Showing 18001 words to 21000 words out of 138378 words

Chapter 7 - Zakisan koni waye

09 Apr 2026

3223

da namiji sukayi abota?"
"Eh mana in kuma babu sai mu zama na farko" tawa shuru tayi bAtace komaiba ba salem ya sake cewa
"So zaki zama ore mi?" Batace komaiba har suka zo gidansu,
"Nan zan sauka" tace mashi, tsayawa yayi ta bude ta sauka sannan tace
"Sakallahu akhaairan..." Murmushi yayi
"Ameen nagode" juyawa tayi ta fara tafiya, Salem yabi bayan ta da kall, cikin ranshi yana
"See hips" Salem da akwai san hips, binta yayi da kallo har saida ta kusa shiga gida sannan yace
"Ore mi..baki gayamin sunan kina?" Ahankali tawa tace
"Tawakaltu"
"Lovely name for a beautiful owner" tawa daria tayi tare da dan girgiza kanta sannan ta shiga gida.
Tun waje Salem kejinmuryan yara suna anty tawa oyoyo. Salem kallon yanayin unguwan yayi sannan yace
"Alhamdulillah" kallon Abdul yayi sanda yake juyawa da motan yace
"Alh yau nasamu mace ta farko da tayi min daria" shima Abdul cewa
"Gaskiya kam..ko mun samu amarya?" Hararan Abdul yayi
"Kanason first love taci ubana kenan" Abdul murmushi yayi
"Sir ai bakasan ikon Allah ba" Dan daga kai Salem yayi kafin yace
"Gaskiya kam Amman kada Allah yabamu abinda yafi karfinmu"
"Ameen" Abdul ya amsa mashi, wuri ya samu yayi parking
"Alh kadawo nan ni nagaji da wannan driving din" ba musu Abdul yafita ya barwa Salem wurin bude Salem ya koma driver seat suka bar wajen, dan yawo suka danyi duk wacce ta tsaida su sai Salem yace kar su tsaya yana cewa
"Alh mu wuce kawai banason shan zagi da yamman nan.

Bayan kwana uku Salem ya stinci kanshi da tunanin tawa ,duk yanda yake kokarin kaudata daga cikin ranshi ya kasa , kwance yake tunanin duniya ya isheshi
" ya Allah koda nafito Neman mata ban fito da niyyan Neman wata kabila ba...why do I want to see her again... Why is my heart always remembering her?...ya rabbi choose the right path for all Muslims " aduan dayake kenan cikin ranshi
"Tawakaltu... Trust in Allah.." Juya kwaciyanshi yayi tare da daukan wayanshi, Khalid yakira, bayan sun gaisa Salem yafara cewa
"Guy wallahi am falling... " da sauri Khalid yace
"From were" daria Salem yayi sannan yace
"In love.. And I think it's love at first sights" ihu Khalid yafara yi yana cewa
"Yeyyy..mission accomplish.. Sai kadawo gida musha shagali..." Dariya Salem yayi, Khalid yakara cewa
"Friend gayamin ya take" ahankali Salem yafara cewa
"Guy bakace, tana da dan tsawo Amman ba sosai ba, sannan tana manyan idanuwa kaman na mage..." Khalid yayi saurin cewa
"Kaman naka kenan" daria Salem yayi sannan yacigaba dacewa
"Tana da dimple sannan ga round face.. In short guy kaman kanwar rihanna" daria Khalid yayi sosai, Salem bai saurareshiba yacigaba dacewa
"Wallahi guy she has the perfect ass..." Wani irin ihu Khalid yayi
"Slim ayya ita kake so...hope ba ass din kawai ya burgeka ba?" Da sauri Salem yace
"Wallahi dukkansu nakeso..dukda hijjab dinta bai bani daman ganin boobs daita ba Amman nasan da akwaisu..wallahi guy the lady is endoured.." Cikin daria Khalid yace
"Wannan kwatancen daka bada bansan yarinyan kake so ko jikinta kakesoba..." Da sauri Salem yace
"wallahi guy I have never wanted something so bad...inason yarinyan nan... I just meet her three days back but am missing her badly"
"Naji...gayamin..yar wacece a garin..." Ahankali Salem yace
"Gaskiya inaji ba yar kowa bace..asalima she's not an Hausa..." Da sauri Khalid yace
"Wace yarece"
"Yoruba" wani irin mugun ashar Khalid ya saki sannan yace
"Shike nan ansamaka wani abu aruwa kasha"
๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ6โƒฃ

Salem lumshe idanuwa yayi, daman yasan hakan zai faru, Khalid yacigaba dacewa
"Friend am disappointed in you...ace duk Matan duniya ka rasa wacce kakeso sai wata Yoruba?...daman muggan masu asirine, kilan sun baka wani abukaci..."
"Please stop screaming... Kar ka kashe min kunne dalla...don na gaya maka damuwata sai ka tsaya yimin maganan banza?...get off my phone!!!" Salem ya fada cikin fada. Da saurin Khalid yace
"It's not like that... Amman Salem ina kai Fulani ina Yoruba?..."
"Please...ka bar magana kaman jahili mana...Yoruba ba mutum bace..ko matanmu finsu sukayi....wallahi tunda nafito she's the first person da bata yimin rashin mutunciba..."
"Haba slim saboda yarinyan kake kirana jahili?...gaskiya sun kamaka" afusace Salem yace
"Wallahi Khalid ka kara cemin sun kamani zamu bata da kai..wallahi ko maganan ban gaya mataba...kawai nagaya maka don Neman shawaran ka Amman you getting me upset" Khalid kwantar da murya yayi
"Slim am sorry... Amman ka duba wannan lamarin..kana ganin Umma zata yarda?..gaskiya ni ashawarata kar ka gaya mata..." Shima Salem ahankali yace
"Am trying not to say anything.. Amman cikin kwana uku nan Kaman shekara uku..." Ahankali Khalid yace
"Yanzu Salem yanda ka tsani tara mata shine kake shirin yin mata biyu..."
"Kaman ya mata biyu?" Salem ya tambayeshi, cikin zolaya Khalid yace
"Ga wata chan zaka aura kuma gashi har yanzu baka daina neman Matan aureba.." Dan daria Salem yayi
"Ai ita wancan ba aurenta zanyi dan muyi zaman aureba..kaima kasan dalilin dayasa zan aureta...dana gama daita zan maidata wurin ubanta..."
"Karfa daga karshe muji chanjin labari..."
"Kaima kasan ba haka nakeba..I always keep my word...yanzu please best meye abinyi.. Wallahi I think I love that gal" Dan daria Khalid yayi
"Hmmm..ni dai yanzu ban abun cewaba sai ince Allah ya zaba mana abinda ya fi alkhairi" haka suka Dan taba hira kafin suyi sallama.

Salem gyara kwanciyanshi yayi yacigaba da tunani, shi kanshi yasan da kyar ummanshi zata amince da abinda ke faruwa.

๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™โค

Abangaren su ameera kam babanta yayi mata order kaya na gani na fada, kuma yar uwan dad mai suna anty safiya ta dauko nauyin gyara ameera don mom kam ko kallo basu ishetaba, da sai gayawa mutane yake zai aurar da yarshi da ance gawa sai yace ga dan tsohon shugaban kasa, da an tambayeshi yaucene bikin sai sai yace jira yake su bashi rana, ko tunanin rashin aikinshi baya yi.

โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›
Tawa kam tun ranar da Salem ya ajiye ta bata kara tunashi ba sai yau da take kwance gaman maminta tanayi mata ta tanayi mata tausa kasancewan kullum mami sai tayi mata tausa in dare yayi saboda yawan gajiya, zumbur ta mike zaune kaman wacce ta tuna abu ta jiya wajen mami tafara cewa
"Mami kin san wannan mutumin da nake baki labarin shi kwana kin baya?" Cikin magana irin ta wayanda basu jin dadi sosai mami tace
"Wane mutum kenan" da sauri tawa tace
"Wannan mutum da wata yarinya ta Mara..."
"Eh na tunashi..me ya sameshi kuma?" "Ba komai..jekaranjiya na ganshi har ya bani lift..."
"Meye lift?" Mami ta tambayeta
"Ya maido gida kyauta..." Baki mami ta bude tana
"Ah..ah..ah..toyin... Kina hawan motan Wanda baki Sani bako?..." Da sauri tawa tace
"Mami ban taba hawan motan kowaba...shima rokona yayi..." Cikin fada mami yacigaba dacewa
"Rokonki din banza...salan a yanke maki kai?...in badan yaran yanzu Baku da tsoro ba ina ke ina hawan motan Wanda baki saniba..."
"Mami..yi hakuri...bazan karaba.."
"Ke kullum cikin bada hakuri kike..." Tafada cikin fada sannan ta sassauta murya tafara cewa
"Omomi...bawai ina hanaki samun sauki bane..Amman irin abubuwan dake faruwa yanzu ya kamata ko wacce yarinya ta guji mutanen da bata saniba.."
"Mami sorry..."/
" naji..kar ki kara" kai Tawa ta gyadawa mami
"Kwanta in cigaba dayi maki tausan" ba musu tawa ta kwanta tayi rubda ciki, acikin ranta tana tunanin
"Da ganin wannan mutumin ba mugubane..wai oromi...shi dole sai yayi yarenmu" mami sai ganin tawa tayi tadan yi murmushi
"Kini?" Mami ta tambayeta, girgiza kanta tayi sannan tace
"Ba komai"

โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

Salem kam yana zaune yana video call da agent dinshi yana nuna mashi yanda gidan yake, daya kalli yanayin gidan sai yayi murmushi don babu abinda yakeyi mashi dadi irin ya tuna ameera zai kai gidan.
"Gaskiya kunyi kokari tunda with in sati daya har kunyi rufi"
"Yes sir...Amman inason in tambayeka" agent din yafada
"Am listening" Salem ya amsa mashi sannan agent din yacigaba dacewa
"Sir a toilet din water system zaa saka? Ko ayishi pit toilet"
"Wane irin water system.. Kawai pit...sannan tunda an kusa gamawa inason..
Forget kawai" yafada kaman Wanda ya tuna wani abu.
Yanzu rabonshi da ganin tawa sati daya kuma shikadai yasan irin kokarin da yake, don so kawai yake ya kara sakata ido koda saudaya ne, kullum in yakira Khalid babu abinda yake kara gaya mashi illah kar ya kuskura ya cemata komai, kawai with time zai mance ta Amman ya lura hakan ba mai yuwa bane
Around 4pm aka chanza mashi fuska ya fita shi kadai, don restaurant din da tawa ke aiki kusa yake da gidan shi.
Bayan ya isawurin yayi parking wani wuri sai ya taka da kafa zuwa restaurant din. Daga nesa ya hangi tawa tana amsan kudi daga hannun wani mutum, hannu tasa cikin apron din dake jikin ta ta fiddo chanji tabawa mutumin tare da Dan runtsunawa. Kallon tayi, sanye take cikin lace Wanda kudin ta bazaifi 3k ba sai dan hijjab Wanda bai wuce kuguntaba,batayiba kwalliyaba Amman fuskanta babu laifi, Dan kara matsawa yayi kusa da wurin , kallon yanda bakinta ke magana ahankali yayi da alaman waka take ji, ahankali ya zo kusa daita, daga kan datayi sai sukayi ido hudu, murmushi ta sakar mashi shima ya mayar mata martani, da sauri ta mike tare da saka hannunta cikin hijjab dinta ta fiddo earpiece sannan tace
"Lah..ina wuni" ta gaidashi
"Oremi ya kike?" Dan daria tayi sannan tace
"Baka mance ba kenan.." Shima daria yayi
"Ya zaayi in mance"
"Inawuni" takara kara cewa wannan Karin har da dan runtsunawa
"Lafiya lau..ya aiki?"
"Alhamdulillah ..zauna " tafada tana nuna mashi inda ta tashi, cikin zolaya yace
"In zauna?..in mai wurin tazo ta tadani fa?" Cikin daria tace
"Sha kuruminka..batanan tayi tafiya" wurin data tashi ya zauna, tawa ta ajiye Wayanta kusa dashi ta shiga cikin inda suke ajiye abincinsu na sayarwa, Salem kallon wayan yayi yaga techno ce Wanda ko 1k bazai iya sayanta ba, earpiece din yadan dauka ya saka cikin kunneshi yaji anacewa
"Dani dake mun dace" da sauri yacire earpiece din daga kunnenshi don kara wayan zata Iya kashe mashi kunne, baijin wakan hausa Amman wakan tayi mashi dadi,
"Dani dake mun dace kam" ya maimaita cikin ranshi, bai ankaraba yaji tace
"Malam bisimillah" sai lokacin ya dawo hankalinshi, daga kai yayi sukayi ido hudu sai yaji tsigan jikinshi na tashi at the same time gabanshi ya fadi, itama tawa Dan daga kirjinta tayi, kuma tayi saurin dauke hannunta, sai yayi karfin halin cewa
"Oremi sunana ba Malam ba..sunana..." Ahankali tace
"Sorry.. Meye sunan ka?" Dan shuru yayi yana tunanin yayi mata karyan sunan shi sai kuma yayi tunanin kar karyan yayi yawa
"Sunana Salem"
"Oga sa..."
"Meye oga kuma...gaskiya banason sunan."
"To sorry...sir Salem" gabanshi faruwa yayi don tunanin ko tasan shi waye yayi, don yasan dukkan maaikatanshi haka suke ce mashi
"Meye kuma sir Salem?" Yayi karfIn halin cemata, Dan murmushi tayi kafin tace
"Ai bazan iya kiran sunanka direct ba.."
"Nima ki kirani da oremi mana" zatayi magana yace
"Please"
"OK..OK..OK...naji oremi kazo kaci abinci" ido Salem ya gwalo
"Ai ba abinci nazo ciba..bani da ko sisi" Dan daria tayi
"Kar ka damu zan saka kudin da kudina..so please kazo kaci" kallon environment din yayi, tunda aka haifeshi bai taba cin abinci a public place ba sannan yasan ko ruwa yayi gigin sha sai ya amayar da dukkan abinci dayaci don shi asalima kyaman wajen yake
"Na koshi" Marairacewa tayi
"Please fa kaci..kaga last time ka rokeni nashiga taxi dinka to nima ina rokonka kaci abinci" shidai yasan yarinya nan is perfect for him
"In na gaya mik gaskiya zaki yarda?" Kai ta daga mashi alaman eh sannan yace
"Azumi nake" Dan hararan zolaya tayi mashi sannan tace
"To shikenan" abinci ta maida sannan ta dawo ta dauki kujera ta zauna Dan nesa dashi, kallonta yayi sannan yace
"Oremi wani taimako nakeso kiyi min"
"Ok...oremi"
"Ance nan Kano da akwai saukin kaya shine nakeson ki taimakamin ki rakani kasuwa inason zan siyawa kanwata kayan boarding school" shuru tawa tayi kaman mai yin tunani sannan tace
"Ok...Amman zan gayawa mami in ta yarda zan rakaka"
G โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ7โƒฃ

Kallon ta yayi for a moment sannan yace
"To in mami ta kifa?"
"Shikenan.. Bazan rakaka ba"
"Allah yasa ta yarda"
"Ameen" shuru yayi yana tunanin abinda zai ce mata don bayan son tafiya yanzu shikuma ba gwanin fira da mata bane,
"To in mami ta yarda nan zanzo sai mu tafi?" Kai ta girgiza mashi
"Aa..sai kazo gidansu mutafi.."
"Ya zaayi in gane mami ta yarda..ko nan zanzo amsan amsata.." Kai ta kara girgiza mashi
"Gaskiya kar kakara yuwa nan tunda madam gobe zata dawo..kawai kazo gidanmu muyi list kar mu shiga kasuwa mu rasa abinda zamu siya..."
"To shikenan" mikewa yayi
"Ni zan tafi" daga zaune ta danyi waving dinshi tare dacewa
"Bye.." Kura mata ido yayi
"Ko in tsaya in ajiye ki?"
"Aa nagode"
"Please.." Yafada cikin muryan yan mata, daria tayi
"No..nima dana baka abinci kinci kayi"
"Bhaki yarda ina azumiba kenan"
"Wane irin azumi akeyi ranar laraba?" Shuru yayi baisan abin cewaba, yafara takawa yana cewa
"Shikenan.. Sai nazo" waving dinshi takarayi sannan ta maida earpiece dinta cikin kunnenta.

Salem yana tafiya yana tunanin halin tawa...wai shi zata siyawa abinci... Dan murmushi yayi sannan yace
"You are kind and generous.." Haka ya koma gida yana tunanin inama bahaushiya ce da yanda yake jin kaunanta acikin ranshi ajiye karyan identity dinshi zaiyi ya aureta cikin sati daya koda kowa batasonshi, Amman in ya tuna yarenta sai hankalinshi ya tashi don yasan da kyar ummanshi zata yarda,dan abbanshi kam bashi da matsala don da akwaishi da understanding saidai ko kadan baya son abinda zai batawa first love dinshi rai.

๐Ÿ’™๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›
Tawa tana zuwa gidan ta gayawa mami abinda Salem tace mata, mami rufe ido tayi tace
"Aa..babu inda zaki.."
"Mami dan Allah" cikin fada mami tace
"Aa..wai baki da tsoro ne?..baki tsoron a kashe min ke?..."da sauri tawa tafara girgiza kanta tana cewa
" mami da ganinshi ba mugu bane..."
"Dalla rufemin baki..mugu lamba gareshi?..." Mami ta daka mata tsawa. Wiwi tawa ta fashe da kuka, tana cewa
"Mami wallahi nasan ba mugu bane... Kuma nayi mashi alkawarin zan rakashi...haka nan sai ya dinga ganina makaryaciya?" Mami bude baki tayi tana ganin ikon rabbi.
"Meye abun kuka...anya Tawa kasuwa zaki rakashi?" Cikin kuka tace
"Wallahi mami.. Kasuwa zan rakashi... Kuma baisan garin ba yace in rakashi" tafada har lokacin bata bar kukaba, mami zuba mata ido tayi na dan lokaci sannan tace.
"Toyin tsakanin ki da Allah meye sakaninki da mutumin?" Da sauri tawa tace
"Mami babu komai.."
"Babu komai.. Amman daga nace baki rakashi kasuwa shine kike kuka?...tawa...tawa..sau nawa na kiraki?" Da sauri tace
"sau biyu" don tasan dukda mami ba lafiyayya bace bata daukan rainin hankali, mami ta sake cewa
"Zan kara tambayan ki..meye tsakanin ki da mutumin?" Cikin kuka tawa ta sake cewa
"Mami bakom...." Mami ta katseta dacewa
"Tawa kar kisa raina ya baci...ki gayamin gaskiya abinda ke tsakanin ki da wannan mutumin?" Tawa shuru tayi tana kuka, gani tayi mami ta mike, ta fara cewa
"Wallahi mami nima ban saniba...Amman duk sanda na tunashi gabana na faduwa..." Tayi shuru, mami ta kara cewa
"Inajinki..kuma ki gayamin gaskiya banason karya.." Tawa Dan share hawayenta tayi sannan tacigaba dacewa
"Kuma mami inayawa tunanin shi.. Sannan ina son in ganshi kullum" baki mami ta bude
"Tawa..Ashe soyayya kike zuwa yi?...don kin gan bani da lafiyan dazan yi aiki in nema mana abinci shine kike fita kina abinda kika gandama?.." Tawa sabon kuka tafara tana cewa
"Mami ni ba soyayya nake.."
"Rufemin baki..wato ke bakisan sonshi kikeba?...yanzu wane yareneshi?" Ahankali tace
"Mami bahaushene" baki mami takara budewa
"Tawa Hausa...Hausa kikeso?.. Hausan da abu kadan sun saki Matan su?...baki ganin wasila da akayi bikinta wata uku dasuka har an saketa?..to ita bahaushiya ma kenan balleke wata yaren..."
"Mami ni ba soyayya nake dashi ba"
"Matsalarki...nidai bazan hanakiba tunda ban taba ganin ki da waniba..Amman kibi a hankali.." Still itadai tawa nacewa tayi kan ba sonshi take ba, abinda bata saniba shine abinda babba yagani zaune to ko yaro zai hau mountain bazai ganshiba. Goge hawayenta tayi sannan tace
"Mami kin yarda in rakashi kasuwa?" Mami dan hararanta tayi sannan ta bude hannuwanta
"Zo" tawa rarrafawa tayi gurin mami, mami ta rungume ta sannan tace
"Ifemi..kinsan inasonki...banason abinda zai saki cikin bakinciki..hausawa basu rike aure..." Cikin shagwaba tawa ta katseta dacewa
"Nifa ba sonshi nakeba.."
"Ai shikenan..zanga abinda zai biyo baya.. Kwanta inyi maki tausa" tawa kwantawa tayi mami tafara yimata tausa, chan kuma Tawa ta karacewa
"Mami kin amince in rakashi kasuwan?" Dan daria mami tayi
"Na yarda" tawa lumshe ido tayi cikin ranta tana aduan Allah yasa sir Salem yazo gobe.

๐Ÿ’™๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

Bangaren Salem kam kaman ana huramashi son tawa don kullum daita yake kwana yake tashi, cikin kwana biyun da bai gantaba kaman ya mutu hakan yasa yayi niyyan zuwa gidansu, tunawa yayi da dazun ankirashi angama gidan ameera, Dan mikewa yayi yakoma bakin window abinda zai yi next, wasu haddadun Porsche Cayenne dake parking tsakar gidanshi ya kalla yayi murmushi tare da shafa sajenshi dake sheki kaman ana shafa masu relaxer.

Da sauri yashiga wanka yana cewa
"Bari inje ingan ikon Allah" bai dau lokaci ba ya fito daure da towel, gaban mirror ya tsaya ya fesa turare sun kala goma jikinshi sannan ya dauki wata armani tuxedo shirt ya saka da wando shi. Nan take yafito kaman ba taxi driver da yan mata ke ciwa uwaba. Yana fita falon koina ya bade da kamshin turare shi masu tsadan gaske, Abdul juyawa yayi dasauri yana cewa.
"Sir ina zamu?" Mukullin motan ya mikawa Abdul sannan yace
"G,R,A sultan road" Abdul baki ya bude zaiyi magana Salem ya hade giran kasa dana sama, shuru yayi ya dauki car keys ya fita da sauri ya budewa Salem gidan baya ya zauna sannan shima yashiga suka bar gidan Abdul sai tunanin yau Salem yayi switching copporate mode.

Daidai gidansu ameera Abdul yayi horning, maigadin na budewa Salem ya tuna da alkawarin da yayi wa tsohon, nan take ya fiddo check book dinshi ya rubuta mashi check na 3m ya bawa Abdul
"In ka shiga ciki ka kiramin uban yarinyan ka bawa wancan tsohon wannan check din" ya fadawa Abdul lokacin dayake parking a farfayiyan gidan.

Da sauri Abdul yafito ya nufi balcony dinsu ameera, knocking yayi affan ya bude mashi koda, kallon yaron yayi sannan yace
"Kaje ja kagayawa dad dinka sir Salem na sallama..." Bai gamaba dad ameera dake kallon CNN ya mike da sauri yana
"Da gaske ne sir Salem a gidana?" Kai Abdul ya daga mashi, da sauri ameera dake zaune ta mike ta hau upstairs da gudu, dad ameera bangaje Abdul yayi ya nufi inda motan Salem ke tsaye, Salem dake kallon abinda ke faruwa ya kauda kanshi tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login