Showing 102001 words to 105000 words out of 189081 words
na kai miki” Ammi tafice ruwa mai zafin gaske takai mata abayi da botiki daya daban na sirki sannan tadawo ganin Hawwa tayi harta cire kaya tadaura zani tasa another hijabi daban, Ammi tabi daki
n da kallo tace “ina kayan da kika cire na bada awanke”? Dasauri tace “uhmm ahh suna cikin akwati na ki barshi zan wanke” Ammi tace “toh muje” kamata tayi daurewa tayi tabi Ammi har bayi ta kaita Ammi tai murmushi kadan kawai ta dawo tadan gyaramata gadon
ta kakkabe taje tadawo da ita daki kuma tafita, Hawwa tacire hijabinta ahankali tadauki ribbon ta kulle gashinta dayake sharkap tadauki dankwali na atampa ta kulle kan kar agane da ruwa, dogon riga har kasa na abaya tasa ta kwanta sai bacci.
Khaleel yadi
nga kiranta rannan taki dauka tama maida wayan silent mode, rannan bacci tayi da daddare mai kyau har gari yawaye ko farkawa batayiba batasan me Khaleel yayi ba but dai kaman ta zubar da abinda ke damunta da daddare.
Da sassafe yau Wednesday aka fara shir
ye shirye henna day, still tayi using hot water zafin yaragu sosai tasoma dainaji, an aiko da bridal dresses nata jiya da daddare, tayi wanka kenan tana cikin saka HKG atampan dasu Hafsa suka fito mata dashi daga akwatinta na henna party Aminu ya shigo yac
e “Ya Hawwa Khaleel na waje yakawo miki Noor” faduwa gabanta yayi sosai dan kallonshi tayi sai kuma tace “okay” kanninta ko wanne yashiga makale dariya shikuma Aminu da gulma yace “suna miki dariya Ya Hawwa” kallonsu tayi aiko suka bushe da dariya Hafsa ta
ce “ayiriri amarya” hararansu tayi tadauki gyale maroon tayafa kan atampan wlh tayi kyau tana tafiya ahankali sai kanshi take tayi waje, a zaure taga Khaleel da Noor da katon box na kayanta, tana ganin Hawwa tai wani ihu tai tsalle Hawwa ta dauketa tana mu
rmushi Noor tace “My FAA” haderai Khaleel yayi yace “careful Noor stop rough handling my wife kaman yanda kikemin batada karfi kaman ni, besides she’s sick” dan hararanshi Hawwa tayi batare data kalleshi ba tana kallon Noor tace “don’t mind him your FAA ha
ve power” kankameta Noor tayi saikuma ta mata kiss a kumata tace “I love you soo much FAA, you look super duper beautiful right Dad”? Khaleel na kallon Hawwa kaman zai hadiyeta yana tuna abinda yafaru jiya tsakaninsu yace “right princess, she’s beautiful e
xternal and internal” sauketa Hawwa tayi da sauri tazo wajen takai hannu zata karbi akwatin Noor sabida su koma ciki kafin yafara iskanci wannan daya fara maganan banza gaban yarinya kawai Khaleel yajawota zuwa jikinshi and just give her a tight hug daidai
Baba da Aminu na shigowa zauren hakama kanninta su Hafsa kawai suka fasa ihu. “Wuyuuuuuuhuuuu” Baba yawani kume murmushi akunyace Hawwa ta fizge kanta kaman zata nutse akasa ganin Baba da kanninta sunga yanda yake rungumeta, Baba yama su Hafsa dakuwa yace
“kunci gidanku me kuke haka”? Noor sai washe baki take tana kallon Dadynta da Hawwa, Hawwa tai sauri zataja jakan wlh Khaleel yakasa daurewa dudda gasu Baba kaman wanda Hawwa tama magana yakama hannunta yace “karki tafiiiiiii” awani shagwabe sai kawai su
Hafsa sukahau “ayiriririiiii” Baba yadan kwashe da dariyan manya kadan yadaga sanda zai rapka musu suka kwasa aguje sukai cikin gida Baba yace “Noor muje na kaiki dakin
Mamanki tunda Babanki na magana da ita” dasauri Noor tabi Baba hakan yasa Hawwa tajuyo
cikeda masifa still taki kallon idanunshi tace “mehaka kakemin gaban mutane”? Kaman zaiyi kuka yace “I’ve missed you, baki daukan wayana, baki magana dani why? Mena miki wai”? Akufule Hawwa tace “I don’t accept you, I don’t accept wannan auren, ban sonka n
agaya maka” shiru yayi yana kallonta yakasa magana, kawai Hawwa ta fizge hannunta da jakan tawuce cikin gida abinta, nan fa aka fara henne party ga komi Juzzyfabevent event takawo, hatta su zubo da bottle water, kunun aya, popcorn amsaka sticker sunan Haww
a da Khaleel so lovely, matan ta iya decoration da kowa yashigo mamaki yake compound din gidan Baba Juzzyfabevent ta komar haka, she sabi the job. Ana playing waka compound na Baba da girma so set up yayi kyau professional masu henna da aka kawo suka fara
mata ana rawa, Noor na rawa dasu Miemie, Hawwa sai kallon Noor take tana kama da Khaleel tanada kyau kaman shi, dasauri ta girgiza kai tana gayama kanta me ruwanta da kyawunsa, duk wnada keson lalle zama kawai yake amai, Hawwa kawai bin kowa da kallo take
especially yan uwanta barinma Ammi da Baba, Ammi stood as her Mom, komi ita keyi, ita ake tambaya, yan unguwan na Maman Amarya kawo gishiri, kawo omo, abada this and that duk haka suke kiran Ammi, Baba na farin ciki bini bini yashigo yaduba zanen da akema
Hawwa yatafi yakara dawowa yace amata mai kyau, yasake dawowa yace azana sunan Ibrahima atafin hannunta, har aka faramai dariya, Hawwa kawai taji kuka na taso mata, she wish aure ne da mutumin arziki wanda yasan darajan mace, all this prep, farin cikin da
Baba keyi, dasu Ammi da yan uwanta Allah yasa tamayi 1month bai saketa ba.
EPISODE
Har dare party akeyi bamatasan yaushe aka sai generator agidan ba, itafa komi yi akeyi batasan ya aka samu ba dan su Ammi sun daina sata a lissafi maybe Khaleel yakaw
o, wanka tayi Munawwarah ta turareta ganin su kadaine adakin tace “Ibrahima yadan rage miki jaraban ko”? Kunya kama Hawwa tayi ta sauke kai kasa da gangan taba Hawwa wani magani a cup dudda Ammi tace adakata a daina bata haka Hawwa tasha tana tane baki suk
a gama komi tawuce taje gado, yau su Ramla ma sun sauka kasa daga ita sai Noor, Noor is so happy kaman ba yar gidan
masu kudi ba, Ramla sun mata wanka tasa kayan bacci suna wasa kowa na son yarinyar she’s so sweet, abubuwan da aka samata a box ma bataci ba
, tuwo da miyan kuka da aka dafa agidan taci cikinta kaman zai fashe saida Hawwa tama hanata ci ta hakura.
Kiranta Khaleel yahauyi awaya taki dauka, tai lamo tana sauraron su Hafsa dake planning dan gobe bridal shower kanninta sai planning suke tana kallo
nsu ita yar kallo ce kawai.
Washe gari Alhamis aka fara baki yan uwa da abokan arziki, yan uwan su Baba daga kauye sunzo wayanda ko bikin su Hafsa ma basu zo ba amman anzo na Hawwa, yan uwan su Ammi ma haka sunzo yan Bauchi kuma sun nunama Hawwa tanada da
ngi, sun kawo waina tundaga Bauchi, ga yan uwan Baffa ma mijin Ammi duk ya gayyacesu duk anzoma Ammi biki, gida ya kachame abubuwa kawai ake kawowa drinks, menene, menene, banda girkin dasu sukayi Juzzyfabevent suma sunyo abinci cus they also handle cateri
ng services, babu kalan abincin da babu, kowa dazaizo yanada gifts, ko yaushe akai wannan planning din oho yan uwanta suma kowa ya gayyaci mutanensa da friends nasa, Aminu ma ya gayyaci abokansa na school dudda babu daurin aure akwai event.
Wuraren 4 aka s
hiryata makeup artist tazo Hawwa sai kallon ikon Allah take dan batasan daga ina takeba kowa yaturota akama Hawwa makeup aka shiryata cikin gold gown kunga Hawwa aka fara rawa kawayen kannenta ne kawayenta dan batada kowa ga DJ, ga masu hoto ga MC, ga jama
’a ga abinci akai wasa akai quiz akan amarya aka gama games na balloons, it was fun, Hawwa tagaji still taki waya da Khaleel.
Yau Friday budan kai a hall za’ayi tun around 1 motoci luxurious bus na yan gayu sukai layi a unguwan kai mutane zuwa venue ga ka
ya an kawoma duka kanninta ashobe harda su Noor ga kayan Ammi na yan gayu, kasa daurewa Hawwa tayi tace “waya muku kayan nan”? Doddo tace “mijinki duka harda kayan ranan asabar yama kowa da takalma da jaka, wasu ma’aikata sukazo suka aunamu muma mu zama ya
n gayu” shiru Hawwa tayi aka shiryata cikin wani traditional clothes na atampa blue light and dark daya mata bala’in kyau ga katon lullubin atampa da aka dauramata akai, da Ammi tashigo taga Hawwa sai hawaye yataru a idanunta duk yanda taso ta daure saita
fashe da kuka Hawwa tafashe da kuka itama Ammi tace “inama Mamanki na raye taganki Hawwa kinyi kyau Allah miki albarka, Allah sanya albarka a aurenki” kankame Ammi tayi da kyar aka hanata kuka aka gyara makeup din kafin finally aje asata awani arnen sabon
jeep gal aka tattafi Umma kawai aka bari agida da
Baba, Event aka fara harda yan uwan su Khaleel but banda Mom but Maman Sam da Hajiya Daraja na wajen, duk wanda yazo daga side na Khaleel dadan korafinshi Khaleel na auren yar gidan talakawa ya auro da akag
a Hawwa sai ayi shiru cus Hawwa ta hadu ba karya, Khaleel carry better eye go market, chan akai annoucing zuwan ango yaye lullubi, waka aka saka na burina by Hamisu breaker saiga Khaleel yashigo yana sanye da dark blue yard da babban riga dayamai kyau na b
ala’i yasa hula ga manyan abokanshi Moh da Sam da sauran abokanan all in white da black huluna kana ganinsu ka ga big boys, mic yarike yana murmushi yana kallon Hawwa yafara mata wakan yana nunata da hannu filled with love ba kunyan iyaye yace.
Babban buri
na ki kasanche dab da ni
In za ki kirga masoya ne ki sanyo dani
Ki duba kan ki ana kallo na majanuni
Ni kuma nace indai kai naki ne ban fadi ba
Sako ya bayyana ni tun daga zuciya
Sannan kaunar ki tana kaman zuciya
Kin kama mini kurwa ta tun jiya
Har ya kai
matsayin bana samun lafiya….. yawani nuna kirjinshi yace
Kin shiga raina
Kin zauna dan kin sami guri
Naji kiranki
Na amsa kuma nazo da wuri
Kece farko kuma kece karshe
Bishiyar nan tai girma wadda kikayi mini dashe daidai ya iso gabanta yawani duka yana
kallon fuskanta yanuna kanshi yace
Bana ji bani gani bana son mai kushe
Buri na rayu dake har numfashin karshe
Kin rikita duka tunani na
Taimaka ki bani gurin kwana
Son ki ya hana mini bacci na
Ina ganin ki har a mafarki na
Son ki yanai mini dadi ban son
mu rabu
Ki jaddada jarumta ta ki nadan kambu
Bani da komai sai ke
Ina tafe ya wa wani falke
Ina duhu ki kunnan haske
Ina na je dake?
Ihu akahau yi na bala’i awajen na Khaleel is super romantic, he’s just madly in love da Hawwa, yamika hannu Moh yabude jaka
n LV dasuke rikeda shi yafara zubama Hawwa dollars Mom Sam tarike baki da sauran
kawayen Mom like dama Khaleel ya iya soyayya haka? Ya iya wakan hausa haka wat? Rufe Hawwa sukayi da manni shida abokanshi, MC tace “abudemai fuskan amarya” Babban Aminiyan Am
mi Anty Lami ta zo tabudemai fuskan Hawwa fuskan Hawwa da Khaleel yagani kawai saiya rungumeta baimasan meyake ba zokaji ihu DJ yasaka musu kida MC tace “Ango fito da amarya ku taka” dayake kamu ne wakokin hausa ake sawa komawa baya su Moh sukayi Hawwa bat
aso ta tashi amman haka Khaleel yadagata yana rungume da ita kunya ya gama kasheta, yafito da ita dance floor kanta akasa daidai DJ na sakin beat yasaka wakan Mai kishina na Sadiq Saleh kaman Khaleel aka samawa kawai kama hannun Hawwa yayi yawani jawota ji
kinshi yakama waist nata ko kadan baida kunyan iyaye, Hawwa namai wani irin kallo da jama’a ke gani na soyayya ne but shi yasan na haushi ne dana mehaka, yawani lumshe mata idanu yana daga mata gira daidai anfara wakan yace”
uhm Uhmmmmmmmmmmmmmm
Uhmmmmmmmm
mmmmmm
Uhmmmmmmmmmmmmmm
kunga inajin dadi
inajin dadi na samu muradin raina tana kishi na nidai
kunga inajin dadi inajin dadi na samu muradin raina ya na kishi na nima
Uhmmmmmmmmmmmmmm
Uhmmmmmmmmmmmmmm
sonki ya fattatakenii harna durkusa shiya addabeni har
yasa na fallasa Ni Dake mu raini so takai mu kyankyansa nayi binciken kamarki babu na rasa”
woooo haukacewa akayi a hall din kawayen Mom su Hajiya Daraja da Mom Sam suka taso ana ciro bundle na kudi dan Khaleel da Hawwa sunyi kyau, abokannan shi suka taso
su Ammi da Jama’anta suka taso dan Khaleel yabama Ammi sababbin kudi dayawa bana wasaba tai manni cus itace Maman Amarya, Khaleel ganin an tattaso za’azo kawai yawani bude babban riganshi yajawo Hawwa cikin jikinsa yarufe babban rigan da ita yana rawa.
Tundaga kan Abokan Khaleel da family shi babu wanda yataba ganin Khaleel this happy, su Moh at first sun dauka this marraige is just to teach the police girl a lesson but yau different abu suke gani a idanun Khaleel cus this is love! Khaleel has never been
this happy, sosai Hawwa take kallon Khaleel ganin farin cikin dayakeyi and he looks damn handsome bata taba ganinshi da manyan kayaba sai yau.
EPISODE
Wajajen 7:30 aka gama kamun su hafsa kanninta da Khadija wanda sune suka dawo best ladyn Hawwa su
ka kaita jeep ganin Khaleel na cikin jeep din yasa tahade fuska ta shiga ta zauna suka rufe kofa suka wuce tasu motar, Driver yaja motan Khaleel yakai hannunshi zai kama hannunta dayasha lalle ta dauke hannun dasauri maida hannunshi yayi back sai kawai yac
iro wayanshi yataho inda take yawani jawota zuwa jikinshi yamusu hoto tana turomai baki sannan yasaketa yace “lemme post it on insta all those girls Susan I’ve been taking ga yar sandan data kwance musu ni” hararanshi tayi shima bai kulata ba ganin kumbure
kumbure takeyi kiris take jira so he’s going to be patient daga gobe ne on Saturday ware haka an kawomai ita gidanshi har gida sukaje da kanshi ya sauko yabude mata mota yamika mata hannu danta rikeshi ta sauko sabida gown nata ta kabar da hannunshi ta sa
uko ahankali abinta tawuce shi tai cikin gida yabita da kallo dakinta tawuce Ammi kadai ne tana kwasan some jakan gifts ganinta yasa tace “kun dawo Amaryana” adan kunyace ta sauke kanta kasa tace “Ammi zip” ijiye bags din tayi tazo tashiga jamata zip tana
kwance mata head tace “Hawwa Khaleel na miki matsanancin so kinga hakan kuwa?” Shiru Hawwa tayi tashiga cire kayan tana mamaki inasu Noor dasu Ramla da Miemie, Ammi tace “suna gidan Malam Sama’ila wajen yammatan gidan wai harsunyi kawaye, bari na sallami b
aki na” Gyadamata kai Hawwa tayi tana mamakin duk inasu Hafsa wannan da dakinta is empty.
A uwardaka duka suka zagaye mahaifiyar tasu dake zaunw abinta tana duba wani azkar, daga Aminu har Hafsa, Kadija da Rahama Mimie ce kawai babu wajen suma sabida yara
ne. Anatse Aminu yace “Umma this is your last chance akanme zaki rike Hawwa aranki kan abinda ba itane tamiki ba? Bata duniya akayi? Ni aganina koma menene mahaifiyarta tamiki base on abinda yarinyar nan tamana yaci kin hakura kin yafemata, Umma school din
a kap zuwa yau dana gama Hawwa ce babu kwandalan Baba, gasu Khadija, Hafsa da Rahama su basuyi university ba amman Hawwa ce ta aurar dasu Baba baida ko sisi kudaden Hawwa ne akayan dakinsu, banda haka akai akai take turamanakudi takirasu ta
tambayesu yaran
su, Mama kinga makarantan masu kudi da Miemie keyi Hawwa ce Umma menene wannan abun wannan wani irin tsana ne eh Umma” ahankali Hafsa tace “Umma dukanmu yaranki mun hadu yau muna miki fada muna nuna miki gaskiya bazaki dauka ba?” Khadija da duk tafisu zuci
ya tace “kai wlh Umma Allah karya bani bakar zuciya irin taki” dasauri Umma ta kalleta saikuma tafashe da kuka tace “ohh nice mai bakar zuciya ba Mahaufitae Hawwa data rabani da baban ku ba, nakasa auruwa sai bayan tarasu yadawo yawani aureni kuna cemin ka
za kaza, ina mahaifiyarku baku sona kin fison Hawwa shikenan na barkı da Hawwa gaku ga ita kufitarmini daga daki” shiru Aminu yayi saikuma yace “shikenan Umma bazamu tursasaki kiyi abinda bakiso ba, kituna Allah yana tareda masu hakuri, sannan Allah baya k
ama laifin wani da wani, banda haka Umma shi Allah yanada adalci” yawuce yafita, su Hafasat suka bishi abaya dakin Aminu duk suka shiga.
Hawwa na zaune kan dadduma tareda Noor sun idar tana koyama Noor azkar yarinyar is 4 amman wai bata zuwa islamiyya sa
nnan babu mai koya mata agida, Baba kuma na hira da Ammi da Dado da Anty Lami Miemie da Ramla basa dakin sallama akayi Aminu ya bude kofan dakin yashigo dawata katuwar kwali na LG washing machine saiga su Hafsat duka biye dashi Hawwa tabisu da kallo Ammi t
ace “a’ah wannan kuma menene Aminu haka”? Dan murmushi yayi yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Ammi hada kudi mukayi muka saiwa Ya Hawwa washing machine na tambayi Hafsa tace shine kadai baku sayo ba dakukaje sayayyan kayan daki” yadanyi shiru yakalli Hawwa
ahankali yace “Ya Hawwa I wish nafara aiki and I wish I can afford more than this wlh Ya Hawwa zan iya baki duka duniyan nan kin chanchanci haka”dakin kowa yayi tsit yana kallonsu, Ahankali Hafsa tashare hawayen daya zubomata tace “Ya Hawwa baki taba kall
onmu kaman yaran kishiya ba, ko ki kallemu da abinda Umma take miki, Ya Hawwa da Baby Minal na ciwo bataci abinci ance a asibiti she is under weight Babanta baida kudin soyamata abinci” tai dan shiru saikuma tafashe da kuka sosai tace “Ya Hawwa kadaice taf
ito da kudi tadinga siyanma Minal abincin yara daban daban, kala kala, wlh babu wanda bata siyamana ba, cerelac su gaber rice babu kalan abincin yara da bata soyama Minal ba har yarinyar tazo tafara ci tanata kumari” ahankali Hawwa ta tashi dagakan dadduma
idanunta yayi ja kanninta are making her emotional, Hafsa tace “I wish kowa aduniya zai sami big sister kaman Ya Hawwa, she takes care of dukanmu zuciyan Ya Hawwa daban ne, she’s too good” hannu Hawwa tabude mata dasauri Hafsa ta rungumeta tsamtsam a jiki
nta su Khadija