Showing 39001 words to 42000 words out of 138378 words
kike indauko maki" tafada tana shiga cikin kitchen dinta , cikin kayan ta duba ta dauko sashana ta wullawa hinde, babu bata lokaci wuta ya kama
"Kawo tukunya in Dora" hinde ta fada mata
"Ubanwa zaki dafawa abinci?.. Dan matsa baya ki gani" ta fadawa hinde, matsawa baya tayi daga inda wuta yake,ameera kitchen ta koma ta dauko tukunya,
"Me zan fara sawa cikin tukunyan?" Dan takowa hinde ta farayi
"Dalla tsaya inda kike ki fada min abinyi" ameera ta daka mata tsawa, daga nesa Matan ta tsaya tana gaya mata steps din da zata bi, cikin kankanin lokaci abinci ya dahu, ameera kitchen ta shiga ta dauki kwano ta zuba ta fara ci, kaman wacce bata taba cin abinci ba , haka ta dinga ci ,dukda dadin abinci bai kai Wanda ta saba ci ba, tana ci tana zagin Salem, hinde ta nan daga tsaye, ameera ko kallon inda take batayiba har saida ta koshi sannan ta kalleta
"Ke ki tafi mana" ta fada mata,
"To" hinde ta amsa mata kuma daga gani ranta ya biya, Amman ameera bata kalleta ba, kuma abinci na da yawa. Sauran abinci ta kai kitchen sannan ta nemi sabulun wanka da soso, sabulun wanki ta gani, sabon kuka tafara, idanuwanta sunyi mugun kumburi, ahaka tayi wanka da sabulun wankin, mai cocobutter ta dauka, tabude Amman ta maida ta rufe don warinshi ma takeji.
๐๐๐๐โค
Umma Salem zaune tana waya, ji nayi tana cewa
"Kina nufin baa taba bude office dinshi ba?"
"Eh..guys din cewa sukayi kwata2 babu alaman shi akano don cewa sukayi duk binciken da akayi ya nuna cewa tunda shi ba boyeyyen mutum bane zamanshi a Kano ma bazai boyeba.." Matan ta fada mata daga chan bangaren, shuru Umma tayi kaman mai tunanin wani Abu,
"To me hakan yake nufi kenan?"
"Gaskiya inajin bai Kano"
"To shikenan, but please keep on finding him cos nasan yan Kano,..tunda nasan bayayi min karya"
"To hajiyata..da akwai daya daga cikin yarona Wanda yake aboki da wani bodyguard din Salem, zansa shi ya kirashi muji in suna Kano..."
"Ok ..haka ma yayi..make the call right away".
" yanzu nan insha Allah "Umma ta katse wayan tare da kara kiran kawanta dake abuja ta jadadda mata akara tsaro wurin duba gidan Salem. Don yanzu babu abinda take so kaman tasa tawa a idonta
โค๐๐๐๐
"Tawa wace irin abinci zaki dafawa mutum a 15k kuma kullum?" Mami ta tambayi tawa
"Mami nidai ban saniba...cewa wannan mutum dake zuwa wurina yace mutumin mai kudi ne" mami shuru tayi tana tunanin maganan tawa
"Hmmm..kina ganin da gaske yake?"
"Eh mami don bai cika karyaba..ko yanzu ma cewa yayi inki yarda zai koma gidan mutumin ya amso kudin"
"Kuma yace babu inda zakishi zai kawo kudi yazo ya amshi abinci?"
"Yes mami..ni kawai indafa abinci shine nawa"
"To kina gani zaki Iya dafa kalolin abinda zai gansar da mutumin?"
"Insha Allah"
"To shikenan.." Bata idaba tawa ta mike ta dauki wayanta ta kira
Salem tana tsale tana cewa
"Ifemi.ta yarda" karaf sai kunnen mami, don tunda take kirnashi ifemi mamiba tabajiba
"Tawa me kika kirashi?" Tawa dauke wayan tayi daga kunnenta Amman bata tuna ta kashe wayan ba don yanda jikin ta ke rawa
"Mami...ba..komai..," tafada kaman zatayi kuka, duk abinda suke cewa a kunnen Salem
"Tawa Hausa kike cewa ifemi.. Tawa..."
"Mami sorry" mami bata sauraretaba ta nufeta
"Tawa Hausa kike cewa ifemi" kunnenta takama da karfi, daga chan bangaren Salem yaji ihun tawa sai hakuri take bawa mami, ji yayi ranshi yayi mugun baci
"If you don't want it the easy way...we will do it the hard way" yafadawa kanshi, har lokacin bai bar jin ihun tawa ba, yaji mami tana gayawa neighbors dasuka shigo ceton tawa da hausanta Mara fita
"Wai wannan yarinyan Hausa take so..bata ganin abinda suke yiwa Matan su?..yau aure gobe babu" hakuri aka dinga bata, tawa share hawayenta tayi
"Mami I love him.." Salem dake jinsu ya lumshe idanuwa kwalla na taruwa idonshi, mami kunnen tawa takara kamawa, banda ihu babu abinda takeyi, sai ka rantse yankata akeyi kuma kunnenta kawai mami ke kamawa.
A lokacin anayiwa Salem Chanjin fuska, ture artist din yayi ya mike ya koma daki ya kwanta, har lokacin wayan bai katseba, yaji tawa nacewa
"Mami he's not a bad person" mami kara kama kunnenta tayi da karfi sosai, wannan Karin da karfi tarike don da kar aka kwace kunnen tawa daga hannunta, Salem kaman yashake mami yakeji, daga baya wayan ta katse, dagani kudinta ne ya kare.
Salem kwantawa yayi yana juye2.
Bayan kaman minti talatin ya kirata bata dagaba, kara kiranta yayi, saida ya kusa tsinkewa sannan tayi picking, muryan ta chan kasa tayi mashi magana, pretending yayi kaman baisan abinda yafaruba
"Princess na amso kudin inzo mutafi?" Ahankali tace
"Ka bari saida yamma kaina ke ciwo"
"Ayya sorry.. In sayo maki magani?"
"Aa"
"OK..I love you" bata amsa ba ta katse wayan ta.
Da yamma yazo gidan, yau mami bata yi mashi faraa ba.
๐๐โค๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐โค๐๐
ยฎzuwairat(ummu maryam)
3โฃ0โฃ
Falonsu yazauna kanshi kasa, mami amsa gaisuwan shi tayi babu yabo babu fallasa, daki ta shige, baa dade ba tawa ta fito, daganin idanuwanta kasan tasha kuka, tana kallon shi ta sakar mashi murmushi karfin hali, kura mata ido yayi
"Tawa ciwon kai din ne yasa idanuwanki kumburi?" Ahankali ta daga mashi kai hawaye na taruwa idanuwa ta,
"Sorry.. Inje in sayo maki magani?" Girgiza mashi kai tayi tana goge hawayen dake sauko mata, hannu yasa cikin aljihunshi ya dauko 300k
"Gasu, yace tunda farkone ki sayi duk abinda kike bukata..sauran ki ajiye" daga red eyes dinta tayi ta kalli kudin
"Ka ajiye su..muje kasuwa tare" ta fada a hankali, maida kudin yayi ita kuma ta mike tashiga ciki dakin, yana zaune yanajin mami sai fada take Amman baijin abinda take cewa, bayan kaman minti goma ta fito cikin skirt da riga na atampa da gyale, mikewa yayi tabi bayan shi.
Bayan sun shiga mota ya kalleta
"Am sorry for all the pains..you won't regret it" kallon shi tayi tadan wayance.
"ban ganeba?" Bai kara cewa komaiba ba ya tada motan, ita ta nuna mashi hanya har suka shiga jifatu,abinda ya bashi mamaki shine yanda ta wartsake kaman ba itaba,
Kayan kitchen suka siya, babu yawa sai shegen tsada
"Ifemi wannan food warmer yayi tsada da yawa..just 1 for 40k?" Daria Salem yayi
"Ai godi am mutumin bayason kayan banza..shiyasa ya baki enough money.. Kinsan har extra 100k yabani in case kudin zasuyi kadan..." Tawa tsayawa tayi tana kallon shi, kura mashi ido tayi sosai..don yau ne rana ta farko data nutsu ta kalleshi sosai
"Wannan kallon fa?" Ya tambayeta, Amman still bata daina kallon fuskanshi ba, ahankali ta daga hannu zata shafa a fuskanshi, kauda kanshi yayi tare da rike mata hannu
"Wai meye?" Ya kara tambayanta, ahankali tace
"Sir da akwai wani abu afuskanka..." Da sauri ya kauda kanshi gefe daya, don sai lokacin ya tuna bai bar makeup artist dinshi yayi mashi blending din kayan sosaiba, har lokacin bai saki hannunta ba
"Ciwon kan ke saki ganin biji biji?" Itakuma har lokacin bata daina kallon shi ba
"Serious da akwai wani abu a fuskanka...bari in nuna maka" tafada tana kai dayan hannunta kan fuskansh, daria ya farayi tare da kara dauke fuskanshi yana tunanin
"Wannan yarinyan tana son tonamin asiri yau" kara rike dayan hannunta yayi, hannuwanta biyu cikin hannunshi, still kura mashi ido tayi
"Habibty kurajene suka fito min na shafa magani" yayi mata karya yana aduan Allah yasa ta yarda don yasan Yoruba da smartness, mutanen dake wucewa ta inda suke sai kallon yanda ya kama mata hannuwa suke, da sauri ta zame hannunta
"Muyi sauri mu gama, kaga lokacin dinner na gabatowa" ta fada tana kallon uban kayan kitchen din da suka saya
"To..sauran fridge da gas cooker" yafada yana nufan wurin wani katon gas cooker mai kai shida, bin bayanshi tayi tana cewa
"Kam...ina zan ajiye wannan gas din ...kawai mu sayi stove mai kai biyu" bai kara cewa komaiba suka sayi stove, wurin fridge ya nufa
" me zamuyi da fridge kuma?"
"Ai kina bukata don ki dinga saka ingredients da spices..kinga ba sai kin dinga yawon Shiga kasuwa kullum ba" wani foreign cool room ya nufa, tawa baki ta bude
"Gaskiya wannan yayi girma..kawai ka sayi wancan" ta nuna mashi wani medium sized freezer " haka suka dinga sayan kaya har Salem ya kashe over 400k Amman tawa bata saniba.
Daga nan kasuwa suka shiga suka sayi kayan abinci Da manyan dry fish, suna dawowa gida yan unguwa da neighbors suka bude baki, wata yarinya cewa tayi
"Tawa kodai aure zakiyi baki gaya mana ba?" Dariya tawa tayi
"Duka nawa nake da zanyi aure" kallon mamaki Salem yayi mata batare dayace komaiba.
Suna shiga da kaya ciki mami ta mike tsaye tana mamakin yawan kayan, saida suka gama kai kayan tawa ta rako Salem waje, har ya shiga cikin mota, ya kalleta
"Wai cewa kike baki isa aureba?" Daria tayi
"To na isa ne?"
"Ai you are ripe for harvesting..."
"Ka fara ko?"
"To sorry.. Ni zan tafi..around 7pm wannan abokin nawa zai zo ya amshi abincina" yafada , kallon mamaki tayi mashi
"Abincin ka kuma?"
"I mean abincin mutumin"
"OK"
"I love you" ya ce mata , Amman bata amsa mashi ba,
"Tawa.."
"Sir" ta amsa mashi,
"Ki bawa mami hakuri ta amince ta bani ke..in ba hakaba...zan daukeki inkai wata kasar in aureki" dariya tawa tafariyi tana kallon shi sai taga Sam babu alaman wasa a fuskanshi, juyawa tayi tana cewa
"Sai kun zo amsan abincin" yabi bayan ta da kallo
"Zaki Sani in wasa nakeyi maki" yafada tare da tada motan ya bar wajen.
Tawa na komawa gida tabawa wani yaro ya sayo mata kerosene, babu bata lokaci tafara hada kayan fried Rice da chicken pepper soup.
Bayan sallan ishai Salem da Abdul na zaune a dinning suna kwasan garan da tawa tayi masu, sai wayan Abdul ya fara ringing, kallon Salem yayi Salem yace
"You can receive your call if you want" Abdul picking yayi
"Guy sai yau ka tuna ni?" Abdul ya fada, daga chan bangaren akace
"Wallahi Dan uwa kayi hakuri.. Wai kana inane?"
"Me akayi kake tambayan inda nake"
"Wallahi haka nan.. Kawai inason shiga garin abujane nace tunda kaine dan abuja bari in gaya maka" daria Abdul yayi
"Ai kusan wata na biyu bana abuja...muna tare da the boss"
"Amman gaskiya Abdul baka da mutunci.. Ashe kayi wata biyu gida Amman baka nememuba?...to ni fadamin inda kake sai inzo" Abdul zai bude baki yayi magana yaga Salem ya bata fuska
"Kayi hakuri kasan I can't disclose the boss's address" daria dayan guy din yayi
"Kayi gaskiya.. Amman Dan Allah da gaske ne wai oganka yana son wata yarinya Yoruba.." Karaf sai akunnen Salem, Abdul kallon shi yayi Salem yayi mashi alaman yace eh
"Eh..ya akayi ne?"
"Yarinya tayi saa.. Amman ba nan garin take bako"
"Ya akayi ne guy..what's happening?" Salem hannu yayi mashi ya maida wayan hands free, Abdul maidawa yayi, guy din yacigaba dacewa
"Kana cikin mutane ne?"
"No..talk to me" Ahankali mutumin yafara cewa
"Cewa akayi mu dauketa mu kaita..." Sai kuma yayi shuru
"Ina akace Ku kai ta kuma wayace ku daukota?" Abdul ya tambayeshi, Salem kam tuni zufa ya fara keto mashi
"Yola akace mu kaita..saidai gaskiya bansan Wanda yace mu daukota" yayi mashi karya, zaiyi magana Salem ya kwace wayan daga hannunshi, afusace yafara cewa
"In wani abu ya sami..fingers din dake hannunta.. Daku, da uwayenku, ubanku.. In short your entire family will pay dearly.." Bai ida magana ba aka katse wayan. Salem wurgar da wayan Abdul yayi
"Waye wannan?" Salem ya tambaye Abdul
"Wani abokina ne" bai kara cewa komaiba ya dauki wayan shi number shugaban police gabaki daya yakira ya fada mashi yana son ayi guiding wata yarinya akano, sannan yanason akama wasu yara,
"Yes sir " kawai mutumin yace mashi sannan ya katse wayan.
Shugaban Mtn yakira
"Wai har yanzu baku gama painting gidan ba?"
"Pardon me sir..dazu da yamma aka gama..cewa nayi kar in dameka sai gobe" tsaki Salem yaja
"Zan gayawa person in charge of my account ya turo maki 30m, sannan zan tura maka number da zakuyiwa albishir da kayan...make sure you send the message tonight.. Gobe Ku kirata Ku fada mata ranar Thursday zaa rufe, so taje abuja ta amso kudin da gida"
"Yes sir" kawai mutumin ke cewa sannan yace
"Sir kace 30m.. I thought 25k ka fada da farko"
"The remaining 5k is for your boys"
"Ah thanks sir..we will do it right away" Salem katse wayan yayi sannan yakira manager ya fada mashi what to do. Salem bai kara cin abinci ba ya mike yakoma bedroom,
"Umma what have I ever done to you... Umma please let me be happy for once.." Ya fadawa kanshi
๐๐โค๐๐
Abangaren ameera, abinci da sukayi da hinde ta yini tana ci, har yayi sauran ta zubdashi, around 5pm ta kara wanka, kayan jikin ta ta cire ta duba ledan da aka ajiye mata kaya ta dauki Riga da zani, ameera dai bata taba daura zaniba balle ta iyashi, haka ta cukuikuya shi a waist dinta , tafiya daya sai ya fadi, kurya ta shiga don tunda tazo bata shigaba, shima gani tayi daga student foam sai leda, tana cikin debe2 cikin gidan aka bude, agent din Salem ne da masu saka CCTV ameera ko kallon su batayiba ta koma bayan gidan tayi zamanta tana kuka don tasan dukkan su under Salem suke don haka babu mai taimakonta, duk Wanda ya ganta sai ya tausaya mata, don from Saturday zuwa yau Monday ta rame sosai.
Su agent basu dade ba suka saka CCTV cameras a falon, kurya sai compound, ameera kam bata damu tasan abinda sukeba, tanajin sun tafi takara fashewa da sabon kuka, banda daddy babu Wanda take kira.
Yauma bakin gate ta koma bayan sallan ishai.
๐๐โค๐๐
Around 10pm Salem ne kwance sai juye2 yake,hannuwanshi biyu dafe da maranshi, da kyar ya mike ya balli magani yasha, Amman har 10:30 bai samu sauki
"Wane irin matsala ne wannan... Why is the medicine not working..." Yana cikin haka wayanshi yafara ringing, da kyar yayi picking kasancewan yasan mai kira
"Guy how far?" Ya fada mashi ahankali, da sauri Khalid yace
"Bestie meke damunka?" Ahankali Salem yace
"Am having abdominal pain"
"Sorry dear.. Kasha drugs dinka mana"
"Nasha..its not working" yafada yana nishi
"Guy in banda abinka ..gaka da mata Amman you are suffering your self.." Ahankali Salem yace.
"Wace mata?"
"Wacce ka kai sambisa forest mana" shuru Salem yayi For a moment
"Wallahi mantawa nake daita...dukkan hankali na yana kan tawa"
"But you don't have tawa now..sai kayi amfani da abinda kake dashi" ahankali Salem yace
"I don't want to use that gal...nasan in Allah yabani tawa ta isheni..kuma tawa is not the kind of gal dazata zauna da kishiya..kawai just pray for me in sameta..don na samu labarin Umma ta sa a dauketa and dazun da safe itama saida maminta ta doketa because of me..am just confused"
"Am sorry you are going through a lot...I wish there is something I can do to help"
"Just help me prayer"
"I will.. About that gal..your wife in sambiza, meye ma sunan ta?"
"Ban saniba..but I think it's sameera"
" to ita sameera tunda ba zama zakayi daita ba.. I suggest you let her go" Salem da sai cije lower lip dinshi yake saboda azaban da cikin shi keyi mashi yace
"I will.. But not yet...she has to learn her lessons"
"But..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Best..let's talk tomorrow.. Wallahi yanzu kaman zan mutu nakeji"
"OK" Salem katse wayan yayi ya rike yana juye2 , muryan tawa kawai yakeson ji, Amman bayason ya jamata wani fadan.
Har 11 baiyi bacci ba sai nishi yake kaman daga sama yaji ta kirashi, kaman yana jira yayi picking
"Habibty" yafada Amman dakaji kasan bashi da lafiya, cikin rada tace.
"Ifemi meke damunka?" Ahankali Salem yace
"Wayyo cikina" yafada yana kara rike cikin shi da hannu daya
"Habibty cikina zai kashe ni" kaman zatayi kuka tace.
"Sorry.. Sorry ifemi.. Please kasha drugs"
"Love I don't need drug.. I need you..please let's get married before next month.. Please I need you" tawa shuru tayi
"Please am dying"
"Stop calling death for your self.. Allah zai baka lafiya"
"Habibty baki ganeba.. I am 35..I have known no woman.. I need a woman.. That woman is you" yafada yana nishi sosai, still cikin rada tawa tace
"Ife..its not fair...the way you are talking to me is not fair..am just 18 kuma kana gayamin irin wannan maganan.. So kake ka lalatani?.. Do you want to take my pride away?..."
"No..am sorry.. I can't help it..kusan shekara ta takwas ina Neman the right person...now I have found you.. Dukkan feeling din da nake suppressing da drugs is rushing back..and is killing me.. Banason in fada wata hanya.." Tawa dai batasan abinda zatace ba, duk nishin Salem ya shika mata kunne,
"Sorry"
"Thanks.. Just go to Sleep"
"No..zan tsaya kayi bacci tukunna"
"Then let me call you back" yafada batare daya ji opinion dintaba ya ya katse wayan, yakirata, haka suka dinga hira, inbasuba babu maijin abinda sukecewa, sai around 12:30 bacci yayi gaba dashi sannan itama ta kwanta.
๐๐โค๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐โค๐๐๐
ยฎzuwairat(ummu maryam)
3โฃ1โฃ
Kowannensu mafarkin junansu yayi, sai yau Salem yaga fuskan yarinyan dayake mafarkin ya dauka a taxi da fararen kaya, kuma tawace, itakuma tawa mafarkin, Cinderella tayi, kuma wai itace Cinderella, and the most handsome guy on earth took her away from all problems.
Wacegari Salem yadawo daga masjid ya koma ya kwanta, har lokacin bai jin dadi sosai, around 9am ya kira tawa ya sanar mata Abdul zaizo daukan abinci
"Har yanzu baka da lafiya ne?" Ta tambayeshi
"Am OK...thanks for yesterday"
"You are welcome.. Ife..bari in kammala shirya kayan kafin ya iso"
"OK" Salem saurare yake ko zata gayamashi Mtn sun turo mata message Amman shuru, kashe wayan yayi ya kara kiran, shugaban Mtn ya tambayeshi ko an tura mata yace eh sun tura har sau biyar. Kashewa yakira shugaban police ya tambayeshi ya tura police location din daya basu, shima cewa yayi sun tura three undercover police, amma har yanzu baa kama yaron dayace akamaba.
Kwantawa yayi yana jira Abdul ya dawo daga gidansu tawa da abinci don wayam ya kwanta jiya.
๐๐๐๐โค
Abdul na zuwa daukan abinci, tawa tayi serving mami sannan ta shiga wanka, shiryawa tayi cikin material mai saukin kudi ta zuba sauran abinci ta fara ci tana duba messages din da akayita tura mata tundare Amman bacci ya hanata dubawa, tana buda na farko taga an rubuta
_"Dear costumer you have win the the sum of 25m and a house in maitama abuja, kindly goto the following address to redeem your price before Thursday"_address da date tagani, daria tayi tacigaba da cin abincinta, sauran ta