Showing 60001 words to 63000 words out of 70769 words
ta ce "Ba ka nuna min ka fi son Umar akaina ba, kuma Umar
ɗ
in da ya cuce ni"
Ya ce "Wa ya fa
ɗ
a miki, Lalle har yanzu baki san yadda nake ji da ke ba, y
anxu dai mubar wannan zancen Daddy ya ce "Gobe zamu je Bauchi dukan mu "
Hararansa tayi ta ce "Ni ba inda zanje"
Ya ce "Baki son ganin su Ya Abubakar ko"
Shiru tayi can kuma ta juyo da jikinta gurinsa ta ce "Ehhhh haka ne, su ya Abubakar
suna nan, amma badan su ba ba inda zani "
Da yamma kuwa saiga Mommy, Daddy, Maryam da Umar, Bilkisu ta musu tar
ɓ
a ta Musamman ta gaida su Amma Umar ko kallon sa bata yi ba. Daddy ya fara magana ya ce "To Bilkisu abin da nake so da ke, kiyi haƙu
ri ki manta da komai gobe zamuje Bauchi gun iyayen ki"
Ta sunkuyar da kai ta ce "To Daddy duk abin da ka ce haka za'a yi"
Maisun ce ta fito da yake yau Alhamis ba Islamiyya tana ganin su ta fa
ɗ
a jikin Daddy tana gaishe shi, Daddy ya nuna mata
Umar ya ce "Ga can Daddynki kije ki gaishe shi"
Kallon sa ta ringa yi can ta ce "Daddy na kuma, wannan fa me wanki ne, " Ta nuna Aliyu ta ce "Nika ga Daddy na nan" sai kuma ta fa
ɗ
a jikinsa.
Kunya ce ta kama Aliyu sai ya janye ta ya ce "Maisun
wannan ma Daddyn ki ne kije ki gaishe shi"
Ta je ta hau jikinsa ta ce "Shine tun tuni baka zuwa sai yanzu"
Shidai Umar yana Shiru ba Magana. Sai da
ɗ
i da yake ji ƴarsa na jikin sa.
Washe gari Sassafe suka
ɗ
auki mota
ɗ
aya Aliyu ne ke j
an mota, sai Bilkisu a gaba, Daddy da Mommy kuma suna can baya, sai Maryam da Umar riƙe da Maisun sune a bayan su Aliyu, wato tsakiya kenan.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐
ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa
.
✍
🏻
[6/10, 7:24 AM] Mim
😘
:
🌐
_*
🇭
ιĸιмaн
🇼
rιтer'ѕ
🇦
ѕѕocιaтιon*_
🌐
( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........
✍
🏻
🌐
BILKISU
Labari da rubu
tawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 69-70
Aliyu ya iya gudu a mota, wai dan ma Daddy yana masa magana, wannan yasa suka isa
da wuri. Gidan Abba suka yi da Umma ce kawai a gidan sai Khadiyo da tazo dama Umma tasan da zuwan su taji komai, Khadiyon
ɗ
in ne bata sani ba, tana ganin Bilkisu ta je da gudu ta rungumeta sai kuma tasa kuka tana cewa Aunty ina kika shiga ne mukai ta ne
man ki, kinsan jalin da muka shiga kuwa?"
Zama suka yi Umma da Khadiyo suka kawo musu abinci da Abinsha, kafin su gama kuwa Umma ta kira Abba, Baba, Abubakar da Usman. Ita kan Bilkisu sam ta kasa cin Abincin ma tana cewa da Umma ita yayyenta.
Ba jimawa suka Baba ya shigo gidan yana ganin Bilkisu yaje ya zauna gefenta ya kama hannunta ya ce "Bilkisu! Kece haka ina kika shiga"
Murmushi kawai yake take tayi. Ana ta gaishe shi ko ya kula shidai ta Bilkisun yake kawai sai daga baya ne suka g
aisa Umar kuwa ya matso ta jikin ƙafar sa ya ce "Baba Tun tuni ina ta gaishe ka baka amsa min ba"
Shiru ya masa baice komai ba Bilkisu kuwa tana lure da haka.
Can saiga Abubakar da Usman ayko bata bari sun ƙaraso ba ta tashi da gudu taje ta ru
ngume su Aliyu kan yana ta cewa " Ahhhh"
Mommy ta masa ido alamun ya bari a hankali ya ce "Mommy Cikin ta fa take gudu"
Ta ce "Wai a kanka aka fara ciki ne"
Yayi shiru.
Sun da
ɗ
e ruƙe da juna suna murna sannan suka saki juna suka fara g
aisawa da jama'a Usman ya kalli Maisun ya ce "Wannan ce ƴarmu "
Ta ce "eh"
Ya
ɗ
auke ta suka fito waje ay bata iya zama ba ta bisu Aliyu ma ya tashi ya bita a baya Ɗakin su Abubakar yaga sun shiga ya bisu zama suka yi shima ya zauna ya ce "Baki ci
Abinci ba fa ina kallon ki, dan Allah kizo kici kada ki zauna da yunwa"
Ta kalle shi ta ce "Ayya Yayana, ni na ƙoshi ma da naga ƴan uwa na"
Usman ya ce "Kodai shine mijin yanzun"
Kafin ta amsa Aliyu ya amsa da "Eh yayan mu"
Dariya
suka yi duka Abubakar ya ce "Harda saurin Amsawa "
Aliyu ya ce "To na kawo miki Abincin nan"
Ta ce "A'a"
Abubakar ya ce "Khadiyo zata kawo mana zamu ci anan ma, Kaima nasan baka ci da yawa ba tunda taƙi ci"
Suna haka kuwa Khadiyo ta sh
igo da Abincin, tare suka ci duka har Aliyun ma.
A falo kuwa Baba ne yake maida Maganan yadda akayi da irin cin Amanar da Umar yayi"
Alhaji Yusuf ya ce "Ka daina fa
ɗ
an haka fa ka dubi
ɗ
anka tunda ka shigo nan yake baka haƙuri baza ka haƙura b
a"
Ya ce "Nifa na riga na Sallama wannan
ɗ
an a duniya dan haka yaje kawai, bani da wani
ɗ
a "
Abba ne ya shigo Falon shima gaisuwar akai tayi Umar ya gaida Abba ya Amsa ya ce "Kai dai baka da dattaku Umar sai ka wuce ka tafi baza'a a ganka ba kaƙ
i dawowa gida ina hankalin naka yake"
Ya matso ya ce "Abba kayi haƙuri "
Baba ya ce "Yanzu ma komawa inda ya fito zaiyi"
Abba ya ce "Ba ya dawo maka da ƴarka ba. To ka kyale shi kuma ya isa haka"
Bayan sun gama suka shigo duka Bilkisu
ta fa
ɗ
a jikin Abbanta tana murna ya ce "ni dai
ɗ
aga ni ay dama kin watsar damu kin yaye mu"
Ta ce "Ay haƙuri Abbana bazan kuma ba"
Magana Aka ci gaba da maidawa aka yafi juna amma sam Baba yaƙi ya saurari Umar.
Baba ya ce "Kai me yasa kake d
a taurin kaine haka"
Alhaji Yusuf ya ce "Shine nima na gani ay"
Abba ya ce "Ka ganshi tun yana ƙarami akwai kafiya da taurin kai"
Ganin Umar yadda yake kuka yasa gaba ki
ɗ
aya zuciyar ta ya tsinke, Namiji kamar wannan amma yayi ta kuka haka,
dan haka ta matsa kusa da Baba ta ce "Baba kayi haƙuri ka yafe masa ni na yafe masa, idan saboda ni kaƙi yafewa kayi haƙuri Baba"
Baba yayi shiru yana kallon ta Can kuma ya ce "Kin manta abin da ya miki ko"
Ta ce "Baba ka manta da komai kaima
dan Allah "
Ya ce "To shikenan Allah ya yafe mana gaba ki
ɗ
aya"
Wani sanyi Umar yaji a ransa ya ce "Nagode Ƙanwata Allah ya sauƙe ki lafiya "
Abubakar kan tun da ya shigo yake lure da Maryam da duk da ake magana bata sa baki ba, tayi
shiru Maisun na jikinta, Miƙewa yayi ya kira Bilkisu ta taso suna zuwa ya tarar da Usman yana waya suka zauna ya ce "Wacece waccar ƴar budurwan da kuka zo tare"
Ta ce "Wai Maryam, Ƙanwar Mijina ce"
Ya ja hancin ta ya ce "Baki da kunyar cewa
mijinki a gaba na, ko da yake naga mijin ma ba kunya gare shi ba, Ita Maryam
ɗ
in An mata miji ne"
Ta ce "A'a amma kasan baza ta rasa masoya ba"
Ya ce "To idan so samu ne a sani a ciki"
Da sauri Usman ya kashe wayar ya miƙe ya ce "Tab amm
a ko yau ga abin Al'ajabi"
Bilkisu ta ce "Dan ya ce yana sonta "
Ya ce "Ay baki san wani abu ba, shifa a rayuwan sa bai ta
ɓ
a yin budurwa ba, ga ƴan mata sai bibiyansa suke amma duk yaƙi su har ana cewa Aljana ce ta aure shi"
Ya ce "Ni kaw
ai banga abin da zaisa ina
ɓ
ata lokacina bane kawai, wannan
ɗ
in ma idan ta nuna min tana da wanda take so zan barta"
Bilkisu ta ce "Ayko baza'ayi haka ba, idan Maryam ne kamar ka same ta"
Ya ce "Yawwa My sister Nagode miki"
Usman ya ce "
Su sabon shiga fa an fa
ɗ
a"
Abubakar ya ce "Tashi ka gyara mana
ɗ
akin yanzu za'a kira min ita"
Ta ce "Kaga kuwa ita ma Barrister ce"
Ya kama hannunta ya ce "Dan Allah fa! Kai kashe wayan nan kazo ka gyara mana
ɗ
aki yanzu zata zo"
Usma
n ya miƙe ya ce "Kaga ni fita ma zanyi bazan gyara
ɗ
aki saboda mace ba"
Bilkisu ta ce "Yi shirun ka Yaya ni barin gyara "
Gyarawa tayi sannan ta shiga ta kira Maryam suka shigo tare, Abubakar kan harda canja kaya yasa kaftan ya saka hula. Maryam
kan zama tayi a can gefe Bilkisu kuma ta miƙe zata tafi Maryam zata bita Ta juyo ta ce "Magana za kuyi dai"
ita ko Bilkisu ta koma ciki ta samu wai su Mommy zasu koma sun yanke shawaran zasu bar Bilkisu da Maisun su kwana biyu. Bilkisu ta ce "Momm
y abar Maryam ma dan Allah"
Ta ce "Idan zata zauna sai a barta tunda ay bata da aikin komai"
Ita ko Bilkisu tayi hakan ne dan su samu su daidaita kansu da yayan nata.
Tuni Maryam da Abubakar suka daidaita kansu. Ita kan ya burge ta, kod
a ta shigo Mommy ta ce "Maryam zaki zauna idan yayanki yazo sai ku tafi tare ne ko zaki bimu"
Ta ce "Zan zauna Mommy "
Ta ce "To"
Da yake sunyi Sallar Azhar yasa suka shirya tafiya, Mommy ta kira Bilkisu gefe ta ce "Idan Umar ya ce zai ka
r
ɓ
i ƴarsa ki bashi kayansa, sai a turo masa kayan ta daga nan'
Ta ce "Mommy kuma... "
Ta katseta ", Kiyi haƙuri idan yace yana buƙata ki bashi amma idan bai buƙata ba shikenan"
Ta ce "To"
Aliyu kan baiso barin matar sa ba, amma ba ya
dda ya iya haka suka tafi.
Da yamma kuwa ƙarfe biyar saiga Mama Sauda duk ta rame kamar ba Mama Sauda mai ji da kanta ba. Tans zuwa ta rungume Bilkisu tana cewa "Ki yafe min dan Allah Bilkisu, ganin Umar na kallonsa yasa Bilkisu ta ce "Haba Mama n
i ƴarki ce ay kada ki damu komai ya wuce"
Umar kuwa matsowa yayi Bilkisu ta ce "Mama Yaya yana magana"
Tana ganin sa rungumeshi tayi tasa kuka tana cewa "Ina ka shiga ne, nayi rashin Baban ka gashi kaima nayi rashinka"
Rarrashinta ya ringa y
i har saida tayi shiru.
Bilkisu dai taga gata duk inda ta matsa Bilkisu Shiko Umar yana maƙale da Maisun, Sauda ma da tazo har goya ta sai da tayi, tana mamaki halarci irin na Bilkisu da ta iya sa Sunanta bata yi tunanin irin cutar da suka mata ba.
Da daddare kuwa
ɗ
akin su Abubakar suka tafi duka, Bilkisu, Usman Khadiyo da Umar riƙe da ƴarsa Abubakar kan janye maryam yayi suka tafi Ɗakin Umma.
Hira sukayi ta sha kamar daga Sama saiga Ruky ta shigo har
ɗ
akin, kowa ya juyo yana kallon
ta.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐
ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.
✍
🏻
[6/10, 6:15 PM] Mim
😘
:
🌐
_*
🇭
ιĸιмaн
🇼
rιтer'ѕ
🇦
ѕѕocιaтιon*_
🌐
( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........
✍
🏻
🌐
BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUN
ATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
P
age 71-72
Umar ne ya
ɗ
aure fuska ya ce "Kefa me ya fawo ki"
Ta ce "Nazo ne ka mu tafi gida"
Ya waro ido "Gidan wa"
Ta ce "Naji labarin dama ance ka samo Bilkisu kuma da auren ta, to tunda tayi aurenta ba shikenan sai mu ci gaba da
zama ba tunda dama baka sake ni ba"
Ya ce "wa ya ce Miki zaki koma gida na, ƙarya kike ay, aurenki kuma sa ke kaina kije na Sake ki, kada na ƙara ganin kina bibiyata, Kinci darajan Ƙanwata Bilkisu amma badan haka ba... " ya yarfar hannunsa.
Komawa tayi kamar zata tafi sai kuma ta dawo ta ce "Umar dan Allah kayi haƙuri"
Usman ya ce "Wai kai ka kira yarinyar nan ne da baza ta bar nan ba"
Umar ya ce "Saina balla
ɗ
ayan hannun ya kuma lalacewa tukun na"
Usman ya miƙe tuni taba
r gurin.
Kwanan su biyu Aliyu yazo ya
ɗ
auke su, Umar kan yayi wa Maisun hidima da yawa yayi mata siyayya kuma bai nuna alamun zai amshe ta bama.
Saida suka biya suka gaida Zalimu mijin Ummi tukun dan tin da yayi hatsarin nan kasancewan ba asib
iti aka kaishi ba, daga baya aka gane dama ya samu matsala a haƙarƙarinsa, kuma gurin yana damunsa sosai.
Ummi ji tayi kamar kada ta rabu da ƴar tata amma ya zata yi dole suka rabu da Alƙawarin zasu dawo mata idan ta haihu.
Daga nan suka
ɗ
au
hanya suka koma Kaduna saidai sunyi dare sosai dan ma Aliyun yana gudu sosai a mota.
A gidan Maryam ta kwana saida Washe gari ta koma gida.
Cikinta yakai wata takwas lokacin kuwa ansan da Maganan Abubakar da Maryam dan har an sa musu r
ana nan da wata biyar.
Aliyu yana zaune ita kuwa tayi matashi da cinyarsa wayan sa ne yayi ƙara ta
ɗ
auka ta miƙa masa dan bata son ya motsa dan taji da
ɗ
in kwanciyar.
Ya duba yaga Mommy ce ya
ɗ
aga da Sallama daga can ta ce "Ina Bilkisu ne an
a ta kiranta bata
ɗ
aga waya ba"
Ya ce "Wayar tana
ɗ
aki ne, ita gata a falo"
Ta ce "To saidai haƙuri Mijin Umminku ne Zalimu ya rasu"
Ya ce "Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un Allah ya jikansa da rahma"
Mommy ta amsa "Amin, Daddynku
ya ce Gobe zamuje ya kace kai"
Ya ce "Mommy makarantan Maisun fa"
Ta ce "Nima nayi tunanin haka to amma zata zauna da Maryam, zamu barta a gida.
Ya ce "To Allah ya kaimu goben, amma Maryam nan zata zo ko"
Ta ce "Eh"
Sukayi Sa
llama suka kashe wayar ya kalli Bilkisu ya ce "Wai Mijin Ummi ne ya rasu"
Ta tashi zaune ta ce "Allah sarki Ummi, Allah ya jiƙan Baba Zalimu"
Ya ce "Amin"
Washe gari tun Sassafe sukayi shirin su dan sai zasu dawo a ranan ne shi yasa ma ko k
aya basu
ɗ
auka ba, Bilkisu kan jikin t ne yayi sanyi duk bata jin ƙarfin jikinta ya kalleta ya ce "Yaya dai,?
Ta ce "Ni Wallahi duk bana jin da
ɗ
in tafiyar nan Yaya dama a fasa ba yanzu ba"
Ya ce "A'a taya za'a fasa kuma, gaisuwa ne idan munyi sai
mu dawo"
Ta kama hannunsa tasa a daidai zuciyar ta ta ce "Yaya ta
ɓ
a ƙirjina kaji sai wani bugawa yake Wallahi kamar wani abu zai same ka"
Ya ce "Kina min Addu'a ba abin da zai same ni Insha Allahu"
Ta ce "Yaya dan Allah kada ka rabu dani d
uk wuya duk da
ɗ
i ka kasance dani"
Rungumeta ya yayi ya sa kanta bisa kirjinsa ya ce "Wa ya ce miki zan rabuda ke, mai raba mu da ke sai mutuwa "
Daidai lokacin suka ji horn alamun su Daddy sun zo, ya je
ɗ
akin Maisun yaga tana barci ya mata kiss a
kumatu sannan suka fito Maryam ta fito ta shiga ciki tana
ɗ
aga musu hannu, Aliyu shine mai jan motar