Showing 75001 words to 78000 words out of 132173 words

Chapter 26 - JENNIFER COMPLETE

11 Jul 2025

5179

da
ikonsa ya dawo mana dasu a tare a had'e alokacin da xuciya ta cire tsammani alokacin da
jikkunan mu suka xama tamkar basa tare damu sai ubangiji mai hikima ya dawo mana da
jikinmu da farin cikinmu kai Allahu akhbar ! lallai shine gwani sarki mai hikima akan komai mu
kuma gode masa da wannan falala da baiwa da albarka da yai mana,
Allah mun gode maka,
ya yi shiru sannan yaci gaba da bayani " adamu nasan kai da mahaifiyar yaran nan a yanxu kun
sami kwanciyar hnkl wanda baku tab'a tsammaninshi lokaci d'aya ba cikin wannan ranar acikin
irin wannan yanayin shin tashin ku a yau ko asatin nan kun tab'a tunanin Allah xai nuna muku
fuskokin y'ayanku cikin wannan sigar ? fashewa da kuka hajiya na nabila tayi " kokad'an ranka ya dad'e,
shikam adamu girgixa kai yayi dan ya kasa mgn sai yarfe hannu da yayi,
murmushi sarki yayi,
"Allah kenan aduk lokacin da ubangiji ya hanaka abu ka gode masa dan idan ka gode masa to
tabbas gaba kad'an xai maka wata hamshakakkiyar baiwa da bakayi tsammanin ta ba lokacin
daka fidda rai, wannan shine babban misali addu'a bata fad'uwa k'asa banxa kai tayinta kada
kagaji ubangiji yana jinka kuma ya na amsa akwai wahalar da xai yanke maka ita wacce xata
xame mk baiwa da farin ciki nan gaba,

ga bayin Allahn da suka had'a maka y'ay'anka adamu su baka lbrn komai,
a kid'ime suka kallesu dukansu, adamu ched'e ya girgixa kai ya cije lebe sam yarasa wanne irin
kalan harafi xaiyi mgn dashi cikin girgixa kan ya fara mgn dan muryar shi ma sai da ta canza
" ban san wacce irin gdy zan mk ba kayi min abinda duk yawan tarin dukiyata batai min ba dole
na jinjina maka kaxama mutum mai k'ima da daraja a wajena ka xama mutun na musamman
wanda baxan manta tulin tarin alherin da kaimin b duk wanda ya kalli yaran nan yasan sun sami
gata kasa k'arasa wa yayi dan muryar shi rawa ta farayi tabbas in ya cigaba da mgn xai iya
kecewa da kuka, da sauri abban A.k ya dafa kafad'ar shi yana girgixa kai,
a hnkl adamu ya sauke ajiyar xuciya yana magana jikinsa asanyaye,
" kabeeru ina jina cikin yanayin da bantab'a jinsa ba ashe farin ciki iri iri ne ? yau nake tantance
yadda kake jin sa arayuwa, zan iya yin komai dan tabbas ina jin bak'on al'amari na musamman
atare dani,
hajiya nabila cikin kuka tace,
" bawan Allah kayi mana gata wanda muka kasa yiwa kanmu duk yawan dukiyar mu da yawan
danginmu shekara sha tara kenan ana bincike ba'a gano komai ba amma cikin ikon Allah ka
dawo mana dasu lokaci k'alilan, kuma dukansu, da sauri d'aya matar tasa gyalenta tana share
mata hawaye tana kuka, " anty ki daina kukan nan yau fa ba ranar kuka bace a wurinmu rana ce ta musamman na Allah
ya kawo mana farin cikinmu Allah ya had'amu da yaranmu,
tsohuwar da suke tare ce tayi wani guntun murmushi ta kalli momy,
"baiwar Allah nasan ke kika xamewa jikokina uwa keda bawan Allahn cen mijinki bamu da bakin
da xamu iya biyanku ko gd muku sai dai kawai muce,Allah ya.... ta fashe da kuka Allah ya
biyaku,
sarki ne ya gyar murya,
"dr bashir Allah yai maka Albarka Allah ya raya maka xuri'a Allah ya albarkaci rayuwarka da
xuri'arka lallai kayi namijin k'ok'ari na jinjina maka ina son ka kwashe labarin rayuwar yaran nan
mai ban ta ujjibi kafad'awa iyayensu,
jikin dady asanyaye dan muryarshi ma sai da tayi mugun laushi sbd tausayi suna kukan yana
rayawa aransa ace shine a irin yanda suka samu kansu tabbas xai iya yin fiye da abinda sukayi,
ya fara da gdy ga Allah sannan ya kwashe labarin komai ya fad'a musu,
kamar ya xugasu suka kece da sabon kuka na ban mmk,
sarkine yace,
"ku dakata ! ku dakata kukan ya isa haka Allah xa mu gode masa,
" hjy na nabila ta kalli jannat datake gefe guda tayi ta gumi,
"y'ata xo nan xo kirabu da jikina plx kixo na ji guminku duka a cikin jikina,
jannat tana xubar da hawaye ta girgixa kai tana wa uwar wani kallo wanda ya bawa kowa mmk,
" baxan iya xuwa ba naganku tabbas ku iyayena ne amma har yanxu xuciyata bata dai daita da
tunanin yadda muka tsinci kanmu ba,
sulthana da sauri ta fincike jikinta ta matsa kusa da momy hade da sakin wani sabon kuka,
"momy kina jinsu wai sune iyayenmu kalli irin kukan da sukeyi dan muji tausayinsu su sam basu
ji namu ba shiyasa suka watsar damu a bola momy ki kalli irin rayuwar da anty hindu tayi ita da
Jennifer wai muna da iyaye masu sanmu wllh ban yadda ba tayi dariya wacce tafi kuka ciwo ta
kalli jannat " anty jannat kinji fa kin yadda ?

irin dariyar da sulthana tayi irinta jannat tayi
" ina fa zan yadda nifa kallonsu kawai nakeyi, cike da mugun mmk suke kallonsu,
hindu itama xare jikinta tayi tana dariyar wacce tafi kuka ciwo,
" baxan iya yadda ba fa sam shekara nawa ina cikin kunci da masifa lokaci d'aya na yadda da ta
tsuniya ta yaya sulthana jannat ?
mik'ewa sulthana tayi cike da tsiwa da rashin kunya,
" ko kunya bakuji ba kuke kiranmu y'ay'anku wanne laifi mukai muku kuka kasa xama tare damu
? idan ma sace mu akayi tayaya kukayi sake har hakan ta faru ? kaina fa bai d'auki wannan ba,
khaleel ne yace " sulthana meyasa kike haka ne iyayenki nefa,?
xare ido tayi
" iyaye ? su wa din ? iyaye xasu watsar da y'ay'ansu abola ? kasan yadda mukeji kuwa ta
girgixa kai tan xubar da hawaye masu k'una kada kace komai dan bakasan xafin rabuwa da
iyaye ba,
kwatsa mata tsawa yayi,
" ya sheki iyaye ba abin wasa bane ba kowacce mgn ake musu ba,
itama tsawar tayi,
"plx ya khaleel ! dan kaga ina tsoranka kada ka shiga wannan maganar kabarni dasu kamanta
wahalar da Jennifer da hindu suka sha !! ?
kallonta kawai sarki yayi yai mata alama ta xauna,
a tsorace had'e da kid'ima ta xube a wajan tana kuka mai ban tausayi, tsohuwar nan da sauran
matan suka sa kuka tsohuwar ta rarrafo ta rungume sulthana yi shiru jikata bamu da laifi a
b'atanku sanadiyyar rasaku sandin xamana kan wannan keken shekarata goma sha takwas ina
xaune akanshi sbd bak'in cikin rasaku, waccen ita ce mahaifiyarku, tunda kuka bace take rashin
lafiya sai yanxu inaga xata warke,
mahaifinku rabonshi da dariya tunda aka rasaku waccen hajiya murja matar babanku ce tafi
shekara tana suma ayanxu haka tana da ciwon xuciya sanadiyyar b'atanku munfiku bakin ciki
da damuwa kiyi hkr yanxu kuwa xakiji komai abakin hjy murja matar babanku,
a daddafe hjy murja ta iso kusa dasu ta janyosu jikinta inshaa Allah xakuji lbrn ku mai ban ta
ujjibi da mmk idan sarki yai min ixni,
gyran murya sarki yayi,
" nayi miki ixini murja
muryar ta asanyaye ta fara


CHED'E FAMILY
wani babban dangine wanda yayi fice afadin kasar nan harda kusan duniya fulani ne su usul,
Alhaji yahaya ched'e shine mahaifin adamu yana da tarin dukiya wacce tasa sunanshi yayi fice
a duniya yana da mace d'aya hajiya zainab ched'e wacce take y'ar'uwa awajansa sai d'ansu
guda d'aya tal da suka haifa shine Adamu ched'e wanda suka dauki son duniya suka dora masa
kasncewar shi kadaine hajiya zainab ita da mijinta suka haifa,
sun so suk'ara samun haihuwa amma Allah baiyi ba musamman hajiya tana son y'a mace
arayuwar ta dan ko lokacin da tana da cikin Adam addu'a ta dink'ayi Allah ya bata mace cikin
ikon Allah kuma ya bata d'a namiji ya taso cikin gata da soyayya taban mmk kasancewar shi

kad'aine duk da gatan daya samu hakan baisa ya xama fand'ararre ba sbd iyayensa tsaye suke
a kansu da kuma kulawa ta dangi dan atare suke xaune waje d'aya ched'e estate nan cikin g.r.a
basa xama ararrabe sbd kansu a had'e yake komai nasu acikin ched'e estate yake, hakan tasa
suke kula da junansu da tarbiyyan y'ay'annsu, adamu mutun ne mai tausayi da taimako da son y'an'uwa uwa uba mai son addini, dalilin
dayasa yai fice cikin dan ginsu kowa na sonshi da nan nan dashi a kullum burinsu su kyautata
masa Allah yasa ya kai mun xalin aure nan da nan dangi sukayi caa kowa yana so yabashi
y'arsa sanadiyyar hakan rikici ya fara k'ulluwa dan kowa gani yake adamu da y'arsa ta dace tun
abin ana yinshi a b'oye har takai takawo ana gaba da jin haushin juna hakan tasa mahaifin shi
Alhaji yahaya ched'e ya tara yan'uwanshi dukansu yai musu nasiha sannan yace,
"Adamu ba yaro bane yana da hnkl da ilmin da tunanin da xai zab'awa kansa wacce ta dace
dashi yanxu fa ba xamanin da xa'a xab'awa yaya abokan rayuwar su bane ku barsu su xab'awa
kansu dukkannin mu nan jini d'ayane xuri'a d'ayace har abada muna tare babu mai rabamu kuyi
hkr nabawa d'ana damar ya xab'i duk wadda yaga ta dace dashi kuma kuyi hkr ku bari y'ay'anku
su xab'i wayanda suka dace dasu,
haka dai yai musu nasiha suka gamsu jikinsu asanyaye suka watse bayan sunyi addu'a

ranar talata adamu yana b'angarenshi akwance mahifinsa ya shigo dakin ya sameshi akwance
idonshi a bud'e cike da kulawa yakalleshi,
" Adamu lafiya kake ?
mik'ewa yayi daga kwancen yana murmushi "Baba lafiya nake,
"toh alhamdulillah ka shirya anjima kad'an xaka rakani fada wajan sarki,
" toh baba,
ya fice yana fita yashiga toilet yai wanka ya sa manyan kaya yayi shiga irin ta mahifinshi wacce
yake so fararen kaya abinka ga farin mutun kayan sukai masa kyau sosai bayan ya gama ya je
babban falon su ya tadda mahaifinshi da mahifiyarshi suna hira, ta d'ago kai ta kalleshi
" oh dannan,
da ke bata kiran sunanshi,
"ina xakaje haka ?
" kodai xakaje wajan y'ata surukuta ne ?
dariya sukayi shida babansa,
" unguwa xai rakani wannan d'annaki inaga matsoracine yakasa fidda mata,
"baba adai tayami da addu'a
murmushi baban yayi,
" Adam addu'a dolece taxama dole ko bamu haifa ba dole miyiwa y'ay'an dangi dana musulmai
Allah yai maka albarka Allah yabaka mace ta gari shida hjy suka amsa da, "amin,
hjy tace "nidai in an fita yau adawo min da lbrn surukata, suka fice suna dariya bayan tayi musu
addu'ar Allah ya dawo mata dasu lfy


By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

83&84

basu b'ata lokaci ba suka isa gidan sarki falon shi suka isa na tarar bak'i kasancewar akwai
babbar sanayya atsakaninsu cikin girmamawa da biyayya suka gaishe shi ya amsa had'e da
sakin fuska,
suna cikin gaisawar sarki yai bak'i dan'uwan shi wanda baya k'asar yaxo shida iyalinsa matarsa
da y'ay'ansa hud'u biyu maza biyu mata,
bayan sungama tattauna abinda ya kawosu sukai sallama da sarki da bak'insa suka taho kan
hanyar su ta dawowa Adam yakasa daurewa har sai da yaiwa babansa maganar,
" baba kasan wannan wanda ya shigo fadan sarki ?
"a'ah adam ya akayi ?
sosa kansa ya farayi yana murmushi,
"naga babbar y'arsa ne naga kamar tana da hnkl,
dariya baban yayi
"d'an nema kafad'i mgnr ka kai tsaye kasan dai ni ba surukin ka bane,
dariya shima adam din yayi
"baba da gaske nakeyi ina ga tazama surukarku idan zan samu,
cikin murna baban yace,
"Alhmdllh haka akeso inshaa Allah gobe zanje na tambayo lallai ashe dai hajiyanka da gaske
take tunda tace fitar yau axo mata da lbrn surukarta gashi xa a je mata dashi ubangiji Allah yasa
adace,
cikin xuciyarsa ya amsa da "amin


ba'a d'auki wani dogon lokaci ba suka dai dai ta kansu sai dai an samu matsala daga wajan
dangin yahaya ched'e fur suka k'i yarda da auren akan baxaiyiyu ya auro musu bare ba duk
tulin danginsu ace babu wacce tai masa, suka dink'a k'aramar mgn suna aibata rashin dacewar
abin, ran Alhaji yahaya ya b'aci ya tarasu duka yai musu fad'a had'e da nasiha ya kuma ce babu
wanda ya isa ya hana auren Allah ne ya had'ashi, ganin yanda ranshi ya b'aci yasa suka
amince dan suna gudun b'acin ranshi suka saki komai akayi auren mai ban mmk,
auren Adam ched'e da amaryarsa Nabila Idris sarki,
amarya ta tare nan cikin ched'e estate tasamu soyayya da gata wajan y'an uwan mijinta yanda
suke sonshi haka itama suke nan nan da ita,
kwanci tashi asarar mai rai sai da suka kwashe shekara goma da aure batayi ko b'atan wata ba
hakan ya dami dangi sosai akayi ta rokon Allah akan Allah ya bashi haihuwa hajiya Nabila da
surukarta Hajiya zainab sunfi kowa damuwa dan kullum atafe suke k'asashe daban daban ana
duba hajiyan Nabila duk inda sukaje amsa d'aya ce bata da matsala Allah ne dai bai kawo ba
kwatsam Allah ya dauk'i ran Alhaji yahaya ched'e sakamakon y'ar rashin lfy ta sati biyu,
mutuwar ta gigita kowa dan kaf arewa babu kamarsa haka danginsa kamar suyi me basu da
yadda xasuyi ubangiji ya amshi abinsa haka akai zaman makoki xuciyar kowa akarye akayi aka

watse akabar iyalanshi da azabar rashi ba kad'an ba,

sanadin mutuwar baban shi yasa komai na kasuwancin mahaifinsa ya dawo kansa shiyake kula
da komai
komai yanayin shine batare da jin dad'i ba abubuwa masu yawa sun tunkushe masa ga
matsalar danginsa da suka sashi a gaba da sai ya k'ara aure ga mutuwar mahaifinshi sannan
ga babban jigo shine rashin samun magaji abun ya had'u yai masa yawa yarame kana kallonsa
kasan yana cikin tashin hnkl shi sam bashi da burin k'arin Aure tunda yasan matsalan rashin
haihuwan ba daga wajansu bane Allah ne kawai bai basu ba

abin duniya ya ishe hajiya zainab ga rashin mijinta ga matsalar da danginta suke son takurawa
danta hakan yasa ta tarasu ta samu su kuka tace sam bata yadda ba. d'anta da matarsa basu
suka hana kansu haihuwa ba Allah ne bai basu ba su kyale shi yaji da abu biyu dan uku yai
masa yawa, da kyar dai ta shawo kansu dan rigimammune haka dai suka hkr suna matukar jin
haushi akan sunk'i yadda da mgnr su


kwanaki suka wuce sati ya shigo ya wuce haka watanni had'e da shekaru sai da suka shafe
shekara 20 sannan Adamu ya k'ara aure ya auri SAKATARIYARSA, abinda ya bawa kowa mmk,
akayi sa'a bata da fad'a sai d'an karan mutunci da biyayya dan soyayyar da take nunawa hajiya
Nabila da surukarta yasa kowa yake sonta ciki kuwa harda shi kanshi Adam dan yana son
uwargidansa da mahaifiyarsa suna xaune lafiya xama na biyayya murja tana matuk'ar girmama
su, basa kishi ko kad'an kowa yana son kowa idan ma ba amfad'a maka ba baxaka taba tunanin
kishiyoyi bane kwatsam baiyi wata da auren ba uwargidansa ta sami ciki, wohoho karkaso kaga
farin cikin wajan dangi biyu dangin ched'en da dangin hjy Nabila kowa son cikin yake gata na
duniya hjy Nabila tasameshi surukarta hjy Zainab kamar ta had'iyeta hakama kishiyarta hajiya
murja da ita akaita renon cikin har ya kai wata tara hajiya Nabila Allah ya sauketa lafiya ta haifi
y'an biyu mata, yasalam hajiya zainab kamar ta had'iye yaran abinda takeso Allah ya bata shi
kanshi adamu ched'en jinsa yake tamkar sabo Allah ya bashi magada nan fa dangi akaita
murna ana tururuwar zuwa dan kullum acikin biki ake har ranar suna ta xagayo a ka rad'awa
yaran suna Ta farko aka sa mata Zainab sunan hajiyan Adamu suke ce mata afrah,ta biyun
Aysha sunan maman Nabila ita kuma suka b'oye da Hishma, akayi shagali da wadak'a da arxiki
kamar baxa a dainaba dan adamu rabon motoci da bubura ya yi tun lokacin da aka samu cikin
yake raba abubuwa tun ana mamakinsa har ake masa kallon murna tasa ya fara xaucewa haka
ya dink'a jidar danginsa da abokanan arxiki xuwa ummara sutaya shi yiwa Allah gdy na yasamu
y'ay'a,

bayan suna da sati d'aya suna xaune a falo hishma tana hannun hajiya murja Afra na hannun
hajiyarmu Nabila na kusa da mijinta suna hira cike da farin ciki hajiya Nabila tace,
" hajiyanmu ki shaida na bawa murja hishma halak malak dana yayeta ta rik'eta a hannunta
kafin Allah ya bata dan na d'an d'ana rashin y'a nasan hakan xai sanya ta cikin farin ciki,
ai kam tana kawowa nan hajiya murja ta fashe da kukan farin ciki cike da farin ciki Alhaji yace
"Nabila na jinjina miki kinyi namijin k'ok'ari Allah yai miki albarka,

itama hajiyarmu mmk tayi kamar ta xubar da hawaye tace,
"Nabilata Allah yai miki albarka kin biyani labila kin gama min komai kin birgeni ta waiwayo kan
murja data ke rungume da hishma tana kuka,
"murja ki yi hkr ki daina wannan kukan dan kin cancanci abaki hishma sbd alkairinki da
mutuncinki tunda kikaxo gidan nan kike mana biyayya da girmama mu cikin yaran nan kikai ta
mana hidima babu abinda yake ranki najin haushi ko akasin haka kowa ya san da wannan
duniya ta sheda hakan babu abinda xamiyi mu saka miki irin haka, ubangiji Allah ya baki naki
y'ay'an suka amsa da "amin
jikin murja asanyaye tace " ina kukane na farin ciki dan wllh banta b'a jin cewa bani na haifi
yaran nan ba ina jin su kamar tsokata ina jin soyayyarsu fiye da yadda nake son kaina ubangiji
Allah ya raya min su jikinsu asanyaye suka amsa da "amin


mutane da yawa sunyi farin ciki da wannan kyauta da hjy Nabila tai wa kishiyarta hjy murja cikin
kuwa harda dangin Nabilan dan suna matukar son murja saboda tsananin kirkinta uwa uba
soyayya da wahalar da jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login