Showing 57001 words to 60000 words out of 132173 words

Chapter 20 - JENNIFER COMPLETE

11 Jul 2025

4186

ba ya runtse ido yanajin
wani iri aransa oh ya rabbi ! jannat me kike nufi da kin gode da soyayyat kina nufin bakya sona
?? kada kiyi min haka meyasa kika xama ta musamman awajena hangota yayi nesa da kitcean
d'in atsaye ita da suwaiba da sa'a suna hira tana murmushi alamun ba abinda ke damunta dafe
kai yayi yarasa gane inda yarinyar nan ta dosa ya wuce dakinsa yana shiga sageer ya shigo
hannu ya bashi suka gaisa cikin farin ciki sageer yana dariya yace ya dai khaleel naganka
arikice gashi fad'a naxo muyi kallon sageer ya yi, sageer din shima kallonsa yake jidda ta kawo
min kararka,
had'e rai khaleel yayi yaja tsaki ya kwantar da kanshi jikin kujera, cikin fad'a yace meya ke
damun jidda ne ?
sageer yace dole ta damu tunda kasan tana sonka bai kamata dan kayi aure ka juya mata
baya ba, akufule khaleel yace,
me take so na mata ? tana so na wulakanta matata sbd ita ? na fuskanci abinda take so kai
ka sani sageer ni ba sakaran namiji bane, idan xata iya hkr tayi idan baxata iya ba babu dole ta
kyaleni na huta nagaji da korafi ya k'arashe maganar da tsaki,
dariya sageer yayi ka dai kara yin tunani jidda yar'uwarka ce bai kamata.....ya isa sageer
bana son wannan maganr,
da xoyala sageer yace kafi son mgnr jannat ko ? kallon sageer d'in yayi bai tanka masa ba,

na manta fa kai angone yayi dariya sosai tun kafin aje ko ina sun fara rikita,
ka na ganka so cool me ya faru ??
kamar baxaiyi mgn ba sai kuma ya girgixa kai sageer jannat daban take,
ban gane ba khaleel,
yarinya ce amma tasan kanta tana ja min aji sosai,
murmushi sageer yayi da tsokana yace amma dai ta fad'a maka tana sonka ko ?
zaro ido yayi na fda maka jannat daban take, yanxu kam darajar ta ta karo a idona soyayyar ta
kullum karuwa take sbd halayenta tana da aji da biyayya,
yayi shiru bai k'arasa ba,
tashi sageer yayi ya bud'e frige ya dauko coke ya bude yana sha,
na fad'a maka yaran yanxu bana wasa bane, na jinjinawa jannat da ta haukatar min da
aminina ya shek'e da dariya, ka cigaba da lallabata, kasan mata yan rarrashine,
kallonshi yayi yai murmushi ya canza musu wata hirar

**********
misalin k'arfe hudu ya shigo falon ya tadda su gaba d'aya ya xauna kusa da momy ya
gaishe ta idon shi akan jannat data k'urawa tv ido,
jannat ! ya kira sunanta gaba d'aya suka kalleshi,
" kije ki shirya xaki rakani unguwa,
ya mike ina jiranki in kin gama, ya fice daga falon kunya ce ta kamata ta nok'e tak'i tashi sai da
momy taga da gaske takeyi ta kalleta cikin kulawa,
jannat tashi kishirya mana, da kyar ta iya mik'ewa cike da jin kunya ta hau sama k'arar test taji
tana dubawa taga sakonshi........ ki shirya ina jiranki kisaka hijab da nik'af...... ya mutsa fuska
tayi kayan daxan sa ma sai an xab'amin ta shirya less tasaka green collour da kwanliyar amy
ajikinsa tasa hijab amy ta kalmi amy ta d'auki hand bag dinta green ta d'ora nkaf ta fito dukansu
suna falo a kunyace taiwa momy sallama muryar sulthana taji tana cewa asiyo mana alewa me
tsinke, dukansu sukai dariya har da momy da sauri ta fita itama tana dariyar ta hangoshi jingine
jikin motor dinshi yasa shadda milk hular kalan xaren da aka yiwa shaddan aiki tayi masa kyau
sosai ta k'araso ya bude mata kofa ta shiga ya xagayo ya shiga mota ya tada ita danjuma ya
bud'e musu get ya fice daga gidan

*************
tun da suka tafi babu wanda yai magana wa'axi ya kunna na sheik ja'afar akan ma'aurata
shiru sukayi suna jin wa'axin jikinta yai sanyi ta lumshe ido tana jin dad'in sauraran waaxin wata
unguwa suka shiga babu mutane a unguwar dai dai k'ofar wani babban gida yai hon me gadi ya
bud'e ya shiga cikin gidan, gabanta ya fadi ganin wasu motocin na daban yasa ta sakin jikinta ya fito daga motar ya xagayo
ya bude mata ta fito ya shiga gaba tabi bayansa jikinta asanyaye dan btasan inda take ba
sallama yayi aka amsa masa ya shiga falon gidan wani farin mutun ya taso da sauri ganinta da
shi yasa ya xaro ido lalala ! khaleel kaine da amarya ? yau ka cika alkawari sannunku da xuwa
amarya shigo a d'arare ta xauna khaleel din ya xauna kusa da ita ya shiga cikin gidan bai jima
ba suka fito shida matarshi da sauri ta k'araso inda suke oyoyo oyoyo jannat ! yau kam ranar ta
muce ankawo mana amarya xama tayi suka gaisa ta mike tace xo mu shiga ciki kawata, ta mike

tabi bayanta suka shiga d'aki ta xauna ta debo mata kayan motsa baki tana mata hira sosai sai
bayan ta xauna tace amarya cire nikaf din na ganki sbd in mun hadu gaba na ganeki, ta xame
nikaf din suka had'a ido tayi murmushi so young mashaa Allah anata samin rana xa a kawo ki
yau dai gashi an kawo min ke, sunana kausar matar abokin mijinki murmushi jannat tayi, haka kausar tai ta janta da hira, dan tasaki jiki, ta fuskanceta tana da son mutane da kuma kirki
mijinta ne ya shigo cikin fara'a yace amarya mijinki yana jira xaku tafi khausar tace kai ! daga
xuwansu d'age hannu yayi ba ruwana mijinta ne yace taxo ta mike, tana mitar kamata yayi a
barta sai dare, tace wa mijin nata yatafi yanxu xasu fito leda ta dauko jannat ta mike tabi
khausar ta riko hannunta suka fito falon cikin wasa tace, khaleel gaskiya wannan xuwan ba a
dad'e ba ka kawomin ita ta yini,
murmushi yayi ya mik'e sukai sallama tabawa khaleel ledar tace ya bata yai gdy suka fice ya
bud'e mata kofar motor ta shiga shima ya shiga ya tada ita suka fice daga gidan
kai tsaye store ya kaita yace ta fito ta taxab'i abinda take so,
ta fito daga moto ta bi bayansa suka shige store din ya kaita b'angaren kayan kwalliya kasa
tab'a komai tai, ganin xata b'ata musu lokaci yasa ya d'auki box yana loda kayan da duk yaci
karo da su, bayan yagama lodan kayan masu yawa ya yaje wajan biyan kudin akai masa total
ya biya suka fito daga store din da kayan lodi lodi a hannunsa ya bud'e mata mota ta shiga
shima ya shiga suka fice sunxo dai dai danja aka tsayar dasu sbd jiniyar da masu bada hannu
sukaji suka bawa bangaren hanno suka danno kai farko motar sojojine bayansu yan sanda sai
wasu dank'ara dank'aren motoci jannat tabi motar da kallo ta tsakiya tana tafiya a hnkl ita
kadaice glass dinta ba tintac ba, had'a ido sukayi da ta cikin motar gabanta yai mummunan
fad'uwa ta tsirawa matar ido ji tayi kamar ta santa kuma tai mata kama da wata amma batasan
wacece ba tsurawa matar ido tayi babbar macece, karaf matar ta waiwayo suka tsurawa
junansu ido idanuwan jannat kadai ta kalla sbd nikaf din data sa, amma taga kamar matar ta
rikice da ganinta wani abu jannat taji yana mata yawo ajikinta motar matar ta wuce, dukansu
suna waiwayon juna, abinda jannat bata tab'a jiba taji yana tsirga mata jikinta lokaci d'aya taji
tana son matar sosai jikinta na bata wani abu akan matar amma takasa tantancewa runtse ido
tayi tana jin wani chock na musamman ajikinta hawaye ya sauko mata dai dai time din da
motocin suka gama wucewa aka ba hanyar hannu ya khaleel ya tada moto din suka wuce da
sauri basu dad'e ba suka shigo layinsu sai da suka shiga gida ya waiwayo yaga tana xubar da
hawaye da sauri ya riko ta yana tmbyr ta shiru tayi dan tarasa me xata ce masa rungumota
jikinsa yayi yana rarrashinta tayi lamo cikin kuka tace masa, iyayena ! runtse idonsa yayi cike da
jin tausayinta, kamar ya xubar da hawaye shima yace, kiyi hkr babyna in shaa Allah xaki sansu
ki cigaba da addu'a ta xamo daga jikinshi still hawayen bai bar xuba ba dan ita kad'ai tasan mai
taji dataga matar gaba daya son ganin iyayenta take, shiga cikin gidan tayi yabi bayanta cikin
tausayawa tana shiga falon ta tadda su, ganin hawaye na xubar mata yasa momy da dady suke
rige rigen tmbyr ta fadawa jikin momy tayi had'e da sakin kuka mai tsuma xuciya khaleel ya biyo
bayanta ya xauna yana kallon kukanta mai k'ona masa rai sai da ta gama kukan sannan ta basu
lbrin matar da ta gani,
tundaga ganin matar tajita cikin sabon yanayi da sauri hindu ta matso kusa da jannat, tasa
kuka ta rungumeta tana kukan tace watakil mahaifiyar mu ce jin haka yasa sulthana fashewa da
kuka itama ta xamo daga kujerar data ke tana kuka sosai

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




69&70

Kuka sosai sukeyi cikin wani axababben yanayi da suka dai sukasan yadda sukejin shi, shiru
kowa yayi sbd mutuwar da jikinsu yayi dakuma tausayin su daya kamasu, share hawayen ta
jannat tayi muryar ta na rawa take mgn tamkar xata kara fashewa da kuka, baxan iya fasalta me
nakeji ba amma ta yaya mutun xai rayu da farin ciki ko annushuwa bai San kansa ba ? Bai San
suwaye suka kawo shi duniya ba bai San wanne laifi yayi aka watsashi cikin duniya aka jefar
dashi tun yana kwana arba'in? Kuka ya kufcemata takasa k'arasa mgnr,
Sulthana ta kallesu cikin kuka, laifin har mu uku ? Bayan Ku nima aka jefar dani ba'abar mu
haka sai da aka lahanta mna rayuwa kowacce akwai dafi mai muni da'aka hada dashi, hindu ta
katseta cikin kuka, hakane sulthana da ace mutun xai iya kiyasta shine a halin da muke ciki
wanne irin hawaye xai xubar ? Wacce iriyar kuna xuciyar shi xatayi, ga kiyayyar junanmu da aka
jefa mana duk sbd kada mu rayu tare, na fiku illa sun fi illatani nida suka maidani wata iri suka
wulakanta min rayuwa suka dank'ani wajan rik'ak'ken dan fashi, tun da nashi nake cikin tashin
hnkl sbd a kullum yana fada min bashi ya haifeni ba, ban San farin ciki ba Sam ban sanshi ba
haduwa ta dakune na koyi dariya da murmushi kullum acikin kunci nake da axabar xuciya,
jannat ta daga hannu sama cikin xubar da hawaye ranta na suya ya Allah! ya Allah ! Ga bayinka
kasa karasa wa tayi sai kuka mai kuna, dadyne ya cije da kyar ya fara lallashinsu jikin shi duk
amace da kyar ya hadiye hawayen da ya taso masa, Momy kuwa tare dasu suke kukan ya
khaleel ma ta maxa yayi Dan kadan ya rage shima yayi hawayen, da kyar dady ya lallabasu
sukayi shiru,jikinshi asanyaye yace " wannan alama ce ta kun kusa haduwa iyayenku alamace
ta ubangiji yana karbar addu'ar da mukeyi dagewa xamuyi mucigaba da kai masa kukanmu
Allah ya baiyana su suka amsa da amin kowacce hawaye na ambaliya a fuskarta kiran sallar
magruba da akayi yasa suka tashi kowanne xuciyarshi ba dad'i

**************
Bayan ta idar da sallar isha'i had'e da shafa'i da wutr ta dade tana xabga addu'a
akan Allah ya kawo musu mafita ta shi ta kwanta idonta a lumshe tana kallon fuskar matar data
gani d'axu a hnkl taji an shigo dakin da sauri ta kalleshi ya xuba mata ido cikin tausaya ya
karaso inda take ya xauna kusa da ita hade da janyota jikinshi, "kiyi hkr babyna ki kwantar da
hnklinki in sha Allah xaki hadu dasu komai mai saukine a wajan Allah janye jikinta tayi daga
nasa hawaye yagani kwance kan fuskarta, da sauri yasa hannu kan fuskarta yana girgixa kai "
ki daina babyna ki daina kuka bana so ! Ba kuka xakiyi ba addu'a ya kuma janyota jikinshi yana

jin kamar yata yata xubar da hawayen tayi lamo akirjinshi hade da sakin kuka mai sauti haka ya
dinka jijjigata kamar karamar yarinya sun dade a haka tun yanajin sheshshekar ta har yafara jin
ajiyar xuciya jikinta yaji asake alamar bacci ta fara ya gyara mata kwanciya ajikinshi, har saida
baccin nata yai nisa bai so ba ya raba ta da Jikinshi ya kwantar da ita hade da rufeta da bargo
yasa hannu yana shafa fuskarta, ya Dade yana kallonta da kyar ya lallashi xuciyarsa ya fice sbd
dare yayi sosai dakinshi ya koma da kyar ya samu bacci Dan fur ya Nemi baccin yarasa,

**************
Washe gari yaxo yin breakfast yana ta xuba ido bata fito ba hnklinshi atashe yake har
suka gama kasa daurewa yayi sai da ya tmby Momy tace tana sama bata jin dadi mikewa yayi
ya fice ya kasa karasawa dakinshi yana tunanin me ya sameta ? Yana son hawa sama ya
dubata ga Momy da dady a falon, shigowa yayi ta karamar kofa wacce take dai dai stairs din da
xaka hau sama a hnkl ya fara hawa muryar sulthana yaji "ya khaleel a dawo lafiya,
Ya waiwayo yaga duk kallonsa suke suna dariya kasa kasa ya galla mata harara ya wuce
saman, kai tsaye dakin ta ya wuce ya murda ya shiga, ta fito daga wanka jikinta daure da towel
ganinshi yasa da sauri ta dauki hijab tana kokarin sawa, murmushi yayi ganin yanda ta rude
kusa da ita ya karasa ya Sa hannu ya rike hijab din ya ajjiyeshi kan gadonta ta sunkuyar da kai
cikin jin kunya, hannunta ya riko yaji hannun na rawa ya kalleta yaga ilahirin jikinta rawa yakeyi,
da sauri ya janyota kusa dashi sosai, "babyna meyasa kika tsorata haka ? Kasa bashi amsa tayi
Dan bata San me xata ce masa ba ya dago da fuskarta data ki yadda suka hada ido, muryar shi
asanyaye yace " bude idonki ki kalleni, bata son yi masa gardama, ta kalleshi kadan suna hada
ido ya kashe mata ido, yes beauty na ki kalli mijinki da sauri ta sunkuyar da kai, murmushi ya
subuce mata, yaji dadi sosai ya rungumota jikinshi yana kissing din duk inda yaci karo dashi na
jikinta kasa kwace kanta tayi sbd kyakkyawan rukon da yai mata kukan shagwaba ta saka masa
ya saketa da kyar, cikin wani yanayi yace mata plx beautyna ki fada min amsata ta jiya, hannu
tasa da sauri ta rufe fuskarta, yasa hannunsa yaxame hannunta yana murmushi cike da jin dadi,
yace I love u beautyna, da kyar da furta I love u too, wata wawar runguma yai mata kamar xai
maida ita cikin cikinshi, yana furta mata wasu xafafan maganganun na soyayya, cike da mmkin
shi take sauraron sa, ya xamota ya na kallonta ta rufe fuskarta tana kokarin kwace kanta yaja
mata hanci cikin dariya yace ba inda xaki gudu ki barni, yau ajikina xaki yini, xaro ido tayi ta
marairai ce murya, plx ya khaleel karsu sulthana suxo fa kayi hkr ka tafi, girgixa mata kai yayi ya
kwaikwayi yanda tayi mgn, nifa gsky ba inda xani, kamar ta fashe da dariya Dan tasaci kallonsa
taga yanda yayi mgnr ta kanne, "katashi plx kar suxo,
Janyota ya kuma yi jikinsa, menene idan sunxo ? Matata ce fa xasu hanani shakar kamshin
kaykkyawar jikin matata? Shagwabe fuska tayi, "nidai gsky katafi,
Kina so na tafi ?
Da sauri ta daga masa kai,
Yasa hannu ya shafa karamin lip dinta sai kin min kiss da wannan lip din,
Xaro ido tayi sosai tana kallonsa hade da kwabe fuska ashagwabe tace nifa..nifa.... Nifa gsky
ban iya ba, da sauri yace " bari na koya miki, xatayi mgn taji bakinshi cikin nata yana shansu
tmkr ya samu wani daddad'en mint hannunsa na shafa gashin kanta mai santsi da kyar ya
saketa yana maida numfashi xubewa tayi akan gadonta ta rufe fuskarta da filowa itama tana
maida numfashi, dariya yayi ganin ya sama mata kwanciyar hnkl ganin ta tashi yau bata jin dadi

sbd abinda ya faru jiya kissing din gashinta yayi ya juya xai fita, dai dai bakin kofa ya tsaya
asanyaye yace babyna anjima ki kawo min coffee shiru tayi bata bashi amsa ba, cikin wasa
yace tunda baxaki mgn ba bari naxo na kara miki wani kissing din, da sauri tace a'a xan kawo
ya fice yana dariya ya fita ta mike tana kallon gashinta daya hargitsa mata shi da sauri ta fara
gyara jikinta Dan kar su sulthana suxo su ganta a haka,
Yana sauka kasa yaxo xai wuce su a falo Momy ta bar falon gab da xai fita sulthana tace ya
khaleel ya mai jiki bata jira amsar saba tace Allah ya kara sauki, banxa yayi da ita ya fice Dan
yasata a sahun yi mata uxiri, yana sautin dariyar sauran


*********
Tunda sulthana ta bawa Momy lbrn abinda taga jidda tayi yasata kin sakankancewa komai
akan idonta akeyi abincin dare kullum jannat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login