haushin ta yake ji domin duk ita ta ja komai ranar dai inda ya ga rana haka ya ga dare ko da Asuba da ya yi Sallah bai iya yin baccin ba addu'a kawai yake yi Allah ya bayyana ta sai dai zuwa lokacin shima ya fara karaya akan idan ma ta dawo dakyar ta so shi saboda yasan cewar yanzu haka haushin sa take ji.
Yana zaune har gari ya yi haske wanka kawai ya yi suka k'ara fita neman su ba tare da ya ko yi breakfast ba ranar ma haka suka wuni neman su Sabeeha amma basu ba labarin su domin Ummi har Fulani ta kira ta tambaya Amma aka ce basu je ba.
Haka ranar ma Maleek ya komawa Ummi kamar zai yi mata kuka dakyar ta rarrashe shi amma duk yadda taso ya ci Abinci k'in ci ya yi ranar ma haka ya kwana bacin abinci ga rashin bacci.
Sabeeha ce kwance da daddare haka kawai taji bacci ya k'auracewa idanunta sai juyi take yi Sabreen ta yi juyi ta ce "Sabeeha dear lafiya kuwa? A hankali ta ce "Bansaniba dear banjin bacci ne kawai amma kina ganin mu koma gidan nan kuwa?" Sabreen ta ce "Eh mu koma mana idan bamu koma ba Ina zamu je?" Sameeha dake jinsu ta ce "Nima ji nake kamar kar mu koma saboda kar suyi tunanin saboda dukiyar su zamu koma," Sabeeha ta ce "Nima abinda nake tunani kenan sannan Wallahi yayan Rinaz bai da kirki akan Matar sa ita Kuma da gani makira ce tunda har ta nuna bata son mu nasan kad'an muka fara gani a cikin makircin ta Ni nasan tabbas akwai abinda zai faru gaba," Sabreen ta ce "Haka ne Kuma dear yanzu meye mafita?" Sabeeha ta ce "Kawai gobe mubar gidan nan," haka suka tsayar da shawarar gobe zasu bar gidan gara ko k'auye ne su koma abinda basu saniba shine duk firar su Dija na jinsu sannan sun burge ta ta wani b'angaren sai dai bata ji dad'in tafiyar da suka ce zasu yi ba domin har ta saba da au gasu da shiga rai sannan tasan indai ta b'angaren su Ummi ne basu da matsala sai dai Nasreen domin bata da kirki ko kad'an.
Washe gari da wani zazzafan zazzab'i Maleek ya tashi domin tun daren jiya ya rufe shi gashi yak'i ya sanarwa kowa Yana kwance lullub'e da blanket fuskar sa ta yi jajir da kyar ya iya tashi ya yi sallah ya yi wanka ya koma ya kwanta gashi bai ci komai ba balle ayi maganar magani hatta soldier's d'insa dake tsaron sa basu san baida lafiya ba gashi har lokacin Nasreen bata dena Kiran sa ba.
Kasa jurewa Nasreen ta yi ta shirya ta nufi part d'in nasa tura k'ofar d'akin nasa ta yi ta shiga can ta hango shi duk'un k'une a blanket da sauri ta k'arasa ta ce "Ya Maleek baka da lafiya ne?" Saurin runtse idanunsa ya yi domin baya son ganinta domin ita ce silar faruwar komai ganin yayi mata banza ne yasa ta zari wayar sa d'aya dake bedside drower ta lalubi number d'in Ummi ta kira lokacin Ummi zata tafi office ta kalli Rinaz ta ce "Mamana zan tafi office daga nan zan je na bayar da cigiyar su Sabeeha na damu da rashin ganinsu gari ko garin su bamu saniba gashi son ya damu sosai," jinjina kai Rinaz ta yi.
Wayar Ummi ce ta d'auki k'ara ta d'auka sai Kuma ta ce "Subhanallah gani nan zuwa," tana fad'ar haka ta nufi k'ofa hankalin ta a tashe domin sanin kanta ne Maleek Yana da ciwon zuciya Wanda tun yana yaro yake da shi Kuma bai fiya tashi ba sai ya shiga damuwa.
Ganin Ummi ta fita hankalin ta a tashe yasa Rinaz binta da gudu tana tambayar ta lafiya ba abinda Ummi ta iya furtawa mota kawai suka shiga zuwa part d'in Maleek.
Da sauri suka shiga d'akin suka same sa kwance a cikin blanket da sauri Ummi ta k'arasa ta ce "Son," sai lokacin ya bud'e idanun sa da suka yi jajir ya kalli Ummi ba tare da yace komai ba dafa goshin sa ta yi taji zafi zau ta ce "Son tashi mu tafi hospital," janye masa blanket d'in ta yi ya mik'e duk da bai da lafiya jarumtar sa na nan domin mik'ewa ya yi tsaf Ummi ta rik'e hannunsa suka fita Rinaz na biye da su ita da Nasreen.
Suna fita Ummi ta bada umarnin a kawo motoci ba tare da b'ata lokaci ba aka jera motoci suka shiga sojojin suka ja motar suka bar gidan Rinaz na gaban mota Ummi na back seat Maleek ya d'ora kansa a kafad'ar ta Yana tunanin wane hali yarinyar sa take ciki.
A haka suka k'arasa asibitin suka yi parking aka bud'e musu k'ofa Ummi ta fita hannun ta rik'e da na Maleek direct office d'in ta suka nufa su Salman na biye da su har sai da suka shiga office d'in sannan suka tsaya daga waje domin tsaron ogan nasu yayinda su Ummi suka shige ciki tare da su Nasreen.
Suna shiga Ummi ta zaunar da shi kan kujerar ta ta fara yi masa gwaje gwaje nan ta gane zazzab'i ke damunsa wanda tunanin da yake yi ne ya kawo masa shi d'akin dake office d'in ta ja shi tasa masa drip sannan ta zauna gefen gadon yayin da Rinaz ke gefe a tsaye Nasreen Kuma zaune kan wata hadadd"iyar kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sun dad'e a haka kawai suna kallon sa Ummi ko ba a fad'a mata ba tasan akan Sabeeha ne itama Rinaz tunanin da take yi kenan Nasreen Kuma tunani take yi Mai ya kawowa Maleek wannan zazzab'in cikin k'ank'anin lokaci.
Ummi ta kalli Rinaz ta ce "Rinaz ku je da Salman ki had'o abinci ki kawo mun," Rinaz ta ce "To Ummi," ta fad'a tare da juyawa da niyyar fita wayar ta ta fara ringing tana dubawa ta ga Dija ce ta ji dad'in Kiran dama so take ta kira ta domin ta aika a dawo da su Sabeeha sai dai tana d'agawa ta ji Dija na cewa "Beb akwai matsala fa jiya da dare naji su Sabeeha na shawarar barin gidan mu domin baza su dawo gidan ku ba domin gudun abinda zai je ya dawo gashi yanzu sun fita ba yadda banyi da su ba sun k'i zama," a rud'e Rinaz ta ce "Kina nufin su Sabeeha sunbar gidan ku to Ina suka tafi?" Dija ta ce "Nasan baza su wuce tasha ba domin gida suka ce zasu koma," Rinaz ta ce "Bari naje tashar," Maleek na jin haka ya yi saurin tashi zaune ya fisge drip d'in da aka sa masa ya mik'e ya yi hanyar waje tare da cewa Rinaz "muje," bin bayan sa ta yi suka fita daga office ya ce "Salman muje," bin bayan sa soldier's d'insa suka yi.
Ummi kuwa kasa magana ma ta yi tana kallon ikon Allah mara lafiya da tafiya neman Sabeeha lallai ba k'aramun so yake mata ba.
Nasreen kuwa wani bak'in ciki ne ya mamaye mata zuciya ganin Wai ya tafi tasha neman su Sabeeha lallai dole ne ta d'au mataki a kansu.
[10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️
RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)
SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)
Page 8
Maleek yana fita aka bud'e masa mota ya shige yana jin wani farin ciki a zuciyar sa gudu sosai soldier's d'insa ke zabgawa a hanyar ga jiniya na tashi duk inda suka wuce sai an kalle su.
Rinaz na gaban motar da Maleek ke ciki a hankali ta juya ta kalle shi suna had'a ido ya zabga mata harara ya ce "Wallahi zaki gane kurenki wato dasa hannunki a rashin lafiya ta ko?" Ya yi k'wafa ta ce "Sorry Yaya ita ce fa tace baza ta koma ba Kuma ai kaine baka tsaya kaji meya had'a mu ba," ya ce "Hmm baza ki gane baki da wayo ba sai idan bamu ga yarinyar nan ba," ya fad'a Yana k'ara aika mata harara ita kuwa Rinaz shiru ta yi tana addu'ar Allah yasa ma a gansu d'in.
Shi kuwa Maleek lokaci zuwa lokaci yake kallon agogon hannunsa domin gani yake duk wasu mintunan dake wucewa suna nufin tafiyar su Sabeeha.
Kai tsaye ya ce a shiga har cikin tashar aikuwa suka shiga cikin tashar Nan fa kallo ya koma kan motocin sa domin ko ba a fad'a ba ansan shine a ciki kowa mamaki yake yi to me ya kawo MG Maleek tasha yake yi ya yinda shi kuwa MG bai damu da kallon da akewa motocin sa ba.
Cewa ya yi su yi parking aikuwa suna yi bai jira an bud'e masa k'ofa ba ya bud'e ya fita Rinaz ma ta fita haka ma sauran soldier's d'insa suka fito suka tsaya a bayan sa kowannen su rik'e da bingiga.
Kai tsaye ya nufi inda motocin tashar suke yayinda mutanen dake tashar kowa yabar abinda yake yi ya tafi kallon MG Maleek wasu sun sanshi a TV wasu a jarida domin ba Wanda ya tab'a ganinsa a araha haka wani ma sai dai ya ga wucewar motocin sa amma yau gashi har cikin tasha.
Mata kuwa har ma da mazan sai nuna shi suke yi domin ganin tsananin kyawunsa sanye yake cikin army green d'in trouser da farar t-shirt sai Kuma army green shirt a sama takalmin k'afar sa ma army green ne sumar kansa sai shek'i take yi gashi ta sha wani had'adden aski sai k'amshi ke tashi Nan fa matasan suka fara "Allah ya kare mana MG," hannu kawai ya d'aga musu yana sakin murmushi Wanda ya k'ara faranta ran masoyan nasa domin Yana da masoya sosai saboda bai da girman kai Yana da son al'umma.
Sabreen ta kalli Sameeha dake kusa da ita ta ce"Sameeha dear kalli fa gab'a d'aya 'yan cikin tashar nan sun taru waje d'aya lafiya kuwa?" Sameeha ta ce "Nima dai abinda na gani kenan gashi Kuma Sabeeha dear har yanzu bata dawo ba,"
Sabeeha kuwa cikin wani shago ta je siyo ibon sweet ta dawo ta ga gaba d'aya tashar ta wani rikice kowa ka kalla fuskar sa tabb farin ciki a fili ta tab'e baki sannan ta nufi wajen mutanen tana fad'i a zuciyar ta Kai nima bari naje na ga Mai ake kallo haka da a bani labari gara na bayar.
Lokacin da ta nufi wajen Maleek ya fara tafiya shi da Rinaz domin duba ta aikuwa mutanen gaban su na matsawa domin basa hanya ya wuce ita Kuma na k'ara kutsa kanta aikuwa sai tsintar ta ta yi gaban su cak ya tsaya yana binta da ido kamar bai tab'a ganin ta ba sai ranar Sabeeha kuwa kallo d'aya ta yi masa ta kauda fuskar ta ba Wai dan ta gaji da kallon sa ba a'a kawai dan tana d'an jin haushin sa ne ga kuma wani hamshak'in kyau da ta ga ya k'ara.
Rinaz kuwa da gudu ta k'arasa wajen Sabeeha ta rungume ta tana murnar ganin ta ita kuwa Sabeeha murmushin yak'e ta yi tana satar kallon Maleek Wanda ya kafeta da idanuwa Rinaz ta ce "Yanzu Sabeeha dear da tafiya zaku yi ku barni?" Kad'an Sabeeha ta yi dariyar da iyakar ta fuskar ta saboda ita har ga Allah taso sun tafi.
"Sameeha dear muje mu gani me yake wakana a can wajen muma," cewar Sabreen ta bud'e k'ofar motar ta fice itama Sameeha ta fita suka nufi wajen mutanen.
Suna zuwa suka tarar da Sabeeha tare da Rinaz su Sam basu kula da Maleek ba da yake gefe a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon Sabeeha.
Rinaz ta ce da Sabeeha "Ina su Sabreen fa?" Sai lokacin ta hangi su Sabreen suna tsaye ai da sauri suka k'arasa suka rungume juna da Rinaz suna farin ciki sai lokacin idanun Maleek ya sauka a kan su Sabreen da Sameeha zare ido ya yi cikin Mamaki Yana kallon su sannan ya kalli Sabeeha ya sake kallon su ya kalli Sabeeha shi a dole yana son ya nemo banbancin su amma ba bambamci a zuciyar sa ya ce "Tofah MG kana ruwa yanzu wacce nagani that time," su Sabreen ma sai lokacin suka kula da Maleek kallon sa suka tsaya yi kamar guma ka gani suke yi kamar a mafarki ne suke kallon wannan balaraben yadda ya tsaya kallon su su d'in ma haka suka tsaya kallon sa shi Yana mamakin kamar su su ukun su Kuma suna mamakin kyansa.
Su kansu mutanen tashar tsayawa kallon 'yan uku suka yi ganin tsananin kamar dake tsakanin su juyawa kawai Maleek ya yi ya nufi motar sa ana bud'e masa ya shiga ya yinda Rinaz da su Sabeeha suka shiga motar dake bayan tasa suka bar tashar.
Kai tsaye gida suka nufa Rinaz ta kira Ummi a waya ta ce "Ummi mun wuce gida tare da Yaya da kuma su sabeeha," cikin jin dad'i Ummi ta ce "To shikenan sai na dawo," daga haka suka ajiye