Showing 6001 words to 9000 words out of 70769 words

Chapter 3 - BILKISU COMPLETE

17 Oct 2026

419

yarinya karama amma daga baya ya lura yarinyar ba irin wacce za a ji kunya bane, dan su Mama Suwaiba sun nuna mata koda zana jin kunyar kada ta ji kunyar mijinta.

Mama Sauda kuwa ganin Hali yariya ce ta fara shiga

dan ta zugata saidai kuma bata samu nasara ba dan Umma da Mama Suwaiba sun

ɗ

ora ta akan turba me kyau karshe ma ce mata tayi "Kinga Mama Sauda Idan fa baki barni ba zan fada wa Umma da Mama su dau mataki a kanki"

Ta ce "Eyeh! Umma da Mama ma kike ce

musu, niko me zaisa iyi wannan in kira kishiya ta Umma ko Mama"

Hali kuwa Murgu

ɗ

a mata baki tare da jan wani dogon tsaki tayi ta tashi a gurin.

Haka ta hakura bata sake bi ta kansu.

Watanta biyar da tarewa Umma ta fahimci Hali ciki gare

ta, saboda farin ciki bata iya boyewa ba ta fada wa yan gidan, tana ji kuwa Hali ta shige

ɗ

aki ta kasa fitowa duka dariya suka yi har kowa yayi shiru Alhaji ya

kasa rufe bakin ji yake kamar yau za'a fara masa haihuwa, Mama Suwaiba ta ce "To Alhaji rufe

bakin mana"

Ya ce "Ohhh wai bakin a bu

ɗ

e yake"

Tunda aka bayyana cikin take zaman

ɗ

aki bata fitowa sai idan taga ba kowa a faron zata fito da dogon hijabinta tayi abin da zata yi ta koma, suna lure da ita hakan ma ya basu daman yin aikace-aikace

n da ta hana su ne"

Idan ko ta fito taci karo da Umma ko Mama Suwaiba da gudunta zata koma

ɗ

akin saidai suyi mata dariya kawai, su Abubakar ne bata jin kinyarsu kuma sukan shiga

ɗ

akin har ta musu tatsuniya.

Cikin hakan ne cikin ta ya kai na hai

huwa, tana zaune kan Sallaya bayan ta idar da Sallah isha Usman na zaune bakin gadon ta, yana jiran ta masa tatsuniya ta kalle shi ta ce "Usman yau bana jin dadi zan kwanta da wuri kuje kuyi karatu da Mama "

Ya ce "Nima anan zan kwana"

Ta ce "To

Abubakar fa"

Ya ce "Ohonsa"

Tun tuni take jin maranta na mur

ɗ

awa yanzu kuma taji tana jin bayan gida ta tashi zata na

ɗ

e sallayan sai ta koma ta durƙusa a gurin saboda wani azababben ciwon da koda uwarta ta haife ta bata taba yi ba.

Ta durƙus

a tana salati, ganin Halin da take ciki ne yasa Usman ya fita da gudu yayi Falo dukan su suna falon ya ce "Ummi bata da lafiya kuzo kuga yadda take"

Kafin kowa ya tashi Abubakar yayi gaba da Gudu Umma ne ta jawo shi ta ce "Kada naga ka shiga

ɗ

akin na

n"

Suna shiga suka samu tana nishi ga zufa da ta hada ga kuma kwaton hijabinta, suka kamata zasu

ɗ

agata tayi wani dogon Nishi sai ga Yarinya ta sullu

ɓ

ota, tana fitowa ta zandara kuka da kara, da sauri Umma ta tare ta tana fa

ɗ

in Alhamdulillah, Mama

Suwaiba kuwa fita waje ta fada wa Alhaji cewa Hali ta haihu, ya washe baki ya ce "Me aka haifa? "

Ta ce ay sai sun fito

Suna zazzaune Umma ta fito da Babyn ta miƙawa Alhaji ta ce "Barka Alhaji an samu ƴa mace"

Ya amshe ta yana mata Addu'a, Sa

nnan ya miƙawa Mama Suwaiba ita ma ta amsa tana mata Addu'a sannan ta miƙawa su Abubakar sai murna suke, Tuni aka kira yan uwa da abokan arziki ana shaida musu haihuwa

Saida aka gasa mata jikinta aka yiwa jaririyar wanka ita ma tayi wanka sannan Alh

aji ya dauke su tare da Umma suka yi asibiti, aka duba su, da uwar da ƴar duka lafiya.

Sai dai kuma Hali sam taki yarda ta amshi yar wai kunyar ta take ji idan an mika mata ma saidai ta kauda kai ta rufe idonta. Umma tayi tayi amma ko

ɗ

ago ido ta

kalli ƴar ma taƙi yi, Mama Suwaiba kuwa da tazo bata mata da wasa ba haka ta

ɗ

aga mata riga tasa mata ƴar a cinya ta kama hannun ta ce "Idan baki rike ta kin bata nono ba wallahi baza mu shirya da ke ba, wannan wani irin abu ne "

Haka ta rike tana bata

saidai kanta na gefe ko kallon ƴar bata yi. Basu ce mata komai ba sudai burin su ya cika da har ta yadda ta batan.

Bayan kwana biyu kuwa Alhaji ya ce zai ra

ɗ

a mata suna to dama Mahaifinsu Malam hamza ne mai ra

ɗ

awa yaransu sunan saidai shi ya rasu

dan haka ya samu Hali ya ce "Wani suna za'a sawa ƴar taki"

Ta kwanta ta nutsa kan ta cikin filo a hankali ta ce "A saka mata Sunan Adda Bilki"

Dariya yayi ya fito falo ya amshi yar a hannu Umma ya ra

ɗ

a mata suna BILKISU, Dama ƴar a gurinsu take

sai in zata sha nono ne suke kaita sai kuma bsrci, da daddare kuwa sai ta tashi tayi ta kuka amma Hali haka zata juyar da kanta gefe tana jin ta sai wani daga cikin su ya shigo ya dauketa a mata magana ta bata nonon.

Anyi taron suna inda yarinya ta

ci suna BILKISU, Saidai yarinyar kwata-kwata bata san da

ɗ

in uwa ba, saidai Mama Suwaiba ne ke jigila da

ɗ

awainiyarta,

Haka rayuwa ta ci gaba inda Bilkisu tayi girma amma bata san da

ɗ

in uwa ba, ko tana kuka saidai yayyenta su lallashe ta ko Umma ko

Mama amma da zata kwana tana yi Ummi baza ta ce mata ci kanki ba sadai ta kawar da fuska. ( Nikan na ce ohhh wannan kunyar Fulani na

ɗ

an fari bata yi ba) shekaranta

ɗ

aya aka yayeta Mama Suwaiba ce ta dauke ta ta kwashe kayanta ma daga dakin Hali ta kawo

dakinta, a tunanin su zata damu sai suka ga ma hakan da aka yi tafi sake wa.

Gata kuwa tana samu gun yayyen ne ga Umma ga Mama har da Alhaji suna ji da ita, amma banda Hali, ita kan Bilkisu ma ko gurin ta bata zuwa, saidai idan su Abubakar sunje

suna barin gurin ita ma zata bar gurin.

Shekaranta biyu suna zaune suna wasa da su Abubakar ita kuma Ummi tana kicin su kuwa su Umma suna Falo suka ji Sallama Suka fito Sarkin Fulani ne tare da wata Mata da yaron ta sa'an Abubakar sai yarinya mace a b

ayanta, Mama Suwaiba ne ta shigo da su har falo Matar ta kyalla idon ta a kan Bilkisu sai kallonta take, Mama Suwaiba da taga haka sai ta dauke ta ta sata a baya, Mama Suwaiba ta shiga kicin dan ta kawo musu abin sha taga Hali a ciki ta ce "Ki fito munyi

baƙi"

Hali ta dauko ruwan yayin da Mama Suwaiba ta tsaya ha

ɗ

a musu kayan ciye-ciye ta fito da ruwan kenan suna ha

ɗ

a ido da Matar Hali ta saki abin shan hannunta ta ruga da gudu tana cewa "Addana" suka rungumi juna sai suka saki wani kuka me ban tausayi

, Saida sukayi Kukansu sosai ba wanda ya lallashe su sai tausayin da akayi ta ji, Saida suka ci suka sha sannan Sarki ya ce "Halima duk abin da kika ji daga bakin ƴar uwar ki kada ki tada hankalinki ki kwantar da hankalinki haka Allah ya kaddaro muku.

_*Mrs Aliyu ce*_

lιĸe

coммenт

ѕнare

🌐

ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.

✍

🏻

[5/16, 7:38 AM] Mim

😘

:

🌐

_*

🇭

ιĸιмaн

🇼

rιтer'ѕ

🇦

ѕѕocιaтιon*_



🌐

( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)

Hikmahwritersassociation2019@gmail.com





loadιng...........

✍

🏻



🌐

BILKISU



Labari da rubutawa

MAIMUNA ISAH MUSA

(Mrs Aliyu)

Marubuciyar:-

INA DANGINA

IZZAR MULKI

JININA

YAK'I A SOYAYYA

AMANATA

FAHIMTA FUSKA

MAIMUNATU

MAHAUKACINA

and now

BILKISU

*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*

_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_

_Gaskiya bana ganin Sharhi kuma ya kamata a

na yi

ɗ

in_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 9&10



Kallonsa duka falon suka yi Umma ne ta ce "To baza ka jira Alhajin ku gaisa ba"

Ya ce "A'a zan tafi kawai"

Yana tafiya Hali ta ce "Adda kinga yadda Allah yayi da mu

ko"

Ta fara bata labari daga farko har ƙarshe har irin yadda su Umma ke kula da ita, saidai kwata-kwata bata sa labarin Bilkisu a ciki ba, ko fa

ɗ

a ma ta haihu bata yi ba. Saida tayi shiru shiru Mama Suwaiba ta ce, "Lallai ma Ummin Yara kin iya fada

mata komai amma baki fada mata labarin takwaranta ba"

Ta ce "Hmm "

Umma ta ce "Ay dama na san baza ta fa

ɗ

a ba, to dai nata fa

ɗ

a miki maganan haihuwa ba"

Umma ta bata labarin komai da yadda akayi ta fama da ita wajen renon yarinyar karshe ta ce

"Tunda Maman yara ta dauke ta har yau ko kallo ba ya ha

ɗ

a su da ita, na rasa wannan wace irin uwa ce, ace ka haifi

ɗ

a a cikin ka amma ka nuna rashin kulawa."

Adda ta ce "Ni ya kamata nayi wannan rainon wa yara na, tunda ni nasha wahala, dan na taso

koda ina buƙatan taimako idan ban samu ba zan mutu mahaifiyar mu ba za ta ta

ɓ

a taimaka min ba, Sai Baffa shine gata na shine ya raine ne, Amma Inna ko zan mutu ba ruwan ta dani. Amma kin ganni tunda nayi aure na haifi Aliyu naga yadda ƴan binni suke ji

da yaran su nima na

ɗ

auka, Aliyu y more ni sosai dan ban kuma haihuwa sai kwana nan yanzu Maryam watan ta bakwai bazan bari su sha wahala ba, ni tunda na shigo naga yar sai naga Fuskar Hali, don abin da tabar Hali tana ƙarama. Hira suka yi sosai kamar s

un san juna

Daga baya ne Hali ta ce "Adda me ya faru naji

ɗ

azu sarki yana min wani magana wai inyi haƙuri da abin da zaki fa

ɗ

a min"

Adda Bilki ta ce "Haka ne Hali Saidai muyi haƙuri da iyayen mu, an samu labarin su a wani riga saidai kuma bukkan

su ta kama da wuta sun ƙone gaba dayan su "

Hali ta dafa kirji ta ce "Inna da Baffan? "

Nan fa ta fasa kuka Adda ta rungume ta tana kuka tana bata hakuri sannan taci gaba da fada mata, An kawo wa Sarkin Fulani Shanun na cesa ya ci gaba da mana kiw

o"

Alhaji da ya dawo yaji wannan Al'amari ya tausaya musu matuƙa kuma ya kwantar musu da hankali.

Kwanan Adda da yaran ta hu

ɗ

u a gidan sannan ta koma Kaduna Alhaji kuma ya mata Alƙawarin zai kai mata Hali.

Hakan kuwa aka yi ya kaita din daga

baya kuma ita da kanta take zuwa ko ita Addan ta je, ko yaushe Addan nata tana bata baki akan tana kula da ƴarta Bilkisu amma ina ba ma abin da ya dame ta da ita ita ma Bilkisun yanzu bata damu da ita ba.

Idan yayyenta suna gida kullun tana tare da s

u, wataran ma Idan Umar yazo dashi ake, sun shagwabata sosai, ko abu take so sai tasa kuka, idan ance menene sai ta ce "Ita a bata kaza"

Haka kuma iyayen basa son suji ko da nishi ne, uwar gayyar ko ko oho. Tunda ta gane Umar zuwa yake yi, yasa da

zaran ta ganshi sai tasa kuka idan ance menene, sai tace "Ya Umar ya je gidan su "

Abubakar ya kalle shi ya ce ka mata wani abu ko, yakan ce A'a sai ya ce to tafi gidan ku, nan kuma zai fara lallashin ta, ita kuma ta ƙara narkewa, ta jina tana

yiwa Umar haka kuma abin da take masa yana bashi haushi dan haka ya sa mata ƙahon zuƙa da zaran ya shigo tana ganin sa kafin ta fara kuka sai ya bubbuge mata baki yace "kuma kika fada sai na ballaki, shegiya zabiya"

Hakan yasa ta fara jin tsoron sa hak

a zai shigo ya bubbugeta idan anzo anga tana kuka idan aka tambayeta sai tayi shiru su kuma su lallashe ta.

Shekaranta tara Mama Suwaiba ta kwanta ba lafiya koda aka kaita asibiti aka tabbatar tana

ɗ

auke da juna biyu, murna gurin ba'a magana, saida

i cikin nata yazo mata da laulayi ƴan gidan suke taimaka mata da komai Musamman Bilkisu duk da yadda take da ƙananun shekaru amma ba'a barta a baya ba, Makaranta take rabata da Maman nata da ta taso saidai ta zauna

ɗ

aki tare da ita, ko ta ce su fito falo

, kullun tana jikin ta da yake Allah yasa ita

ɗ

in me son jiki ce.

Har cikin yakai haihuwa tana abu

ɗ

aya ga kumburi da tayi, bata cin gishiri, daban ake mata girkin ta.

Lokacin haihuwan kuwa nayi riƙe ta suka yi asibiti saboda jikin nata, kul

lun Bilkisu na tare da ita wata ran ma bata zuwa makarantar, koda haihuwan tazo tasha wahala dan saida aka saka mata ruwan naƙuda ta haifi ƴarta mace, tubar kallah da ita, saidai kuma ita ta ha

ɗ

u da tsinka-tsinka Bilkisu kan kuka ta sa Abubakar ya fita

da ita, shi

ɗ

in ma ya daure ne saboda ƙanwar tasa, tana kukan Umar ya shigo yana mata wani kallo duk kuka da take ta gimtse ta kwanta cinyar Abubakar ta rufe Fuskar ta da tafin hannun ta.

A ciki kuwa tana dawo wa hayyacin ta ta kalli Hali dake rike

da ƴar Hali ta ce "Kinga abin da kika haifa"

Tasa hannun ta a akan jaririyar ta ce "Allah ya mata Abarka, Allah yasa ta Amfane mu haba

ɗ

aya, "

Umma ta ce "Ɗan rungumeta ki bata Nono"

Ta ka

ɗ

a kai ta ce "Ummin yara zan bar miki Amana, ga Bi

lkisu Amana ce a gurin ki, ina son daga nan har ƙarshen rayuwarki ki kula min da ita, nasan su Umma da yayyen ta zasu bata kulawa, kece baza ta samu ba, amma ina roƙon ki ki cire kunyar nan ki rungumi ƴarki dan Allah. "

Hali dasaurin kuka nan da nan

ta fara kuka tana cewa "Ni ki daina wannan magana lafiyarki ake nema yanzu "

Ta ce "Bazan bari ba har sai kin min Alƙawari daga yanzu zaki jata a jiki"

Ta ce "Eh nayi Alƙawari kema kiyi shiru"

Ta ce "Alhamdulillah nagode miki"

Ta kauda

kai ta yi kallar shahada daga nan kuma tayi ƙatuwar shaƙuwa sannan rai yayi halinsa.

Suna zaune suka ga Ummi ta fito tana kuka Umma ma nayi Abubakar ya miƙe ita ma ta miƙe ta ce "Umma Mamana ta mutu ko"

Umman ta rungumeta tana kuka tana cewa "Muy

i haƙuri Bilkisu "

Kuka tasa me tsuma zuciyar me sauraro, Abubakar ya kamata shima yana zuba hawayen yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, Baba Jafaru Mahaifin Umar shi ya maida su gida Alhaji da sauran Al'umma kuma suka taho da gawar. Nan aka mat

a sitira aka kaita gidanta na gaskiya, (Gidana, Gidanki, Gidanka, Allahu Akbar Allah yasa mu shiga a sa'a)

Bayan anyi bakwai kowa ya watse yarinya dai aka mata hu

ɗ

uba da suna Khadija Hali take shayar da ita, kuma shayarwa ba irin wanda akayi wa B

ilkisu ba, ta bata kulawa sosai ta mata kyakykyawan shayarwa.

Tun bayan rasuwan Bilkisu ta fara ganin abin Mamaki wai Ummi tace take sata a cikin maganar ta har ta ke kiran ta Addana ko ta sata aiki, Amma hakan baisa Bilkisu walwala ba har yanzu ta

na jin mutuwar Mamanta.

Tun tashin Khadija bata samun kulan da akewa Bilkisu a gidan bata shagwaban da Bilkisu take, ta girma ma amma abu ka

ɗ

an saita fara kuka, nan kowa yan gidan zasu zo kanta har Khadija ma da Ummi take ce mata Khadiyo shine kowa y

a

ɗ

auka ta gane dane idan abin ya tashi da ita ake lallashi. Umar ne ke taka mata burki idan yazo gidan bata sakewa kwata-kwata, shi kuma hakan ya bashi daman yi mata mugunta yadda ransa ke so idan su biyu ne a gurin.

_Kan labari_

_*Mrs Aliyu ce*_

lιĸe

coммenт

ѕнare

🌐

ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.

✍

🏻

[5/16, 8:11 PM] Mim

😘

:

🌐

_*

🇭

ιĸιмaн

🇼

rιтer'ѕ

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login