Showing 84001 words to 87000 words out of 132173 words

Chapter 29 - JENNIFER COMPLETE

11 Jul 2025

5155

kuka tasaka Abba ya tarasu duka iyalansa hajiya nabila harda kuka
wajan yiwa maman david da papa gdy cikin farin ciki papa da maman david suma sukayi gdyn
abinda Abba yai musu yabasu gida anan g.r.a tare da makud'an kud'ad'e da motoci kud'ine
masu yawan tsiya tuni suka sa kuka sbd basu tab'a tunanin xasu sami dukiya mai d'umbin yawa
irin taba tare dasu suka xauna nan suna hira duk yawanci hirar akan rayuwar jannat ne maman
david ta basu lbrn ranar da ta tsinceta da yanda suka rayu hajiyarmu da hjy nabila sai kuka
suke sai yamma suka tafi


bayan kwana biyar
ammin sulthana taxo ita da y'ay'anta maxa biyu da mahaifinsu cikin farin cikin sulthana ta fad'a
jikinsu tana kuka ita kanta ammin kuka takeyi ita da y'ay'anta dan bak'aramin rashinta sukayi ba
suna matuk'ar k'aunarta a babban falo suka xauna Abba ya gabatar musu da kansa da kuma
iyalinsa sannan yai musu gdy sosai itama ammy ta gabatar da kanta "sunana hajiya mariya mahaifiya ta y'ar nan dawakin tofa ce dan mahaifina shine hakimin
dawakin tofa,
da sauri hjy nabila ta kalleta tana mmk cikin murna tace
"idan kuwa hakane ke yar'uwata ce dan kakan hakimin dawakin tofa ai d'an gidan sarkine kin ga
kuwa duk kakan ninmu d'aya cike da murna ammy tace "tabbas hakane ashe sulthana a
hannun uwa ta tashi ba banxa ba tun dana kalleta ranar da na tsinceta naji ina sonta sosai ikon
Allah jininka jininka ne wannan shine mijina Abdul jabbar ibn yassar shima balarabe ne amma
mahaifiyar shi hausa fulani ce dan y'ar nan 9ja ce adamawa state ga y'ay'ana nan babban

shine mukarram k'aramin kuma yusuf suka d'ai Allah ya bani sai kuma macen su uwata takaina
sulthana, dariya sukayi hajiya nabila tace " ngd sosai ammy kinyi k'ok'ari kin jure duk wata fitina
ta sulthana,
murmushi kawai tayi had'e da girgixa kai
mukarram ne yace,
" ukhty kika tafi kika barni narasa abokin fad'a gsky ukhty nayi missing dinki
dariya babansu yayi
"af dama na fad'a maka duk randa sulthana tayi aure kai ka d'ai xaka ci kanka gashi ma batayi
auren ba kullum sai ka mana mitar aje a dawo da ita
yusuf yakatse babansu
"abu nifa na kwana biyu banga fad'ansu ba kace suyi in sha kallo dan in ina kallon fad'an anty
sulthana da yaya mukarram ba ruwana da kallon tom and jerry,
dariya sukayi
sulthana ta harari yusuf
"mune ma tom and jerry ko ?
hindu ce tace
"oh sulthana yanxu da wancen yayan naki babba kike fad'a?
kwafa mukarram yayi
" hmm ai ammy ce ta fad'a mata wai ita take bina sakuwa tace shiyasa ta rainani,
yusuf ne ya kuma mgn
"nifa gsky ya mukarram kuyi fad'a da anty sulthana nayi missing kallon fad'an ku,
dariya abbu yayi
"sulthana yanxu ta daina yiwa yayanta fad'a ko sarauniyar ammy ?
gyada kai tayi tana dariya hawaye ya sauko mata ta k'ara shiga jikin ammy tana kuka tace,
"ammy duk wannan gatan da soyayyar da kukai min ace ba ku kuka haifeni ba ?
idan na tuno da hakan ina jinjina abun araina,
share mata hawaye ammy tayi,
"meyasa xakice ba ni na haifeki ba ? kina ji fa yanxu agabanki kakannin mu d'aya da mahaifiyar
ki kinga kuwa ke y'ata ce ta cikina dad'i sosai ya kama sulthana tana dariya tace "hakane
ammyna
haka sukai ta hira cikin farin ciki da murna


washegari suna falo kamar ko yaushe dangin ched'e suka xo dan su sanarwa da dady gobene
gagarumar walimar da suka shirya na jin dad'in dawowar y'ay'ansa gida yak'e kawai yayi yace
Allah ya kaimu


Alhaji adam yana xaune a d'akinsa yana duba wasu takaddu na wasu kamfani daya manta
dashi wayarsa tayi k'ara bai tsaya duba number ba yad'aga sbd hnklinsa nakan takaddun
sallama yayi wata murya mara kan gado yaji ta shek'e da dariya
"waalaikumus salam gawa
gaban Abba ya fad'i

yace "me ?
aka maimaita da
"gawa matacce kana murna y'ay'anka sun dawo ko ? toh mutuwar ku ce ta xo gaba d'ayan ku
sai mun tura ku barxahu wannan shine hukuncin dana yanke akan b'atamin aiki da kukayi.
kafin yayi mgn an kashe wayar a tsorace ya mik'e da sauri ya fito harabar gidan ya hango
khaleel yana waya da sauri ya k'arasa wajansa abinda yaji yana fad'ane yasa shi k'ara tsorata
"ban gane gawa ba ??
bai ji me suka fad'a masa ba ganin abba yasa ya kashe wayan jikinsa asanyaye,
cikin tashin hnkl Abba yace
" me suka ce maka ?
shiru khaleel yayi
" fad'amin mana khaleel
jikinsa asanyaye yace
" sunce min matacce me yasa na auri jannat dan haka sunana gawa dani da ita da kuma
dukanmu
" wani bak'in ciki mai had'e da tsoro ya kama Abba,
da sauri ya kira wayan dady kafin dady yayi mgn yace masa
" dr bashir plx kaxo dukanku kaida iyali akwai maganar da xamu tattauna ya kashe wayan
hango jannat sukayi ta durk'ushe tana kuka hannunta rik'e da waya ta ajjiye flask a k'asa da
sauri suka k'arasa kanta cikin kid'ima Abba yace "lafiya jannat ?
shiru tayi tana kukan
"lafiya nace kin d'aga mana hnkl
rushewa tayi da kuka cikin kukan tace
"wasu ne suka kirani suka cemin matacciya wai xasu kashemu duka tunda muka b'ata musu
aiki muka dawo gida
cikin takaici Abba ya yarfe hannu khaleel ma runtse ido yayi hajiya nabila ce tak'ara so wajansu
da gudu gudu hannunta rik'e da waya cikin tashin hnkl take mgn
" meya same ku ? kuna lfy dai ko jannat ce ta rik'e ta lafiya ummee ?
kuka tasa ka
"bana so na rasa ku bana so Abba yace menene ?
"wasu ne suka kirani awaya kafin tak'arasa Abba yace " duk sun kiramu,
ki kwantar da hnklinki nasan ba ke kad'ai bace akwai saura duk xasu kira kowa ina son
muhad'u waje d'aya mu tattauna

*dan Allah kuyi hkr readers kwanaki biyar xuwa shida nayi deleting whatsap din duk wacce
taimin mgn baxan gani ba tunda na goge kuyi hkr idan kuka ga ban amsa ba kusake yimin mgn
sannan dan Allah ina cigiyar bilkisu wacce take posting din Jennifer a fcbk plx kiyi min mgn
narasa contacts dina sbd delete din danayi dan Allah kuyi hkr na yau xaku ganshi kadan wllh da
kyar ma na[truncated by WhatsApp]
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

89&90

duk abubuwan dasu ka faru xuciyar shi na cike da xargin y'an'uwansa dan tun farkon aurenshi
da mahaifiyar su basa so hakama lokacin da Allah bai basu haihuwa ba suka dameshi da sai ya
k'ara aure ya auri danginsu,
kallonsu kawai yakeyi dan aransa yanda yakeji da ana sauya dangi da ya sauya uwa uba
rigimarsu suna damunshi,

su kam farin ciki suke tayi sun had'a k'aramar waleema anan suke fad'awa Alhaji Adam din
cewa wannan kwarya kwaryar liyafa ce suna nan suna shirin hada babba dan sununa farin
cikinsu da jin dad'insu na dawowar y'ay'ansu gida shikam yak'e kawai yake musu ya kuma bisu
da toh ba yadda ya iya, yasan bai isa yace ah ah ba yanxu yanxun nan su tada fitina da tashin hnkl haka akayi ta lafiya
aka gama
kaf dangin ched'e sunyi wa dady da iyalansa kyakkyawar addu'a,

basu koma gida ba sai wajan 5:00 na yamma agajiye suka koma gida sbd gajiya jidda kam
jikinta a sanyaye yake ga azababbiyar kunyarsu datake ji ganin yanda take d'ari d'ari dasu yasa
suka d'inka janta jikinsu bayan sunyi wanka suna xaune a d'aki dukansu suna hira hjy murja ta
kira su falonta wasu manya manyan akwatuna ne masu shegen kyau ko wanne dank'are da
kaya acikinsa tace kowacce ta d'auka anjima xa'a k'aro wasu sulthana tace
"toh kafin mu k'anana mu xab'a sai manya sun fara anty jidda itace babba ki fara,
turus tayi a kunyace tarasa yaxatayi hjy murja dake bata san komai ba da murna tace " plx anty
ki dauka mana idan kuma duka kikeso to ba matsala anjima suma aka wo musu,
xaro ido tayi jiddan da sauri ta girgixa kai ta d'auki biyu,
hjy murja ta mik'e tana mgn
" sai nayi da gaske dan naga alamar kunk'i sakin jiki dani nifa mahaifiyarku ce bari ni na xab'a
muku tunda kunki xab'a ta janyo akwatunan ta rarraba musu tace,
"anjima xa a kawo sauran tace su koma d'aki baxa su iya d'auka ba xata sa ma'aikata suka wo
musu

d'aki suka koma suna hira suna jin dad'in ganinsu tare ba rigima ko tashin hnkl bayan sun huta
Alhaji ya kira su babban falo dukansu yace,
"Afrah ke ce babba da kanki xan fara,
turo baki tayi
"dady nifa sunana jannat,
murmushi yayi
" toh jannat ina so ki fad'amin marik'an ki ina son ganawa dasu dukansu,
cikin murna tace,
" toh Abba yanxu ma kuwa,
ya kalli sulthana,
"kema jasrah ki kirasu a waya ki fad'a musu ciki satin nan xansa aje ata ho dasu,
ashagwabe tace

" dady nifa sunana Zainab shi ammina tasamin sunan mamanta shine ta saya da sulthana,
dariya yayi cike da jin dad'i
"ikon Allah kinga sunan jannat kenan a da sunan hajiyarmu,
itama hajiyarmu dariya tayi "to takwarata Allah dai ya ramin ku,
suka amsa da amin
ya kalli hindu sai kuma yai shiru had'e da xuba mata ido itama idonta tane ya cicciko da hawaye
da sunkuyar da kanta sai kuma ta d'ago kai kamar xata fashe da kuka,
" Abba ni nawa marik'in yana kurkuku amma ya bani kariya sannan ya gatantani alfarma d'aya
nakeso Abba kaimin
da sauri yace, "ina jinki akwai wata alfarma da xaku nema wacce xan kasa yi muku ?
sai dai inbani da yadda xanyi in dai kud'i na maganin alfarmar konawa ne zan miki
mik'ewa tayi "ina xuwa Abba tai b'angaren su bata dad'e ba ta dawo hannunta rik'e da wasu
takaddu ta mik'awa Abba ya amsa yana kallon takaddun bayan yagama dubawa ya d'ago kai
yana kallon ta cike da rashin fahimtar abinda take nufi,
"Hindu ban fahimci me kikeso ba naga sunan mutum goma da wasu kud'ade,
ajiyar xuciya tayi
"hakane Abba sunan mutanen dana karb'ewa kud'ine ina so abiya su,
"girgixa kai yayi cike da takaicin yanda aka wulakanta masa y'a "kada kidamu hindu ko so kike a
ninka musu kud'insu sau miliyan zan musu bare wannan d'an abin da bai wuce ko ke kiyishi da
kanki ba,
Ya khaleel ne yai magana,
tabbas wannan shine dai dai dan dama sharud'd'an tuba irin wannan na tsakaninka da mutun
guda 4
na farko shine
ka daina aikatawa kwata kwata
sannan kayi nadama akan aikata xunubin da kayi
na uku shine
ka k'udirce aranka baxaka k'ara ai kata shi ba har abada
na hud'u shine ka nemi ya fiyar wanda ka cuta idan ya kasance dukiyane sai ka mayar masa da
ita,
haka yayi sosai ubangiji Allah ya yafe mana dukkan xunubanmu jikinsh asanyaye suka amsa da
amin ita kam hindu kuka ta saka
mahaifiyarta ta kalleta ta runtse ido tana jin takaici mara misaltuwa hakama hajiyarmu kamar
tasa ihu dan takaici tsam hjy murja ta mik'e jikinta asanyaye ta dawo kusa da hindu datake ta
rusa kuka muryar hajiya murja asanyaye kamar xata sa ihu dan bak'in ciki ta rungumota jikinta,
"hinduna ki daina kuka kad'dara ce kuma daga Allah take kisani wannan halin da kika tsinci
kanki aciki ba da son ranki ba bada niyyanki ba kin san shi addini gaba d'aya yana tafiya ne
akan niyya Allah yaga niyyanki banda an rabamu dake da baxaki tab'a tsintar kanki a wannan
halin ba baxama kisan da xaman masu aikata shi aduniya ba Allah mai gafara ne da kuma
rahma ki daina wannan kukan tunda ayanxu komai ya wuce ya xama tarihi yatafi yaxama kamar
ba ayi ba ki daina da mun kanki ki d'inka d'aukan kanki tamkar sabuwa addu'a kawai xaki dage
kinji hishma ta ,
ajiyar xuciya hindu tayi, tana kallonsu tayi d'an guntun murmushi,

"hakane umma kallon ku kawai innayi ni kadai nasan irin farin cikin dana keji ina jina kamar yau
na fara rayuwa hakane sbd bansan da dangiba ni kad'ai natashi daga ni sai babana sai kuma
yaranshi wato barandansa wannan kad'ai ya isa yasani cikin farin ciki ubangiji Allah ya yafe min
kura kuraina suka amsa da amin dady yayi addu'a suka tashi yamma tayi sosai


bayan sallar magrub da kyar momy ta lallashesu suyi hkr su xauna suka hkr sbd tabar su
rubayya da zahra sai anty jidda da itama tace ba inda xata dady yace baxai barta anan ba har
sai takira mijinta ya amince ba yanda taso haka ta kira danjuma yace bakomai dama ranar ya
yini xur bai ganta ba duk yana cikin damuwa shi baiyi tunanin ma tana da numbers ba jin
muryarta ba k'aramin dadi yaji ba,
sai da dady yakira danjuma dakansa yace "eh ya amince sannan suka tafi shi kuwa ya khaleel
yana jin sun fara zancen tafiya ya sulale ya koma b'angarensa dan baijin xai iya barin jannat
dinsa anan ya tafi gida ba
dady ya hau cigiyarsa hjy murja tace,
"dady khaleel ai yaxama namu abar mana shi dan ba inda xashi muna tare cikin wasa
hajiyarmu tace,
"ba inda mijina xashi ya barni,
suna dariya suka tafi,

suna komawa d'aki danjuma yaita kiran jidda awaya komawa gefe tayi tasa wayar agaba tana
hawaye,
cike da tausayawa jannat tace "anty jidda meyasa kike son takurawa kanki da kad'darar Allah
ajiyar xuciya tayi tana kallon jannat,
muryarta adashe tace
"baxaki gane bane jannat,
girgixa kai jannat tayi "plx anty jidda ki d'aga wayan nan kada ki shiga fushin Allah,
ba ydda jidda taso haka ta d'aga wayan
sautin kukanshi kawai takeji ganin haka yasa tasa wayan a hansfree suna jinshi yana ta uban
kuka dan shi yafi jidda jin takaicin halin daya ke ciki
cike da mugun tausayinsa suke sauraronsa hawaye masu k'una suka sauko mata ta kashe
wayan had'e da fashewa da kuka dukansu sukayo kanta suna rarrashinta cikin kuka take mgn,
" daga shi har ni babu mai maraba da juna na cuci kaina ! wllh nayi nadama ngd wa Allah da
abin ya tsaya iya haka wllh ni kaina ina jin tausayin halin dana jefa bawan Allah taya ya xamuyi
rayuwa ?
rubayya ce tai mgn cike da gwarin gwiwa
" anty jidda akwai mana akwai yadda xakiyi rayuwa dashi mai dad'i idan har xaki cire girman kai
dukansu suka kalli rubayyan da itama idonta ya cicciko dan tana da tausayi sosai itakam tafi
tausayin danjuma dan shi baiji ba bai gani ba
" meye laifin danjuma ?
kawai sbd talaka ne kodan kina tunanin kin fishi wayewa ?
tab'e baki ruby tayi,

"babu macen datafi namiji wayewa sai dai kawai ya kalleki kina masa kallon sakarai yana miki
kallon shashasha kiyi hkr ki tallafi mijinki ki nuna masa irin yanda kikeso ki ganshi danjuma fa
kyakkyawane farin bafillace dayaji gyara xakiyi mamakin yanda xai koma ki sashi a hanyar da
kikeso da bakinshi ya fad'awa dady yayi diploma da sauri suka kalleshi d'aga musu kai tayi " haka yace har takaddunshi ya nunawa dady plx anty jidda kinga yanxu haka kinsa shi cikin
mugun yanayi har yanxun inajin sautin kukansa ki kirashi ki lallashesa wallahi idan ba haka ba
xaki kwasowa kanki wani hakin wanda kuma sai Allah ya saka masa
da sauri jidda ta xaro ido hannunta na rawa ta d'auki wayarta ta kirashi a hansfree tasaka ring
d'aya tayi ya d'aga still kukan yakeyi bak'in ciki ya taso mata ta kanne da kyar ta lallashe sa yayi
shiru
" kukan me kakeyi ?
muryarshi asanyaye yace,
" inajin mugun sonki araina ina jin zan iya komai akanki ina kukane sbd d'axu naga kamar ranki
ab'ace yake kika kirani rashin sanin meya b'ata miki rai ne yasa ni wannan kukan dan ji nakeyi
ko cemin kikayi na kashe kaina zan kashe idan har hakan xai saki nishad'i,
kuka ya taso mata ta danneshi da kyar su kansu tausayinshi kama su yayi sukayi jugum suna
sauraronsa ya cigaba da mgn
"d'axu nayi kwalliya irin ta y'an gayu nasan xakiji dad'i in kika ganni kud'ina na kwashe duka
naje boutique na siyo irin kayan da oga khaleel yake sawa kuma nayi hakan ne dan na birgeki
dana shiga cikin gidan yayi jimmm ya cigaba da mgn jikinsa asanyaye
" hjy umma ta k'i kulani sai hjy Aisha ce tace min bakyanan kin fita da dady jidda kibawa
ummanmu hkr idan nai maita laifi,
share hawayenta jidda tayi dan sai yanxu tafara jin tausayinsa muryar ta tai mugun taushi
" zan bata hkr nasan ba laifi kai mata ba bata jin dad'ine tayi k'aryar ne kawai dan tasa yasaki
ransa,
suna jin yasaki ajiyar xuciya yacigaba da mgn,
" Alhmdllh ngd wa Allah dayasa ba laifi nai mata ba kinga jiddata har turare na siyo mai kamshi
dama oga khaleel yabani takalma da agoguna kada ki damu kinji tawan tabb ! ai ni nan da kika
ganni mugun d'an gayune a k'auyen mu fa nafi kowa gaye da kinje gezawa tasha in dai kikace a
kaiki gidansu danjuma MUGUN GAYE nine nan yayi dariya cike da son ya birgeta kowa ya
sanni wllh jidda ko wankan asdown kike so zan miki
zamess ba wllh duk na iya yadda nake sonki ke ni k'arshe ma har wankan sark'a irin ta gayu
ma inkina so xan miki kona d'an kunne duk na iya,
wani tuk'ikin bak'in ciki ya taso mata
sulthana kam gimtse bakinta tayi dan kad'an yarage ta tuntsire da dariya jannat ce ta d'inka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login