Showing 72001 words to 75000 words out of 132173 words

Chapter 25 - JENNIFER COMPLETE

11 Jul 2025

5154

yayi,
"Kina tunanin ankusa rabani dake ko ?
Da sauri ta xamo kanta ta kalleshi,
Daga mata gira yayi,
Ta koma kirjinshi hade da sakin ajiyar xuciya,
Har sai da yaji,
Dad'i yakamashi ya k'ank'ameta ajikinshi, yana jin kamar ana k'ara mishi soyayyarta,
a hnkl ya sa bakinshi daidai kunnanta,
" Allah yana tare damu babu Wanda ya isa raba wannan soyayyar ki kwantar da hnklinki,
Yana rad'a mata mgn yana shak'ar k'amshin turarenta daya keso,

Lumshe ido tayi tana addu'ar Allah ya kuma tsare mata ya khaleel dinta, ya xame dankwalinta
yana shafar gashin kanta,
Ta xame jikinta daga nashi ta mik'e tana k'ok'arin saka hijab,
Mik'ewa shima yayi yana kallonta da manyan idanuwansa masu kama dana mai jin bacci,
"Ina xaki tafi ? Ya fada Kamar Wanda vaison ta matsa daga kusa dashi,
Kanta ta sunkuyar katsa,
" zan koma d'aki,
Kusa da ita ya matso sosai,
"Meyasa kike son rabani da ke ?
Da sauri ta kalleshi idonta cikin nashi,
" a'ah ya khaleel,
"Sheet! Ya fada hade dasa Dan yatsanshi kan lip dinta,
Bana son ki dinka gujemin nafison Na dinka Jinki a jikina kin kasa fahimtar irin son dana ke miki
ni nagaji da wannan rab'e rab'en cikin week din nan xa ayi biki mu koma gidanmu Na damu da
yawa,
Ta shagwab'e fuska tana kallanshi
" nifaa..... Ya katse ta,
"Kefa me ?
Ta rausayar da kanta,
"Nifa ba gudunka nake ba, ya kalli karamin lip dinta daya ke matukar so
Janyota yayi jikinsa,
Muryarshi asanyaye yace,
" idan bakya guduna yau anan xaki kwana,
Arikice ta xame jikinta
" ya khaleel ....... Bakinta taji cikin nashi kyam ta tsya har sai da ya gaji ya tsaya Dan kanshi
hade da kura mata idanu muryarshi asanyaye yace I extremely love u jannahh ! Hannunshi cikin
nata, kunya ta kamata ta sunkuyar da kai ya kalli dogon wuyanta xuwa kirji ya cije lebe,
Yasa hannu ya shafo cikinta daya ke ashafe kamar ba'a xuba abinci,
Dai dai kunnanta ya rad'a mata nakusa ajiya anan ya fad'a da murmushi,
Murmushi itama tayi tasa hannu ta rufe fuskarta ya sa hannu ya tallabe fuskarta hade da xame
hannunta suka kalli juna tai dariya a kunyace ta fad'a kirjinshi, lokaci daya sukai ajiyar xuciya
dukansu da kanshi ya dagota daga kirjinsa ya dauki hijab dinta ya sa kamata,
Ta juya dai dai bakin kofar shi ta tsaya tana masa wani shu'umin kallo, da mmk yake kallonta ta
bude Dan k'aramin lip dinta
" I extremely love u ya khaleel da sauri ta fice,
Zo ! Zo ! Jannah,
Ina ta fice tana dariya,
K'ofar ya tsurawa ido yana jin kamar ya bita ya had'iyeta,



Washegari suna dining dukansu break fast sukeyi kana kallonsu kasan har yanxu basu gama
wartsakewa daga abinda ya faru ba wayar dady tayi k'ara yana dubawa yga bak'uwar number

Ya d'aga sallama akayi ya amsa yana naxarin me muryar,
Murmushi dady yayi cike da murna yace,
Mashaa Allah ngd sosai inshaa Allah anjima kad'an Ina nan tafe a gagguce ya gama breakfast
d'in yana jin dad'i sosai ya kira khaleel su xo su tafi tare ya shiga mota khaleel ya shiga wajan
driver suka fice daga gidan


Ya kalli dady ,
" dady ina xamu?
Da fara'a dady yace gidan sarki xamu ya dawo jiya,
Shima khaleel din murmushi yayi hade da jin dadi da gudu yake Jan motar Dan ya matsu suje
wa sarki da buk'atarsu,
Basu b'ata lokaci ba suka isa abban A.K Garkuwa ne yai musu jagora falon sarki daya ke
ganawar sirri da mutane,
Cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa cike da kulawa,
A hnkl sarki yace,
"Dr bashir anbani sakon kana son ganawar sirri dani ina fatan dai lafiya ?
Sunkuyar da kansa dady yayi cike da biyayya,
" hakane ranka shi dad'e naxo ne kan wait muhimmiyar mgn akan Alhaji Adam ched'e,
Sarki yace
" toh ched'e lafiya dai ko bashir ?
" lafiya lau ranka ya dad'e akwai yaran da suke gidana y'anmatane guda uku muna binciken
iyayensu sai aka tabbatar mana da y'ay'an shi Alhaji Adam ched'e be
Da sauri sarki da abban A.K Garkuwa suka kalli dady
Sarki cike da jindad'i yace
" Alhamdulillahi ai bama sai anbincika ba tabbas y'ay'ansane Dr bashir yau shekara goma sha
tara muna binciken inda yaran nan suke,
Wannan tafiyar tawa umara bayan naiwa katsata addu'a da jahata sai da na rok'i Allah akan ya
bayyana mana su, gashi kuma Allah ya karb'i addu'armu Alhamdulillah , Allah mungode maka,
Dady daya khaleel suma hamdala sukayi duk da b'acin ran da dady yake ciki sai dayaji ya kau
farin ciki sosai yakeyi,
Sarki yace
" Dr ya akayi ka tsincesu haka ahad'e bayan ararrabe aka sacesu ?
Nan dady ya kwashe lbr ya fad'a musu,
Sunyi mmk sosai,
Sarki yace aje ataho dasu ya gansu nan da nan aka tura fadawa da driver

a tsorace suka taho tunaninsu ko ba'a dace ba suna xuwa babban falo inda dady yake da
sarki,
Suka gaishe da sarki cikin biyayya,
Murmushi sarki yayi hade da fad'in
Allah Akbar tsarki ya tabbata ga Allah duk Wanda ya kalli y'ay'an nan yasan y'ay'an adamu
ched'ene,

Dr ngd maka zan kira ched'en yau yau din nan akan yaxo da gaggawa ina nemanshi gobe ko
jibi Dan baxa a baiyana su ba sbd mugayen mutane,
Hamdala dady yayi
" bakomai ranka ya dad'e Allah yakara tsawon rai idan an mana umarni zamu tafi inyaso idan
yaxo sai a kiramu,
A hnkl sarki yace
" inshaa Allah Dr katafi da y'ay'anka babu mai rabaka dasu hannu da hannu ka dank'asu gun
mahaifinsu Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka Allah ya tsare maka iyalinka,
Suka amsa da amin sarki yace su tafi jibi su dawo ya kuma gargad'esu da kada kowa yaji
zancen suka fito daga gidan sarkin cike da jindadi,


Da murna suka shigo gida a falo suka xauna anata maida bayani dady ya kallesu yaga duk
suna cikin farin ciki Wanda bai tab'a ganinsu cikin irinshi ba ya lumshe ido shima yana jin farin
ciki Mara misaltuwa cikin farin ciki jannat tace dady,
Suka dago kai duka suka kalleta,
" yau na san yadda farin ciki yake, hawaye ya taro a idonta, na kasa tantance yadda nakeji
ji Na nake kamar sabuwa yau naxo duniya,
Dafa mata kafad'a momy tayi,
Kada ki damu y'ata haka rayuwa take Allah xaki godewa Dan shi yai muku wannan baiwar duk
lokacin daka tsinci kanka cikin bakin ciki sai ka gd masa haka inka sami kanka cikin farin ciki ka
gd masa sbd shine mai badawa kuma shi yake hanawa,
Ajiyar xuciya Hindu tayi,
Hawaye ya sauko mata,
" hakane momy ni kaina yanxu Na fahmci yadda akejin dadi da farin ciki, Allah shine yai mana
wannan baiwar dole mu gd masa,
Cikin farin ciki sulthana tace,
Babu avinda nake jira a yanxu sama dana ga fuskokin su, ko ayanxu alhamdulillah, Allah ya sa
na gane ina da dangi da kuma iyaye Alhamdulillah
Murmushin farin ciki dady yayi,
"Masha Allah y'ay'ana Allah yai muku albarka nagode wa Allah daya nuna min wannan ranar
ina kara godiya ga Allah ubangiji Allah ya kaimu jibin kamar gobene awajan ubangiji,
Rubayya tace dady, na ji farin ciki mara misaltuwa akan ubangiji ya amshi addu'armu tabbas
Allah yana amsar addu'ar bayinsa sai dai kawai jinkiri kuma duk inda yake alkairi ne mukam
gashi nan mungani munga yadda Allah yai da jinkirinmu,
Ya haisam ya kalli sulthana yaganta cikin walwala dady ya kamashi hnkl kwance yace,
Dady saura d'aurin auren mu da sulthana,
Dariya sukayi duka falon banda sulthana data b'ata rai,
Dady cikin wasa yace,
Mantawa nayi da an hada jiya anyi Dana Jidda,
Turo baki sulthana tayi, cikin shagwab'a tace,
" nifa dady Na fasa auren ya haisam,
Xaro ido haisam din yayi,

Momy plx kiyi mata mgn ta daina wannan wasan banajin dadi axuciyata,
Momy ta ware ido,
" ba ruwana kun fi kusa na sa baki naji kunya mu dai namu kwasar rawa ne ranar biki,
Kwashewa sukayi da dariya har da dady,
Mahboob yace xanso naga ustaz khaleel yana chasu,
Dariya suka kumayi har tafi ta d'axu shi kanshi khaleel din sai da yayi dariya, ya kalli mahboob
yace,
" mai xai hanani yin rawa ranar bikin sulthana da haisam,
Cikin dariya dady yace kamar gaske,
Hindu tace wai ! Sulthana amarya zanso naga rawar kai,
Cikin shagwaba sulthana ta mike tana dire diren k'afa ni fa nafasa aurenshi ta hau sama da
gudu gudu,
Cikin wasa momy tace dawo,
Dady ya k'arasa dawo amaryarmu,
Dagudu sulthana tak'arasa hawa sama tana dariya,
Mik'ewa haisam yayi xai bita,
Mahboob ya rik'o hannunsa haba guy bi a hnkl mana,
Fincike hannunsa haisam yay"
ba ruwanka,
Dady yace kyaleshi yaje kada xuciyarshi ta fasa kirjinsa ta fito,
Suka had'a ido da khaleel sukayi dariya a tare, komawa haisam yayi ya xauna kunya ta
kamashi ya mik'e yabar falon,
Rabon da suyi farin ciki irin wannan har sun manta sun da d'e suna wasa da dariya da tsokane
tsokane har aka kira sallar la'asar suka mik'e dukansu



Tana idar da sallah ta jingina jikin gadonta lumshe ido tayi fuskarta d'auke da murmushi turo
k'ofar d'akin yayi,
Ta bud'e ido ta kalleshi da sauri ta mik'e ta k'arasa kusa dashi had'e da fad'awa jikinsa,
K'ankameta yayi yana jin sautin fitar dariyar ta wani farin ciki Na musamman ya xiyarce shi haka
yakeson ganin jannat d'inshi cikin walwala da annushuwa, ta dad'e ajikinshi yana shafa bayanta
sannan ta xamo suka kurawa junansu ido hancinta yaja,
Beautyna yau rana ce ta musamman,
Far tayi da ido
" hakane ya khaleel
Hannunshi taja ta xaunar da shi gefen gadon ta ta xauna kusa dashi tana kallonsa,
"Ina jina kamar sabuwa nagode wa Allah ta kalleshi kamar xatayi kuka tasa hannunta a kirjinsa
ngd mk ya khaleel kai Na musamman ne arayuwata, hawaye ya sauko mata sbd kai ne ummul
aba isin canxamin rayuwa daga duhu xuwa haske ngd maka ya khaleel kuka ya kufce mata ka
so ni lokacin daya kamata a k'ini ka taimaka min lokacin dana ke neman taimako, Rungomata jikinshi
Muryarshi asanya ye yace jannah ! Meyasa kikeson b'ata farin cikinki ?

Yau rana ce ta musamman awajan mu, kada ki b'ata farin cikin ki da wannan tunanin babu gdy
a tsakaninmu kada ki kuma godemin Allah shine abin gdy, k'ara kankameshi tayi,
" tayaya xuciyata xata rayu batare da taka ba ?
Da sauri ya xamota daga jikinshi
Wow ! Beautyna maimaita abinda kikace ? Kunyace ta kamata ta b'oye fuskarta a kirjinshi,
Yasa hannu yana shafar gadon bayanta,
sulthana ta bud'e k'ofa ta shigo da sauri jannat tai k'ok'arin janye jikinta k'am taji ya rik'eta,
Xaro ido sulthana tayi tana in ina tace,
" ah ah yi hkr ta juya da sauri ta fice,
Dago kai jannat tayi had'e da turo baki,
" kaga fa sulthana ta gammu,
Tab'e baki yayi to menene ?
Kefa matata ce,
K'ara turo baki tayi
Hancinta yaja "gyara bakin kona gyara shi yanxun nan ,
Da sauri ta saki fuska suka kalli juna sukayi dariya ta kaiwa kafad'arshi duka kad'an
Accchh ! Ya fada had'e da dafe wajan da ta kaiwa duka "Sai Na rama
Matsawa tayi had'e da xaro ido,
Ya dawo da ita jikinshi,

Suka d'ai suka San yadda sukeji a xukatansu




Ranar alhamis tunda sassafe suke xaman jiran kiran sarki dukkan su suna had'e waje daya,
kowa ka kalla cike yake da annuri, shiru shiru sarki bai kiraba har akayi sallar la'asar gaba
d'ayansu jikinsu yai sanyi jannat da sauran y'an'uwanta kamar su fashe da kuka shi kanshi dady
jikinshi yayi sanyi ya fara jin ba dad'i yana feeling din wasu abubuwa da shi kad'ai yasansu,
sunyi jigun a falo wayar dady tai k'ara gaba d'ayansu suka kalleshi,
Sbd gaggawa ko duba number baiyi ba,
Muryar abban A.K Garkuwa yaji
Dr gamu nan muna jiranka kaxo kaida y'ay'anka,
Kashe wayar dady yayi yana kallonsu Ku tashi mutafi,
Da murna suka mik'e suna Allah Allah suga fuskokin iyayensu mota suka shiga suka d'au
hanyar gidan sarki


Basu b'ata lokaci ba suka isa jannat da sulthana da Hindu tuni jikinsu ya hau rawa sunajin wani
yanayi Na musamman falon ganawa da manyan bak'i suka shiga sarki suka gani da Abban A.K
Garkuwa da shi kanshi Prince A.k,
Cikin biyayya suka gaishe da sarki da murna had'e da walwala sarki ya amsa ya kalli prince "
jeka kira min su gaba d'ayansu,

Cikin gaggwa ya mik'e ya fice daga falon
Rawar da jikinsu jannat yakeyi ya k'aru suka k'urawa k'ofar falon ido suna kallon isuwar
iyayensu,
Bai jima ba ya dawo tare da mutane su hud'u mata uku manyan mata d'ayar turata ake a keken
guragu me shegen kyau kamar Na xinare sai Adam ched'en shine farkon shigowa, lokaci d'aya
jannat ta mik'e tsaye tana kallonshi kamarsu daya karaf suka had'a ido jikinshi yai masa wani
mugun shock, da sauri ya shigo sulthana da Hindu ma mik'ewa sukayi bai kula dasu ba sbd
suna cen gefe jannat ce take xaune facing din kofa,
Cikin matukar raxana Adamu ched'e ya nuna jannat da hannu idonshi yayi jaa
" wannan jini nace jikina ya bani tsokata ce,
Dai dai lokacin da sauran matan suka k'araso suma idonsu kan jannat ya sauka wacce take tura
tsohuwar a kid'ime ta k'araso da gudu tana kuka, wannan y'atace ta rungomata jikinta had'e da
tsurawa fuskarta ido araxane cikin masifaffan kuka tace AFRAH ! wannan afrah tace


By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



81&82

a kid'ime take sbd rikicewar da tayi,daya matar itama da sauri ta k'araso kusa da jannat cikin
wani masifaffen yanayi ta rungumota jikinta had'e da fashewa da kuka mai tsuma rai, Adamu
ched'e kasa mgn yayi wani farin ciki ya keji wanda bai tab'a jinshi ciki ba, tsohuwar matar da
take xaune kan keken guragu,tana wani irin kuka ta mik'e a duk'e tana taka k'afar da kyar ta
k'araso kusa da jannat tana surutu mai cike da ban tausayi,
"ashe kafin na mutu Allah xai nuna min jiko kina ashe ina da rabo ?ashe bak'in cikina ya guje
daga yau ? wannan ranar taxama ranar cikar farin cikina innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la ilaha
illallah, subhanallah Allah shine abin gdy, tana fad'a tana wani irin kuka mai had'e da gunji,
hawayen kafi ciwon xuciya ciwo adamu ched'e yayi hawayen ido daya tal,duka wajan xuba
musu ido sukayi,
da sauri ya kalli sauran mutanen cikin falon har idonshi ya kai kan su sulthana da hindu da suke
ta uban gunjin kuka, a kid'ime ya xaro ido cikin wani mugun chock da ta ujjibi da sauri ya k'arasa
kusa dasu yana kallon su cike da mmk, araxane yace "Aysha fateema ?had'esu yayi ajikinsa
yana salati da k'arfi yana hamdala, "Alhamdulillahi bini'imatihi ta tummusalihun, Allah ngd maka, narasa y'ay'a lokaci d'aya kabani
har guda biyu, sannan karaba ni dasu ba tare da sun mutu ba ka kara bani kuma still kara bani
da ita batare da ta mutu ba, yanxu kuma ka dawo min dasu lokacin da banyi tsammani ba ka
axurtani da baiwar ka Allah kaine abin gdy Alhamdulillah,yana surutun ne sam bai san me yake
fad'a ba sbd kid'ima da firgici na ban mmk, da rarrafe d'aya matar tak'ara sa kusa da hindu tana
gunjin kuka,

"ashe ba afra kad'ai bace y'ay'a nane suka dawo gareni plx idan mafarki nake kada atashe ni
akyaleni nayi ta yinshi ina jin dad'in ganinsu a mafarkin har mutuwa ta taxo ta riskeni kada ku
tasheni tana rarrafen tana wannan maganganun masu karya xuciya,
itama tsohuwar da rarrafe ta nufo su jikinta na mugun rawa,
tana fad'in "nabilata ba mafarki bane hawayen da muka shafe shekara sha tara munayi ne yaxo
k'arshe k'uncin mu ya k'are ayau b'akin cikinmu ya yanke,
d'aya matar da sauri ta mik'e a daddafe bari na xo na tab'a jikin y'ayana masu albarka yan
baiwa babu abinda xamuyi wa Allah sai gdy addu'ar da muka shafe shekaru munayi yau ta
amso hasbunallahu wa ni'imal wakeel, alhamdulillah Alhamdulillah,
duk wan da ya kallesu sai ya xubar musu da hawaye dan sanbatu kawai sukeyi suna kuka
mai gunji da wani irin sauti na ban tausayi,sam sun manta a inda suke,
dady ta maza yayi yagoge guntun hawayen daya sauko masa, shi khaleel kasa jure ganin
kukan jannat yayi ya karasa kusa da ita yana lallashinta, sam bata jin me yake fad'a gaba d'aya
hankalinta nakan iyayenta da danginsu,
sarkine yai gyran murya dan shi kansa xuciyar sa ta karye momy kuwa tuni ta biye musu suna
kukan tare su rubayya da zahra ma kukan suke cike da tausayi mai narkar da xuciya, mahboob
da haisam ma xuciyoyinsu akarye suke
gyaran muryar da sarki yayi shi ya fara dawo da hnklinsu suka fara nutsuwa har suka fahimci
inda suke dan sun manta sbd yanayin dasuka tsinci kansu ahnkl cikin karyewar xuciya sarki ya
fara mgn dan yaga alamar aka dad'e ana wannan maganganun da koke koke tabbas kowa na
gurin sai ya kuka, " alhamdulillah ! Alhamdulillah ! Allah shine abin gdy dan shiya dawo mana da farin cikinmu da
yaranmu garemu shekara goma sha tara ana cikin k'unci da damuwa da b'acin rai da tashin
hnkl lokaci d'aya kuma Allah ya dawo mana dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba shin baxa
kuyi mamakin ganinsu atare lokaci d'aya ba ? wannan wata baiwa ce ta musamman daga rabbil
ixxati daga ubangiji mai rahma mai jin kai, yaran nan an sacesu daban daban amma Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login