Showing 108001 words to 111000 words out of 132173 words
uba tun farko ki kauda idonki ki danni xuciyarki ki maida ita uwa ki had'a kai dashi wajan faranta
mata ki samu soyayya mai k'arfin gaske agun mijinki dan wllh ya fuskanci kina takun sak'a da
mahaifiyar shi ko kina kishi da ita tsanarki xaiyi
duk yadda yake sonki ki
gwada akanki xaki so wanda yake k'in mahaifiyar ki ?
babu ruwanki da duk abinda xai mata sbd ko mai yai mata bai biyataba tana da hak'k'i mai
girmna gaske akansa.
uwar miji:
kiji tsoron Allah idan kika takurawa y'ar wani sbd tana auran d'anki wllh naki y'ay'an sun shiga
uku agun surakansu sbd hadisi ne ingantacce duk abinda kayi sai ammaka ki kauda idonki akan
kyautatawar d'anki akan matarsa dan hak'k'inta ne yaxama dole ya sauke shi babu ruwanki da
hidimar da xai mata kada kiga ke uwace kin isa da d'anki sbd haka bari ki muxgunawa matarsa
to wllh Allah baxi barki ba dan kin tab'a hak'i idan baki da y'ay'a mata sai Allah ya baki wata
surukar mara imani daxata dink'a casaki
d'anki yakasa katab'us kinga sakayyar wancen wacce kika takurawa ne
ki taya shi bawa matarsa hak'k'inta kinfi kowa sanin tana da babban hak'k'i akansa kada son
xuciya yasa ki manta Allah idan har ya cuceta ta dalilinki Allah ba xai barki ba meyasa xaki tsani
matar d'anki ? baxaki so abinda yake so ba ? baxaki taya shi sauke babban nauyin dake kansa
na matarshi ba ? meyasa baxaki tausayawa d'anki ba ? idan ke kika haifeshi bafa halittarsa
kikayi ba babu abin biyayya wajen sab'awa mahalicci babu babban abin kunya irin kishi da
matar d'anki kin xubarwa da kanki k'ima da daraja bama awajan matar ba har awajan
mak'otanki da yan'uwanki kin xama abar kwatance a layi kiji tsoron Allah ki so d'an wani a so
naki
k'annan miji da yayyansa:
musamman mata wllh duk abinda kikayi sai ammiki kada ki raina matar wanki sbd kina k'anwar
mijinta kema naki k'annan mijin suna jiranki kada ki kuskura kiyi balle aimiki ki xauna lfy da ita
dan matsayin yayarki take idan kuwa ba haka ba xakiyi dana sani lokacin da komai ya cab'e
miki sbd hak'k'in matar wanki baxai barki ba sai Allah yasaka mata.
Rowa:
masifa ! bala'i !
rowa itake haddasa muguwar k'iyayya awajan abokan mu'amalarki idan kina da rowa baki da
sauran k'ima ko mutunci balle kwarjini awajan mutane asalima kowa haushinki xai d'ink'ayi ki
xama saniyar bare acikin alummah.
kin manta babbar illar rowa ? itafa kyauta yalwace idan kika kasance mai kyautatawa to baxaki
tab'a xama cikin rashi ba domin ita kyauta tana bud'e k'ofofin arxik'i rowa kuma tana toshesu ne
kin b'oye kin hana kowa kin ji dad'i
baki san kanki ki kaiwa illah ba kin toshewa kanki da kanki k'ofar wani arxik'in daya tunkaroki.
sai kiji mace ta tak'ark'are tana fad'awa kowa dangin mijinta basa sonta ki ganta abar tausayi
kina yin bincike xaki ga babbar marowaciya ce. tana yiwa dangin mijinta rowa .
tayaya xa su soki ? ko ba su bama wllh mak'otanki ma baxasu soki bah sannan bake ba
rahamar Allah sbd hadisine ingantacce mai rowa baxai shiga aljannah ba !
subhanallah ga babbar illar toshe k'ofofin arxik'in ga rashin samun rahamar ubangiji uwa uba ga
k'iyayyar kowa ina xaki sa kanki ?
tayaya xakiyi rayuwa mai dad'i Allah baya tare dake? tayaya xakiyi rayuwa mai dad'i kowa najin
haushinki ?
bari na tuna muku wani abu dan nasan duk kunsani tuni ne kawai nawa.
rowa tana farawa tun yaro yana shekara 2
yes hakane da kin fuskanci d'anki marowacine ki cire soyayya ki rabashi da ita misali:
kin bashi biscuits sai kikace "sanwa y'an uwanka" ya d'age miki kafad'a baxai baxasu ba ko
kikace "sanwa abokananka" yak'i cire soyayya agabansu ki kwace biscuits d'in kiraba biyu ki
bawa abokanan nashi idan ke ka d'aice
dan kiraba shi da wannan masifar ta rowa kice ya sammiki in ya k'i ki kwace
da kin kwace xai fasa kuka sosai kina jin sautin
i hun kukan har cikin kwakwalwarki ki daure ki cije ki shanye wannan soyayyar ki taimakeshi ki
cire masa wannan mugun ciwon na rowa idan yai xuciya ya wullar da biscuits d'in sbd kin d'iba
d'auki ki k'ara rabawa xai xo da gudinsa ya amsa yana kuka ki kyaleshi kada ki rarashesa ki
barsa yayi ya gaji ki daure plx ki taimaki kanki ki taimaki al'umma dankece malamar y'ay'anki na
farko aduniya washegari ma ki maimaita hakan kice ya y'an miki in ya hana ki kwace ki raba
biyu ki d'au rabi
idan yai kukan ki cije kiyi masa haka sau hud'u ko sau uku ajere
wallahi baxakiyi sau shida ba kafin kice y'an min da kanshi xai raba yanda yaga kinyi ya baki
koya bawa abokansa ko y'an'uwansa ko ya baki da kansa kafin ma kice ya yanmiki xai ce
umma gashi.
Alhmdllh kinga shikenan kin taimaki kanki kin taimaki y'an'uwansa duk abinda ya samu baxai
banbanta kansa da su ba
xai xama mutum mai taimako da rashin kyashi musamman ma mace sbd marowaciyar mace
bala'i ce sbd har y'ay'anta sai ta koya musu
iyaye adaure araba y'ay'a da rowa tun suna yara anuna musu kyauta dole ce dan idan kika
kwace wannan abun xasu tabbar da kyauta taxama dole
ayi hkr acire soyayyar nan ta d'an wannan lokacin idan inkikayi haka kin taimaki kowa ta dalilin
alherinsa sai kiga kema kin samu rahama
idan kika fuskanci d'anki ko y'arki tana da son kanta bata so kowa ya tab'a abinta ko tana
zaluntar y'an'uwanta had'a musu kwanan abinci d'aya kada ki raba wajen kwanciyar su ma ki
had'a musu in dai jinsin su d'aya suturarsu ma ki had'a kisawa wannan ta wannan tun suna jin
haushi akwana atashi xasu daina jin haushin hakan kin had'a kan y'ay'anki baxa su tab'a jiwa
kansu kyashin sadaukar da komai nasu akan junansu soyayya da shak'uwa xata k'ullu
tsakaninsu da wuya kiga suna wannan fad'an nasakonni xasu xama abin sha'awah agun kowa
amma fa sai an daure
agurguje agurje bari mu tab'a y'anmata:
mutattauna abinda ke damunsu yawancin y'anmata 98% an tab'a yaudararsu kusan kowacce
budurwa tana da ciwon k'irji sbd damuwar soyayya sai saurayi ya yaudaremu daga baya kuma
mu komawa Allah bayan tun ada yakamata musan da Allah ba sai mun fad'a cikin halin ha'ula'i
shawarar da xan bamu idan har kina son ki kare kanki daga yaudarar saurayi lokacin da kikayi
sabon saurayi kika ganshi da irin qualities d'in da kikeso had'uwar ku ta farko kada kiyi sanya
sallolinki na wannan ranar kiyi addu'ar ya Allah wane sabon saurayin danayi idan alkairine
aratuwata Allah katabbatar da alkairin idan kuma ba alkairi bane shi ya Allah kahad'ani da
wanda yake mafi alkairi
had'uwarku ta uku ki tabbata kinyi addu'ar istikhara akansa cikin sauk'i idan shi ba alkairi bane
Allah xai rabaku batare da ciwon xuciya ko b'acin rai haka kawai xakiga kun rabu kirasa dalili kiji
ya fice miki arai duk kuwa da had'uwarsa kinga kinsa Allah alamarinki Allah kuma ya taimakeki
idan kuma alkairinr sai kiga kin aureshi
tayaya xakiyi addu'a akan wani sha'ani nada ban?
yanxu yanxun nan kikai sallar nafila kika dad'e kina addu'a bayan kin idar kika kunna music
indian music ko na hausa kinayi kina gyad'a kai kina jin dad'i tayaya Allah xai kalleki alhali kin
had'a rayuwarki da shagala?
addu'a fa kika gama kuma kin koma sauraron wak'a keda kanki kinsan bai dace ba. kiyi
tawassali da sunan Allah ki kiyi imanin ubangiji xai amsa miki addu'ar ki ubangiji Allah ya bamu
maxaje nagari
kada ki cika babban buri wajan xab'an wanda xaki aura ko bashi da arxik'i in dai yana da abinda
xai ciyar dake kin yadda da addininsa da kyakkyawan mu'amalarsa ki auresa kawai akwai
ingantaccen hadisin dayace wa iyaye
ku aurar da y'ay'anku koda maxajen basu dashi Allah xai axurtaku dan shine mai axurtawa.
ta dalilin wannan auren sai kiga Allah ya baku arxik'i na ban mmk.
saudaya wa xakiga kin kwashe shekaru kina soyayya da saurayin ki lokaci 1 kiji ance ya auri
wata abinda xai baki mmk shine my b wacce ya aura kinfita komai ya barki ya aure ta.
kin san babban kuskurenki rashin taka tsantsan shifa namiji inyana sonki duk dad'ewarku wllh ki
d'ink'a kaffa kaffa sbd yana lura da komai naki yana sa miki ido ba ke kad'ai ba har tarbiyyarku
idan kika fiya ashar kina ganin kun xama d'aya babu abinda xaki b'oye masa duk yadda yake
sonki xai iya rabuwa dake sbd tunaninsa bawai asoyayyarku ba a'ah akan tarbiyyan yaranki
baxai so ki d'ink'a xagin y'ay'anku ba ko wataran ma shi da kanshi xaki xaga haka inyaga
gidanku ba tarbiyya duk yanda yake sonki ya gwammace ya hkr
dai dai da yanayin maganganunki ma in basuyi masa ba kyaleki xaiyi ko yana sonki yaya kike?
mai saurin fushi ce ? ko masifaffiya ce kina da raina mutum ? ko mai hkr ce
ko kuma a'ah ballagaxa ce baki da aji ko kad'an ko kuma gidanku ba tarbiyya k'annanki
k'anana sun rainaki dan haka baku da tarbiyya
daya fuskanci abu mara kyau shikenan sai kiga yayi baya baya dake kirasa dalili wani ma
baxaiyi bayan dake ba sai dai kwatsam kiji ance yayi aure
kice ya yaudareki alhali shi kuma akwai wata illa da ya hango duk k'ank'antar ta
ta dalilinta ya rabu dake da xaki samu wanda yake amininsa ki ce ya fad'a miki akan
meyasa bai aureki ba idan har amininnasa yana jin tausayinki xai ce wai dan abu kaxa da kaxa
ke aganinki ba babban abu bane idan har yana sonki baxai k'iki ba shi kuma tunaninsa wannan
k'ank'anin abun watarana xai girmama ya wuce xatonsa misali:
kina hira dashi k'aninki yaxo yace "anty kixo inji mama"
dad'in soyayya ya kwashe ki bakyason abinda xai raba hirar ku dashi kikacewa k'anin naki "ina
xuwa"
kawai kika cigaba da hirarki xuwa cen wani lokaci har sai yai miki tuni "mama fa tana kiranki"
kika basar "ai zanje"
my b ma shi xai
taku raki ki je sannan xaki tafi
kin k'i xuwa kiran mama sbd kina sonshi ba kyason abinda xai raba hirarku dashi
shi kuma yana kallonki a mara tarbiyya mamanki na kiranki kin k'i xuwa
ya tabbata bakya girmama iyayenki duk lokacin daya aureki idan kikayi bak'i haka xaita
kiranki kina k'in xuwa.
amma da mama ta aiko kije kada kibar yaron yaje yace kina xuwa
ku tafi da yaron batare da kin nemi ixininsa ba kice masa
yi hkr bari naje mama tana kira ku tafi da yaron
xai tabbatar da kinsan darajar iyayenki kina daraja su koda ya aureki baxaki had'a hidimar sa da
ta kowa ba.
mu dage da addu'a dare da rana safiya da maraice kixama mai tak'wah da tsoron Allah ki
tsarkake harshenki ba ruwanki da yin gulmar wata kiji da kanki
kada burin duniya ya mamaye ruhinki babban burinki ya xamana samun falalar ubangiji babban
burinki ya ka sance samun rahamar Allah.
dan me Allah ya haliccemu ? dan mu bauta masa ba don ki cikawa kanki wani buri na cen da
ban
na neman duniya koda kina da wasu burikan tunda ba'a rasa mutum da buri manyan burikan ki
yaxama shine na Allah samun falalarsa da rahamarsa da cetonsa da ceton annabin mu annabi
muhammad sallal lahu alaihi wasallam.
akwai bayanai da yawa abakina ga lokaci na hararar mu dole na katse anan ma had'u agaba
insha Allah.
tayi addu'ar rufe taro aka watse jikin kowa asanyaye dan malama
*Maryam Garkuwa*
ta sanyayar musu da jiki matuk'a.
yamma nayi aka fara shirin kai amare da jikinsu yake asanyaye kowacce tana tunanin rabuwa
da junansu sbd shak'uwar da sukayi bayan sunyi wanka aka shirya su cikin less mai shegen
kyau kowacce aka kaita d'akinta suna rusa uban kuka tamkar baxasu kuma had'uwa waje d'aya
ba sai da suka karyawa kowa xuciyarsa mutane da dama xun xubar musu da kwalla sbd
tausayin rabuwarsu bayan sun shak'u da juna sosai.
nan cikin G.R.A CHED'E CRESCENT aka kaisu unguwa guda Abba ya ware akayi wa kowa
gini gidajen nasu iri d'aya
jannat na xaune gefen gadonta tana xubar hawaye tana tuna rayuwarta da y'an'uwanta da irin
budirin da sukeyi d'akin kowacce daban amma kullum suna tare da ita wataran ma ad'akin nata
suke kwana sbd shak'uwa yau gashi sun rabu wannan rayuwar ta wuce taxama tarihi tana son
y'an'uwanta sosai gashi yanxu sun rabu kowacce ai kaita gidan mijinta kuka sosai takeyi
ayimin afuwa gobe na cigaba☹
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍
111&112
*Ummee Garkuwa*
satin su 2 a dubai suka wuce Singapore sun sha amarcinsu sosai sun nunawa junansu soyayya
satinsu 2 acen Abba ya kirasu awaya akan su xo hjy murja bata da lafiya sosai ba shiri suka
dawo batare da sunyi adadin kwana kin dasuke son yi ba tun acikin jirgi jannat take kuka sosai
sbd basu san yadda jikin hjy murjan yake ba gaba d'ayansu hnklin su atashe yake har suka
dawo 9ja kai tsaye gidan su suka wuce suka tadda shi empty ba kowa duk suna asibiti megadin
su ne ya fad'a musu asibitin da suke nan cikin G.R.A lameedo crescent kai tsaye asibitin suka
xarce a babban d'aki suke wanda d'akin an wareshi ne sbd kwantar da manyan mutane tunda
suka shiga hnklin y'an'uwansu ya dawo kansu kowa na mmkin dawowar tasu dan basuyi
tsammanin su yanxu yanxu ba hjy murja na kwance kan gadon marasa lfy ta rame kana ganinta
kasan tasha jinya da sauri ta tashi daga kwanciyar datayi tana kallonsu fuskar ta d'auke da
murmushi hannu ta nik'owa jannat
"Alhamdulillah jannat kin dawo xo na rik'eki naji ko kece ba gixo kikai min ba"
hawaye fal idon jannat ta k'arasa kusa da ita ta rik'e hannunta k'am tamkar wacce xa'a kwace
ta.
hannu ta mik'owa khaleel dayake a tsaye yana kallonsu fuskarshi d'auke da tausayinsu.
"matso khaleel ngd wa Allah daya dawo min da ku lfy ban mutu ba"
hjy Nabila tadake gefenta a xaune tayi tagumi muryar ta asanyaye tace,
"haba murja tun yaushe zan fad'a miki ki daina wannan zancen ? cuta fa ba mutuwa bace kin
damu bakiga jannat ita da khaleel damuwar hakan har ciwonki ya tashi gasu nan sun dawo
kusa dake ki saki ranki,
ki daina sa damuwa aranki Allah xai kiyaye miki su"
tak'arasa idonta fal hawaye.
tunda ta fara mgn falon yai tsit suna kallonta har tagama
wani irin murmushi hjy murja tayi cikin muryar mara sa lfy dasuka fara warwarewa tayi mgn
"bana ji na dai dai idan har bana jin nimfashin su kusa dani babban burina duk na waiwaya
naga idanun y'ay'ana "
momy tasa baki,
"yanxu ga sunan sun dawo kusa dake ki cire damuwa murja y'ay'anki sun dawo"
dady da Abba ne basu ce komai ba sai binsu da ido,
jannat da hawaye suka cika mata ido tuni suka b'alle hawaye ke xuba kamar an bud'e fanfo
zaro ido sulthana tayi tana kallon jannat dake tsiyauar kwallah
"anty jannat hawayen me kike ? kun tafi kun barmu da kewa kina cen kina hutawa kinyi k'iba da
kyau kin xama k'atuwa kin bar umma da kewa gashi nan har ciwonta sai da ya tashi,
kukan me zaki ai mun gama kuka tunda ta warke fatanmu Allah ya bata lfy ke kuma Allah ya
sauke ki lfy "
idonta fal hawaye hakan bai hana ta jefi sulthana da uban harara kamar idanuwanta zasu fad'o
hjy Nabila sunkuyar da kai tayi fuskarta k'unshe da murmushin jin dad'i dan taga y'arta ta ta
canza alamun akwai motsi a cikinta dan ga alamu nan b'aro b'aro sun bayyana
momy kam hamdala tayi axuciyarta najin dad'in samun jikanta na farko a duniya itama yau
taxama kaka.
k'ara rik'e hannunta hjy murja tayi tana hararar sulthana kad'an
"karki matsa mata yanxu lallashi take buk'ata Allah ya sauki jikana lfy"
dukansu suka amsa da amin
hajiyarmu tace
"banda muna asibiti dana yi gud'a Alhamdulillah ! ina kallonki nasan jikata akwai kyakkyawan
motsi a jikinta"
tuni ya khaleel ya manta a inda yake
"hajiyar mu da gaske kikeyi jannat tana da ciki ?"
hararar wasa tai masa cikin wasa tace
"ah 'ah bata dashi sai k'aton toilet"
dady da Abba ficewa sukayi fuskokinsu k'unshe da murmushin wannan lbrn na samun k'aruwar
da sukayi..
khaleel ne yai hmdl mai cike da xak'uwa da murna matuk'a dan bai tab'a tunanin ajiyar tashi ta
xaunu ba
"Alhmdulillah na zama baba nima Allah na gode maka da wannan ni'ima jannat! Allah ya biyaki "
sulthana kwashe wa tayi da dariya da sauri ta kame baki tana kallon hjy murja
ta waiwayo kan ya khaleel daya xubawa jannat ido yana jin kamar ya had'iye ta,
"majnun kalli umma da hajiyarmu da momy kada kayi sub'ul da baka"
waiwayo wa yayi fuskarshi kamar ammasa albishir ko kad'an baxai iya k'iyasta abinda