Showing 3001 words to 6000 words out of 50955 words
Chapter 2 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam
na sosai a ranka ?
Numfashi ya ja kamun ya fara yi mun magana kamar haka "nayi soyayya a baya wanda na so faɗawa cikin tashin hankali na so ta sosai,tunda muke da ita nine na fi damuwa da ita akan ita, yar unguwar muce sunan ta A'isha da farko ta So ni daga baya kuwa ta shiga yi min wulaƙanci in ban kira ta ba ba zata taɓa kira na ba in kuwa ta kira ni wani maganar ce kawai zata gaya min daga baya wulaƙancin yayi yawa na haƙura".
Amma yanzu kam ba kwa tare ko don gaskiya ni kishi ne dani?
amsa ya bani da basa tare amma yana ganin status in ta ɗaura shima haka, "haba Noor ina so ka goge number ta daga wayarka don tunda bata son ka ni kam ina son ka, ya tabbatar min da ya goge sannan ya tura min number ta nace me zan yi da shi? anan ne na gane tabbas soyayya da yaro yarintar zai yi ta maka na nunawa JB tsantsar soyayya nasan zan samu matsala a gun iyayena don koda giya suka sha ba zasu taɓa yarda in auri yaron nan da sa'an ƙanina na uku ba amma babu ruwa na don shi nake so shine mahadin dukkan rayuwa ta, suna muka sawa junan mu Noor shi kuma Hayat tsabagen kunyar shi da nake ji ban taba kiran shi da sunan shi ba nasan duk wata soyayya da ba'a gina ta ta fuska mai kyau ba an dinga samun matsala farkon abun da ya ɓata mun rai kullum nine ke yawar kiran shi amma shi sai ya wuni bai Kira ni ba ina zaune naje gidan ƙawata kenan nayi' mishi' sallama ya amsa a WhatsApp bayan mun gaisa shine nace mi shi kai kullum nine ke yawan kiran ka amma ba komai kamar daman jira yake yi ya fara gaya min magana .
Ke nifa ba za ki takura min ba taya kinsan ina da shago sannan mutane zasu zo siyan kaya a guna in ƙi kulasu in biye Miki mu yi hira nifa kina takura min gaskiya wato ke dai burinki, kiji murya ta ko, gaskiya ki canja tunani " duk yasa jikina yayi sanyi a hanyar dawowa gida ne na kira shi nayi mishi' tas .
Ina da zuciya in raina ya ɓaci nayi mishi magana "Kaci sa'a don na kira ka don na cire ka cikin samari ka sani in na jure maka mai ƙarancin shekaru ba zata jure ba sannan ya kake mai da ni kamar wata marar gata sai kace soyayyar dole .
ka sani banyi banzan da wani bazai ganni da daraja ba yawan faranta maka da nake yi baya bayyana maka na rasa masu sona ba kaji da kyau .
Yaga raina ya ɓaci yayi shiru ko kulani bai yi ba kwana uku na daina yi mishi magana don in karɓawa kaina yanci tun daga nan ban ƙara shiga wani ruɗani na rashin mutuncin saba.
Naƙara da cewa muddin kawuce kwana uku baka zo in da nake ba wallahi ka nemi wata bani ba sannan in har kana tunanin ba zaka zo guna ba saboda mahaifiyar ka bata gari ka zauna sai ta dawo kace an bar maka kannen ka nono suke Sha ne da zaka gaya min haka bance karka bi umarnin iyayen ka ba amma ka sani ni ban gina rayuwata ta haka ba da to kawai ya bini .
Naji ya ce ikon Allah !
Kwana uku yayi yawa tsakanin mu kawai naji ya Kirani gobe yana kan hanya da safe na yi mishi girki na daddafa wasu abubuwan nau'ikan abinci a lokacin da na ganshi sai da nace Allah ya tsinewa soyayya yau kuma nan ya kawo ni ? siriri ne sosai bashi da jiki sai tsawo kaman dogon karfe a nan hankalina ya tafi don in ba soyayya ba babu abun da zai sa na kula JB don ƙaunar da nake yi mishi ne ya jawo haka tabbas haka muka ta surutu da shi don yadda ya ganni a hoto a zahiri nafi haka kyau a ranar na tsinci kaina cikin farin ciki kunya nake ji na cewa iyaye na wannan saurayi nane daman bance zaizo ba ganin shi suka yi na kuma ce da iyayena ƙanin kawata ne. zai wuce Gashua .
Dare yayi kusan ƙarfe tara i yaye na sun yarda dani,sun yaba da hankali na da tarbiyyar da suka bani basu kawo komai a ransu ba a daren soyayya ta ɗebo mu muka aikata alfasha ban baro ɗakin ba sai da nayi wanka kafin kusan goma da rabi na fito naci azaba sosai amma shi kuma ko a jikin shi babu ruwan shi naga farin ciki a tattare da shi na wuce ɗakina dake cikin gida bacci ne ya gagara ɗauka na.
ganin hoton mu nake yi a ido na yau ba kuɗi ba ba komai na rasa budurci na na tsawon shekaru talatin da uku a duniya saboda so a washe gari da safe nine naje ta shin shi yayi Sallah bayan yayi Sallah ya jawoni jikin shi nayi rumfa da ƙirjinsa, a safen muka ƙara kasancewa da junan mu.
Tare muka shiga wanka dani da shi kamar wasu ma'aurata, idan na tuna yanzu wannan yaron shine yayi min abun da manya ma ba su samu dama a kaina ba sai takaici ya dame ni, abun haushin ma Naira ɗari biyu ne ya hada su da kanne na don baizo da komai ba daga shi sai kayan jikin shi kawai yazo da shi .
Wajajen ƙarfe biyu yace zai koma gida, ya koma garinsu tunda ya tafi daman wayar shi ta ɓaci a hanyar zuwa kwana biyar bai Kirani ba, lokacin da ya Kira ni maza mutanan mu wasu kam kalar halin su irin nasaran su ce a rayuwa kwata-kwata JB bai dace da tsarin rayuwa ta ba sai sajen sane irin wanda na ke so amma na miji kamar bishiya.
"Saunawa kika Kira ni?"
Abun ya bani haushi bai ma tambayi ya lafiya ta ba amma yake tambayar sau nawa na kira shi tsabagen takaici shiru kawai nayi narasa abun faɗa kawai a haka muka ci gaba da gudanar da soyayyarmu ba tare da mun yi nadama ba, a duk lokacin da muka kasance tare sai naga wani sabon soyayya a gun JB .
Mungu ne maƙaryaci ɗan sharri ne azzalumi har gidan mu yazo ya keta min haddi don so ko cuta Allah ka saka min sakayya na har a bada Allah kasa yadda zan auri wani ba tare da na kai mishi daraja taba kasa shima kar ya auri kamila.
A karon nan kuma son da yake min yafi wanda nake yi mishi ya fara fita a raina sosai wani rana kawai mahaifina ya Kira ni akan cewa zai yi min miji akwai wanda zai ba dani a shi amma na ƙi amincewa ga mutumin babba ne ga kuɗi ga ilimi amma naƙi shi, kiran JB nayi nace akwai babbar matsala sosai tambaya ta yayi.
"matsala a kan me kenan ki gaya min mata ta"?
a na so a haɗa ni aure da wani ina ji JB yace ''babbar magana!'' daga nan zuga ni yayi yace kar na yarda nace to na amince ni kai kadai nake so Saide kuma kash! namiji munafiki ne na nunawa a jarida amma masu hali irin na JB.
Maza sun daɗe suna cutar da mu sun daɗe suna jefa mu cikin ukuba da tashin hankali zance maza lawurjen wandonsu mutum ɗaya ne mai ɗinka wa wallahi wasu mazan ba su da maƙiya sama da mu a tattare da muma haka.
Ina cikin zama na rana ɗaya an rabani da kima na da kuma daraja ta da martaba na hawaye Masu zafi da ciwo ne ke zuɓa daga ido na' ni kai na abun tsoro ye bani ina wayo na da nake tinƙaho da shi.
So mungune wannan kalman shine ya ruguza wa ,wasu lissafi wannan lafazin shike bawa sheɗan daɗin zuga mu ,ina ma nayi zamana a haka .
[11/5, 11:20] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
MARUBUTAN JAHAR YOBE
Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam
LAMBA TA UKU
*Labarin Nusaiba abun dubawa ne ina yan mata labarin Nusaiba da JB ya,isa kugane maza halin su duk ɗaya ne amma a kwai kaɗan na kirki a* *cikin su Allah ka shiga lamarin Nusaiba ka dafa mata kabata juriya* *kasakawa duk macen da ,a ka cutar da ita ta fannin soyayya.*
*Maza maza halin ku sai wanda ya halicce ku*
A duk lokacin da nake cikin farin ciki tabbas ina jin daɗi sosai nafi bawa JB lokaci na fiye da komai haka zai ce in baya komai ki hau online a kwai magana mai daɗi bana video call amma dole, saida na fara.
JB ne ya kira ni wato irinsu JB halin su daban ne bana raba ɗaya cikin biyu soyayyar da JB yayi soyayya ce wanda har da na yarinta a cikin ta ba ya hangen nesa ko kaɗan ina cikin farin ciki in har zan ga ya Kira ni kamar an yi min kyautar dubu goma in nace zanje kitso sai ya ce yafi son gashi na a haka .
Watarana JB ya yi min magana
"ki yi haƙuri don Allah "
Me yasa kake ba ni haƙuri
me ya faru ne?
"a gaskiya ba zan cutar da ke ba iyayena sunce sun zaɓa min mata sannan yarinyar tun ban kai haka ba take so na nasan auren mu dake ba lalle ne ya kasance ba muddin haka ya kasance me zance miki don Allah ki fahimce ni sannan in kin samu wani kiyi auren ki kar ki jira ni don jira na gaibu ne har ga Allah, a lokacin da yake gaya min tamkar an watsa min ruwan zafi.
Me yasa ba ka sanar dani ba sai da ka bari son ka yayi min illa kafin nan? me yasa sai da ka bari muka samu matsala kafin zaka sanar dani ka janye maganar auren mu? me yasa kayi min haka?
Daman yaudara ce ta shigo da kai cikin rayuwa ta?
Ka cuce ni Allah kuma zai yi min Sakayya ta hanyar da ba ka yi zato ba amma ka sani ban cutar da kai ba muddin akwai wanda ya cutar da wani Allah ya bi mishi kadun shi wallahi zan barka ne kayi aure amma muddin nasa wani abu a raina har ka mutu ba za ka yi aure ba.
A lokacin da yaga saƙon ranshi ya sosu kalmar ''Hmm'' kawai ya rubuta min ni kuwa kamar zuga ni a keyi na fara magana "da na san kai mayaudari ne da ban baka kaina ba amma muddin kace tukunyan wani ba za ta- tafasa ba haƙiƙa naka ko zafi ba zai yi ba sannan ka sani ba lalle bane ka auri kamila, raina ya ɓaci na gaya mishi magana sannan nace mishi mu zuba mu gani.
A ranar ciwon zuciya ta ya tashi nasha wahala don alluran da aka yi min masu tsada ne da su, magani, kuwa an siya min ya kai na dubu talatin duk dangi na suna tausaya min muddin ciwo na ya tashi to kowa sai ya tausaya min, naga rayuwa sati nayi ina kwance a asibiti saboda numfashi na rabewa yake yi nayi da na sanin haɗuwa da JB don ya ɗaga min hankali sosai.
Rufe waya ta nayi saboda nasan babu wata alaƙa da zai shiga tsakanin mu da JB tunda ya furta a yadda na fuskanci JB ƙarya yake yi ya yi hakan ne kawai don ya guje min, babu ra'ayin aure a tattare da shi kawai ya samu mafita ne kawai na barshi da Allah babu wanda yasan me ya haɗa mu tunda daman gidan mu basu san da shi ba sun ɗauka kawai ciwo na ne ya tashi sun bani kulawa sosai a tunanin yan gidan mu ban ƙara sa wani a raina ba tunda Muhammad ya rasu mahaifina har ya shiga ruɗani da fargaba yadda ya je ya duba ni.
Ina zaune naga anyi min magana a kan cewa in yi haƙuri don Allah komai ya wuce "JB bana ƙara soyayya a cikin rayuwa ta ni ban san daɗin soyayya ba wahalar ta na sani, Muhammad bai taɓa sani damuwa ba, yakan girmama buƙata ta wallahi na rasa me sona na har abadan don haka bana jin wani zai ƙara samun gurbi ta soyayya a tattare dani .
Sai ce mun yayi
"Ko da na dawo gare ki "?
Koda ka dawo gare ni ba zan yi soyayya ba don babu komai cikin ta sai azaba amma na gode wa Allah yanzu fa idan kayi la'akari soyayyar da ka nuna min na lokaci ne ƙalilan don haka mu bar maganar zai fi ko dai me ka gani?
"Ki yafe min ban san za ki jefa rayuwar ki cikin tashin hankali ba amma ina neman afuwa ki yafe min ".
Jiki na ne yayi sanyi nace babu damuwa komai ya wuce Allah ya rufa asiri muka dawo kamar ba muyi komai ba bayan yayi min alƙawari zai shawo kan iyayen shi sai naji sanyi a raina sosai in banda so.
JB banda sana'ar da yake yi wanda kudin sana'ar in an haɗa shi bazai kai miliyan ɗaya ba amma yanzu yana yaron shi wani zama za muyi da shi kenan don a yadda yake koda ance ya kawo kuɗin aure na wallahi ba shida shi dubu hudu ne ya shiga tsakanin mu kati kuwa ban taɓa ganin shi a waya ta da zumar shi ya sanya min ba. wannan soyayyar da shi da babu duk ɗaya ne . Lokacin da muka yi faɗa har zance ya turo account no na tura mishi kuɗin shi amma kawai nayi haƙuri da yawa a cikinmu mu ne mu ke janyo wa samari suke raina mu ba don komai ba sai don yawan yarda da muke yi da su da sauri ba mu kiwaci hankalin su ba muke basu saurin yarda su kuma yan yarima a sha kiɗa ne maza gaskiya basu da imani su cutar da mu ko don sun ga su ba ta yadda za'ayi a gane sun banzatar da kan sune duk yawan rashin mutuncin su basa nadama Allah ya ɗaura su a kan mu . shiyasa suke haka amma na tabbata a kan ƙannen su za'a rama mana ko kan ƴaƴan su azzalumai.
A kullum ina nadama sosai sannan na roƙi Allah ya yafe min Allah da kan shi ya ce zinar ma kada mu kusance ta yau gashi son wanda zai walaƙanta ni ya janyo min na rasa komai nawa nayi hawaye a duk lokacin da nake kuka babu wanda nake gaya mishi damuwa ta don bashi da magani .
Idan mun shirya haka za mu yi ta marmarin juna kamar ba za mu ƙara faɗa ba ashe kan faɗa ya na gaban mu, na fuskanci tunda muka haɗu, ciwo na ya cika tashi ba don komai ba sai matsalar JB amma kuma ni Nusaiba nayi da na sanin JB don ya zame min ƙarfen ƙafa wannan shine a sanadin ƙadddara ko dai ince a haka ƙaddara ta yazo min, ni Nusaiba wallahi so mugun abu ne ina tsintar kaina cikin jin daɗi don JB ya iya kalamai masu ratsa zuciya shine baiwar da Allah yayi mishi zan jure amma ba a nan gizo ke saƙar ba bana iya jurewa na minti talatin ba tare da naji muryar shi ba, abun walaƙancin ma shine zan kira sai yayi sau uku kafin ya ɗauka koda ya ɗauka to wata ƙaryar zai min ina ganin shi a online amma zai iya ce min ya dade bai hauba.
Tambayar shi nayi me yasa baya daukar waya wannan baya kyautawa sannan wannan cin zali ne bana kaɗan ba yana dubawa daya gani bai bani amsa ba naga yayi blocking ɗina a facebook da Whatsapp da telegram har ya cire photon sa akan dp duk na duba babu komai nace to naso gaya mishi magana amma kawai na ɗaure JB mungu ne azzalumi mayaudari, yafi son iyayena su dinga kashe kuɗi a kan jinya ta babu ruwan shi a nawa tunanin ban yi mishi magana mai zafi ba.
Da na cancanci kyautar fushi daga gareshi walaƙancin ne ya tashi kawai irin nashi Allah ya shiga lamarina ya sakamun to kowa ce hanya yabimin hakki na ,maza a duk lokacin da ka yadda da namiji tashin farko zai baka kunya ne bana kaɗan ba JB yagama da rayuwa ta.
[11/5, 11:20] Maman Khairat: *WATA MAHANGAR*
Story and writing by
*Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam*
LAMBA TA HUDU
Lumshe idanuna na yi a karo na barkatai ina cije leɓɓana da matuƙar ƙarfi. Tare da sakin sakekken ajiyar zuciya, idanuna tar na buɗe a bisa rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakani na da sararin samaniya.
A hankali nake jin ɗumin hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatar fuskata da ta sha gyara da dilkar amare tayi fes da ita. Duk inda ruwan hawayen ya bi ji nake tamkar ana watsa mini garwashin wuta, duk yanda naso danne kukan da ke ƙoƙarin suɓuce mini sai da lamarin ya ci tura. Cikin sauri na zaro kallabin dake kaina na tura cikin bakina, a ƙoƙarin hana sautin kukan fita.
Ɗakin cike yake maƙil da ƙawayena da suke jiran wayewar garin gobe domin gabatar da dinner ɗin bikina. Jibi kuwa warhaka na zama matar aure na zama mallakin yaya Sufyan kuma halaliyarsa. Babu shiri sautin kukan ya karaɗe dukkan ɗakin da duhun daren ya mamaye ko ina, muryar Sakina babbar aminiyata ya ratsa ƙofofin kunnuwana. Ta kunna fitilar ɗakin take haske ya gauraye ko'ina, ta nufo ni tare da jeranta mini tambayar lafiya wani na bin wani, kwantar da kaina kawai nayi a kan kafaɗarta ina cigaba da kukan tausayin kaina da yanda zanen ƙaddarata take ƙoƙarin rufe shafukan farin cikin rayuwata.
"Ke Surayya wai lafiya kuwa?, ko fasawa yaya Sufyan ɗin ya yi?".
Ban iya furta