Showing 42001 words to 45000 words out of 50955 words

Chapter 15 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2118

ɗago kaina da sauri cike da zaƙuwar son ganin wanda ya aikata hakan a gare ni.
Sakina ce tsaye a kaina ta tsura mini idanu. Ban damu da yanayin fuskarta ba kamar yanda ban ji ɗar da ganin ta ba na ce"me ye haka? Ba ni wayata malama".


Na ƙarkare zancen ina miƙewa tsaye.
"Me ye haka? Daman abinda kike aikatawa kenan da auren ki Surayya?". Ban tanka mata ba na miƙa hannuna na kuma cewa"ba ni wayata".


"Ba zan bayar ba, ba zan bayar ba. Har sai kin sanar da ni yaushe kika yi wannan lalacewar?. Ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare da kike aikata wannan jahilcin da aurenk?".


Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya ina koma na zauna daga inda na tashi, na fashe da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya da kai tsaye yake fitowa daga ƙasan raina.
Sai da ta zauna kusa da ni kana ta cigaba da"sai yaushe za ki mance da Suraj? Sai yaushe za ki bambamce tsakanin masoyin ƙwarai da kuma wanda yake buƙatar a lokacin da yake nashi buƙatatun suka taso? . Sai yaushe za ki gane cewar Allah ya yi miki babbar kyauta da ya mallaka miki mutum irin yaya Sufyan, wallahi Surayya na rantse miki har da Sarkin da bashi da abokin tarayya, wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. A zamanin da muke cikinsa yanzu ire-iren su yaya Sufyan ƙalilan ne sukar rage, kuma ke kin sama ɗaya daga cikin su amma kuma nema yin wasa da damar ki".


Shuru na yi mata hakan ya bata damar cigaba da faɗin"yanzu ke fa matar aure ce kin san hukuncin macen da take da aure kuma tana tunanin wani a cikin ranta. Ki cire Suraj a cikin ranki ki sanya yaya Sufyan wallahi na tabbatar miki sai ya maida ke sauraniya a dukkan nahiya".


"Abinda nake ƙoƙarin yi kenan Sakina".


"Ba ki ɗauko hanyar yin hakan ba sam. Da kin ƙudurce a cikin ranki za ki hakan da ba zo na iske ki kin kafa waya a gaba kina karanta banzayen saƙonninsa masu cike da kalaman ƙarya da yaudara ki na kuka ba. Allah ya gani na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na jawo ki daga faɗawa halakan da kike son jefa kanki".


Wasu hawayen masu zafi suka kwaranyo mini"ba za ki gane bane. Ba za ki gane yanda nake ji a cikin raina bane. A tunaninki a son raina nake yi wannan abun?. Ko kina tunanin nima bana son na yi rayuwar aure kamar ko wacce mace cikin kwanciyar hankali da mijinta da son farantawa juna?".


Sai da na numfasa na ɗaura da"nima da akwai zuciya a cikin ƙirjina, ni na da mutum ce mai 'yancin zaɓar abinda nake ganin ya dace da rayuwata. An tauye mini haƙƙina ta hanyar fifita dacewar yaya Sufyan da ni ba tare da koda da rana ɗaya an tuntunɓe da suna jin ta bakina ko ina son shi ko akasin hakan ba".


Na lura ta fara fusata domin zance kaɗan wani lokacin yake sanya ta tunzura, a lokuta da dama na fita haƙuri da kawar da kai ga wasu abubuwan.
"An tauye miki haƙƙi fa kika ce?. Sai yanzu na tabbatar da cewar lalle Surayya ba ki da hankali wallahi kin zauce. Ba zan ƙara yi magana akan wannan lamarin ba ki yi duk abinda kike ganin ya dace Allah ya ba ki sa'a. Amma ina tabbatar miki da cewar idan kika yi ganganci kika rasa yaya Sufyan za ki nadama mai tarin yawa a rayuwarki".


A kufule na ce"ko yaushe zancen ki idan na rasa shi zan yi nadama zan yi nadama. Shin ko sau ɗaya ba ki taɓa yin tunanin jin yanda nake ji a cikin raina ba?. Zafi da zogi nake ji suna sukar zuciyata. Na zaɓi na rasa komai da kowa akan wannan lamarin, in yaso ke sai ki auri yaya Sufyan ɗin tunda a idanunki babu mutumin kirki a kaf duniyar nan kamar sa".


Duk muka miƙe tsaye ni da ita muna kallon juna, har yanzu hawaye yana zuba daga idona. Na bude baki da nufin cigaba da amayar da zancen da yake kartan zuciyata, na hangi yaya Sufyan tsaye a ƙofar falon ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa tare da kafe mu da idanu.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR




©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam


LAMBA NA ASHIRIN DA SHIDA


Ina wani irin huci na juya na shige ɗaki tare da murza key a ƙofar, na bar su tsaye a wajen. Ba damuwata yaya Sufyan ya ji ya abinda na furta ba domin ba shi ne a gabana ba a halin yanzu.
Ina shiga na zube akan gado ina sakin wani gigitaccen kuka mai matuƙar ƙarfi, ina yi ina taune naman bakina tamkar ba jikina ba.


Sosai da na yi kukan sai da na ji jikina gabaɗaya ya mutu ga wani zazzaɓin da ya rufe ni sannan na tsagaita. Ba domin na ci sauƙin zogin da nake ji a cikin zuciyata ba.


A hankali kunnuwana suke jiyo mini ana bubbuga ƙofar ɗakin tare da ƙiran sunana. Jin muryan yaya Sufyan ne ya sanya ni tsintar kaina cikin faɗuwar gaban da ban san dalilinsa.


Na san ko takardan saki ya damƙa mini ba ni da damuwa, to amma menene dalilin tsintar kaina a cikin wannan yanayi?. Take zuciyata da take bugawa a raunane ta bani amsa da faɗin Surayya wani fuskar ya fi ƙarfin mari.


"Don Allah ki buɗe ƙofar nan na roƙe ki".


Ya furta muryarsa a sanyaye, ko motsawa daga inda nake kwance ban yi ba. Ya cigaba da faɗin"ina son magana ki taimaka ki buɗe ƙofar nan".


Shuru na yi tamkar bana jin abinda yake faɗi. Ina da tabbacin idan ba ni na tashi na buɗe ƙofar ba babu ta yanda zai iya shigowa ɗakin. Irin ƙofar da idan aka rufe ta ta cikin to ba za a iya buɗe ta ta waje ba.


"Surayyaaaa".


Ya furta kalmar sunan cikin wani irin muryar da sam ban san ya mallake ta ba. Wani yar na ji a jikina da hakan ya tilasta mini runtse idanuna da ƙarfi wasu hawaye suna gangarowa daga koramar idanuna.


Babu irin magiya da roƙon da bai yi gare ni ba, ƙiran wayata kuwa ya yi yafi a irga amma na kasa cewa dashi komai. Haka har aka yi ƙiran sallan zuhr na miƙe ina jin wani jiri ya ɗeba ta na shiga banɗaki na yi alwala, a zaune na yi sallan saboda rashin ƙarfin da nake ji bani dashi ba.


Na kasa furta komai yayin da na ɗaga hannayena sama, illa hawayen da nake yi. Na tabbatar da cewar ubangijina shi kaɗai ka san irin radaɗin da nake ji a cikin ƙalbina kuma shi kaɗai zai iya kawo mini sauƙi da mafita daga tsaka mai wuyar da na faɗa ba.




Ina shafa addu'ar na ji yaya Sufyan yana buga ƙofar, yanda ya kwantar da murya ya sa naji kifiyar tausayinta ta caki ƙirjina. Ina tafiya ina dafe bango hakan na miƙe na buɗe masa ƙofar.


Ban yarda na ga inda yake ba na juya ya yi saurin riƙo ni na faɗa jikinsa.


"Me yake faru? Me yake faruwa Surayya ki sanar da ni. Sakina ta tafi bata ce min komai ba".


Ya ƙare zancen yana jijjiga na matse idanuna gam. Cikin sarƙafewa harshe na furta"babu abinda ya faru face abinda ka ji".


"Me ye kike nufi?".


Sai a lokacin na yi nasarar kwace kaina daga riƙon da ya yi mini, na koma cikin ɗakin na zauna a ƙasa dirshan.
Ya tako ya zauna a gabana kamar mai ɗaukar karatu ya kafe ni da ido"tun kuna ƙanana ku ke tare da Sakina, babu wanda bai san ku a matsayi ƙawaye ba daga danginmu har na ta, kowa ya shaida irin yanda kuke kulawa da juna da ɗaukar matsala da damuwar ɗaya tamkar ta ɗayan. Na yi mamakin ganin kuna cacar baki da ita a yau me ya faru?".


Na ɗago idanuna da suka kumbura tsimtim na ce"kana nufin bata sanar da kai komai ba har ta bar cikin gidan nan?".


"Ƙwarai kuwa".


Na sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tare da faɗawan tunanin dalilin da ya hana Sakina sanar dashi komai duk da fusatan da tayi game da lamarin. Sautin muryarsa da suka yi dirar mikiya a na'urar jiyo mini sauti ya katse mini zancen zucin da nake yi.


"Me yake faruwa? Don na yi imanin ba ƙaramin abu bane zai sanya ku mayarwa irin wannan martanin da zafafan kalamai ".


Na kasa cewa komai sai da ya ƙara maimaita tambayar a karo na biyu. Haka siddan na tsinci kaina da sakin wasu hawayen da na kasa tantance dalilin zubar su. Shin na halaccin da Sakina ta yi mini wajen ganin ta ƙara zuba ƙasa a ramin da na haƙa na ɓoye sirrina bane, ko kuma na takaicin ƙaryar da zuciyata take shirya mini ne na gaza ganewa.


Cikin rawar murya na furta"zuciyata ce ta kasa daurewa na kuma gaza jure zantukan da take yi mini a kanka. Na ga take taken ta kamar sonka take yi domin kullum cikin yi mini zancenka take yi da kuma yabon kyawawan halayenka tare da addu'ar Allah ya mallaka mata miji irin ka. Ko yau ma da tazo zancen ta yi mini kenan na kasa daurewa har ka shigo ka ji ina furta mata idan sonka take yi ta aure ka tunda a idanunta babu mutumin kirki a kaf duniya nan kamar k....".


Tun kafin na dire zancen ya katse ni"innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Surayya kika faɗa mata haka"?.


Na gyaɗa masa kaina, ya cigaba da cewa"Sakina ta wuce haka a wajen ki, na tabbatar tana ɗaya daga cikin masoyanki masu ƙaunar ganin farin cikinki. Ta taimaka min sosai wajen samun soyayyarki bana tunanin idan tana yi min kallo so zata yi min wannan taimako. Surayya idan hankali ya gushe hankali ake sawa a nemo shi, shi harshe bashi da ƙashi amma yana da dafi sosai".


Sosai na fashe da wani irin kuka har jikina rawa yake yi.
"Subhallahi lafiya?".


"Kai ma kenan goyan bayan ta kake yi?".
Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa jirin da yake walagigi da na ya dawo da ni na zauna. Ya riƙo hannuna na fizge.


"Ba ina goyan bayan ta bane face ina sanar dake gaskiyar da idanunki suka makance suka kasa gano miki su. Kin san ina sonki wallahi ba zan taɓa fifita wata 'ya mace akan ki ba ki yi haƙuri kin ji?".


Banza na yi dashi, rashin kula shin da nayi bai sanya shi dakatawa daga furta mini kalaman ban haƙuri ba tamkar shi ya aikata mini laifin. Bai tsagaita ba har da ya yi nasarar sanya zuciyata da take tafasa lafawa.

A karo na farko a rayuwarta da na roƙo Allah idan son Suraj ba alkhairi bane a gare ni Allah ya cire mini shi har daga zuciyata gabaɗaya. Ban taɓan jin tausayin yaya Sufyan ba kamar yau domin da farko na yi tunanin cewar ya ji duk tattaunawar da muka yi da Sakina ashe har yanzu lalume yake yi a cikin duhu.


Har na fara fita makaranta ban nema Sakina ba kamar yanda ita ma bata nema ni, sannu kawai shi yake shiga tsakanina da ita ko mun haɗu a cikin makarantar.


Duk wasu abubuwan da muke yi tare bamu daina ba magana ce dai kawai bana yi, hakan ya sanya mutane da yawa basu gano taskaron da ya gifta a tsakanin amintar mu ba.


Wata ranar asabar bayan yaya Sufyan ya dawo daga lecture ɗin ƙarfe goma sha ɗayan da yake dashi ya ce na shirya zamu je gidan su Sakina. Direwa na yi akan babu inda za ni tun ita ma har yanzu ba ta tako tazo inda nake ba to ban ga dalilin da zai na kwashe ƙafafuna nake inda take ba.


Sai da na ya nuna mini ɓacin ran da ban taɓa gani akan fuskarsa ba sannan na shirya muka je.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam


Zaki sanya kuɗin ki ta wannan asusun Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984


LAMBA TA ASHIRIN DA BAKWAI






Yau Nusaiba ni kika mara sabo da kin tsane ni kaicun wannan ranan nasan nayi miki laifi ki yafe mun don girman Allah zan gyara kuskure na kiyi mun afuwa .


"Wallahi JB muddin baka fita daga rayuwa ta ba zan baka mamaki sannan kace zaka kashe mu ,duk kan mu sannan ka kashe kanka ina jiran wannan ranan fisge hijabi na nayi nafice ko wai-wayo wa banyi ba haka na nufi ɗaki na na kwanta ina fitar da numfashi mai wahala jin wani yanayi sai da gaba na ya faɗi nayi ƙoƙarin dai dai ta numfashi na amma ina bazan iya ba ido na yafara juyawa baki na yafara kumfa bugun numfashi na da sauri yake yi tsintar kaina nayi a asibiti a lokacin kwana na uku ina kwance wanda duk wani masoyi na ya fidda ran zan rayu duba wa nayi naga banga Hajiya ba sai ƙanwar Abba na takaici duk ya cika ni yanzu daman da gaske Hajiya take yi wani likita ne da ban ba doctor Ibrahim ba shima yanzu fushi yake dani kenan.


Jin wani yayi mun magana "kin tashi sannu Allah ya baki lafiya irin wannan rashin lafiyar taki sai wanda zai,iya fatan mudai Allah ya baki lafiya tambaya na ina ne yake mun ciwo nace babu Anty mariya ce ta matso in da nake tayi mun sannu da jiki na amsa "Anty ina Hajiya ban ganta ba ?"kiyi haƙuri tayi fushi da ke a kan hakan ne ma suka samu matsala da Abban ki muma kan mu bamu ji daɗin hakan ba Allah ya baki lafiya ".


Kuka nakeyi sosai Anty mariya tabani haƙuri "amma taya Hajiya tana fushi da ni zan samu sauƙi a zuciya ta ya zanyi yadda na keji sai nake ganin kamar ba zan rayu ba fatana Hajiya ta yafe mun wallahi zan auri ya Ibrahim sannan zan zauna da shi ko dani nawa farin cikin zai dirƙushe ina son ganin Abba na don Allah a kira mun shi zamuyi magana jikin Anty mariya yayi sanyi kiran Abba tayi juyowar da zatayi ganin ina aman jini numfashi na ina ta kokuwa da shi ban ƙara sanin in da hankalina ya ke ba


Sai da nayi kwana hudu kafun na dawo hankalina karan nan har Abba na ya fitar da tsan mani zan rayu narame sati ɗaya nayi ina kwance kamar wata nayi ,karan nan Hajiya tazo duba ni amma an ce mun bata jima ba na gaya wa Abba a daura auren kawai ko da ina Asibiti da ya tambayi ya Ibrahim ya ce a dakata a bari sai na warke nasan fushi yayi don bai Kirani ba sannan bai zo ba sai da Abba na ya ce ya na son ganin shi kafun ya zo shi yaje du bani a asibiti ko minti talatin bai yi ba ya dawo .




Zuciya ta a tunku she take matsaloli sunyi mun yawa in na tina irin ƙaryan da JB yayi mun ji nake kamar in haɗiye rai na duniya yanzu ba yadda masoyi yaci amanar masoyiyar shi ƙawa taci amanar ƙawar ta duniya ke nan a ranan da za,a sallame ni a ranan ya Ibrahim ya bar damaturu .






Lokacin da zamu bar asibitin a lokacin naga doctor in badan na gan shi sannan mun haɗa ido hudu ba bai yi niyar ƙariso wa ba kunya yaji ya kari so "ya jikin har an sallame ku kenan ? "e doctor daman kana nan na ɗauka ba kanan ne shiya sa Allah sarki "Nusaiba ba na son in ƙarasa bata miki rai shine nace doctor Garba ya duba ki .




Kayi fushi dai kawai taya zakace baza ka duba ni ba tunda ka gaji nima bazamu ƙara zuwa asibitin nan ba wani zamu koma kallon da yake mun kallo ne na wasu abubuwa da ban nasan waye doctor tunda yace har sun samu saɓani da matar shi a kaina haƙiƙa so mungun abu ne na tabbata da son da doctor ya ke mun da na ya Ibrahim shine asalin so amma in a kace JB yazo a wata mahangar don son shi ya zame mun illa ya cutar ni sallama yayi man ko kallo na ba yason yi jan motar mu,mukayi muka bar asibitin .




Sati na ɗaya da warke wa,ina kwance naga sai kirana a ke da wani number naƙi dauƙa cen wani zuciyar ta bani umarni da in ɗauka na ɗauƙa bayan sallama da nayi a gigice a ka amsa "a kwai wani ne yayi hatsari a mota duka yan cikin motar Allah ya musu rasuwa sai shi ƙadai ne ya rage a hanyar su ta zuwa Biu wayar shi babu kati shine muka kiraki don number ki ne yafi yawa wajen kiranki ".


A gigice nace malam ka gaya mun sunan shi da number wayar yace mun bai san ya zai yi ba ba kati a wayar gaya mishi wasu number da zai sa number mai shi zai fito a lokacin da yake gaya mun number na gigice ba kowa bane illa JB sake kiran mutumin nayi nace ya duba zai ga an rubuta my mum ya kira yace mun baya shiga ,na rasa wazan kira A'isha na kira nace bata da number abokin JB ko dai na yan gidan su tace bata da shi amma bari taje shagon shi ko zata,ga wani a shagon nace tayi sauri don babu nisa tsakanin su.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam




LAMBA NA ASHIRIN DA TAKWAS




Jiran kiran Aisha nakeyi ina ta zullumi sai naga kiranta ya shigo waya ta da sauri na ɗauƙa take sanar mun babu kowa a shagon ita kuma tana tsoron ta gayawa wani tunda babu komai a tsakaninsu yanzu tambayar ta nayi wata gani a bakin shagon tace wani makwabcin shine mai sai da magani nace ta bashi wayar sanar da shi nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login