Showing 66001 words to 69000 words out of 140483 words

Chapter 23 - 'YAN UKU COMPLETE

11 Jul 2025

19390

yi da ita Ummi bata damu ba ta kalli Hajiya Asiya ta ce "Asiya Ina wuni?" Tsaki Hajiya Asiya ta ja Ummi kuwa ta ja bakin ta ta yi shiru Rinaz kuwa ganin da Daddy a wajen ta gaishe da Uncle amma ko kallon ta bai yi ba bare ya amsa shiru falon ya d'auka


Tsayuwar motoci suka ji a k'ofar part d'in Maleek ne ya yi sallama a falon Ummi Daddy ne da Rinaz kad'ai suka amsa Nasreen kuwa da kallo ta bi shi kamar ta had'iye shi saboda tsabar kyan da ta ga ya k'ara shi kuwa waje ya samu ya zauna sannan ya ce "Daddy Ina wuni ka dawo lafiya?" A ciki-ciki Daddy ya ce "Lafiya," saboda haushin Maleek yake ji saboda yana basa matsala shi da yayan sa.




Maleek kuwa kallon Ummi ya yi abun tausayi saboda bai ji dad'in yadda Daddy ya amsa masa gaisuwa ba ya ce "Ummina Ina wuni?" Ta ce "Lafiya lau son ka iso lafiya?" Ya ce "Lafiya lau Ummina," Rinaz ta gaishe shi ya amsa.




Saboda iyayi Nasreen ta ce "Ina wuni ya Maleek ka dawo lafiya?" Banza ya yi mata Uncle ya ce "Au baza ka amsa ba ana gaishe ka?" Shiru Maleek ya yi kamar bada shi ake magana ba sai ma cewa ya yi "Uncle Ina wuni," Uncle bai ko amsa ba ya fara balbala fad'a "To bari kaji daka amsa gaisuwar daughter da karka amsa dole ne ka mayar da ita wato saboda bamu isa da kai ba shine zamu aura ma yarinya ka sake ta har saki biyu saboda baka da tarbiyya?"




"Saki fa?" Daddy ya maimaita yana kallon Maleek Uncle ya ce "Eh saki har biyu saboda shi mahaukaci ne kuma sakin ma akan budurwa," shiru Maleek ya yi kansa a k'asa idanunsa sunyi jajir saboda b'acin rai ga zagi ana k'are masa.



Daddy shima ransa a b'ace ya ce "Saki Abdul-maleek ka saki 'yar uwar ka har saki biyu to akan wane dalili," kafin Maleek ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Ba shi da wani dalili wanda ya wuce a kan budurwar da yake so wannan ne dalili idan Kuma ni baka yadda dani ba nayi k'arya to ka cigaba da tambayar sa," Uncle ya fad'a duk Dan kar aba Maleek damar magana saboda yasan duk abinda Nasreen da mahaifiyar ta suka aikata.




Daddy kuwa jin abinda Uncle ya fad'ane yasa shi yin shiru Ummi ta ce "Son bai sake ta ba dalili ba..," d'aga mata hannu Uncle ya yi ya ce "To masu d'a kare shi Zaki yi kenan ai dama naji ance budurwar tasa 'yar gidan aminiyar ki ce dole ki so a saki Nasreen domin ya aure ta domin naji labarin a gaban ki aka yi sakin amma baki tsawatar masa ba kece ma ki kasa ya yi sakin," kallon Ummi Daddy ya yi girgiza masa Kai Ummi ta yi alamun ba bata da hannu domin jin Uncle na neman had'a mata sharri wajen mijin ta.




Sai lokacin Maleek ya d'aga Kai ya kalli Daddy domin baya son abinda zai had'a tsakanin Ummin sa da Daddy ya ce "Ba ruwan Ummina dan ra'ayin kaina na sake ta domin bana so na cigaba da zama da ita,"





"Ato Hamisu ka dai ji da bakin ka ko ya sake ta ne dan ya tozar ta mu," Fauwaz ne ya yi sallama a falon waje ya samu kusa da Maleek ya zauna baice komai ba.



Ucle ya ce "To baka isa ba tunda ba Kai ka haifemu ba yanzu sai ka mayar da ita Kuma babu saki tsakanin ka da ita Kuma wannan yarinyar dole ne ka rabu da ita," a razane Maleek ya kalli Uncle idanunsa kamar an watsa masa jajjagaggen attaruhu Uncle ya ce "Kalle ni dakyau yarinya tun yanzu tasa ka saki 'yar uwar ka ai bata arzik'i bace saboda haka ba kai ba ita Kuma yanzu yanzu ka mayar da daughter,"




Zumbur Fauwaz ya mik'e tsaye ya ce "Saboda me Yaya zai mayar da Nasreen bayan ba k'aunar sa take yi ba mahaukaciya ce ita dabba wacce taso ta ga bayan...," Kasa k'arasa maganar Fauwaz ya yi saboda marin da Daddy ya zabga masa ya ce "Ashe dama baka da hankali bansani ba idan ka Kuma magana anan saina b'ata maka rai Kuma lallai ka fito da mata kayi aure kabar gidan nan tunda baka da amfani a gidan kai kuma umarni ne wannan ba shawara ba yanzu ka mayar da matar ka," Daddy ya fad'a ransa a b'ace.



Hannu Maleek yasa ya rik'o na Fauwaz ya zaunar da shi zama Fauwaz ya yi dafe da kunci domin Daddy bai tab'a sa hannu ya daki d'ansa ba sai ranar Rinaz dake gefe sai hawaye take yi Ummi ma hawaye ta goge idanunta na kan Maleek domin ganin yanayin sa ya canja sosai jikin sa har rawa yake yi sannan ga gumi Yana yi duk da Ac dake falon shiru kawai ta yi.




"Kai muke jira," Daddy ya fad'a cikin had'e fuska yana kallon Maleek.




A hankali Maleek ya bud'e baki murya na rawa ya ce "Na mayar da ita," ya fad'a hawaye na zuba a idanunsa sannan ya ce "Daddy bazan yi saki ba tare da wani dalili ba amma na mayar da ita duk abinda ta yi mun Allah yana ganin ta amma Daddy Ina so na k'ara aure," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Baza ka k'ara auren ba saboda yarinyar bata da tarbiyya tun tana waje tasa ka saki matar ka ina ga ta shigo sannan saboda ba son daughter ka ke ba ita ke son ka idan ka auri waccan baza ka yiwa daughter adalci ba saboda haka baza ka yi auren ba," Daddy jin bayanin Uncle ya ce "Haka ne baza ka yi adalci ba saboda haka karna k'ara jin batun aure a bakin ka," zuwa yanzu kukan Ummi Mai sauti take yi domin tausayin yaron ta.




Maleek kuwa lokaci guda zuciyar sa ta yi wani irin bugawa da sauri ya mik'e tsaye ya yi hanyar fita sai dai kafin ya fita sai ji suka yi timm ya fad'i a wajen.




Da gudu Ummi Fauwaz Rinaz Daddy dama Nasreen suka yi wajen sa suna Kiran sunan sa amma ko motsawa bai yi ba.




A rikice Ummi ta ce "Fauwaz mu kai shi asibiti," da gudu Fauwaz ya fita ya Kira Salman suka kama Maleek zuwa mota Ummi da Daddy suka bisu a baya Rinaz ma zata bisu Daddy ya ce ta zauna a gida su kuma suka tafi.





Uncle kuwa tab'e baki ya yi ya fice shi da Hajiya Asiya.



Rinaz kuwa Kuka ta saki ta kwanta taita kuka



Sabeeha kuwa hankalin ta kasa kwanciya ya yi ko abinci kasa ci ta yi duk ta damu jiran Kiran Rinaz kawai take yi gashi har yanzu magrib shiru sannan Maleek ma shiru bai kirata ba kasa hak'uri ta yi ta Kira wayar Rinaz.





Rinaz dake kwance zazzab'i ya rufe ta ta d'auki wayar ta ce "Hello," Sabeeha ta ce "Please Dear maike faruwa?" Hawaye ne ya fito daga idanun Rinaz ta ce "ki hau WhatsApp yanzu,"




"Bani da WhatsApp lafiya ki ke kuwa?" Sabeeha ta tambaya a rikice jin muryar Rinaz wani iri Rinaz ta ce "Ki karb'i ta Sabreen zan tura miki sak'o yanzu," Sabeeha ta ce "Ok turamun," Sabeeha ta fad'a tare da kashe wayar ta nufi down stairs da sauri.




A zaune ta samu Mama da Abba da su Sameeha a falo ta kalli Sabreen ta ce "Sabreen dear bani wayar ki," mik'a mata Sabreen ta yi ta karb'a tare da komawa d'aki da kallo suka bita ganin ta kamar a d'an hargitse sai dai ba Wanda ya kawo komai a ransa.




Tana shiga d'aki ta kunna da ta kasancewar ba chart da mutane sosai Sabreen ke yi ba dan da nan message d'in Rinaz ya shigo jiki na rawa Sabeeha ta bud'e recording ne Rinaz ta tura mata wanda ta yi shi tun shigar su Uncle part d'in Ummi.




Zama ta yi gefen gado tana sauraro tass take jin abinda ke faruwa da maganar Uncle da ta Daddy duk abinda aka tattauna tana ji wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata jin abinda Uncle ke fad'i a kanta Wai bata da tarbiyya tausayin kanta da Maleek ne ya kamata kuka Mai sauti ta fara tana yinsa kamar ranta zai fita bata ji k'arar fad'uwar Maleek ba sai dai ji da ta yi hankali take su Ummi na Kiran sunan sa daga nan recording d'in ya k'are.





Hankali tashe ta tashi zaune gaban ta na fad'uwa jiki na rawa ta d'auki wayar ganin da voice a k'asa ta yi saurin bud'ewa ta kara a kunnen ta.





Muryar Rinaz na kuka ta ji tana cewa "Sabeeha Yaya yanke jiki ya yi ya fad'i tun lokacin har yanzu suna asibiti tare da su Ummi tun lokacin likitoci suke a kansa amma har yanzu bai farfad'o ba," Sabeeha na jin haka ta mik'e zumbur gaban ta na fad'uwa idanunta kuwa sai ambaliyar hawaye suke yi.



Kamar mahaukaciya ta fara magana a fili "Ya fad'i likitoci na kansa ko dai ya mutu ne Rinaz ta b'oye mun A'a bai mutu ba to meyasa bai tashi ba har yanzu?" Wata zuciyar ce ta bata amsa da kin manta yana da ciwon zuciya ko dai ya tashi ne.



Ai da gudu Sabeeha ta nufi down stairs yana kuka ko kallon inda su Mama suke bata yi ba ta yi hanyar fita ganin ta a hakane suma ya razana su da sauri Sameeha ta rik'o ta ta ce "sister Ina Zaki je lafiya kuwa?" Tana kuka ta ce "Cikani Sameeha ki cikani naje naga halin da yake ciki," wajen Mama da Abba suka yi ganin yadda Sabeeha ta koma kamar mai aljanu Sabreen ta ce "Dear lafiya?" Cikin kuka Sabeeha ta ce "Sister mutuwa zanyi kinsan me Rinaz ta fad'a mun kuwa?" Jin haka Sabreen ta nufi stairs domin d'auko wayar ta ta kira Rinaz ta ji meke faruwa.




Doctor ta rik'o hannun Sabeeha ta ce "Lafiya maiya faru Ina Zaki?" Abba ma ya ce "Aminiya ta maiya faru ne?" Kuka ta fashe da shi ta ce "Mama na shiga uku," tana fad'ar haka ta fad'a jikin Mama a sume.




A rikice suka fara Kiran sunanta Amma ko motsi bata yi ba.
[10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 17


Da sallama Kawu Bala ya shiga gidan sa ransa fess domin so yake idan ya je d'aurin auren yarinyar malam saleh ya bawa abinci mamaki.




Lantana ya k'walawa kira ta fito tana hura hanci tab'e baki Kawu ya yi ya ce "Je ki ki d'auko mun wannan kayan nawa babbar riga zani d'aurin aure," hanyar zaure Lantana ta nufa Kawu ya ce "Baki ji me nace bane kayana nace ki kawo mun fa," ba tare da ta waiga ba ta je har sharar da ta zuba kayan ta d'ebo su ta je ta zubar a gaban Kawu Bala.




Ba tare da ya kalli Kayan ba ya ce "Wai ni kuwa Lantana baki samu tab'in hankali ba taya Ina yi miki maganar kayana zaki d'ebo mun bola?" Kyalkyalewa da dariya Lantana ta yi ta ce "Kalli dai dakyau Bala kayan naka ne ai," saurin kallon gaban sa Kawu ya yi aikuwa idanunsa suka yi masa tozali da kayan sa da Lantana ta yiwa gutsi-gutsi.





Saurin mik'ewa Kawu ya yi ya nuna Lantana ya ce "Me nake gani haka?"



"Kayan ka mana ai nasan bayan su baka da komai shiyasa na huce haushin marin da kayi min a kansu Kuma wallahi kad'an ka gani daga aikin Lantana," jinjina kai Kawu ya yi zuciyar sa fal takaici da jin haushin abinda ta yi masa ya ce "Eh lallai ne naga aikin ki Lantana yanzu kuma zaki ga na Bala," ya fad'a yana d'aukar wani itace dake gefe.



Kamar wasa Lantana ta ji saukar itaccen a goshin ta wani uban ihu ta saki dan lokaci d'aya ta ji kanta ya yi mata mugun nauyi da gudu ta nufi d'aki sai dai kafin ta rufe har Kawu Bala ya shige yana shiga yasa sakata a k'ofar ya fara jibgar ta.




Ihu Lantana ke zabgawa tana cewa "Na tuba wallahi na tuba bazan k'araba shikenan zai kashe ni wayyo Allah hancina," haka lanatana tai ta ihu tana neman taimako amma Kawu bai dena nad'arta ba fad'i ya ke yi "Yau ai banga mai ceton ki ba a gidan nan dan Wallahi sai nayi Miki mummunan duka shegiya mai bak'in hali,"



Nasreen ce kwance saman gadon ta sai kuka take yi a fili ta ce "Wallahi Allah ya isa Umma da kika rabani da mijina," ta fad'a tana k'ara fashewa da wani sabon kukan sannan ta d'auki wayar ta ta kira wayar Uncle yana d'agawa ba tare da ta gaishe shi ba ta fashe da kuka har cewa ta shiga uku.




A rikice Uncle ya ce "Daughter lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Daddy ya Maleek ya sakeni,"



"What!?" Daddy ya tambaya tare da cewa "Ki kwantar da hankalin ki ki dena kuka next week zan zo k'asar zanji dalilin da yasa hakan dan uban sa tunda shi ba a isa da shi ba yaro sai rashin tarbiyya to zamu dawo tare da uban nasa naji ko shine yasa shi ya sakar mun ke," ya fad'a tare da katse Kiran.



B'angaren Lantana kuwa sai da Kawu Bala ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta ya fito daga d'akin ya fice yana masifa.




Lantana kuwa da dafa bango ta fito daga d'akin ga wani jiri dake d'ibar ta mayafin ta ta zara dake kan igiya ta fita tana tangad'i ko da ta fita bata ga Kawu Bala ba ta zari hanya ta tari mai machine ta fad'a masa inda zai Kai ta tana suna zuwa ta nuna masa wani gida mai koren fenti ya tsaya.





Sauka ta yi a hankali sannan ta kalli mai machine d'in irin d'an yau d'in nan ne Kuma daga ganinsa yana shaye shaye ga gashin nan an tsayar da shi a tsakiyar kai yayi buzu-buzu Lantana ta ce "D'ana yi hak'uri bari na shiga cikin gidan nan na karb'o maka kud'in ka," kallon banza ya yi Mata ya ce "Bangane d'anki ba Kinga malama bana son rainin hankali kawai ki ba mutum kud'in sa ya ware," a zuciyar ta Lantana ta ce "Na shiga uku ni Lantana gashi bani da ko sisi bari naje na samo masa kud'in sa idan ba haka ba tsaf na lura wannan zai d'ora wani dukan kan na Bala,"



"Kinga iya muna jira fa haba kinsan Baki da kud'i har da wani hawa babur," shiru Lantana ta yi ta juya tare da nufar k'ofar gidan.



Sadam ne ya fito daga gidan fuu kamar an jefo sa ajiyar zuciya Lantana ta sauke domin ba k'aramun jin dad'in ganin sa ta yi ba yana zuwa ko kallon Lantana bai yi ba ya kalli mai machine d'in ya ce "Kai yane zaka juya ne?" Mai acab'ar ya ce "Gaskiyar ka fad'a,"





Sadam ya ce "To muje," mai acab'a ya ce "To ke iya jira nake yi fa dan ba kwana nazo yi a nan ba ki bani kud'ina mana ke dan fa kece wallahi da tuni na bazar dake a nan," ya fad'a cikin wata k'atuwar murya Lantana ta kalli Sadam cikin bada umarni ta ce "Kai Sadam bawa wannan yaron kud'in sa,"





Wani kallon banza Sadam ya yi mata kamar ya ga kashi ya ce "A matsayin ki nawa a wajena zan baki kud'i kinga malama ki ba shi kud'in sa kawai ni wallahi mutane suna bani mamaki ace baka da kud'in kaza kace sai kayi haba," ya fad'a yana jan wani dogon tsaki.




Cikin gidan Lantana ta nufa tana fad'a a zuciyar ta shikenan komai ya lalace asirin da muka yiwa Sadam ma ya lalace.




Da sallama ta shiga gidan turus ta tsaya ganin Zainabu zaune ta rafka uban tagumi tana hawaye ga ciki duk ta rame ta k'anjale tayi bak'i har Lantana ta je ta d'auki naira hamsin d'in dake gabanta ta fice bata saniba sai da ta dawo sannan ta zauna gefen Zainabu tare da dafe goshin ta da ya yi wata uwar kumbura gashi har jini yake yi.





Dafata Lantana ta yi ta ce "Zainabu ta lafiya Mai ya faru?" Firgigit Zainabu ta yi tare da kallon Lantana tana ganin ita ce ta rushe da kuka ta fad'a jikin ta ta ce "Na shiga uku Lantana Dan Allah ki tafi dani gida Wallahi kashe ni zai yi idan ki ka barni a nan," a rud'e lantana ta ce "Zainabu baki da lafiya ne ki ka zama haka kamar mai ciwon k'anjamau?,"





"Lantana ni dai ki tafi dani kullum dukana yake yi baya bani isasshen abinci gashi baya barina fita Lantana asirin jikin sa ya barsa cewa yake yi uban meyasa aka aura masa ni ai shi bani ya ke so ba Sabeeha yake so sannan an kore shi daga wajen aikin su yanzu abincin da zamu ci ma gagarar mu yake yi," hawayen tausayin Zainabu ne ya fito daga idanun Lantana ta ce "Mu dai kam munga ta kanmu yanzu haka ma Bala ne ya yi min duka na taho nan gashi yunwa nake ji Zainabu bani abinci naci,"




Girgiza Kai Zainabu ta yi ta ce "Lantana kenan ai ko ruwan sha bamu da shi a gidan nan wannan hamsin d'in da ki ke gani ita ya bani na nemi abinda zanci na k'oshi," ta fad'a tana kallon gaban ta inda ta ajiye hamsin d'in ta ga wayam dube-dube ta fara yi ganin babu hamsin d'in inda ta ajiye ta.


Lantana ta ce "Ai hamsin d'in ita na d'auka na biya Mai acab'a da ita," Zainabu ta mik'e tana karkad'e daddaud'an zanin ta ta ce "Lantana tashi mu tafi," mik'ewa Lantana ta yi ta ce "Shawarata Zainabu ki zauna a gidan mijin ki domin idan ki ka bini sai kin dawo domin Bala yanzu banda talauci ba abinda yake fama da shi gara ma a nan kina samun hamsin d'in amma a can garin k'waki na ashirin babu me baki," kuka Zainabu ta fashe da shi tana rik'e wuyan hijabin ta da ya yage ta ce "Wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login