Showing 6001 words to 9000 words out of 50955 words
Chapter 3 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam
mata ko kalma ɗaya ba domin nauyin da bakina ya yi mini, na gaza samun yawun da zan sarrafa. Ina jin ina ma fasawan ya yi da sai nafi zama cikin kwanciyar hankali da samun nutsuwar ruhi fiye da halin da nake ciki yanzu. Miƙewar da tayi tana faɗin"bari na ƙira Hajiya don tabbas akwai matsala". Ya San ya ni jin wani kuzarin da ban san ina dashi ba a wannan lokacin ya sauƙar mini, na riƙe hannunta gam cikin nawa.
Har yanzu hawaye yana zuba daga idona na cira kaina tare da watsa idanuna akan fuskarta da razani ya bayyana ɓaro ɓaro. Sai da nayi kokawa da numfashina da yake sarƙewa kafin na sama zarafin faɗin babu buƙatar ki ƙira Hajiya.
Ina iya jin ajiyar zuciyar da ta saka kana ta zauna cikin sanyin jiki tana fuskan tana ta soma faɗin "to menene matsalarki?, kamar ba ke bace kike cikin walwala awannin da suka gabata.
Ina wannan annurin fuskarta kin?". Shuru nayi mata ba tare da na ce da ita ko kanzil ba, hakan mai hana ta ɗaurawa da"kowa ya shaida yanda yaya Sufyan yake tsananin sonki, da hakan yake bada tabbacin zai kula dake".
Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe ina jin wani ɗaci yana gauraye mini dukkan kusurwa bakina domin ba a nan gizo ke saƙar ba. Komawa nayi na kwanta lamau saboda ɗaɗɗakun mutanen da suka fara tashi, ina jin suna faɗin wai Sakina ta kwantar da hankalinta. Dukkan wata amarya tana tsintar kanta a irin wannan yanayin na damuwa da fargaba matuƙar bikinta ya gabato.
Wata irin ƙaddara ce take ƙoƙarin yin diran mikiya a rayuwata a wannan lokacin?. Me yasa Suraj zai bayyana a cikin rayuwata a dai dai wannan gaɓar?, waye zan tunkara da batun kuma ya fahimci ni ba tare da ya yi mini kallon bututu ba?. A take zuciyata ta sanar da ni ko Hajiya da ta kasance uwar ta haife ni ba lalle bane ta fahimci ni. Amma tabbas dole nayi yaƙin nemawa kaina yanci da farin ciki na har abada a gidan aurena.
Haka na ƙarar da dare ina tufka da warwara cikin raina, ƙiran sallan farko na assalatu kuwa tamkar a kunnuwana ladanin ya ƙwala. Wayata ta soma ruri ko ban duba ba na san yaya Sufyan ne domin ko wacce rana dai dai irin wannan lokacin yake ƙira na na tashi nayi sallah. Jawo wayar nayi na tsura mata ido ina jin wani raɗaɗi a cikin raina, na rasa dalilin da ya hana ni ɗaga ƙiran kamar yanda na kasa katsewa. Sai da ya ƙira a karo na biyu sannan na ɗaga.
Ban amsa sallaman da ya yi ba balle gaisuwar a taƙaice na furta na tashi. Ban jira amsar da zai bani ba na gimtse ƙiran tare da ajiye ta gefe guda, tunin aka fara tashi don gabatar da salla hayaniya ya ɗauki gabaɗaya gidan.
Sai da na jira duk suka gama ɗauro alwalan sannan na ɗauki wayata da na sanya a airplane mode don ƙar yaya Sufyan ya ƙara ƙira na na shiga banɗakin. Na mayar da ƙofar na rufe sannan na buɗe ruwa yana zuba. Zaman dirshan nayi tallafe da kuncina sannu a hankali hawaye suka fara tsere a bisa fuskata, na shiga manhajar whatsapp ɗin wayata na latsa saƙon muryan da Suraj ya turo mini na fara saurara.
Cikin kuka da muryan dake bayyanar da tsantsar nadamar guje mini da ya yi, yake bayyana mini cewar ya dawo gare ni dawowa ta har abada. Tare da alƙawarin kasancewa tare da ni har izuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinsa. A bayyane na furta me yasa me yasa Suraj?, me yasa za ka bayyana a wannan lokacin da kwanaki biyu kaɗai suka rage na zama mallakin wani?. Me yasa ka guje mini a lokacin da nake tsananin buƙatar ka a kusa da ni?. Waye zan tunkara na sanar dashi cewar soyayyata na tsawon shekaru uku ya dawo?. Rashin Suraj ya sanya ni amsar tayin soyayyar yaya Sufyan kasancewar sa ɗan uwana, amma babu wani namijin da zan gwada soyayyarsa da ta Suraj a cikin zuciyata. Ko yaushe zuciyata cikin yi masa uzuri take akan laifin da ya aikata mini, shi kaɗai nake da tabbacin zan iya zaman aure na mutu ka raba dashi.
Sai da na saurara ya fi sau goma sannan na cire airplane mode ɗin da na sanya. Saƙon yaya Sufyan na fara karo dashi yana tambayar na yi salla da kuma fatan na tashi lafiya haɗe da tuna mini adadin awannin da ya rage a ɗaura auren mu. Share saƙon nayi na kunna data na mayarwa Suraj da amsa akan ina so mu haɗu da yammacin yau, hoton dake bisa DP ɗin sa na tsurawa ido domin sunana ne aka rubuta da manyan harrufa da ƙaton hoton zuciya a ƙasa.
Ban damu da inda ya sama lambata ba na soma shafa hoton wasu sabbin hawayen suna bin kuncina, ina takaicin rashin kula shi da nayi tun lokacin da aka fara yi mini magana da lambar ina sharewa da rashin mayar da amsa, har sai da ya sanar da ni wanene a ƙurarren lokacin da aski ya zo gaban goshi.
Na rasa mafita da madafa sai dai tabbas ba zan taɓa yin gangancin rasa Suraj ba tunda har ya kawo kansa cike da nadama. Da wata mahangar iyayena zasu dubi lamarin?. Tsam na miƙe har zuciyata nake jin zan iya ɗaukar duk wani abin da zai je ya dawo matuƙar zan mallaki Suraj, sai da na wanke fuskana sannan nayi alwalan na fito cikin sanyin jiki. Duk da ban ɗago kaina na kalli kowa ba tabbas jikina ya bani tabbacin cewar duk ni suke kallo. Hijabi na zura na tada kabbara sosai nake godewa ubangijina da ya dawo mini da Suraj gabannin a kai ni cikin gidan wani.
Gaisawa muka shiga yi da ƙawayena suna ta yi mini tsiya da faɗin amarya gobe da yardan Allah, taɓe baki nayi na haye gado nayi kwanciyata na kunna data ko Suraj ya maido mini da amsa amma shuru. Tagwayen ajiyar zuciya na saka ina matse wayar a jikina ban san sanda bacci ya yi nasarar ɗauka ta ba sai ji nayi kamar a mafarki Sakina tana tashi na tare da ƙiran sunana. A hankali na buɗe idona sannan na tashi na zauna ina kallon ta.
"Hajiya ce ta ce a tashe ki kiyi wanka rana tayi".
Sai a sannan na lura da hasken ranar da yake shigowa ta tagar ɗakin, na ƙara yin wata miƙa sannan na sauƙo na nufi banɗaki. Wanka nayi na fito na shirya cikin doguwar rigar atamfar da ta bi jikina ga farin fatar hannu da ƙafata da aka yiwa zanen jan lalle ya fito ya yi ɗas dashi. Ban tsaya ɗaura kallabi ba nayi lulluɓi da gyale na fice sashin Hajiya, ina ta cin karo da jama'ar da suka cika gidan.
Cike na iske falon Hajiya ana shigowa da abin karin kumallo na tsuguna na gaishe su sannan na wuce cikin ɗakinta. Tana zaune da ƙanwarta ɗaya tilo da muke ƙira da Mami sai yayyena mata biyu Anty Sadiya da Anty Suwaiba, da alama tattaunawa suke yi na katse musu hanzari. Suka haɗe baki wajen amsa sallamar da na shigo da ita har na zauna suna bi na da kallon dake bayyanar da tsantsar ƙaunar su da babu algus a cikinta gare ni. Ɗaya bayan ɗaya na gaishe su suka amsa cikin sakin fuska kafin Hajiya ta ce"na ga har ƙarfe goma ba ki fito ba na ce Sakina taje ta ƙira min ke, lafiya kike kuwa?".
Kaina kawai na ɗaga mata alamar e kafin Anty Suwaiba ta ce"ku shirye ke da ƙawayenki mai baƙin lalle tana tafe da ƙarfe sha biyun rana, sannan Sufyan ya ƙira ni wai na baki waya yana ƙiran naki bakya ɗagawa. Ki ƙira shi zaku yi magana".
Take naji raina ya tunzura ko sunansa bana ƙaunar a ambata kusa dani yanzu, da kalmar to na amsa mata dashi na miƙe na fice. Sanda na dawo na tarar an shigo da abin karin daƙin, su Sakina suna ci suna hirar yanda taron dinnern da za a gudanar ƙarfe huɗu zai kasance. Gefe na samu na zauna duk abin duniya ya ishe ni wayata na ɗauka na tarar da missed call ɗin yaya Sufyan rigis ban bi ta kan su ba na kunna data kai tsaye na wuce whatsapp ɗina amma har yanzu Suraj bai maido mini da amsa ba.
Zancen da wata ƙawata da muke da bambamcin addini Sonia ta fara mini ya dawo dani cikin hayyacina. "Lafiya kuwa kika zauna kika yi shuru?, ga abinci ki sauƙo mana". Dariyar dole na ƙirƙira na dasawa fuskata na ce lafiya ƙalau. Na sauƙo na fara cin abincin ba don ina jin yunwar ko don ina jin daɗin abincin a bisa harshena ba, sai don tabbatar da furucin lafiya ƙalau ɗin da na furta. Ina gama tura abincin na haye gado shaf na manta da batun ƙiran yaya Sufyan, sai da sha biyu ta gota mai lallen ta iso na ce a fara yi wa su Sonia ni sai nayi salla tukunna.
Ban tashi daga kan sallayan da na sallame sallan ba na tisa wayata a gabana, ban san sanda hawaye suka fara zarya a tsakanin kuncina da tudun wuyana ba. Sai da naji hannun Sakina bisa kafaɗata. Kamar mai raɗa take faɗin"wai me yake faruwa ne Surayya? kuka fa kike yi". Hannunta dake dafe da kafaɗata na riƙo na tashi na taja ta muka fice daga ɗakin. Can cikin lambu na dakata na zube akan kujerun simintin dake jere da juna a wajen.
"Kin bar ni cikin duhu don Allah ki sanar dani meke faruwa. Kar ki bari zargin zuciyata ya tabbata".
Ba tare da na ɗago kaina ba na ce wani zargi kike yi?, sai da yi ɗan jim kafin ta ce"cutar ƙanjamau kike ɗauke dashi ko kuma ciki?". Girgiza mata kaina nayi ina zuƙe majinar kukan da ya zo mini kafin na furta da hakan ne sai nafi samun kwanciyar hankali ma. Matso ni ta kuma yi tare da sausauta amon muryarta ta ce"to menene?". Wayata na buɗe na shiga tarin saƙon Suraj na nuna mata, cikin rawar jiki ta karɓa tana bi sannu a hankali har ta ƙare.
Ta kafe ni ido ta ce"amma kin bani mamaki da kika azawa kanki damuwar wanda bai san darajarki ba balle kimarki. Kin manta yanda ya rabu dake bayan ya dasa bishiyar soyayyarsa da ta yi rassa a cikin ranki?, kin manta halin da ya jefa rayuwarki a ciki?. Kin manta sanda kike bibiyarsa yake wulaƙanta ki?, shin kin manta lokacin da mahaifinki ya sauƙar da duk wani matsayinsa ya ƙira Suraj har cikin gidan nan. Yake roƙonsa da ya aure ki saboda halin da kika shiga amma ya shafawa idanunsa toka ya ce ya gama soyayya dake ko da kyauta aka ba shi ke?".
Sai da ta numfasa ta cigaba"wallahi tun wuri ki farka daga wannan baccin da kike yi Suraj bai dace dake ba. Ta ko'ina kin yi masa fintinkau, har akwai wani kalmar yaudaran da zai zo miki dashi ya sama matsuguni a cikin zuciyarki?. Ko da Allah bai musanya miki da yaya Sufyan ba wallahi bana goyon bayan ki komawa masa, kiyi blocking ɗin sa sannan ki sanya yaya Sufyan ya canja miki layi. Wallahi tsantsar yaudara ce kawai irin na jinsin maza yazo miki da ita amma babu wani soyayyarki a cikin zuciyarsa".
A hankali na zame hannuna daga tagumin da na zabga na ce kar ki ce haka domin Allah ne kaɗai masanin sirrin zuciya. Harara ta watsa mini alamar ta fara fusata ta ce"kar ki zama butulu ki tuna yanda bawan Allahn nan Sufyan ya sadaukar da farin cikinsa don inganta naki, ki tuna yanda ya yi juriya wajen samun soyayyarki. Wallahi matuƙar kika fifita Suraj akan yaya Sufyan za ki ƙarar da rayuwarki ne cikin tafkin nadama, yaudaran ki yake wasa yake so ya yi da hankalinki ki nutsu kiyi tinani".
Ƙatuwar ajiyar zuciya na saka komai ya dagule mini, na fahimci Sakina ba zata fahimta yanda nake ji a raina ba don haka nayi mata shuru. Hannuna duka ta riƙo ta sanya cikin nata cikin kwantar da murya ta ce"ba za ki taɓa da na sanin auren yaya Sufyan ba na tabbatar miki da haka". Da sauri na ce amma ai zan yi dana sanin zuwa gidansa da soyayyar wani a raina. Take ta sakar mini hannaye tana kallo na fuskarta ɗauke da maɗaukakiyar mamaki.
[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
Story and writen
By
Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA TA BIYAR
"Surayya kina nufin za ki iya juyawa yaya Sufyan baya kenan? da kuwa kin tabbatarwa mutane cewar bakya cikin hankalinki. Me ki kike nufi?". Ba tare da wani dogon tinani ba idona a cikin nata na ce abin da kunnenki suka jiyo miki shi na faɗa, ai na san ba ki da lalurar da ta shafi ji. Bayyanannen ajiyar zuciya ta saka tana ƙara matso ni sai da matso dab da ni ta soma furta"kar kiyi wannan gangancin wai shin ina ilminki ne? ina wayewar ki tayi ƙaura ta tare?. Yanzu ke har sai an zaunar dake ana biya miki karatun yaudaran maza. Ai nayi tunanin abinda Suraj ya aika a gare ki kaɗai ya isa ya sa ki zama malama mai bada ilmi a wannan fannin, babu wanda zai saurare ki da wannan zancen a duk danginki". Hannu na ɗaga mata alamar ta dakata mini hakan nan idanu taf da ƙwalla nake faɗin shikenan idan mutum ya aikata laifi kuma ya yi nadama ba za a yafe masa ba?. Ko Allah muna yi masa laifi kuma ya yafe mana. Kai tsaye zantukan suke fitowa daga ƙalbina domin ina jin zan iya kare Suraj a gaban ko wani mahaluki ciki har da iyayena, duk da tun bayan rabuwar mu ban ƙara sanya shi a idanuna ba.
Rurin da wayata ta soma yi da maganar da Sakina ta soma suka dirar mini a kunne a tare. Ajiye mini wayar tayi akan cinyata tare da cewa"gashi nan yana ƙiran ki sai ki ɗauka ki sanar dashi cewar hasken tauraron soyayyar da kike masa ya dishashe, yayin da na Suraj yanzu take haska ko'ina". Hawayen da suka ciko mini ido suka zubo a fuskar wayar sai da ƙiran ya kusa tsinkewa na ɗaga tare da karawa a kunnena. Ina iya jiyo ajiyar zuciya da ya sauƙe yana faɗin kalmar alhamdulillah wani na bin wani kafin ya ce"ina kika shiga yau gabaɗaya ban ji muryarki ba?, duk da na ƙira Anty Suwaiba ta tabbatar mini da lafiyarki ƙalau amma na gaza samun kwanciyar hankali". Sai da na dai daita nutsuwata kana na ce dashi ina lafiya ƙalau kawai na bar wayar a ciki ne. Hamdala ya kuma yi haɗi da faɗin"ina son ganin ki anjima zan zo kafin lokacin dinner ɗin". Da sauri na tari numfashinsa da a'a mai lalle tazo yanzu za ta fara yi mini ka bari kawai mu haɗu a can. Sai da ya ɗan yi shuru kaɗan na ɗago ido ina satar kallon Sakina naga ta maida hankalinta gefe guda. Muryarshi ya ratsa kunnuwana"to shikenan ki kula mini da amanar kanki da na ba ki", kaina na ɗaga kamar ina gabansa sannan na ce ina sha Allah. Kit na kashe wayar ina maida numfashi tamkar wacce tayi gudun ceto rai, na saka ran Sakina za ta cigaba daga inda ta tsaya sai na ga saɓanin hashashena domin tsuke bakinta tayi. Sai ni na furta a raunana don Allah wannan ya sama sirri tsakanina dake bana son kowa ji. Ba tare da ta kalle ni ba ta furta"ke zan yi wa wannan roƙon Allah ya saka ki iya riƙe abin, don naga gabaɗaya ki zuzuce". Tana ƙare faɗin hakan ta miƙe ta bar ni zaune a wajen tashin ta ya yi dai dai da isowar yaya Sa'eed wajen ya zauna kusa dani sai da ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya ce"meye amaryar gobe take yi a nan?". Ɗago kaina nayi cike da shagwaɓa na ce yaya Sa'eed, ban ƙarisa ba sakamakon dakatar dani da ya yi ta hanyar ɗaura yatsansa a bisa leɓensa yana faɗin"shiiiit bana son jin komai tashi ki shiga ciki ki gama shirye shiryen ki". Bani da zaɓi face bin umarninsa haka na miƙe jikina babu kuzari tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri na koma ciki. Sanda na isa an ganawa kowa Sakina ake yiwa ana gamawa aka fara ɗanɗasa min nawa cikin ƙanƙanin lokaci aka gama. Wasu danginmu suka shigo tare da su Anty Suwaiba suna ta yaba tsarin lallen nawan da bai cika yawa ba suna ɗauka na a hoto.
Kafin ƙarfe uku kowa ya fara shirin zuwa dinner gidan ya ƙara cika da mutane babu masaka tsinke. Sai na gabatar da sallan asr mai kwalliyar da Anty Safiya da suke tagwaye da yaya Sufyan ta aiko ta musamman don ni ta fara tsantsara mini kwalliya, dukkan wasu tufafi da zan sanya a bikin ita ta samar mini dasu. Ina jin mai kwalliyar suna taɗi da Sakina tana labarta mata yanda Anty Safiya ta buɗe bakin jakarta a kaina don ganin na fita daban.
Mahaifin yaya Sufyan da mahaifina wa da ƙani suke duk wanda ya san su ya san irin yanda suke so, ƙauna da kuma kulawa da junan su. Su kaɗai iyayen su suka haifa jinkirin haihuwar da mahaifiyar su yaya Sufyan ta samo, ya sanya Abba damƙa musu yaya Sa'eed tun yana shekara ɗaya da haihuwa wanda ya ci sunan mahaifin su yaya Sufyan. Sai da ya cika shekara ɗaya da rabi sannan Allah ya azurta su da haihuwar yaya Sufyan da Anty Safiya yayin da yaya Sufyan ya ci sunan Abban mu, basu cika watanni