Showing 138001 words to 140483 words out of 140483 words
ja hannun ta ya karb'i key hannun Adam ya shiga driver seat Sabeeha ma ta shiga suka d'auki hanya ba tare da su Ummi sun ankara ba ya ja motar da gudu yana fad'in "Yanzu sai ki ga 'yan jarida sun cika airport d'in nan ni kuma hakan ne banso," ajiyar zuciya Sabeeha ta sauke ta ce "Nima kam baso nake yi ba kana ganin ranar da zamu tafi inda suka zagaye mu a airport d'in nan," dariya ya yi ya ce "Ke Kuma ki ka so ki nuna musu ke rigimammiya ce ba kuka fa na ga Zaki yi," dariya itama ta yi ta ce "Allah husby naga ba Kai suka fiya ba," haka suka k'arasa gida suna fira abinsu ga mamakin Sabeeha Rashida suka samu a part d'in Ummi tare da su Hadiza suna jera abinci a daining su suka tarbe su.
A airport kuwa yarinyar nan tana ganin so daga hannun wannan sai hannun waccan yarinya kuwa ba dai wayo ba duk Wanda ya d'auke ta sai ta yi masa k'urr da idanu tana kallon sa Sabreen Bata damu da cikin dake jikin ta ba ta yi tsalle ta ce "Wayyyo my heart kalla ka ga blue eyes gare ta wayyo kyau," Sameeha ta ce "Wow nikam dama a barmun," Fauwaz ya ce "Masha Allah yarinyar kama take yi da Yaya har tafi Yaya kyau ma,"
Umar dake gefen Fauwaz sai aikin hoto yake wa yarinyar ya ce "Gaskiya MG ya iya haihuwa wannan kyakkyawar yarinya haka ita ba yar indiya ba ita ba balarabiya ba,"
"Sameeha dear dai ta iya haihuwa," Sameeha ta fad'a tana k'ara kallon yarinyar "Ummi mu wuce gida ina MG d'in?" Umar ya fad'a suna waigawa suka ga ba Sabeeha ba Maleek sai tulin 'yan jarida da suka gani wajen.
Dakyar suka samu suka zille suka shiga motocin su suka tafi gida sai dai yarinya tasa hotuna da videos.
Ga mamakin su suna zuwa suka samu su Sabeeha har sun yi wanka suna zaune a daining suna cin abinci abinsu suna dariya.
A falo su Ummi suka ya da zango da baby girl da wutsil-wutsil da hannu da k'afa take yi Yarinyar daga ganin ta akwai wayo a wajen Umman Nasreen ce ta shiga falon itama ta karb'i yarinyar tana yaba kyan ta itama sai farin ciki take yi domin yanzu Allah ya shirye ta.
Kafin kace me su Fauwaz da Sabreen sai waya suke yi suna fad'ar haihuwar Rinaz dake India kuwa da su Hanfa da Hany har an cika musu wayoyin su da pictures d'in baby.
Su Zainabu kuwa suna jin haihuwar suka tafi gidan Ummi Abba da Daddy har ma da Uncle sai waya suke yi suna tambayar baby domin suma labari ya Kai musu.
Haka Baby da Maman ta ke samun kulawa a ta kowanne bangare ko yaushe gidan zaka samu ana farin ciki ana fira da dariya yayin da baby tana yin kuka hankalin kowa a gidan idan ya yi dubu ta tashi saboda so da k'aunar da ake nuna Mata a haka har ranar suna ta kusa inda ake ta yin shirye shirye ba kama k'afar yaro.
Ana I gobe suna Rinaz ta sauka a 9ja nik'i nik'i da tsarabar da ta yiwa baby su Sabeeha sai murnar ganinta suke yi da daddare Kuma su Daddy suka dira a k'asar har falon Uncle aka Kai musu baby a take Uncle ya yiwa yarinyar kyautar car key domin ji ya yi yarinyar ta shiga ransa sosai.
Washe gari suna gidan a cike yake da bak'i na kusa dana nesa su Hanfa duk sunzo da Mama Aisa har ma da su Aleem domin lokacin ansa ranar hanfa da Ashraf Hany da Alim saura wata d'aya.
Yarinya taci sunan Ummi Aysha amma suna Kiran ta da Alizah kaya kuwa yarinya tasha shi har iyayen ta sun rasa wajen sawa kyauta har da su car keys d'in da ta samu da yamma aka yi gagarumar walima ta gani ta fad'a anci ansha ba k'arya 'yan jarida da gidan televisions suka cika gidan uwar 'ya ta ci kwalliya kamar wata amarya domin idan ba fad'a maka akayi ba baza ka ce ita ta haihu ba.
Walimar babba ce domin har Nigerian army sunje inda a nan ne aka k'arawa Maleek girma daga MG zuwa Marshall social media ko Ina ka shiga su ake d'orawa a haka aka tashi yarinyar da iyayen ta sun samu kyauta babu k'arya.
Ranar da daddare Ummi tasa Sabeeha ta shirya tare da Baby alizah zuwa gidan Doctor domin su yi wankan gida Doctor su Ummi suka yi mata rakiya inda lantana ta tare su cikin farin ciki can aka cigaba da basu kulawa kullum Maleek na gidan hakama su Sabreen da Zainabu kowa ya d'orawa Alizah soyayya.
Satin su d'aya a gidan aka kawo kud'in auren Rinaz tare da saurayin ta Faruk aka sa rana one month hakan na nufin idan akayi nasu Hanfa da sati d'aya kenan Amma Daddy ya ce a had'a kawai a yi.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har Sabeeha ta yi arba'in da haihuwa inda a lokacin Kuma zasu tare a sabon gidan su.
Haka suka tare a sabon gidan su da ya gaji da had'uwa Ummi ce ta zuba komai na gidan tun daga compound d'in gidan za kasan mai gidan ba wasa b'angaren kud'i saboda motocin dake parking space baza su irgu ba da nasa dana matar sa da Kuma na baby Alizah balle ka shiga ciki fad'ar had'uwar gidan ma b'ata lokaci ne su Sabreen sai santi suke yi d'akin baby Alizah kuwa ba a cewa komai saboda tsabar had'uwar sa yaji kayan wasa komai na d'akin baby pink ne gwanin sha'awa haka aka watse akabar masu gidan.
A haka bikin su Hanfa ya matso tare da na Rinaz gaba d'aya su Ummi tarkatawa suka yi suka tafi Abuja har dasu Sabreen da su lantana har ma da su Uncle domin dama suna da family house nan za ayi bikin gida ne mai girman gaske Mai d'auke da wajajen hutawa da swimming pools da iska Mai dad'in gaske kasancewar gidan ya yi bayan gari ba abinda kake ji sai kukan tsintsaye sai duwatsu Kai wajen gwanin burgewa.
A nan aka yi shagalin bikin su Hanfa bikin ya k'ayatar ba k'arya kasancewar bikin ya samu gidan naira anyi harkar girma hakama ango faruk ba dai uban dukiya ba haka aka yi biki aka tashi lafiya aka Kai kowacce gidan ta Rinaz ma gidan ta dake Abuja aka kaita kafin subar k'asar zuwa India inda dama a can faruk ke aiki sannan dama Rinaz d'in bata gama karatun ta ba tayi kuka har ta gaji lokacin da su Ummi zasu koma kaduna sai dai ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta da angon ta su Hanfa kuwa ba wacce ta yi kuka domin suna ganin basu bar gida ba gasu ga yayyan su Kuma mazajen su sai ma duniyan cin da suke yi gaban mutane.
Bayan komawar su Ummi gida da sati d'aya Arfat tare da mahaifiyar sa suka je suka samu Uncle da Daddy akan cewar a taimaka aba Arfat auren Nasreen inda su Daddy suka ce ba ruwan su su sami Maleek har gida kuwa suka je suka sami Maleek akan maganar da ya nuna Sam bai yadda da hakan ba Mai hankali da nutsuwa zai ba k'anwar sa sai da Sabeeha tasa baki tare da nuna masa cewar Arfat fa nasan Nasreen sannan itama tana son sa sannan da baya sonta bazai jawo mahaifiyar sa har wajen sa ba tunda har ya riga ya samu abinda yake nema a wajen ta da Dan wani abu yake son ta da haka Sabeeha ta shawo kansa ya yadda inda yace sati d'aya kawai za asa bikin Arfat kam bai Musa ba tunda bai da matsalar komai akwai naira aikuwa sati nayi ba a yi wata bid'i a ba sai dinner aka Kai amarya gidan ta.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kowanne gida suna cikin farin ciki da nishad'i.
BAYAN SHEKARA UKU
abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har auren Salman da Aysha ta wajen aikin hajiya fulani da Kuma bikin dija da Muhsin d'an yayan Ummi da suka had'u a bikin 'yan uku Sabreen kuwa ta haifi twins duk maza kyawawa masu kama da 'yan uku anyi shagali ba kama k'afar yaro yara sunci sunan Daddy da Abba ana Kiran su Aiman da Ammar yaran sun ga gata ba k'arya Sameeha kuwa mace ta haifa Mai kama da Umar sai dai ita fara ce yarinyar kyakkyawar gaske taci sunan Doctor Amma suna Kiran ta ni'imatullah.
Sabeeha ce a kitchen tana aiki ta ji shigowar Alizah da gudu cikin falon ta nufi stairs tana k'wala Kiran "Momma! Momma," cikin hausar ta ta yara da bata gama iyawa ba.
Dafe Kai Sabeeha ta yi ta ce "Wayyo ni Sabeehan Mama naga ta kaina," ta fad'a tare da fita falon ta ce "Alizah me kika dawo yi kuma?"
Kyakkyawar yarinyar dake saukowa stairs tasha kyau cikin farar riga da k'aramun black skirt da toms d'in takalmi da farar safa da necktie da alama daga makaran ta take kallo d'aya zaka yi Mata kasan fitina ta ratsa yarinyar da wayo an gyara mata gashinta kanta an yi Mata two babies da shi ya zubo har kafad'ar ta Tasha jan ribbom ta ce "Momma na manta biro ne a gida ne nazo d'auka," ta fad'a tare da washe bakin ta fararen hak'oran ta suka bayyana dimples d'in ta ya lotsa.
Hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Duk laifina ne da na saki a makarantar dake kusa da gida sai ki dawo sai uku kafin a tashi," k'ifk'ifta blue eyes d'in ta ta fara ta zare idanunta Mai d'auke da zara-zaran eyelashes ta ce "Sorry momma karki ce Zaki canja mun school,"
"Sai Kuma kiyi yarinya canja makaranta ba fashi," Sabeeha ta fad'a tare da komawa kitchen d'in Alizah kuwa hanyar fita ta yi da gudu tana cewa "Na tafi Mama ta see you later," Sabeeha na jinta girgiza Kai kawai ta yi.
Da yamma da Maleek ya dawo ya samu Sabeeha zaune saman kujera tana chart da Sameeha ajiye wayar ta yi ta rungume shi tana masa sannu da zuwa zama ya yi a gajiye ta kawo masa ruwa ya sha ya ce "Ina Alizah fa?"
Kafin ta ce wani Abu sai ga Alizah ta fito da gudu daga sama tana k'ara itama Sabeeha ganin haka ta yi tsalle ta b'uya a bayan Maleek ta b'oye fuskar ta a bayan sa ya ce "Baby Aliz lafiya kuwa," raurau ta yi da ido ta ce "Papa wani Abu ne a d'akin momma zo muje ka gani Ina wasa na kawai yazo," sai lokacin Sabeeha ta kalli Alizah zare ido ta yi ta ce "Kam bala'i ka gani ko My ni kawai Wallahi ka d'auki yarinyar nan ka kaita wajen Ummi ko Mama ko ka kaiwa Sabreen dear ka ga fa inda ta yiwa jikin ta wanka da Mai har ma da jambaki," Sabeeha ta fad'a kamar zata yi kuka.
Shiru Maleek ya yi Yana kallon Alizah shi kansa ya jinjinawa fitinar Alizah ya ce "Yanzu Aliz haka kika b'ata jikin ki,"
"Ni ba wannan ba My kullum ita ce dawowa daga school sai ta dawo sai uku sau hud'u kafin tashi hatta teachers d'in su complain suke akan ta Ni kawai na gaji gara ka Kai ta wajen Umman Nasreen," Maleek kuwa jin Alizah na gudun makaranta take ya had'a rai saboda shi duk fitinar ta bata dame shi ba amma jin tana dawowa daga school sai ya ji bai ji dad'i ba ya ce "Kee! zonan," zare ido ta yi ta ce "Sorry papa ban Kuma ba kaji,"
"Kizo fa nace!," Ya fad'a a d'an tsawa ce Sabeeha kuwa dariya take musu k'asa k'asa a zuciyar ta ta ce gara ya yi maganin mara jin magana Aliza kuwa a hankali ta k'arasa wajen sa.
Jawota ya yi ya d'orata saman cinyar sa ya ce "Oya kiss your daddy," kiss ta bashi a check d'in sa tana dariya shima dariyar ya yi ya bata kiss a forehead d'in ta ya ce "Gobe ma zamu wuce Dubai a can Zan saki school kamar yadda nayi karatu primary da secondary d'ina a can haka ma my Aliz zata yi sannan maman ki ma school zata koma," Sabeeha dake tura bakin jin haushin k'in dukan Alizah ta buga tsalle ta ce "Wayyo da gaske My?" D'aga mata gira ya yi nan kuwa su Sabeeha har da rawar murna ya ce "Ku je ku shirya muje yiwa su Mama Sallama," ba b'ata lokaci suka yi wanka suka shirya suka fice.
Da gidan Mama suka fara sannan gidan Ummi a can suke jin Rinaz ta haifi namiji sunyi murna sosai sannan a can suke jin auren Rashida da Faisal driver d'in Doctor next week sun dad'e a gidan sannan suka nufi gidan Umar Sameeha ta tare su cikin farin ciki suna ta fira abin su Alizah kuwa sai da ta yi musu fitina domin kaca kaca ta yi da kayan dressing mirrow d'in Sameeha.
Bayan sunbar Nan sai gidan Sabreen can suka yi dinner suna ta kwasar fira inda Alizah ta mak'ale sai ta d'auki Aiman yaron da ko da kud'i aka had'ata bazata iya d'auka ba kan Sabeeha ta hana a bata ta dinga kuka har da cewa sai ta gayawa Uncle da Daddy dakyar suka rarrashe ta ta yi shiru da kukan ta da kana ji kasan na shagwab'a ne.
Suna barin gidan Nasreen shopping suka wuce bayan sunyi siyayya suna fitowa suka yi ana Kiran sunan Sabeeha suna waigawa suka ga Yallab'ai khamis tare da fareeda har ma da yara uku gaisawa suka yi cikin fara'a sannan su Yallab'ai suka yi Mata Allah ya Sanya alkhairi kowa ya shiga motar su suka tafi Alizah na damun su da tambaya "Momma na papa wancan Uncle d'an lukutin waye?"
"Malama ki yi mana shiru ke bakya gajiya da surutu ne tunda muka fito baki yi shiru ba," Maleek dake yiwa dramar tasu dariya ya ce "A'a baby kyale ta ta yi tambaya ai abinda Bata sani bane," shiru Sabeeha ta yi bata Kuma magana ba domin tasan yanzu sai su had'e mata Kai.
Nan Alizah tai ta jera tambayoyi domin ko a school haka take shiyasa teachers d'in su ke ji da ita gata da k'ok'ari da uban surutu shiyasa Maleek yasa ta school da wuri a haka suka koma gida.
Washe gari suka d'aga zuwa Dubai inda aka samarwa Alizah wata private school aka sata haka ma Sabeeha ta koma makaranta ya yinda Maleek ke zuwa office abinsa haka rayuwar su ta cigaba da gudana cikin farin ciki da k'aunar juna.
ALHAMDULILLAH
Anan na kawo k'arshen littafina Mai suna 'YAN UKU kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafemun Allah ya bamu ikon amfana da abinda littafin ya kunsa Allah ya yafe mana kurakuren mu Allah yasa mu cika da imani ameen.
Ina jaddada godiya ta ga masoyana Allah ubangiji yabar zumunci ya barmu tare Allah ya sake had'a kanmu Nagode Nagode daga taku a ko da yaushe HAFSAT MAGAJI DABO SHANONO (RUHAZ).