Showing 9001 words to 12000 words out of 50955 words

Chapter 4 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2121

uku a duniya ba Hajiya ta haifo Anty Suwaiba tazaran shekaru uku ne tsakanin su da Anty Sadiya da take tsaran Sultan gambon su yaya Sufyan. Tun daga haihuwar Anty Sadiya Hajiya ta sama matsala har likitoci suka bayyana da wuya mahaifarta ta kuma ɗaukar wani cikin. Kafin Anty Sadiya ta rufa shekara biyu Allah ya ƙaddara kasantuwa ta a cikin cikin Hajiya. Haihuwar da ya zo mata da matsalar da ta sanya aka cire mahaifarta gabaɗaya.


"Wallahi ke kam kin yi dacen iyayen miji da kuma miji irin wannan zallar ƙaunar".


Zancen da kunnuwa suka tsinkayo mini mai kwalliyar ta furta kenan, da ya yi nasarar dawo da ni daga tafkin tunanin da nake ninƙaya a cikinsa. Dai dai sanda take miƙo mini madubi ina duban fuskata da kwalliya ya zauna a fuskar sosai. Tunin ta fara ɗauka na hoto doguwar rigar ta zauna sosai a jikina mai launin ja haka nan ma ɗaurin dake kaina da dogon mayafina ya kasance ja. Ƙiran Anty Safiya ya shigo wayata na ɗauka da sauri bamu tsaya dogon gaisuwa ba ta sanar da ni idan mu shirya ni da ƙawayena mu fito. Takalmin mai tsini na sanya na riƙe ƙaramar jakata a hannu, Sakina da Sonia sune a gefe dama da haguna a ƙofar fita muka yi kiciɓus da Anty Suwaiba da Anty Sadiya suka zuba mini idona suna faɗin kalmar masha Allah. Tunin motoci sun fara iso suna kwasar mutane izuwa wajen dinnern.


Mota ɗaya muka shiga da Sakina da har yanzu bata ce dani komai ba nima na share ta. Hankalina gabaɗaya yana ga wayata da har yanzu ban cire rai da samun amsa daga Suraj ba, har motan taja burki a bakin tafkeken hall ɗin sai da aka ɗauki kusan mintinan uku kafin Anty Safiya da Anty Suwaiba suka ƙariso wajen suka buɗe motar. Tare da umartan Sakina ta sanar da ƙawayen mu su kammala waje guda domin su zasu fara shiga, ta fita domin aiwatar da hakan.


Ƙawaye da abokan ango ne suka fara shiga a jere a layi guda biyu kwalliyan wajen ya kasance ja da fari kalan shirgar da muka yi. 'ya'yan su Anty Suwaiba, Anty Sadiya da Anty Safiya aka sanya a gaban mu suna tafe suna watsa wasu furanni akan lallausan shinfiɗar dake wajen. Tsananta bugun zuciyata ya yi dai dai da tashin ƙidar waƙar Ali Jita mai taken sadaki da ya karaɗe hall ɗin, ƙamshin turaren yaya Sufyan da suka baƙunci hancina shi ya tabbatar mini da kasancewar sa dab da ni. Na yi saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna da suka cika taf da ƙwalla ƙasa, a hankali muke takawa masu hoto da naɗar video suna yi har muka isa ga inda aka tanada domin mu.


Ya matso dab da ni har ina iya jiyo bugun zuciyarsa. A kunnena ya raɗa mini"kin yi kyau matuƙa Gimbiyata, amma menene ya kawar da wannan annurin da baya rabo da kyakkyawar fuskarki?". Sai da na haɗiye wani yawun da ƙyar kafin na sama damar furta kawai yanayin ne bana jin daɗinsa, hayaniya komai kaɗan ɗin sa ka san ciwon kai yake sa ni. Sai da ya ƙara yalwanta fuskarsa da annuri sannan ya ce"to ko dai in yiwa su Abba magana akwai daren yau a ɗaura a cikin gida, saboda amaryar bata son hayaniya". Harara na watsa masa ina ƙara damƙe fuskata. Ji nake yi tamkar na sanya hannu a kai na ta kurma ihu ko zan ji sauƙin zogin nake jin yana sukar zuciyata.


Mami ce ta buɗe taron da addu'a sannan aka fara gabatar da abinda ya kamata komai an yi shi cikin tsari. Duk mahalalta taron fuskokin su a watse da tsantsar farin cikin da ya gaza ɓoya. Lokacin da Momma mahaifiyar yaya Sufyan take gabatar da addu'ar samun dawamamme farin cikin a cikin auren mu sai da hawaye suka zuba daga idaniyata, wani kunya da nauyinta suna ƙara narkar da raunanniyar zuciyata da don Suraj ya gama yi mata illa. Na sama kyaututtuka daga gare ta da kuma wasu dangina. Ƙarfe bakwai aka tashi domin su Abba sun yi gargaɗi kai wa dare, duk yanda yaya Sufyan yaso mu keɓe bijirewa nayi. Raina a jagule nake fige kallabin kaina ina firawa akan gadon ban damu da kallon da mutanen ɗakin suke yi mini ba domin basu bane a gabana. Muradina bai wuce samun amsa daga Suraj ba kafin wayewar gobe da ɗimbun jama'a zasu shaida ɗaurin aurena.


A tare Anty Suwaiba da Anty Sadiya suka shigo ɗakin dukkan su idanunsu a kaina, suka ce ga su Sakina su jira a falo zasu tattauna da ni. Sai da suka gama ficewa gabaɗaya sannan Anty Sadiya ta kamo hannuna ta zaunar da ni ta zauna kusa da ni.
"Me yake damun ki ne? kowa sai maganar yanda kika canja wajen dinner yake yi. Ko akwai wata matsalar ne?". Kaina na jijjija mata alamar a'a ta sauƙe numfashi haɗi da faɗin" ba ki da waɗanda suka fi mu bayan su Hajiya a duniyar nan Surayya don haka ki sanar damu".
Tsinta kaina nayi da faɗin babu wata matsala wacce ni dai na san da ita a yanzu, kawai inna tuna zan yi nisa da Hajiya ne nake jin wani iri. A tare suka sauƙe ajiyar zuciya kafin Anty Suwaiba ta hau yi mini nasiha da nusar da ni cewar hakan normal ne mafi yawan amare suna fuskantar irin wannan yanayin.

Sun daɗe suna kwantar mini da hankali kafin suka fice, wanka nayi sannan nayi alwala sanda na fito na tarar su Sakina su ma suna tasu sallar. Akan sallayar na zauna ina kirari ga ubangijina tare da addu'ar ya zaɓa mini abin da yafi zama alkhairi a gare ni, jikina babu kuzari na shafa addu'ar raina cike da fargaba.
Sai bayan sallan isha'i muka sama keɓewa da Sakina wani kallon da na kasa fahimtar inda ta dosa ta kafe ni dashi kafin ta ce da ni"kin kyauta abinda kika yi kenan?". Cike da rashin fahimta na gwalalo ido tare da cewa me nayi?, Ta tsirtar da siririyar tsaki kana ta ce"duk kin bi kin haɗe rai a wajen dinner ɗin nan kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta". Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina na ce na rasa yanda zan yi ne Sakina wallahi komai ya yi mini zafi.


"Ai dole ki rasa yanda za ki yi tunda kina ƙoƙarin ɗaukar dala ba gammo. Ki nutsu ki san inda yake miki ciwo tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗan kada. Soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa sannan masoyi na gaske baya taɓa juyawa masoyinsa baya cikin ko wani hali na rayuwa. Yaudara ce ta dawo da Suraj cikin rayuwarki a yanzu, da za ki nutsu da kema kin hango hakan. Meye amfanin soyayya da mayaudari marar tausayi?, wataƙila ma sam babu tsarin aurenki a cikin zuciyansa". Daga nan ban ƙara fahimtar abin da ta ɗaura dashi ba sai dai ganin leɓɓanta suna matsawa da hakan ya bani tabbacin maganar ta cigaba yi. Sai bitar zantukan nake yi, tabbas so masifa ya zama a gare ni. Ko da naje kwanciya ƙiran yaya Sufyan ya shigo wayata na katse na tura masa saƙo da uzurin kaina ciwo yake mini ba zan iya maganar ba, daƙiƙu biyu tsakani ya dawo mini da amsa cike da kulawa gami da tausayawa cikin kalamansa yake yi mini addu'ar samun lafiya.
Wayar na ƙurawa ido ƙirjina yana dakan lugudai, sam bacci ya gagari idanuna na kunna data na ziyarci whatsapp. Take na wartsake na tashi zaune ina mirtsike idona don tabbatar da sahihacin abin da nayi tozali dashi. Cikin rawar jiki na buɗe saƙon da Suraj ya maido mini shi.


"Ki yi haƙuri sai yanzu naga saƙonki ina can wajen fafutukan yanda zan haɗa abin da zan mallake ki. Bana son samun sauƙi, taimakon wani ko kuma rangwame wajen samun ki. Zan yi aiki tuƙuru don na mallake ki na samar miki da farin ciki marar yankewa".


Kamar wacce aka tsigarawa allurar dawakai haka na diro daga kan gadon na nufi banɗaki a harzance. Ruwa na buɗe yana zuba domin kar aji sautin kukan da ya ƙwace mini, bayan soyayyar Suraj da ta yi babakere tare da zaman dirshan a cikin zuciyata tausayinsa da ya ƙara mamaye ta. Take naji ya goge mini dukkan haddar da Sakina ta gama tisa mini game dashi.
Hannuna yana rawa na rubuta gobe ɗaurin aurena Suraj gobe na zama mallakin wani ba kai ba. Ina gama turawa na sulale ƙasa na zauna saboda bijirewan ƙafafuna da nuna gajiyawar su da ɗaukar nauyin gangar jikina. Son Suraj yana ƙara bin ko'ina a cikin jikina tabbas so bai yi mini adalci ba. Da ina da iko da na zaro zuciyata na wanke komai na cikinta na sanya soyayyar yaya Sufyan kaɗai na mayar da ita. Sai dai kash bani da wannan ikon, haka nan na tsinta kaina da yin addu'ar Allah ya ɗauki raina kafin wayewar gari gobe domin yanda nake ji gwara na mutu akan a ɗaura aurena da wani saɓanin Suraj.
[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


Story and writings by Amina maaji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam


LAMBA TA SHIDA


Zaku sanya kuɗin ku ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984




Muhammad ya kasance namiji ne matashi mai kamala da natsuwa son kowa ƙin wacce ta rasa, tsayayye ne mai irin zubin jarumai ɗin nan amma a fuska yana kama da larabawa sakamakon kasancewar sa bafulatani ne, ba laifi kam a wajen kyau nan ma ba kafar baya ba ne domin sai de ace Tubarkallah Masha Allah! Domin dukkan wata ni'ima Allah ya wadata shi da ita ga hakuri da kuma riƙon amana sannan kuma tsayayye ne wajen lamurran addini ba ya wasa wajen ibada.


Duk irin wannan baiwa da Allah ya masa sai de kuma shi mutum ne mai saurin fushi shiyasa baya fiye shiga lamurran da basu shafe shi ba saboda gudun raini.


Iyayensa sun kasance mutane ne da zama ya ɗauke su ya kai su jihar Borno a sakamakon mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne aiki ne yasa iyayensa tarewa da zama zuwa can, shiyasa dukkanin ƴan gidansu sai al'adun su ya fara canja wa zuwa na Barebari a sakamakon zama da su amma su asalin su Fulani ne na jihar Adamawa.


Muhammad sun kasance su biyar ne a wajen iyayensu yayun sa mutum biyu maza da kuma ƙannensa biyu shima mata idan da shi su biyar kenan wato shine ɗan tsakiya shiyasa sai ya zama a gidan kowa nasa ne kuma yana girmama kowa ba tare da tawaya ba ko kuma fifiko ba amma da akwai autarsu mai suna Maimuna amma yakan kiranta da Mimi sakamakon tsokalar ta da yawa take mafi yawan lokuta suna wani abu kamar gwaigunan talabijin wato Tom da Jerry amma kuma favorite ta shi ce duk da wasu lokutan suna ɗan dana rikici idan sunan Muhammad ɗin ya motsa.


Ranar sa ta farko a jami'ar Maiduguri wato UNIMAID ita ce ranar da ta zama masa silar ta shi baƙar ƙaddarar duk da ɗan Adam ba ya wuce kaddara amma a WATA MAHANGAR kuwa jarabawa ce domin kowane mutum da irin ta shi jarabawar a faculty na science sashen ne mai girma domin departments din da suke wannan faculty suna da yawan gaske amma sai de kuma shi yana department na Laboratory ne domin shi tun yana yaro yake da burin zama ma'aikacin binciken cututtukan dake cikin jini. Zuwansa bakin department nasu ya duba jadawalin shiga aji ɗaukar darasi yaga sauransu wasu mintinan da basu wuce goma ba nan take ya wuce izuwa ɗakin ɗaukar darasi domin jiran malamin da zai karanta da su.


Bayan sun gama ɗaukar darasi kowa yana fita daga cikin dakin shima ya mike tsaye kenan wata kyakkyawar budurwa su biyu suka masa sallama.
''don Allah idan ba za ka damu ba suna na Khairat, ina so da ka bani lambar wayar ka domin idan bamu da darasi muna yin bitar karatu a tare domin na lura da kai kana da fahimtar abinda ake koya mana fiye da sauran daliban ajin'' tana mai yin murmushi.
''babu komai ai amma cewar na fi kowa fahimtar ki janye wannan maganar'' cikin zolaya ya furta hakan dukkanin su suka tuntsire da dariya haka suka yi musayar lambar waya suka rabu da nufin sai washe gari saboda sun gama ɗaukar darasi na wannan ranar.


Khairat ba ta da wani aboki da ya wuce Muhammad kamar yadda Hausawa sukan ce ''idan kaga wata a gefe za ka ga zara'' to haka suke a kodayaushe don kowa kallon soyayya da juna ake musu suke yi amma su kuwa a nasu bangaren ba haka bane musamman ma shi Muhammad.


A kwana a tashi alaƙar da ke tsakaninsu ta fara barin iya makaranta kaɗai don ko sun dawo gida basu da aiki sai waya da kuma yin bidiyo call a tare da juna, a takaice dai shaƙuwa ta shiga tsakaninsu.


Muhammad yana gida a wata ranar hutun karshen mako sai Khairat ta kira shi a bidiyo call tana sanar da shi cewa ta yi kewar shi don ba ta gana da shi na wuni ɗaya ba yana tsaka da mata dariya sai yaji ta bayansa an fizge wayar da ke hannunsa ''la...l..a..la! ya Muhammad dama Aunty tamu ce kake ɓoye mana ita idan za kayi waya sai ka ɓuya duk don kar mu ganta to yau Allah ya to ni asirinka sai na nuna wa Mama ta gani''
''don Allah ki yi haƙuri kar ki yi haka so kike ki zubar min da girma na ne a wajen Mama"? Mimi kuwa tayi biris da shi kamar ba da ita yake ba sai ma cewa da take ''kyakkyawar Aunty ta ina kwana"? Kin ga ya Muhammad da wani ɓoye mana ke duk don kar mu san ki cikin shagwaɓa take maganar Khairat me take kuwa ban da dariya domin jin yadda Muhammad yake ta magiya da bada haƙuri a autarsu domin ita Khairat duk ta san ƴan uwansa a hoto domin duk abinda ya shafi rayuwar sa da ƴan uwansa duk ta sani nan dai ta lallaɓa auta da alkawarin cewa za ta zo musu takanas ta Kano don ta zo gaishe da Mama amma yanzu kam ta yi haƙuri kar ta aikata abinda ta yi niyya.


Mimi tace zan haƙura amma ki zama shaida sai ya Muhammad ya siya min rake mai zaƙi zan haƙura don idan bai yi ba zan fasa taya!
''e, na yarda zan siya miki mai zaƙi ma kuwa wanda har sai kunnenki ya fadi ƙasa don daɗi'' yana mai durkusawa na rokon da ta ba shi wayar Mimi tace ikon Allah! Yau su yaya har da durkuso! Tana taɓe baki ta mika masa wayar ta yi cikin gida tana dariya ta bar shi yana wayarsa.


Can bayan irin sakaliyar la'asar ana zazzaune a cikin falo ana kallo sai a kalli Maimuna ta kalli ya Muhammad ta yi gyaran murya da sun haɗa ido sai ta tuntsire da dariya shi kuwa sai ya haɗa rai don abun nasu har ta kai ga Mama tace da su kai abun naku lafiya kalau kuwa bana son iskanci fa me kuka ƙulla na munafurci da yake cin ku? Sai Muhammad ya yi caraf! Yace Mama ba komai kawai Mimi ce ta raina ni kuma laifi na ne! Yana mai jijjiga kai ai kuwa Mimi tace Mama ba....ya yi saurin tasowa da gudu zuwa wajen ta ya rufe mata baki da hannu ke me yasa ba kya jin magana ne? Ba mun gama magana ba? ''ikon Allah! Idan ta yi tsami ma ji'' shine maganar da Mama ta yi.


Wasa gaske soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakanin Khairat da Muhammad inda shi Muhammad yana ta tsara rayuwa a tare da Khairat da zarar sun kammala karatu amma kuma Saide kash! Ba a nan gizo ke saƙar ba domin kuwa Khairat kura ce da fatar akuya domin a nata ɓangaren bata taɓa mafarkin ta yi rayuwar aure da Muhammad ba domin ita ta kasance mace ce mai kwaɗayi da son abun duniya don ita shazumami ce duk inda zaƙi yake tana bi ta lasa wanda shi Muhammad kwata-kwata bai san da asalin boyayyar fuskar Khairat ba wanda a nasa zaton mace ce mai kamun kai amma ba haka bane domin da akwai watarana da suna zaune sai ta rike hannunsa yace da ita ta bari haramun ne mutum ya taba wacce ba muharramar sa ba nan ta rinƙa ce masa dama ashe bai waye ba? Maganganu marasa daɗi dai suka bayyana daga wajen ta daga nan Muhammad ya fara ƙokonto a kan wace ce Khairat? Kwatsam! Yana tafiya a cikin makaranta watarana a bayan wasu samari sai yaji suna hirar ai yarinyar ana ganin ta a otel tana yawa da maza wannan maganar ta tayar da hankalin Muhammad sosai don kwana ya yi yana bibiyar maganar a ransa wanda daga ƙarshe tsintar kansa ya yi a gadon asibiti nan ne ya fahimci cewa ba shi da lafiya ne.


A ɗayan bangaren kuwa likita ya sanar da iyayen Muhammad da su kula da rayuwarsa domin tana cikin hatsari a sakamakon ya kamu da ciwon zuciya kuma Sa'a aka ci da zuciyar bata buga ba amma dai su kula sosai wajen kiyaye duk wani abu da zai bakanta masa rai ko kuma zai jefa shi cikin tunani.


Ita kuwa Khairat ko a jikinta domin Muhammad ya rayu ko kar ya rayu ba damuwar ta ba ce domin ita ta cimma nata muradun a tattara da shi don haka ba ta da bukatar shi.


Wannan ita ce rayuwar Muhammad kafin ya fara soyayya da Nusaiba.
[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


MARUBUTAN JAHAR YOBE


Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam






Kai tsaye zaki biya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 400 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984




LAMBA TA BAKWAI




Wace ce khairat ?.


Khairat mace ce wacce ta taso tun yarintar ta ba tare da mahaifiyarta ba dukkan wani irin gata da ɗa yake samu da kuma kulawa ta tarbiyya duk ta rasa su sakamakon mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama, ta tashi a gaban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login