Showing 27001 words to 28895 words out of 28895 words
hanunta rike da leda
Sabeer tausayin su yakeji hakama Fahad
Saida yusrah tayi kuka Mai isanta kafin tayi shiru
Tatashi Ido a kumbure yusrah tace waziri da maimuna Allah ya Isa tsakani na daku kuncuce iyayena kuncuci umma na da kakata Allah saiya saka musu Kuma kusani asirinku ya tonu
Dama ance inzaka Gina Ramin mugunta kaginashi daidai Kai Amma kun Gina Wanda yafi karfinku
Yusrah tace aminiyata Miko ladar hanunki
Ansha kasar yusrah wacce tayi amfani da face din yusra tatashi takawo Mata ledan
Yusrah ta zazzago abinda yake ciki layune dakuma Killin leda Mai dauke da gashin da ake bukata
Yusrah takalli abban ta tace Abba wannan gashinkane da na umma Tamika mishi yabude tabbas kuwa hakane mamaki yakamashi
Bai ankaraba yaji takara cewa abban wannan ma gashin Kane Dana matarka shima Tamika mishi
Tunaninsu ya akayi suka samu gashin su
Wani leda tafitar shima gashin ne aciki tace wannan Kuma gashin wa innan azzaluman ne dasuka cutarmin da iyaye
Takalli waziri da maimuna da buhari Wanda gaba daya hankalinssu baya jikinsu
Sannan taciro wani laya da garin magani tace
Abba umma Mai martaba dakuma umman abbanta
Tace wannan maganin da kuke gani anbani ne Akan nayi kokarin na hadashi da gashinku nakone
Idan harna konesu to tabbas kingama Shan iskar duniya
Anyi asirin da ba Mai iya warwareshi Sai Allah sannan Kuma Ni inzama sila
Inhar bani nanemo wa innan maganinva to bayadda za ayi su umma susarke sukoma kamar da
To alhamdulillah Allah yakawo Mana komi cikin sauki
Yusrah taci gaba dacewa Abba inbaku mantaba nataba cemuku zandawo Amma kuyi hakuri da halin da zancanza
Alokacin kawai nafada ne Amma bansan me zan aiwatarba sabida
Watarana nazo hutu natafi ingaishe da wannan makirar matar wato maimuna
Sai naji suna kulle kullen yadda za ayi akasheku Dan wannan tsohon muna fukin ya hau mulki
Koda naji maganar sai hankalina yatashi alokacin kamar zan juya nakoma Amma saina fasa sabida wasu kwararan dalili Wanda Yaya sabeer yake koyar Dani wato tauheed
Danagama saursrsnsu nakoma lambu nazauna nabasu kamar minti 30 kafin nashigo gidan da murna na rungume wannan munafukar matar
Ahaka kullum burina nasan abinyi Amma nakasa sanin komi Dan Haka kullum sainayi salla da addu.oi Akan Allah yakaremin iyayena
Ahaka harlokcin komawata kano yayi nakoma Amma kullum a cikin tunanin ku nake saidai Yaya sabeer yariga yakoyar Dani tauheed Dan Haka nakara amincewa da cewan Babu Wanda ya Isa yacutar da bawa batare da yaddan ubangijiba
Ahaka zucciyata take tafiya kullum Dan Haka nadogara da Allah
Watarana inajin daddy Yana waya Yana tambayar jikin ummana da umman ka Koda natamvayeshi saiyace Wai ummana zazzabi kedamunta Amma da sauki Dan Haka na hakura Amma alokacin kullum acikin muggan mafarkai nake
********
Yusrah taci gaba dacewa tunda nagama secondary nake ta planning yadda zancimma burina gurin ganin nakawar da sharrin da ake son kullawa awannan masarautar Mai tarin albarka
Kai tsaye abokin shawarana nanema wato Yaya sabeer nasanar mishi abinda akeciki
Tare muka zauna muka shirya planning yadda zamu samu motona ma wa innan makiran asiri ta wannan hanyar da na bullo muku
Yusrah tanuna Aisha tace Abba wannan qawa tace wacce mukayi secondary da ita tun daga jss one tasan komi nawa nasan komi nata Dan Haka takuduri niyyar taimaka min da ita Mike shawara hakama Yaya sabeer da amininshi
Dan Haka Koda nsamu makatanta a kasar waje bakaratun yakainiba Yaya sabeer yanema min wani malamin da yakoyar Dani addu.oi da yadda zan fuskanci makiya sukasa gane a irin suffar da nazo musu dashi
Dan Haka namakda hankali na ga abinda naje koya Haka Kuma alhamdulillah nayi sa.a sosai
Innagama wannan training din na dumfaro gida anan nasoma aiwatar da duk Shiri na
Dukwani Abu da kukaga nakeyi dama nariga na tsara shi ko ince muntsara
Abba sabeer tare dashi mukaje neman maganin kauci alokacin da naji munafukin Nan Yana fada ma munafukarnan wato waziri da maimuna
Nanne na umurci Aisha wacce take acting a matsayina takulamin daku
Kuma alhamdulillah tamin yadda nakeso Dan Haka komai namu take tafiya
Haka Yaya sabeer dayasa fuskan abokinshi shiya taimaka gurin wasu abubuwa da dama Haka abokin nashi yajiyo Mana surruka da dama Wanda takai ga yanzu muncinma burinmu
Alhamdulillah Abba komi yayi daidai komi yatafi yadda akeso
Abba dakaina nahau bishiyar dalbejiya Dan ganin iyayenmu sunsamu lafiya
Anan yusrah tasanar dashi yadda tasami bishiya da irin hadarin da tafada
Yusrah tace Abba Koda nayi nisa da Fara hawa bishiyar harnakai tsakiyar wani aljani yace tabbas kincika sadau kakkiya akan iyayenki Dan Haka zan taimakeki
Banganshi ba kawai alokacin naji komi nawa yacanza SAINAJI kamar baniba
Adaidai lokacin da zan karyi itacen Sai naji anbugi hanuna ansake bugu naji zafi natuna cewa iyayena suna wahala Basu mutuba Amma suna Jin jiki Dan Haka nakara Kai hanu sainaji abun laushi aikuwa ina sakkowa bansan yadda hankalinta yayiba
Sai alokacin sabeer wato Fahad alokacin yace gaskiya ne kamanninki suncanza yusrah alokacin da Kika dumfari bishiyar hakama dakika sakko kinyi doguwar Suma kamanninki alokacin suncanza nida wannan bawan Allah wato hakimi mukaitamiki addu.a cikin ikon Allah Kika samu sauki Kika dawo normal yusrah
Hakimi tunda akafara maganar saifaman hawaye yakeyi Dan Wanda aka rasa hawayen meye
Yayi gyaran murya yace tabbas yusrah kinhadu da maciji Haka saber macijin da ya nade maka hanu tabbas ba asalin maciji bane turosu akayi gareku
Yusrah tun alokacin dakuka zo gidana na ji kaunarku araina Dan Haka nakuduri aniyar taimaka muku
Hakimi ya kalli sabeer yace tabbas sabeer kacika Dan halak Dan uwa ga yusrah Dan kayi jarumta kwarai
Hakimi yaci gaba dacewa macijin da kuka gani anturoshi ne Akan yakasheku Amma tafiyata daku bazasu tana iya cutar dakuba domin tun ina yaro mutanen boye kefamn bina tun suna wahalar Dani har suka Fara sani bada magani basa taba barin acuci Wanda nake da niyyar taimaka mishi Dan Haka suka kasa cutar daku
Sannan inason firdausi ki gafarceni kiyafemin tabbas Baki ganeniba Amma ni naganeki dukyadda Kika canza Dole zanganeki domin ke gudan jini nane
Firdausi nine mahaifin ki
Umma firdausi tamike zumbur ta Isa gareshi tabbas tumfitowasu take kallon shi saidai tarasa gane inda tasanshi ashe mahaifin tane Wanda suka rabu tun tana shekara bakwai tunda yasaki mahaifiyar ta
Cikin kuka umma firdausi baba Kaine dama baba ashe zansake ganinka baba ina mama na
Hakimi yayi kuka Mai cin rai yace mahaifiyar ki Allah yayi Mata rasuwa da jimawa
Ainan sabuwar kuka takaru sarki suna tabata hakuri Dole tahakura dama tunda mahaifiyar ta tabar gidan akabarta agurin matar uba muguwa shikenan karshen rabuwarsu da mahaifiyar ta Allah sarki umma firdausi Allah yajikan ta
Anan ka jakanta
Yusrah tace Abba kasan yadda akayi na yanki gashin wa innan azzaluma
Alokacin danake acting amtsayin ameena dakaina NASA musu maganin bacci a ruwa nabasu suka Sha Basu saniba
Aikuwa bacci yadaukesu agurin Dan Haka na yanki gashinsu Haka buhari yaso yaudarata naki amincewa Koda yaje shagon askin nace musu gashin shi nakeso nabasu kudi Mai yawa sukabani
Haka watarana waziri zaitafi gurin bokanshi nayi saurin rigashi tafiya muka hadu ahanya alokacin nacanza duffata
Wani fuskan robber tafitardashi tasaka tace waziri katuna wannan fuskar
Waziri yimike Yana nunata da yatsa Yace kece
Yusrah tayi.murmushi tace kwarai kuwa akan iyayena zan iya sadaukar da Raina Dan Haka Koda naji abinda boka yafada maka nace tosaina Zama maka ciwon Ido
Anan yamusu bayanin komi
Duk matanen dakin sun jinjina ma yusra da kaifin basirar ta
Yusrah tace Abba yanzu wuka da nama agurinki
*******
Mata biyun nan.dasuke gurin tunda akafara magana Basu tofa uffan Sai yanzu wata tsihuwar Mata tace tabbas waziri mugune Haka diyarshi da ya Haifa
Tabbas yaso kasheni Amma Allah baibashi sa.a ba Allah yasa inada Nissan kwana
Yakasheni ban mutuba har ansani akabari nasoma motsi da rabon zan rayu
Wasu mutane sukaga motsina suka dawo suka tononi
Wani kauye suka nufa Dani anan suka kula dani harnasamu lafiya
Koda naji abinda ke faruwa agarin bauchi nace lokaci yayi danza tona mishi asiri Ashe asirin shi yariga ya tonu
Aikuwa guri yadauki salati
Waziri ya kece da dariya yace munafukan banza da wofi kunason kuci mutuncinmu ko to munfi karfinku yakara fashewa da dariya abu kamar wasa hauka fujajan
Maimuna kuwa ai tuni tasoma barkewa da zawo akayi waje da ita
Former Mai martaba yayi addu.a yace ko Haka akabarku kunshiga uku
Bazamu dauki wani matakiba zakuje kuhadu da Allah
Anan maimartaba yamusu ardu.a yass musu albarka
[7/5, 9:17 AM] UMMY KHALEEL: *******
Mai martaba dakanshi yasa aka gyara ma hakimi wajen Zama da matar waziri
Hakama Aisha yanemi iyayenta yayi musu godiya tare da Fahad abokin Yaya sabeer
Khaleel yace gaskiya Aisha Kinsha Mari duk aka tuntsure da dariya
Sarki Yusuf farin ciki ba a misaltawa agurinshi Haka Mai martaba
Yau ranace tafarin ciki Dan Haka yashirya walima Yan uwa da abokan arzi
Bayan anwatse daga walima Mai martaba hada family meeting
Meeting din akan hada auren yusrah da sabeer saikuma
Aisha da Fahad dama already sun hada kansu suna son junansu
Koda Mai martaba yanemi hakan aikuwa iyayen Aisha Dana Fahad sun amince Dan Haka akasa biki Nan da sati biyu
Mai martaba shiyayi komai Kama daga gidan da zasu zauna har kayan da akasa adaki tabbas komi saidai muce alhamdulillah
Aranar da aka daura aure aka hada kayatacciyar walima wanda yatara dumbin jama.a nagida Dana waje
Gida daya suke saidai kowa dansashin sa Amma komai nagidan iri dayane
Karkaso kaga umman sarki Yusuf Baki harkunne bama ita kadaiba duk Wanda yake kaunar su yusrah to aranar suna Taya su farin ciki
Anyi biki anwatse angwaye anrakasu dakin amaren su
Kowanne ya umurci amarya datatsh sugabatar da sallah nafila
Nidai daganan nafita nabarsu Dan banson shiga dakin amarya lol
Da safe yusrah ce na hango kwance jiki. Saber Sai faman shagwaba takeyi shikuwa Sai biye Mata yake
Rayuwarsu gwanin Sha awa
Bayan wata shida sabeer yafito daga dakinshi yusrah ma binshi take tana faman zumbura Baki yace waike lafiya kike ta zumburo Baki Haka
Yusrah tafashe da kuka tace ninace bazanje karatu wajeba anan gida zanyi karatuna
Sabeer yayi murmushi yakara manneta jikinshi yace is okey zanmema miki admission anan ko yusra da murna tace yawwa nawan ta kwace daga jikinshi taruga shima yabi bayanta
Hakama Aisha da sabeer soyayya sukeyo Mai tsafta Mai cike da so da kaunar juna
Bayan shekara wasu Yara na hango mace Dana miji akalla zasu Kai shekara biyar kansu daya suna wasa
Jiyayi namijin yace sister bazakizo kibani ball dinaba yace bros saidai kazo ka kwace da gudu suka kwasa zuwa inda iyayen nasu suke wato Hassan da Hussaina kenan yaran yusrah
Daga kan da zanyi Naga wata beautiful baby itama tazo tatada jikin yusrah ta tana gwaranci yarinyar batafi shekara dayaba cikin nabiyu wato firdausi kenan diyar Aisha Wanda taci sunan umma firdausi ana kiranta danyasmi
Duka da Hassan da Hussaina sukazo suka dauketa suna murna Dan suna matukar kaunar kanwar tasu
*********
Akwana atashi yusrah burinta yacika tazama babbar lawyer Wanda ake alfahari da ita Nan gida da waje
Aisha da Fahad ne suka jero suna takawa cikin so da kaunar juna yusrah da sabeer ganinsu yasa suma suka tashi Dan taryar su yaransu biyu da Yasmin suka zo dagudu suka rungume iyayen nasu
Tammat bihamdul lah
Anan nakawo karsnen wannan short story Mai dauke da wasu darusa Wanda Mai karatu ya fahimta
Nagode masouana da bani lokacinku da kukayi Allah yaba kauna
My besty ummu afan inamiki fatan alheri keda mummy jidda baiwar Allah tare da ummu haneef Allah yabaki lafiya
Sai kinji Ni dauke da sabon novel Dina Mai zuwa
Taku har kullum UMMY KHALEEL
ummykhaleeel@gmail.com