Showing 27001 words to 30000 words out of 50955 words

Chapter 10 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2119

babu yake kallo ba hankalinsa gabaɗaya yana kan na'ura mai ƙwaƙwalwar dake yake latsawa cike da ƙorewa a gabansa.


Tare muka ci abincin na gyara wajen, Momma tana tashi ta shiga ɗakinta nima na miƙe zan tashi. Maganar da Sultan ya furta ya sanya ni dakatawa.


"To za ki je ki kama sana'ar danna wayar ko?".


"Da Sakina fa muke magana akan karatunmu?".


Ya ɗago kansa ya yi mini kallo ɗaya"kai tsaye ƙarya ki ke faɗa". Na buɗe baki zan kuma yin wani maganan ya ɗaga mini hannu alamar na dakata.
"Yanzun ma ƙaryar za ki ƙara faɗa ki dai nutsu kuma kin san abinda ya dace domin yanzu ke ba yarinya ba ce. Wuce ki ba ni waje".


Na haɗe rai na fice daga falon izuwa ɗakin kwanana. Na haye gado na cigaba da chat ɗina. Sabo tirke wawa kafin a rufa watanni biyu tunin wani shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu ga mutumin da ban san wanene ba. Sai dai tabbas kalamansa sun yi tasiri wajen karkato da hankalina izuwa gare shi har na fara sauraronsa. Na taɓa yi masa tambayar ko dai ya kasance ɗaya daga cikin marubuta saboda yanda yake tsarawa, jeranta da kimtsa zance daki daki.


Babu wanda ya san ina soyayya ko Sakina ban sanarwa ba, na yunƙuce a raina cewar sai na gan shi a zahiri sannan zan sanar da ita. Wata ranar na ce dashi zan je wankin kai ya tambaye ni a ina ne Allah ya sa kusa ne don ba ya son na wahala. Na sanar dashi ya ce kusa da unguwar su ne, ya nema da inda na gana na tura masa saƙo zai zo.


Ina saka da tsallen farin ciki Sakina ta turo ƙofar ɗakin tare da sallama, ta sa ki baki sakake tana bina da kallo. Sai da na yi na gaji sannan na faɗa kan gado ina maida numfashi.


"Ke in ce dai lafiyarki ko?".
"Lafiyarce ta kawo haka".


Na bata amsa ina tashi zaune na kashe mata ido ɗaya, na tashi na shiga ɓandaki ina jin ta tana faɗin"ikon Allah". A gaggauce na yi wanka na shirya cikin shirgar riga da siket ɗin kamfala. Duk da hijabi zan sanya sai da na kashe ɗaurin kallabina, har muka yi wa Momma sallama Sakina ba ta daina mamakina ba. Yaya Sultan ne ya kai mu kuma shi zai ɗauko mu kamar yanda Momma ta faɗa. Da ya ajiye mu ya juya akan in mun kammala mu ƙira shi.


A ni aka fara yi sannan Sakina, ana gama mini na zaro wayata daga jakata na tura masa saƙon na gama. Mintuna kaɗan tsakani ya dawo mini da amsar na yi haƙuri ya ɗan fita amma yanzu zai dawo na ɗan jira. Na mayar masa da amsar Allah ya kawo shi lafiya. Aka gamawa Sakina shuru ban ji ya turo mini saƙo ba. Ina jinta tana faɗin wai na ƙira yaya Sultan na shaida masa mun gama na yi kunnen uwar shegu da ita.


Muka yi sallan zuhr a nan shagon don da ta matsa mini cewa na yi na ƙira ba ta shiga. Ta ce na bada ta ƙira da kanta don na ga alamar bata yarda da ni ba ƙarara akan fuskarta. Dole ba danna ƙiran na sanya a amsa-kuwwa na galla mata harara"gashi sai ki yi magana".


Na ji wani daɗi ya lulluɓe ni da na ji yana faɗa mata wani uzuri ya riƙe shi ba zai sama damar zuwa ɗaukar mu ba, mu nema drop ɗin daidaita kawai ya kai mu gida. Haka muka fito bakin titi riƙe da wayata da nake jiran saƙonsa.
Duk zumuɗin da nake yi ya koma ciki, na ji ni kamar wacce mutuwa ta ɗauke mata wani jigo na rayuwata. Sai da Sakina ta taɓo ni kafin na dawo duniyar zahiri daga na tunanin da na faɗa.


"Tunanin me kike yi haka tun ɗazu ina ta miki magana shuru?".


"Babu".


Sai da ta ƙare mini kallo"to ga adaidaitan in kin gama tunanin zai ki shigo mu tafi, hadiri ne yake tasowa".
Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina kuma waiwagawa, har na gama cire rai zan shiga adaidaitan na ji muryar wani yaro a bayana.


"Gashi in ji wancan mutumin a ba ki".


Na ƙura masa ido daga shi har farar fefan da yake miƙo mini"ina yake?".
"Yana ba ni ya tafi".


Na karɓa cikin rawar jiki na tusa ta a jakata, na shiga. Har muka isa gida ban ce komai ba. Na zauna a bakin gado ina dafe da kaina.


"Me kike ɓoyewa ne Surayya?. Tun safe kika dasa zarginki a cikin raina tabbas akwai wani abun da bakya son na sa ni. Waye wanda ya aiko a ba ki wannan takardan?. Sannan me yake ƙunshe a cikin ta".


"Ban san shi ba ban san shi ba Sakina. Ban san wanene ba".


"Kamar ya?".


Na ɗaga kaina"kamar yanda kika ji na faɗa". Ba tare da bakina ya yi shawara da zuciyata ba na ji ya hau feɗe mata biri har wutsiya. Jakata ta fizgo ta ɗauko takardar ta fara karantawa a bayyane.


"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya azurta ni da idanun da nake iya ganin kyakkyawa kamar ki. Ba zan iya ƙarisowa inda kike ba amma ki sa ni a ko yaushe ke ce abun tunawa a gare ni, ko a farke ko a cikin bacci. Zan bayyana a gare ki nan ba da daɗewa ba".


Muka haɗa ido ƙirjina yana gudun famfalaƙi.....
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam


LAMBA TA GOMA SHA BAKWAI


"Surayya lalle ba ki da hankali wallahi kina dab da haukacewa matuƙar kika cigaba da biyewa wannan mutumin da ya kasa bayyana kansa a gare ki, wai yaushe ma kika canja har haka ne?"


A jere ta watso mini tambayar, na sauƙe gigitaccen ajiyar zuciya ina lumshe idanuna saboda sarawar da kaina yake yi mini tamkar zai rabe gida biyu. Ta dafa kafaɗata"da zan ba ki shawara ki ɗauka to ki gaugauta cike shi daga cikin rayuwarki domin na ga kema kin ɗaukake shi. Ni tsoro na ma kar ya cutar dake wallahi".
Ban ce da ita ko kanzil ba har ta yi ta gama tana haɗawa da nasiha da nusarta da ni illar abinda na ke aikatawa. Har ta bar gidan kalamanta suna yi mini zarya a cikin kwanyata. Ranar ban iya runtsawa ba gabaɗaya. Tabbas zantukan Sakina suna kan gwadaben gaskiya sai dai aikata su zai zango mawuyacin abu a gare ni.


Na ƙara buƙatar ina don mu haɗu a zahiri ko kuma ya daina kula ni, ya dunga kawo mini wasu uzurruka. Na daina kula shi ba wasu kwanaki sai dai ina jinyar zuciyata na share shin da nake yi. A wani yamma ya turo mini saƙo akan ya aminci mu haɗu amma don Allah na yi masa alƙawarin ba zan taɓa rabuwa dashi ba idan na yi tozali dashi. Ba tare da wani dogon tunani ba na yarda da hakan.


Ranar da zamu haɗu tun da asubahi na ƙira zaSakina na sanar da ita tazo muka je tare. A gidan wani cin abinci muka zauna muna jiran shi.
"Anya kuwa bawan Allahn nan ba jirga mu ya yi ba?".


Na sa ki ajiyar zuciya"shi fa ya bamu wannan adireshin, na tabbatar da cewar zai zo". Ina rufe bakina saƙonsa ya shigo cikin wayata domin ba mu taɓa yin waya dashi ba. Yana sanar da ni cewar ya iso na sanar dashi ta inda muke, ban yi sanya ba na turo masa da amsa. Babu ɓata lokaci ya maido mini da amsar cewar gashi a wajen yana ma hango mu na ɗago kaina.


Idanuna suka hango mini abunda ya hautsina tunanina tare da damalmala lissafina, tsam na miƙe tsaye jikina yana rawa. Sakina ta kafe ni da ido tare da tambayar lafiya kuwa?.


Na kasa sanar da ita illa nuni da nayi mata da hannu ga malam Suraj ɗin da yake nufo inda muke. Ya murza shadda da karin hula fuskarsa ɗauke da fara'ar da ban taɓa ganin makamanciyarta a bisa fuskarsa ba.


"Me ya kawo wannan kuma nan wajen?".


Na yarfa hannuna alamar ban sa ni ba, ina ɗaukar jaka da nufin barin wajen. Na ji ya ƙira sunana cak na tsaya na lumshe idanuna da ya ciko da ƙwalla.
Ina jin ƙarar taku har aka iso gabana"ni ne wanda kika daɗe kina muraɗin gani Surayya, ga ni yau tsaye a gabanki buɗe idonki ki ganni".


"Kai ne waye?".


Muka haɗe baki wajen furtawa ni da Sakina a gigice ina ƙura masa ido, ya yi ƙasa da kansa sannan ya ɗauro"ni ne wanda kike magana dashi a whatsapp, sannan ni ne wanda zaku haɗu dashi a yau a daidai wannan lokacin a kuma wannan wajen".


Take na ji wani zazzaɓi ya rufe ni na dafe kaina ina karanto kalmar innalillahi wa inna ilaihir raji'u.


"Malam anya ka san abinda bakinka yake furtawa kuwa?. Shin ka san su waye tsaye a gabanka?. Ko wani abun ka sha wanda ya gusar maka da hankali?".


"Duk abinda nake faɗa daga zuciyana suke fitowa kai tsaye, kuma ras nake domin ina cikin cikakken hankali da nutsuwata. Sonta ne kawai ya rufe min ido bana ganin kowa sai ita ko yaushe ita ce a cikin tunanina".




"Wallahi na tabbatar da ba ka cikin hayyacinka, shi ne zaka ɓoye kanka tsawon wannan lokacin ka ƙi bayyana kanka a gare ta sai yanzu. Ina ganin girmanka a idanuna don haka ka ja kimarka Malam, daga yau ka rabu da Surayya ka daina tura mata saƙonni ka fita daga cikin rayuwarta. Ka bar ta ta huta haka nan ya isa haka basajan da kake yi kana yawo da hankalinta".


Ta na dasa aya a nan ta fige hannuna zamu fice daga wajen ya yi saurin shan gabanmu. Tun kafin ya ce wani abu na yi saurin fizge hannuna daga cikin na Sakina na fice da sauri saboda hankula mutanen wajen da ya fara dawowa gare mu.
Sakina ta fito muka hau adaidaita muka tafi, tsabar rashin hankalin da nake ciki ko motsi mai ƙarfi na kasa yi har muka isa gidansu, ta sallame mai adaidaitan tare da riƙo hannuna domin na gaza sarrafa jikina muka shiga ciki.


Kaina a ƙasa na gaishe da iyayenta da muke iske a tare, kana muka shige ɗakinta ina shiga na zube akan gado ina rero kukan da nake jin ciwonsa har cikin zuciyata. Sai da aka ɗauki wasu mintoti kafin ta ce da ni"ba kuka za ki yi ba ɗaga hannu za ki yi ki godewa Allah ya sa kika gano shi tun kafin abubuwa su yi nisa, sai ki yi wa kanku faɗa da karatun ta nutsu ki san inda duniya ta nausa. Ki sa ni ba ko wacce mu'amala ba ce ake zurfafawa".


"Na ƙure tunanina na gaza gano manufarsa na aikata hakan a gare ni, wallahi zuciyata bugawa take yi da ƙarfi". Ta matso ta ɗago kaina"mugunta ce kawai babu wata soyayya, kar ki ƙara maimaita wani kuskuren na barin kalamansa su yi tasiri a gare ki".


"Sai da ya bari na yi sabo dashi zuciyata ta kamu da soyayyarsa, wallahi in da ban ga saƙonsa ba ko bacci bana iya yi Sakina".


Ware idanunta ta yi a kaina cike da mamaki nake faɗin"malam Suraj ɗin?".


Na sadda kaina ƙasa domin sirrin zuciya sai mai ita, ni kaɗai na san ƙangin da nake ciki. Tun tana lallashina har na soma bata haushi ta ƙyale ni. Sai yamma na baro gidan.
Kullum cikin tunani nake na koma tamkar marar lafiyar da ta yi jinyar shekara. Komai cikin sanyan jiki nake aiwatar dashi na daina kula shi na kuma daina buɗe saƙonsa gaba ɗaya. Sai ya koma ƙiran wayata hakan ya sanya ni barinta kullum a kashe.


Na rame na kuma yi baƙi kullum sai Momma ta tambaya me ke damuna, na ce da ita babu babu tambaya da matsawar da ba ta yi mini ba akan na sanar da ita abinda ke damuna amma na nuna mata ba komai. A haka har muka sama gurbin karatu a jami'ar da Yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suke koyarwa, muka fara zuwa. Ba na taɓa mance wani daren ranar alhamis da ba ɗebo gajiyar makaranta ga shi ranar na yi azumi haka na dawo na yi luguf.


Har bacci ya fara ɗauka ta na ji wayata na ruri na buɗe idona ina lumshewa. Har ƙiran ya katse ban tashi na ɗauka ba, aka ƙara ƙira a karo na biyu na yi tsaki tare da lalumo wayar ban tsaya duba mai ƙiran ba na kara a kunnena.


"Ke ce Surayya?".


Cikin magagin baccin da bai gama barin idona ba na ce "ni ce".


"Suraj ne ya bada lambarki ya ce a ƙira ki".
Duk da mutum ɗaya jal na sani mai irin sunan a rayuwata, amma sai na tsinci kaina da tambayar"wani Suraj ɗin?".


"Suraj masoyinki gashi nan kwance magashiyan rai a hannun Allah, tun yana tafiya da jinyar a jikin shi har ya kai matakin da ta kai shi ƙasa. Tun dare jiya aka kawo shi asibiti baya cikin hayyacinsa sai yanzu ya farka, likitoci sun shaida mana cewar zuciyarsa ce ta kumbura za ta iya bugawa a ko wani lokaci daga yanzu, sunanki kawai yake ƙira don Allah ki taimaka mana ki ceci rayuwarsa".


Take na ji kaina yana juyawa, baccin da ke idona ya wartsake na tashi na zauna hawaye yana bin kuncina. Ba zan iya jurar jin raguwar maganganun ba don haka na datse ƙiran ina fashewa da wani matsanancin kuka, sosai nake kukan sai da na ji numfashina yana cushewa waje guda sannan na tsagaita.


Na danna ƙiran layin da ya ƙira ni dashi ringing ɗaya ya ɗauka, na ce ya ba wa Suraj ɗin wayar. Ya ce da ni ba zai iya amsa ba sai dai ya sanya masa a kunnensa.
A hankali yake maganar muryarsa sam ba ta fita, babu abinda yake faɗa illa roƙona da na furta ina sonta koda sau ɗaya ne kafin Allah ya ɗauki rayuwarsa. Wani kifiyar tausayinsa ta yi tsalle ta dira a zuciyata tare da tarwatsa ta into pieces.


Haƙuri kawai na ke iya bashi da kuma yi masa addu'ar samun lafiya daga wajen Allah. Ban mu sallama ba sai da ƙaninsa Sani kamar yanda ya sanar da ni sunansa, ya ba ni adireshin asibitin da suke na yi masa alƙawarin gobe ina sha Allah kafin na wuce makaranta zan tsaya na duba jikin nasan.
Har alfijir ya keto ban tsunra sai saƙe saƙe nake yi cikin raina da nazarin maganganun malam Suraj, shin daman tsana ta na rikiɗewa ta koma soyayya? Daman haka soyayya take shigewa cikin zuciya ta yi bankan-bankan ba tare da sanin mai ita ba. A bayyane na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina wargaza gashin kaina da na tufke shi ta baya. A gaggauce na yi wanka na shirya ko abinci ban tsaya ci ba na ce da Momma na yi latti kuma malamin zai iya hana ni shiga, addu'ar fatan alkhairiin da ta saba yi mini kullum ta raka ni dashi na fice.


Sai da na shiga cikin asibitin na danna ƙiran wayar Sani kamar jira yake yi ya yi caraf ya ɗaga, na sanar dashi ga ni a cikin asibitin na yi masa kwatancen inda nake. Ya fito tun kafin ya iso na ga tsantsar kamarsa da malam Suraj da hakan ya ba ni tabbacin cewar jininsa ce. Na lura da wani irin kallon da yake yi mini da ya sanya ni tsarguwa da kaina, shi ya yi mini jagora har cikin ɗakin yana kwance ga ƙarin jinin da aka yi masa da ya kusa ƙarewa, fuskarsa ya yi wata 'yar rama.


Yana ganina ya tashi zaune na ƙarisa cikin ɗakin ina jan ƙafata da ƙyar, bai damu da ƙarin jinin dake jikinsa ba ya sauƙo ƙasa ya zube akan gwiwoyinsa yana roƙon na yafe masa a cewarsa duk abinda ya aikata son da yake yi mini ne sila. Na sha kuka kafin na baro asibitin koda nake makaranta ban fahimci komai ba. Sai da muka fito na cewa Sakina za ta raka ni asibiti dubiya dubu ɗayan dake cikin jakata na yi amfani da ita wajen sayan lemo da raguwar kayan zuwa duba marar lafiya.


Muna shiga ɗakin ta yi turus tana kallo na, na yi saurin ɗauke nawa ido ina ƙarisa shiga. Na gaishe shi tare da yi masa yaya jiki ya amsa mini da alhamdulillah. Sakina da ta ƙi ƙarisowa cikin ɗakin ya ƙurawa ido yana ba ta haƙuri cikin tausasan lafuza da nuna tsantsar nadamar abinda ya aikata a bayyane, yanda yake furzo zancen daki-daki ya isa karyar da zuciyar ko wanene.


Tun daga lokacin na soma sauraronsa da kuma ɗaga wayarsa idan ya ƙira ni, malam Suraj mai nuna mini tsantsar tsana sai gashi yau shi ne ya zamo masoyin da ba ya son ganina cikin ko wacce irin damuwa komai ƙanƙantarta. Sau tari na kan lura da Sakina ba a son ranta nake ɗaga wayarsa ba sai dai kawai babu yanda ta iya, amma hakan bai hana ta yi mini kashedi da jan kunne akan na bi a hankali ba kuma na dunga yin ta-ka-tsantsan.


Shaƙuwa ya ƙara shiga tsakaninmu mai ƙarfi kullum sai ya je makarantar mu, ba ma iya yin awa biyu ba tare da mun ji muryar juna ba, ko yaushe shi ne a tunanina. Ya canja matuƙa daga malam Suraj ɗin da na sa ni a da, domin na yanzu mutum ne mai tsananin kulawa da ƙoƙarin kiyaye duk wani abun da zai sanya raina ya sosu. Ya iya tsara zancen da zai tsaye imanin ko waye da kalamai.
A lokacin Momma ta fahimci cewar ina kula wani ba tare da sanin su sosai ta yi mini faɗa da nasiha, tare da umartata da na sanar dashi ya gabatar da kansa ga Abbanmu. Tun a ranar na sanar dashi sai dai na ga yana kwacewa maganar, sai da aka jera sati biyu ina masa maganar amma yana bani wasu uzurruka a cewar yana tsoron kar iyayena su hana sa aurena domin kasancewarsa talaka.


Ranar da ya amsa mini cewar zai zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login