Showing 21001 words to 24000 words out of 138378 words

Chapter 8 - Zakisan koni waye

09 Apr 2026

3226

yin daria na yan second sannan ya kara daure fuskanshi kaman bashi bane, da gudu dad ameera ya karasa gurin motan Salem yana cewa.
"Sir yau kaine a gidana?...ka shigo ciki mana" Dan girgiza kai Salem yayi
"Aa nan ma ya isa...." Da sauri dad ameera ya kara katseshi
"Sir please ka shigo mana...sai ka tsaya waje kaman wani bako...please come in" yafada yana budewa Salem mota, ahankali Salem ya fito da cikin mota, dad ameera gaba yana yimashi jagora shikuma Salem na biye dashi yana tuna irin zagin da ameera ta yimashi da kuma irin maganan da dad ameera yayi mashi.
Ameera kam tanajin ance sir Salem ta Haura sama, direct dakinta ta tafi ,hannunta na rawa ta dauko makeup kit dinta tafara shafawa , cikin sauri ta gama shafawa sannan ta dauki wani dogonhijj ta sumbula sasnnan ta dauki turare ta kusa karar daita jikinta sanna ta nufidownstairs tana tafiya kaman kazan da kwai ta fashema aciki.
Salem na shiga falo ya gaisa da mom sannan sukayi shaking hannu da affan, wuri ya samu ya zauna, bai ankaraba yaji ance
"Ina wuni" cikin wata irin sanyi murya, Salem daga kai yayi yaga ameera, sai ka rantse ba itaba don durkusshe take gabanshi kanta kasa kaman wata salaha, inda bai taba ganintaba zai rantse mutuniyan kirkice
"Haka kuke zaluntan samari in sun zo neman aurenku...sai dagabaya kalanku ta gaskiya ta baiyyana" ya fada azuciyashi a zahari yace
"Lafiya" ahankali ameera ta mike ta nufi hanyan kitchen, dad ameera kam kaman anyi mashi albishir da aljanna, Salem mikewa yayi yana cewa
"Mommy sai anjuma..." Zatayi magana dad yayi sauri
"Sir ka tsaya kaci abinci"
"Aa nagode" yafada har ya kai bakin koda, dad binsu yayi shikam Abdul kallon ikon Allah kawai yake , suna fita Salem ya juya ya kalli dad
"Daman nazo inji in kuna bukatan wani abu don next week nakeson a daura aure..." Baki dad ameera ya bude zaiyi magana Salem yayi saurin cewa
"Oh sorry kace baka bukatan ko sisi...Amman abinda ke nan shine daga nan Spain nayi so ranar asabar by 4 zan turo private jet akaita airport na Lagos sai ta sameni chan...inyaso in tazo zan kaita shopping to make up for the rashin lefe...hope hakan yayi" dad ameera banda daga mashi kai babu abinda yakeyi
"Yanzu sir ranar asabar mai zuwa zaayi daurin auren kenan.."
"Eh...ko da matsala?.." Da sauri dad ameera ya girgiza mashi kai
"Aa wallahi....sir yanzu yaushe zan fara zuwa aiki" Salem shuru yayi yana tunanin yanason ya wahalal da ameera da dad dinta Amman yasan da zaran ya hanashi aikinshi zai dau alhalin mom da affan, hannu yasa cikin aljihunshi ya dauki wayanshi yakira Nigeria head ya bashi umarnin ya maidawa umar Adam aikinshi. Murna wurin dad baa magana, kofa aka bude ameera tafito tana tafiya kaman batason taka kasa, dad ameera barin wurin yayi, shikam Abdul kurawa ameera ido yayi yagane itace yarinyan data mari Salem, jin hiran da dad da Salem keyi ya tabbatar mashi rashin mutunci Salem zaiyi.
Kallon ameera Abdul ya karayi sai ya tsinci kanshi da tausaya mata, don yasan halin Salem.

Salem na ganin yafito ya juya baya ya shiga motan shi, da sauri Abdul ya shiga, sai ji yayi tace
"Allah ya kiyaye" kallon ta yayi suka hada, da sauri ta kauda kanta tare da sunkuyar da kanta kasa kaman mai jin kunya, acikin ranshi yace
"Monster in disguise" Abdul ya ja mota suka bar gidan, ahankali Abdul yace.
"Sir what's happening?" Murmushin gefen baki Salem yayi sannan yace
"So nake in gaya mata KONI WAYE"
๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’™
ZAKISAN KONI WAYE
โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œ
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ8โƒฃ

"Haba..alh. Wane irin aurene wannan?.. Ya zaayi mu aurar da yarmu ga wanda baa zauna akayi magana da magabatan shiba?..gaskiya am smelling something fishy.." Mom ta fada lokacin da dad ya fada mata yanda sukayi da Salem. Dad tabe baki yayi
"Ina ruwanki..yarinyan da baki damu daitaba? ..ai ko saida tanayi ba damuwanki bane"
"Ya zaayi kace ban damu daitaba..ai ko bakomai ni na haifeta..kawai halin da takeyi ke banso Amman ba wai banason yataba.." Dad banza yayi daita ya fiddo wayanshi yafara kiran yan gidan radio station ayi mashi sanarwan bikin yarshi, sannan ya kira yan gidan TV ya gaya masu ayi mashi sanarwa. Mom baki ta bude tana kallon shi, yana gama wayan ya mike zai fita mom tayi saurin tare gabanshi tana cewa
"Yanzu alh baka tunanin wannan abun ba yanda ya kamata bane?..ya zaayi auren yata kwara daya babu wedding event.. Babu lefe....babu miji wurin daurin auren..sannan the most annoying part of all ace yan uwa bazasu rakata gidanta don su san mazaunin taba?..gaskiya something is wrong" dad dirty look ya watsa mata sannan yace
"Aniyanki ya biki..." Yana kaiwa nan ya fice ya nufi dakin ameera.
Ameera kam tunda tayi ido hudu da Salem tazama speechless, don kyaunshi ya wuce yanda take tunani, cos yaune ranar farko da ta taba ganin shi atunaninta , daman tana yawan ganishi cikin news sannan tana following dinshi a social Media, Amman sam photo baya yi mashi adalci don a kasa yafi cikin photo kyau sau dubu.
Dad ameera yashiga ya gaya mata yanda sukayi da Salem, ko kadan ameera batayi tunanin wani abuba, asalima farincikine cikin ranta don bata taba hawan jirgiba Amman yanzu tata zataje Spain tare da the most handsome guy amatsayin mijinta.
Nikam nace ameera you better stop dream cos they is no chance in hell.

๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โค

Tawa kam wacegari ta zuba ido don ganin Salem Amman baizoba, duk sai ta tsinci kanta da bakin cikin rashin ganinshi. Ranan wajen aikinta saida suka gane wani abu na damun ta, Amman dasun tambayeta saitace bakomai. Wacegari ma which is Friday ta zuba ido zuwanshi Amman babu shi.
Yau asabar, dawuri tawa ta dawo daga restaurant don basu yin abinci dayawa. Tana zaune dakin su tayi tagumi duk abin duniya ya isheta, banda tunanin Salem babu abinda takeyi ita kanta abin tsoro yake bata don tunda take bata taba jin mutum na yawan fado mata a raiba sai yanzu, kallon agogon wayanta tayi taga karfe 4 sannan tace
"Allah yasa lafiya wannan sir Salem din baizoba...Allah kasashi yazo yau...inason ganinshi.." Karaf sai kunnen mami dake dawowa daga bathroom
"Me kike cewa?" Mami ta tambayeta, da sauri tawa ta dawo hankalinta,
"Mami ba komai" mami kallon ta tayi tare da tabe bakinta sannan ta wuce cikin kuryan dakin.

๐Ÿ’›โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š
Akan hanyan dawowan Salem daga gidansu ameera ya cewa Abdul ya bi ta hanyan restaurant din su Tawakaltu, ba masu Abdul yabi ta hanyan
"Sir wurin kaman a rufe yake.." Abdul yafada yana kallon wurin daga nesa, Salem kallon wurin yayi, ranshi batcewa yayi don niyyan shi ya tsaya cikin motan shi ya ganta ko yadan samu jin dadi cikin zuciyanshi. Haka suka tafi gida ranshi babu dadi don banda tawa babu wacce yake son gani.
Kallon agogon hannunshi yayi yaga har 5pm dan guntun tsaki yaja don yasan makeup artist dinshi bazai iya zuwa ya chanza mashi fuska ba har yaje gidansu tawa.

Wacegari which is Sunday tun 11 aka chanzawa Salem fuska, 11:30 daidai ya isa gidansu tawa kasancewan babu nesa tsakanin tukuntawa da zoo road, ya zuwa Salem yayi parking a inuwan wani bushiyan neem, sannan ya fita yana neman yaron dazai aika kiranta, bai dade da tsayuwaba saiga wani almajiri yazo wucewa, kirashi Salem yayi yace mashi yakira mashi tawa.
Tawa data gama wankin ta dana mami tare da yin wanke da gyara dakinsu cos basu zuwa aiki ranar lahadi saboda Matan da take saidawa abinci Christian ne, tana kwance tana sauraron sanarwan auren dan tsohon shugaban kasa dazaayi sati mai zuwa aka aiko kiran ta, da sauri ta mike tsaye dukda ta fidda ran zuwa Salem, almajiri na sallama ranta ya bata shine, mami dake kwance kurya tace
"tawa tani?" Maana waye?
"Mami ban saniba bari in leka in gani" ta amsawa mami tana fita daga dakin ko gyale babu jikin ta don Allah 2 take taga mai kiran ta, sanye take da atampha wax dinkin skirt da blouse, fuskanta ko powder babu Amman she's not looking bad, dankwali kawai ne kanta, already almajirin ya fita, ahankali tayi sadaf2 ta taho ta tsaya bayan kofan su tana leken mai kiran ta, a lokacin Salem na tsaye jikin motan hannunshi biyu cikin aljihunshi yana sauraren abinda almajiri ke gaya mashi, tawa na ganin shi ne ta saki wani kayattacen murmushi, shikam Salem baisan tana tsaye wurin, juyawa dazaiyi kofan gidansu sai sukayi ido hudu daita, da sauri ta maida kanta tare da jinginawa jikin bango hannunta dafe da kirjinta dake harbawa da karfi, idanuwa ta lumshe at the same time tana murmushi.
Shima Salem murmushi yayi don yaga irin kallon datakeyi mashi
"You also love me.." Ya fadawa kanshi sannan ya taka zuwa kofar gidan, itakam tawa har lokacin tana tsaya bayan kofan still hannunta kan kirjinta sai cizon lebenta na kasa take tana fidda numfashi ahankali, Salem Dan lekawa yayi yaganta, idanuwanta rufe don haka batasan yana wurin ba , kallon ta yayi from head to toe
"Beauty in disguise.." Ya fada cikin ranshi, tawa bude ido tayi ahankali aikam suka karayi four eyes aikam da gudu ta shiga gida tare da shigewa dakin su, yabi bayan ta da kallon sannan ya sake cewa
_"Perfect shape_ ".

"tani?" Mami ta karacewa, ahankali tawa dakenishi tace "mami mutumin da zan raka kasuwane " tawa ta amsawa mami, kurya dakin ta shiga ta bude wata katuwan ghana most go ta fiddo hijjab Amman ba mai tsawo ba, ta saka sannan ta saka wani flat shoes Wanda kudin ta bazai wuce 1500 ba ta saka, batare da shafa wani abu afuskantaba ta fito tare dacewa mami bari inje
"wurin shi", da sauri mami tace
" kice mashi ya shigo ciki ke ba bahaushiya bace dazaki tsaya rabe2 a waje"
"Yes mami" ta amsa mata sannan ta fita.
Har lokacin Salem bai bar wajen ba, tana fitowa ta durkusa har kasa sannan tace
"Ina kwana?" Mamaki ne ya kama Salem don tunda yake bai taba ganin budurwan da zata kai akalla 18 ta durkusawa saurayiba, da sauri Yafara kalle2 kar mutane su gansu sannan yace
"Oremi tashi mana" yafada ahankali,
"Ai baka amsaba" ta fada muryan ta na rawa
"Lafia lau..please tashi" sai lokacin ta mike Amman kanta kasa tace
"Sir kashigo ciki" cikin zolaya yace
"Ya mukayi dake?..banace banason kina kirana sir ba?" Dan murmushi tawa tayi Amman still bata daga kanta ba tace
"Sorry.. Oremi ka shigo ciki" tsaya kallon inda take avoiding gaze dinshi yayi sannan yace
"Yau tawa kunya ta kikeji ne..kodan na kamaki kina lekena?" Ya fada cikin funny tune,
"Ni ba lekenka nekeba.." Tafada still muryan ta bai bar rawaba, ya gane dalilin rawan muryan ta, yasan hakan na faruwa in mutum yayi maka kwarjini,
"Please ka shigo ciki" ta kara gaya mashi,
"OK" ya amsa mata, juyawa tayi tashiga shikuma ya bayan ta yana tunanin abubuwa daban2 cikin zuciyanshi, yanayin gidan ya kalla yaga gidan talakawane sosai don mutane dake gidan duk talakawane da ganinsu, yarane ke tawasa gidan, daki tawa tashiga shima ya shiga, kallon dakin yayi yaga bakomai sai kujerun roba guda uku sai ledan daki, Amman dakin ko kadan babu kazanta, daya daga cikin kujerun ya zauna, daki tawa tashiga yaji tana kuskus sannan ta fito ta kara fita waje, Salem kam tunani yake
_"Anan princess dina ta rayu...ranakun wahalanki a numbered"_yafada cikin ranshi, gani yayi wata mata tafito daga cikin dakin, sauka yayi daga kan kujrean dayake ya durkusa ya gaidata cikin girmamawa amsawa tayi da murmushi fuskanta har iyayenshi ta tambaya ,sannan ta juya zata koma ciki Dan kara juyawa tayi ta kalleshi sai ta lurada yanda hannuwanshi da kafafunshi suke fari kal sai tayi tunanin kilan wahalan rayuwa ne yasa fuskanshi baki.
Bata dade da shiga dakiba tawa ta dawo, maltina yaga ta ta fiddo daga cikin ledan hanunta, Dan murmushi yayi sannan yace
"Irin wannan tarban haka.." Murmushi kawai tawa tayi tashiga kurya ta dauko wani plastic cup ta Juye maltinan sannan ta durkusa ta mika mashi, amsan cup din yayi tare da hadawa da hannunta, da sauri ta janye hannunta saboda wani taushi da shocking dataji.
๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ9โƒฃ

Tawa komawa tayi ta zauna har lokacin bata dainajin shocking ba, Salem murmushi yayi ya kai cupin bakin shi, wani irin daci yaji don tunda yake wannan ne karo na farko daya sha maltina, hadiyewa yayi, sai yaji makogaron shi nayi mashi zafi, cikin ranshi yafara cewa
"Allah yasa kada wannan abun ya zama ajalina" da kyar ya kara sha akaro na biyu fuskanshi kaman na mai shan giya. Gefe ya ajiye, tawa kallon shi tayi
"Sir ka shanyeshi.."
"Indai bakison daukan gawata kin barni haka nan" yafada cikin ranshi sannan yadan harareta
"Nagode" saida ya Dan goge bakin shi da bayan hannunshi sannan yace
"Oremi dauko pen Muyi list din" mikewa tayi tashiga ciki, few minutes later ta dawo da pen da paper. Zama tayi kasa a gabanshi zata fara rubutawa yadan taba kafadanta ta daga kai, alama yayi mata dasu tafi waje, girgiza mashi kai tayi , shikuma yace
"Please" da ba kowa zaijiba, mikewa ta karayi tashiga ciki tacewa mami sun tafi kasuwan
"Ku dawo lafiya" yaji mami tace cikin hausanta mara fita, tawa tafito
"Mu tafi" ta fada mashi murya chan kasa, kaman yana jira ya mike har ya rigata fita tabi bayanshil.
Yana fita ya bude mata murfin mota Amman taki shiga
"Ki shiga mana" ya umarceta,Dan girgiza mashi kai tayi
"Ka rufe in bude da kaina" Dan daria yayi
"Laifine mutum ya budewa budurwan shi mota.."
"Ni ba budurwan ka bace.." Ta katseshi tana murmushi
"To laifine mutum ya budewa friend dinshi mota?"
"Ai ka girmeni.."
"Nasani Amman inason bude maki cos you are a lady" gyara tsayuwanta tayi
"To mu kwana anan" bashi da choice dole ya maida ya rufe ya zagaya yashiga cikin ranshi yana tunanin
"Daman haka suke kodai she's just kidding with him" shiganta cikin motan ya katse mashi tunani.
Kallon ta yayi
"Oremi please taimakamin zakiyi..kiyimin list din abubuwan da mace kamanki zata bukata in ita kadai ke zaune kuma bata fita" tawa kallon tuhuma tayi mashi sannan tace
"Ban gane ba?" Dan murmushi yayi
"Sister ta nakeson yiwa siyayya"
"But kace boarding school zata" dan shafa keyanshi yayi don ya mance daya fada mata hakan,
"Oh sorry..Ashe hakana gayamaki..daman aure zatayi to mijin bashi da ko sisi so sai nayi niyyan siya duk abubuwa dazata bukata" baki tawa ta bude don sai ya burgeta
"Amman gaskiya kana da kirki".
" kafin kisanabinda zanyi da kayan kenan" yafada cikin ranshi
"Meyasa kika fadi hakan" ya tambayeta, ahankali tace
"Ai naga kaima hustling kake Amman kasan ciwon yan uwanka" murmushi yayi tawa yacigaba dacewa
"To kayan abinci kawai zamu rubuta?.."
"Aa..dukkan kaya harda nasawa..Amman masu sauki na talaka"
"OK" kawai tawa tace sannan tasake cewa
"Bari mu fara da kayan sawa..atampa bawa zan rubuta" Salem shuru yayi kaman mai tunani
"To..ki rubuta shida..Amman kar kudin su yawuce
2k" ba musu tawa ta rubuta sannan tace undie nawa
"Uku each" tawa ta rubuta pant da bra uku,
"Gyale fa" ta tambayeshi, Dan girgiza kai Salem yayi
"Ai cikin gida take babu inda zata"
"Ok..zaka saya da shadda da lace ko materials?"
"Gaskiya bani da kudin.."
"Turare fa?" Tasake tambayanshi
"Matan kauye basu shafa turare sai Ku Matan birni" yafada
"Matan birnin ma sai masu halin" tawa tafada cikin ranta
"Kayan kwalliya fa?"
"Bandasu"
"Amman at least ka sayamata man shafawa ko?"
"To rubuta mata Wanda kike shafawa indai bashi da tsada"
"Cocobutter ne kuma karamin 600"
"Rubuta mata babban" ta rubuta
"Yan kunnefa?" Ta sake tambayanshi
"Nawa kudin na kunnenki?" Ya tambayeta yana nuna bariman dake kunnenta
"250"
"Babu Wanda kudin ta bai kai hakaba?"
"Da akwai mana..har na 70 naira da akwai"
"Kirubuuta na 70 guda biyu" ta rubuta.
"Mun gama da kayan sawa now kayan aikin gida..set din tukunya zamu rubuta?" Ido Salem ya zaro
"Me zatayi da set..kawai rubuta kwano, cup , spoon, pot, knife,.. Hmmm saime kuma..rubuta bibbiyu " duka tawa ta rubuta su
"Yarda broom da dustbin ko?"
"Eh yauwa na mance su..".
Haka tawa ta dinga lissafa mashi kayan aikin gida suna rubutawa,
"Sai su gado da kayan daki" inji tawa
"Wane irin gado..kawai rubuta student foam sai ledan daki sai curtains masu sauki don ba kudin gareniba" ta rubutasu
"Sai abinci" tawa ta fada mashi
"The fun part" ya fada cikin ranshi, kallon ta yayi sannan yace
"Kaman ke kina iya cinye buhun shinkafa cikin wata hudu?" Ya tambayeta, ido ta zaro
"Kam ina hauka?..gaskiya bazan iyaba...why do you ask?" Dan jinginawa yayi sannan yace
"Ai don insan irin yawan rice din da zan saya mata,..lissafamin kayan abinci in gani..ki dinga rubuta su"
"OK" ta amsa mashi sannan ta fara rubutawa tana cewa
"Rice, macaroni, spaghetti, indomie.." Da sauri Salem ya katseta dacewa "banda indomie...ni ban ciba balle in sayawa wani...cigaba" Dan murmushi tawa tayi sannan tacigaba
"Garin tuwo, kuskus,.." Salem ya kara katseta
"Nifa ba kayan birni nace ki rubuta ba..kawai rubuta irin garin danwake, alkubus.." Kayan gargajiya Salem ya dinga lissafawa kaman yana cinsu itakuma sai rubutawa take.
"Sai kayan miya..." Ta fada mashi bayan ta kammala rubuta kayan abinci
"To ki fadesu inji" Salem ya amsa mata yana kallon bayan wuyanta da ya dana bayyana, wasu kananun gashi yagani kwance har bisa gadon bayan ta, sai yaji tana cewa
"Kuka, egusi..tasshi, maggi, gishiri,albasa..." Suma haka ta rubuta su, data rubuta mai tsada Salem yace ta gogeshi don bashi da kudin siyansu.
"Mun gama..." Ta fada mashi,
"Kawo su in gani" ya fada mata yana lumshe sexy eyes dinshi kaman mai jin bacci, mika mashi tayi, amsa yayi ya kara hadawa da hannunta, wannan karinma janyewa tayi da sauri, saiyaga ta hada giran sama sana kasa
"Sorry..mistake nayi" yace mata, batace komaiba, kallon list din yayi
"Wow..kina da fine handwriting..ki gama uni ne..?" Kallon shi tayi for few seconds sannan ta sada kanta kasa
"Ka taba gani degree holder yana saida abinci a restaurant?" Shuru yayi bai bata amsa ba tacigaba dacewa
"Ka taba ganin talaka yayi degree?" Salem saiyaji jikinshi a mutu
"Nayi maki alkawarin zaki gaji da karatu" ya fada cikin ranshi sannan yace.
"Ai with Allah komai ma is possible" yafada ahankali
"Hakane" ta amsa mashi sannan ta kara cewa
"Amman kai kayi karatu sosai" dan murmushi yayi sannan yace
"Kin taba ganin degree holder yana tukin taxi?" Tawa dan daria tayi
"Ai Nigeria kenan everything is possible..Amman seriously kayi karatu"
"Meyasa kike ganin kaman nayi karatu?" Ya tambayeta
"Ai naga turancin ka mai dadi" nikam nace dan baki ganshi a office ba.
"Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login