Showing 123001 words to 126000 words out of 132173 words

Chapter 42 - JENNIFER COMPLETE

11 Jul 2025

5063

Abbu da ya mukarram da zahra suka diro 9jaa sbd sunji lbrn b'atan

khaleel da dawowarsa sai bayan sun xo sukaji lbrn abinda hjy murja tayi sunda d'e suna
mamaki sosai sun jimanta dan zahra da hjy zainab har kuka sukayi abinka ga mata da raunin
xuciya haka suka xauna suna hira sosai suna ta ujjibi da mmk akan abinda ya faru kowanne
xuciyar shi ta kai k'arshe a mmk hjy Nabila tace "ni kaina Zainab har gobe ina tambayar xuciya ta meyasa murja tai min haka duk irin yadda da
amanar da na bata y'ay'ana sukutum duka nabar mata fa itake kula dasu da duk wani
sha'aninsu Allah sarki murja wani gefen na xuciya ta na tausayin halin tada ke ciki danni da
gske ina k'aunarta sbd k'aunar y'ay'ana data yi duk da na makirci ne !"
da yamma jikin jannat yai sauk'i ya khaleel ya d'auketa bayan hjy Nabila ta bashi tana tsokanar
sa
" ga jannar ka nan kar kahana mu sakat Allah ya kare min ku ya sauketa lfy "


gidan su suka shiga hannunshi rik'e da ita wanka sukayi yanda suka saba take kowanne ya fara
komawa nrml bayan sunfito daga wankan yanda suka saba xasu shafa mai ya janyota jikinsa
hannunsa na shafar cikin ta tasa hannunta dai dai ciwon da garadan nan suka ji masa
"Allah yasa kalli yanda suka dokar min jikinka ?"
jinjina kai yayi
"axabar rashinki tafi wannan dukan xafi da k'una ! ni kad'ai nasan bala'in dana shiga rashinki
duk lokacin da suke dukana babu abinda nake tunawa sai kyakkyawar fuskar ki hakan yana sa
naji bana jin dukan duk xafin shi ina tsananin sonki jannah !"

wasu hawaye suka xubo mata
"ban san kaine rayuwata ba sai bayan baka nan baxan iya aiwatar da komai ba sai kana tare
dani dan dakai nake iya komai cin abinci wanka kai ne rayuwa ta !"

girgixa mata kai yayi yana share hawayenta masu xafi da suka sauko mata
"meyasa kike son xubar min da hawayen ki masu tsada ?"

"hawayen farin cikine khaleel narasa wanne abu xanyi na farin cikin gani jikinka jikin da nai
kwana hud'u bana tare dashi shiyasa ni xubar wannan hawayen "

rungumota yayi sosai tamkar wanda xa a kwace ta yana jin axabar sonta idanuwansa na
k'ok'arin ingixo hawayen da suka cika masa ido !.

*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:45 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

121&122
*Ummee Garkuwa*
da sauri ya shanye hawayen bai xuba ba ahnkl ya janye jikinsa yana kallonta hannunshi nasha
far cikinta cikin kasala yake magana

"ajiyata tana nan yadda na barta amma ...."

ware ido tayi tasa hannunta kan hannunshi daya ke shafa cikinta
"amma me....?"
dariya yayi mara sauti
"naga ya rame any'a kina kular min da shi kuwa?"
turo baki tayi ko me ta tuno da sauri ta sauke bakin tana dariya shima dariyar yayi yasan abinda
ta tuno ta sai ta bakin ta
"ina kular maka dashi sosai fiye ma da yadda na ke kula da kaina"
xare ido yayi yana kallonta da manyan idanuwansa
ya girgixa kai
"bance ba ! bance ki kular min dashi fiye dake ba ! ina son ya xama 50&50"
ya saketa ya juya ya d'auko gown me kyau ta shadda ya mik'a mata ta amsa xata saka ya rik'e
hannayenta
"ajiya na baki bance ki saka ba"
ya amsa yasaka mata ita yana murmushi
"kamar dan ke akayita tayi miki kyau sosai ! komai yana dacewa da jikinki beautyna!
murmushi tayi idanuwansu akan juna
"ngd sosai ya khaleel"

bayan sun gama shirin suka fito babban falo yana gyara link d'in hannun rigar sa ya d'ago kai
yana kallonta
"yau fa muna da bak'i"
da mmk ta tambayesa
"suwaye xasu xo ?
"murnar me kike haka"
cikin xak'uwa tace
"sbd xamuyi bak'i"
murmushin da bayyi niyya ba ya sub'ce masa
"xasu xo xakiga ko suwaye"
ya fad'a cikin ko inkula
marairaicewa tayi tana kwab'a fuska
"plxxxxx !!!"
ya kalleta yanda tayi yayi shima
"plxxxxx!!!"
d'ank'aramin duka ta kai masa a k'irji yasa hannu ya dafe wajan
" washhhhh ! ki ka dake ni ? bazan yadda ba sai na rama a inda kika dake ni"

dariya tayi tabar wajan da tafiya da sauri ya xuba mata ito yana dariya
nesa dashi ta tsaya
suna kallon juna
ya tab'e baki
"xan dawo anjima kad'an "

"adawo lfy Allah ya kiyaye hanya"
"amin "
ya amsa ya fice ta dawo falon ta xauna had'e da xabga tagumi duk sai taji kewar sa ko kad'an
bata son yai nesa da ita

bata dad'e a falon ba taji sallama kamar muryar sulthana tana d'ago kai suka had'a ido ta ita taci
ado sunyi anko da mijinta haisam kamar amaryar daxata tare gidan mijinta
washe baki tayi tana mmkin xuwansu
"oyoyo ! oyoyo ! "
haisam ya k'araso suka xauna suka gaisa sulthana na tsokanarta
"lfy antinmu ya ajiyar mu ? hop ana kular mana da ita ?"
hararar wasa jannat tai mata tana girgixa kai haisam yai dariya had'e da mik'ewa
"babyna xan dawo nan da 3 hours ya khaleel na jirana"
cikin muryar jan hankali tace
"ok sweet ka kular min da kanka "
ya tsaya yak'i tafiya yana kallonta kauda kai tayi tana dariya muryarsa asanyaye yace
"taso mana muje "
turo baki tayi
"nifa gsky sweet idan naje raka ka....."
da sauri ya sunkuya gab da ita ya rufe mata baki da hannunsa
"kin san in bakiyi min rakiya ba baxan iya fita ba,
na riga na saba da hakan kin sabar min babyna yi hkr baxan miki komai ba"
da mmk jannat take kallonsu watak'il ma sun manta da ita a wajan

shafo sajen fuskarta yayi
"kinga yanda sajen nan naki yake miki kyau ?"
far ta yi da ido
"oh ya Allah ! ta shi muje babyna"
kafin tayi motsi ya d'aga ta cak ya janyota gab dashi yana mata wani irin kallo me cike da
tsantsanr soyayya
"muje akwai sak'on da xan baki na manta d'axu ban baki shi ba"
hannunta ta d'ora asaman kafad'ar sa tana girgixa kai
"bayan nasan wayo kake min wannan sak'on dai ne na....."
rufe mata baki yayi
" no ! babyna baki sanshi ba wannan sabon sak'o ne na musamman akayi shi saboda ke !"
yaja hannunta suka wuce tana dire diren kwafa na shagwab'a
gaf da xasu fita ya tuno ashe fa da anty jannat a falon
"antynmu sai nadawo anjima" ya fad'a yana dariya k'asa k'asa yana kallon sulthana data kwab'e
fuska dan tasan rakiyar me xata haifar.

murmushi jannat tayi ranta fes tana jin dad'in kulawar da yake da sulthana kamar ya had'eta
tana xaune takusa 1 hour sannan sulthana ta shigo da gudu tana dariya babu jan janbakin data
shafa aleb'enta

da mmk jannat tace "lfy kike gudu haka duk kin hargitse?"
dariya tayi ta xauna
"hmmm ya haisam fa da kyar na kwaci kaina na gudo idan xan biye masa hmmm.."

"ina janbakin naki ?"
wata iriyar dariya sulthana tayi
"yana bakin ya haisam"
"laaa Allah ya shiryamin ke sulthana"
jannat tafad'a tana dariya
"wllh anty jannat ya shanye shi tass haisam fa !?"
suna cikin mgn sukaji muryar Rubayya cike da mmk suka amsa sun shigo ita da mijinta prince
A.K Garkuwa da sauri sulthana ta k'arasa suka rungume juna cike da jin dad'i bayan sun saki
juna Rubayyan ta rungume jannat suna murnar ganin juna xama prince A.K Garkuwa yayi
fuskar sa d'auke da murmushi nan da nan suka fara hira sam sun manta da shi . "oh ku kam mata gaishe ku idan kuka had'u sai Allah rubyna sam kin manta dani ko ? kin sami
y'an'uwa"
da sauri ta matsa kusa da shi ya rik'o mata hannu suna kallon juna
" sorry sweeter ! ya xa ayi na manta ka nasan kana kusa dani dan hankalina na kanka "
mik'ewa yayi ya mik'ar da ita gab da juna
"zan tafi anjima xan dawo ki kular min da ..."
rufe masa baki tayi tana nuna masa su jannat dariya yayi yaja hannunta suka fice daga falon
sulthana ta kalli jannat
"oh anty jannat ?"
xare mata ido tayi jannat d'in
"anty jannat me ? ke wace irin futsara ce bakuyi agabana ba ? naga har janbakin ki kibawa
haisam sbd k'auna "
suka k'arasa da dariya
"to ai naga leb'ensa ne"
sulthana ta fad'a tana turo baki girgixa kai jannat tayi tana dariya
"waya ce dama naki ne ?ko mai ma naki nasa ne"

shigowar rubayyace ta katse musu hira suka kalleta ta d'an canxa ba kamar d'axu ba dan
gyalenta a hannu ma yake ganin haka yasa sulthana tayi dariya sosai ganewa Rubayya tayi
itama tai dariyar tana girgixa kai hira sosai suka hau yi muryar wacce suka jini yasa su kallon
juna cike da mmk jidda ce ta shigo da ita da wani da mmk suke kallonsu cike da murna suka
rungume junansu suna kallon wanda suka shigo tare ya xauna yana danne dannen IPhaat cike
da mmk jiddan take kallonsu ganin suna masa kallon kamar basu sanshi ba
muryarsa asanyaye suka gaisa yana dariya k'asa k'asa

"wai kuna nufin baku sanshi bane?" jidda ta fad'a tana harararsu
xuba mata ido sukayi
"toh mijina ne d'anjuma"
da mugun mmk suke kallon sa ya mik'e yana kallonsu hannunsa kan sajen fuskarsa yana

shafawa
"nayi fushi da ku tunda kun kasa gane ni"
ya fice da sauri jidda tabi bayansa suma bin bayansu sukayi cike da mmk wai danjuma ne
yaxama had'ad'd'an d'an gayu sai wani ji da kansa yake dan yasan yana da kyau yayi kib'a ya
k'ara xama fari tass gashin kansa ya kwanta irin na fulani kai bakace d'anjuman da suka sani ba
ne gab da shi jidda ta tsaya tana mariraicewa hango su jannat yayi yai dariya
suka k'araso kusa dasu suka gaisa cikin farin ciki ya amsa yana magana kmar wani bature jefi
jefi har sun juya xasu tafi yace
"anty jannat ga jiddaty na xan bar miki amanar ta ki kulamin da duk wani motsinta,
kafin na dawo karki bari sulthana ta bibbige min ita"
xaro ido sulthana tayi cike da mmk kafin tayi magana
ya shafo fuskar jidda
"plx jiddaty ki kula fa sosai ki san ba ke kad'ai bace kike da kanki ban so ki wahala"

hannunshi cikin nata mmk ya hanasu magana da kyar jannat tace
"bakomai danju....khaleel xan kula da ita"


suka wuce cikin falon suna zama sulthana tace
"kan bala'i amma fa nayi mmk wannan abu wai d'anjuma ne yaxama wani big guy irin haka ya
xama kamar wani d'an sarki lallai na yadda mace na gyara mijinta"
rubayya tace
"hmmm yanxu fa yafi jiddan ma wayewa"

suna cikin mgrn ta shigo a hargitse hannunta rik'e da d'ankwalinta fuskar ta cike da frin ciki tana
dariya.


nan ta xauna suka hau hirar yaushe rabo basu dad'e ba zahra ta shigo tana dariya da mmk
suka rungume junansu dake basu koma ba tun xuwan da sukayi

jannat take tmbyr ta
"ina ya mukarram d'in ?"
"da kyar muka rabu yanxun nan wai ba xai shigo ba sai anjima
wai wanne biki akeyi yau ? nayi nayi ya mukarram ya fad'a min yak'i"

suma xaro ido sukayi jannat tace
"biki kuma gsku ban sani ba "
suma d'in basu sani ba sulthana tace
"mu xuba musu ido magani"
nan suka cigaba da hirarsu akan irin soyayyar da mazajensu suke musu su kam sunfi mmkin
danjuma dan wayewar sa ta shammace su yanda suka kula jidda kam nacikin jin dad'i da

soyayya mai k'arfi

shigowar hindu da mahboob daya kawo ta ne ya katsesu cikin farin ciki suka rungume juna
mahboob ficewa yayi wai ana jiransa xai dawo anjima hira suka cigaba dayi jidda tana baxu lbrn
xamanta da mijinta

"maza basu da kunya akan matayensu kunga yanda Ibrahim yake min agaban innarsa da
kishiyata? soyayya kamar me haka innarsa ma na sona bakuga yanda suke kulawa dani ba,
matarsa ma yarinya ce irin auren k'auyen nan anty take cemin tunda na girme ta,
da ita ake had'uwa ake nuna min soyayya tana da hkr bata damuwa ko kad'an,

dai dai gwargwado yana kwatanta adalci ni kam sai gdy ga Allah dan yanxu baxan iya rayuwa
babu Ibrahim ba sbd ya shagwab'a ni da yawa"
dariya sukayi sulthana tace

"munga alama kam ni har mmkin haisam d'ina nake baya iya nesa dani ko ina xani k'afarsa
k'afata kulawa ta ban mmk ko cikin gida,
dai dai da toilet sai ya bini shekaranjiya da mukaje gidan momy tana son muyi sirri ya kafa ya
tsare yak'i tafiya yana kusa dani kamar xai shige cikina ko kunya sai da momy ta gaji tace muje
ciki sulthana kai kuma ka xauna anan ya biyo mufa har d'aki momy tace futa ka bamu gu sirri
xamuyi dady ne ya rarrashe sa yace kayi hkr xo mu fita kasan mata da sirri da kyar ya fice
momy tace oh yaran nan ! bamu gama sirrin ba ya dawo wai mutafi gida .."
dariya sukeyi dukansu jannat tace

"yanxuma da kyar ya fice bayan kun kwashe 1 hour awaje daga rakiya"

Rubayya tace
"maxan yanxu kam abarsu nifa hajiyarsa ce min tayi Rubayya kiyi ta hkr dan Allah ya had'aki da
naci kullum yana gida baya iya kyakkyawan motsi sai kina kusa dashi k'annansa har wasa suke
min wai ina mannau d'inki alhmdllh danginsa na sona nayi dacen suruka da k'annan miji bani da
wata matsala sai Hamdala"
zahra ta girgixa kai cikin dariya tace
"ni matsala ta missing d'in ku amma kunsan larabawa da kula tari wannan innayi ammi da Abbu
kamar suyi me,
sun dink'a cemin sannu sannu
haka dangin sa cikin kulawa dani suke, shi kansa ya mukarram Ammi sai ta koreshi da
fad'a

office kafin yaje sai ankusa k'aramin yak'i kusan kullum sai ya makara sai da Abbu yace tare
xasu d'ink'a tafiya mu kam mun dace Allah ya datar da y'anmata masu burin yin aure"

hindu kamar xatayi hawaye tace

"amin ni kuma banyi dace ba ranar da aka kaini dayaxo mukayi hira ya fice yabar min gidan ban
kuma ganinsa ba sai bayan kwana 3 shida matarsa tace min
hindu kada ki b'ata rayuwar ki da b'acin rai kibar min mijina nawa ne ni kad'ai kiyi hkr kije ki sami
wani take tasa ya sakeni saki ma har uku !"
tak'arsa da xubar hawaye tausayinta ya kamasu jannat tace

"ki gdw Allah dan hakan shi ya fi miki alkairi Allah yabaki wanda ya fishi "
suka amsa da
"amin"
suka tashi gaba d'aya suka shiga kitcean suna k'ok'arin shirya lunch

bayan sungama sunyi sallah sun ci abinci suna hira har akai kiran sallar la'asar suka katse hirar
sukaje sukayi sallah suka cigaba da tattauna lbrn hjy murja jidda tace
"shiyasa nake xaune lfy da tawa kishiyar ina gudun hak'k'in wani akaina Allah ya kare mu da
xaluntar wani"
suka amsa da
"amin"
ya khaleel ne yai sallama ya shigo sulthana cikin tsokana
"oyoyo ga majnun "
d'an garamin murmushi yayi dan sulthana sam bata tsoranshi
"oh ! ashe fa tsoranka nakeji" ta kama baki sauran su ka gaishe shi ya amsa ba yabo ba falla
gab da xai shiga d'aki yace
"ya xanyi dake sulthana tunda kin mai da ni k'aramin kakan ki"
dariya suka yi dukansu ya kira jannat ya bata wasu kayan na daban yace ta canza wani
shegen yadi ne mai kyau sosai kamar material maroon colour an masa landing da fari sai head
fari da farin sark'an gold nan da nan da shek'a kwalliya dasu tana mmkin me xa'ayi shima ya
shek'a nashi adon da farin yadi shigen na ta amma shi mai kauri ne suka fito fess da su kamar
ranar dinner wayam taga falon ba su sulthana hannunta ya rik'e suka fito harabar gidan taga
ank'awata shi da decoration maroon da white su sulthana ta hango kowanne yana kusa da
mijinsa ta kalleshi da mmk

"ya khaleel wai me akeyi ?"
janyota jikinsa yayi a hnkl ya rad'a mata a kunne
"birthday d'ina "
xaro ido tayi tana kallonshi ta b'ata rai
"shine baka fad'amin ba?"
"ina son baki mmk ne dan ke zan taya murna khaleel d'inki ya k'ara shekaru"

murmushi tayi rik'e da hannunta suka k'arasa wajen.

wajan xamansu na musamman suka xauna basuyi wani gayyata ba family memmbers d'insu
ne kawai sai masu pix da vedio danjuma Ibrahim ne yai jawabi dan shi yagabatar da komai cike
da birgewa ya birge kowa da barkwanci akayi nishad'i sannan suka mik'e xasu yanka cake

waje ya rud'e ana wak'ar birthday

"happy birthday to u !
happy birthday to u !
happy birthday ya khaleel ! happy birthday to u ! "

ya yanko cake ya bata ta amsa tana k'ok'arin yankowa sukaji muryoyin da ya basu mmk
hajiyarmu ce da hajja da momy da ammy da hjy Nabila suka taho suna tasu wak'ar birthday d'in

dariya sukayi dukansu da mmk haisam yake kallon hajja
"hajja harda ke ?"
ya mutsa fuska tayi
"eh harda ni kun maidamu tsoffi baku gayya ce mu ba toh mun kawo kanmu"

mukarram ya harari yusuf daya ke b'uya cikin gyalen hajiyar mu
"nasan wancen parrot d'in ne ya fad'a musu"
ya nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login