Showing 18001 words to 21000 words out of 50955 words
Chapter 7 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam
na rage yawan kiran shi da nakeyi ,badan komai ba sai don in samu sauƙi a zuciya ta a hakan zan iya cewa Ma sha Allah .ganin nayi kwana biyu ban fita ba shirya wa nayi kusan ƙarfe biyar zanje in duba ƙawata maman Sadiq tambayan JB nayi ce mun yayi kar in kai mangari ba in dawo da wuri da to na bishi . naje munata hira da,ita har ƙarfe bakwai na dare ko sallah bamuyi ba ganin kar in tsaya Sallah dare yayi sallama mukayi ,na dawo gida ina zuwa alwala nayi sai da nayi sallah kafun na kira JB yana ɗauka sheda mishi nayi kaina ciwo yake yi sannu ya ce mun tambaya na yayi yaushe nadawo cemishi nayi kusan ƙarfe takwas ya dinga masifa banace karki kai mangari ba ,ba gashi kin dawo da ciwon kai zaki dameni surutu yatayi haƙuri na bashi na sha magani na kwanta.
Ƙwana biyu ina kwance ciwon kai ya takura mun ko waya bana,iya ɗauka wayar ma,a hannun Aliyu yake a she JB ya kira shi kuma Aliyu ya ɗauka jin muryan shi yaɗinga yiwa Aliyu masifa .
Ina bacci a ka kawo mun wayar tashina Aliyu yayi ya bani ya juya shima bai ce an Kirani ba ranshi ya ɓaci sai ƙarfe goma na dare kafun ya Kirani ,ko sallama bai yi ba ya dinga masifa "a waye kika bada wayar ki yayi mun rashin kunya ko dai a saurayin ki ne wannan cin mutunci ne taya zaki ɗauki waya kibawa wani".
Ka tsaya mana ya kake yi mun masifa kamar wani wanda zai dokeni ka tsaya in yi maka magana ka gagara tsayuwa jinayi ya kashe wayar nace zancen banza daman an daɗe ba,ayi faɗa da kai ba ,daga ciwon kai tsintar kai na ,nayi a asibiti an samun dirif juyawa nayi naga guda biyu sun ƙare a lama ya nuna na daɗe a asibiti na uku ne a jiki na a she tun da na kwanta numfashi na yafara sarƙewa ciwo na ya tashi cewa nayi Hajiya ta bani waya ta miƙa mun tayi .
Buɗewa nayi cin karo nayi da saƙon JB "kin zaɓi farin cikin mutane da nawa kina ganin kin rufa mun asiri kin soni, ina yaro ƙarami to nima haka ban kula yara sa,annun aure na ba natsaya kulaki ,kema haka manyan masu kuɗi suna sonki kinƙi su ,dan Allah mu haƙura da juna zaifi kawai bana so ki rasa ranki ta dalili na nasan yanzu a kwance kike bakida lafiya ina yi miki fatan alkairi .
Jinayi hawaye suna bin ƙunci na ba kalaman JB ne suke damu na,ba yawan damuwa da nayi da shi gani nake in babu shi ba zan ,iya rayuwa ba sau daya wa yawan nunawa samari tsantsan so har su gane son da muke yi musu yafi nasu yawa to nanne hanyar basu daman cin zarafin mu,ko dan na daɗe ban yi soyayya ba sai a kanshi ban sani ba ace masoyin gaskiya ba zai ganni a kwance ya cimun mutunci ba. juyawar da zanyi muka haɗa ido hudu da doctor Ibrahim Sulaiman....
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA TA GOMA SHA DAYA
Na sha jin ana cewar zuciya tana son mai kyautata mata sai dai na rasa wacce irin zuciya ce a cikin tawa ƙirjin. Da ta kasa amsar yaya Sufyan a matsayin masoyi.
Dafe kaina nayi da nake jin kamar zai tarwatse gida biyu don ciwon da yake mini, zuciyata tana harbawa da sauri da sauri. Sai da aka ɗauki mintina biyu kafin ya maido mini da amsa da kalmar innalilahi wa inna ilahir raji'un, sannan ya yi mini saƙon murya da farko na zargi kunnuwa da rashin jiyo mini abin da yake faɗi. Sai da na ƙara saurara a karo na biyu na tabbatar da cewa kuka yake yi bilhaƙƙi, yana shaida mini ba zai iya aiwatar da komai a rayuwarsa ba tare da ina kusa dashi ba ko guje mini da ya yi a baya ya zabga babban da na-sa-ni. Take na ji jikina ya ƙara yin la'asar idanuna ya daina gano mini komai sai baƙin duhu. Rayuwar da muka yi da Suraj ya fara dawo mini sabo fil.
Ya kasance malamin mu lokacin muna aji uku a babban sakandiri. Yana ɗaya daga cikin malaman da suka kasance abin tsoro ga ɗalibai, baya dariya ko bisa kuskure yayin da yake koyarwa sannan ba ya ƙarban uzuri balle ɗaga ƙafa. Darasin lissafi yake mana na fi kowa tsoronsa a kaf ajin mu hakan ya sanya ko darasin da yake koyar damu bana fahimta, duk gwajin da ya yi mana sai na faɗi domin ko sahun waɗanda suka haye maki biyar bana kai wa.
Hakan ya sanya shi tsaurarawa da sanya ido a kaina fiye da kowa, ko sunansa naji an ambata zuciyata sai ta tsinke balle tozali da fuskarsa da babu rahama a tattare da ita.
Tun da ya shigo bugun ƙirjina ya tsananta saboda fargaban kar sunana ya faɗo cikin waɗanda basu haye gwajin da yake mana a duk lokacin da ya kammala darasi ba. Sakina dake zaune kusa da ni ta riƙe hannuna saboda rawar da jikina ya ɗauka kamar mazari, zubar hawayen idanuna ya yi dai dai da sanda ya ƙwala ƙiran sunana. Na ƙara daburcewa.
Tsawar da ya daka mini ya tursasa mini runtsun idanuna da har yanzu yake tsiyayar da ƙwalla tamkar burɗaɗɗen famfo. Kaina a ƙasa na iso gabansa na zube akan gwiwoyina, bai ce da ni komai ba sai ma cigaba da ƙiran waɗanda basu haye ba yake yi. Sai da duk suka fito ya ce"ku je ku zauna yau nayi muku alfarmata da ba kullum ake yin katari da shi ba".
Abin da ya tokare mini ƙirji ne naji ya wuce na miƙe da sauri zan wuce, ya dakatar dani da faɗin"Madam ban da ke". Na koma da baya duk suka koma suka zauna ban da ni. Bai ce dani uffan ba har sai da ya ƙare darasin tsaf ya bada aikin gida, sannan ya dube Ni fuskarsa tamkar magribar ɗinya haɗi da furta"ke kuma za ki zauna a nan har sai wani malamin ya shigo". Yana dasa aya nan ya fice kukan na cigaba da shi saboda sanyin da duk gaɓoɓin ƙafata ya yi, Sakina ce ke ta jeranta mini sannu wani na bin wani.
Shigowar Malam Saminu ya sanya ni jin wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko gaisuwar da 'yan ajin suka miƙe suke yi masa bai amsa ba ya fara da tambaya ta me nake yi a wajen. Na sanar dashi bai ce komai ba illa jijjiga kansa da ya yi ya fice ransa a matuƙar ɓace.
Kafin lokacin tashi zazzaɓi mai zafi ya rufe Ni ko da na isa gida ban iya assala komai ba face kwanciya. Hawayen takaici ne suke gudu a bisa fuskata na rasa dalilin tsanar malam Suraj gare ni da yake yi mini hakan, kamar daga sama naje jin muryar yaya Sufyan da ya sanya ni saurin tashi na fita. Zaune na iske sa da yaya Sa'eed da kuma Hajiya.
Ciki ciki nayi sallama kafin na yiwa kaina mazauni. Yaya Sa'eed ya hararo ni tare da faɗin"kafurai kika tarar a wajen shi yasa kika adana sallamarki ko?". Da sauri na zaro ido na ce "wallahi nayi" . Taɓe baki ya yi yana mayar da kansa tare da mayar da hankalinsa a wayarsa da yake latsawa, idona na zube a bisa fuskar yaya Sufyan ina yi masa sannu da zuwa.
Fuskarsa tamkar gonar auduga ya amsa mini yana ɗaurawa da"kaga autar Hajiya da Momma". Sunkuyar da kaina nayi ina murza zoben dake saƙale a hannu, ban ɗago ba naji ya cigaba da cewa"ki rabu da Sa'eed yau sai an yi masa uzuri shi kaɗai ya san abin da yake ji". Ya ƙare maganar yana kashe mini ido ɗaya dai dai sanda na ɗago kaina, ƙunshe dariyata nayi da ido nayi masa alamar me ya faru?.
Kafin ya yi wata magana yaya Sa'eed ya tare shi da faɗin " wallahi na gaya maka ka kiyaye ni fa bana son raini Sufyan".
"To yaya babba meye kuma nayi?, naga dai bani na kar zomon nan ba rataya aka bani".
A kufule yaya Sa'eed ya kallo Hajiya da ta maida hankalinta ga TV ya ce" ki yi wa yaron nan kashedi bana son raini ni fa".
"Ba ruwana da sha'anin ku".
Ƙasa nayi da kaina ina dariya don yanda yaya Sa'eed ya yi kici kici da fuska a dole baya son raini, Anty Sadiya ta shigo da tray tana ajiye wa a dinning tare da furtawa Hajiya cewar komai ya kammala. Sannu tayi mata sannan ta iso ta zauna tana tambayar yaya Sufyan abin da ke faru, ɗage kafaɗa ya yi alamar me sa ni ba yana mata nuni da yaya Sa'eed.
Har muka wuce dinning area ɗin babu wanda ya ce ƙalla, tare da Anty Sadiya da lokacin ita ce bata yi aure ba muka yi serving ɗin kowa. Kasancewar ranar Abba baya gari. Muna haɗa ido da yaya Sufyan nake jin wani sabon dariya yana zuwar mini dole na danne shi don gudun ɓacin rai yaya Sa'eed.
Gyaran murya yaya Sufyan ya yi, yana kallon yaya Sa'eed da yake juya cokalin kawai a cikin abincin ya ce"malam ka ci abinci da don wallahi yunwa ba ta da hankali, kuma ba ƙanwar su Abba ba c...". Bai ƙarisa ba sakamakon cokalin da ya jefa masa ya kauce da sauri yana dariya. Tsam ya tashi yana huci"Hajiya na gaya miki yaron nan ya gama raina ni, gidan Momma zan koma". Yana gamawa ya fice daga falon gabaɗaya. Duk dariya muka tuntsire dashi ni kam har da riƙe ciki Hajiya ke tambayan yaya Sufyan abin da ya faru.
"Wata yarinya yake so tun da daɗewa ya kasa faɗa mata. Sun daɗe suna alaƙa a matsayin aboka ashe shi ba haka ya ɗauka ba, sai da yau da na raka shi wajen ta muka iske ta da wani da ya tambayi wanene sai take sanar damu cewar wanda zata aura ne. Shine fa duk ya birkice yake ta wannan ƙuncin, bayan shi ya tsaya ganin ruwa kwaɗo ya yi masa ƙafa".
Jijjiga kansa kawai Hajiya tayi ta cigaba da cin abincinta, ni da Anty Sadiya kuwa sai da muka ji ƙwaƙwaf don har hotonta ya nuna mana 'yar guntuwa da ita a gefensa. Na sha dariya sai da na ji cikina ya fara ƙullewa sannan na tsagaita. Muna gamawa na haɗe kwanukan na kai kicin, nake naji cikina ya bada sautin ƙululu tunawa da nayi da aikin gidan da malam Suraj ya bayar da ban yi ba. Na fita da sauri zan wuce na yi kiciɓus da yaya Sufyan ya tsare ni da ido kafin ya furta"meye kika birkice haka?". Take ƙwalla ya ciko mini koramar idona, muryarta tana rawa na furta"aikin gida aka bamu kuma ban iya ba". Taƙaitaccen murmushi ya yi"to shikenan ki je ki jira ni na kaiwa Sa'eed abinci, sai nazo na taya ki ko?".
Kaina na ɗaga masa cike da jin daɗi, na ware idona akan fuskarsa da har yanzu yake sakin murmushi na ce"baka taɓa fushi da yaya Sa'eed ". Rausayar da kai ya yi yana shafi ƙeyarsa kana ya ce"shima baya iya fushi da ni na gudun lokaci, na tabbatar yanzu yana can yana tunanina". Murmushi kawai na yi na matsa na bashi waje ni kuma na fita izuwa ɗaki. Sai da na yi wanka na yi sallan isha'i sannan na ɗauko takardan ina ƙara dubawa, a saki sakekken ajiyar zuciya gani na saka gane komai a ciki.
Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yaya Sufyan da yake tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa. Na kwaɓe fuska na ce"kai fa nake ta jira". Ya saki murmushin da ya zamo ɗabi'arsa kana ya tako a hankali ya zauna a ƙasa a gabana. Na yi saurin dirowa daga kan kujera da nake na dawo ƙasa nima na zauna, dariya kawai ya yi ya jijjiga kansa ya umarce ni da na miƙo masa takardan na miƙa masa da rawar jiki.
Ya karɓa yana dubawa sai ya ya kalla sosai sannan ya ce na miƙa masa biro na bashi, ya fara solving ɗin tambayoyin sai da ya gama tas ya ɗaura mini takardan a bisa cinya. Cike da tsantsar farin ciki na zari takardar ina kallo na mai da idona gare shi na furta"na gode sosai ka ceci rayuwata".
"Na gode sosai ka ceci rayuwata".
Ya furta cikin kwaikwayon muryata na yi kasa da kaina ina yin dariya, ya miƙe tare da faɗin"bari na wuce gobe ina da class ɗin safe". Nima tashi tsaye na yi"kuna ƙoƙari fa bi kam gani nake kamar ba zan iya koyarwa ba".
Ya galla mini harara"ai kuwa koyarwa ba ƙaramin aiki bane sai dai lecturing da sauƙi. Mafi yawan lokuta guiding ɗin su kawai za ka yi". Jinjina kaina na yi alamar gamsuwa da zancen na san, na rako shi har wajen motarsa ina masa addu'ar sauƙa lafiya da saƙon gaisuwata ga Momma.
Washe gari na tashi cikin nishaɗi haka na tafi makaranta, darasi ɗaya muka yi na biyun kuwa Malam Suraj ya shigo. Tsit ajin ya ɗauki shuru tamkar babu wani halitta mai motsi a cikinsa. Ya ce a haɗa masa aikin gidan da ya bayar da zumuɗina na ciro nawa daga cikin jaka na miƙa.
A ajin ya zauna yana makawa har ya gama ya fara ƙiran waɗanda basu haye maki biyar ba, kamar daga sama na ji ya ambaci sunana. Cikina ya bada ƙarar ƙululu na miƙe tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki na fita. Bulala uku uku aka yi mana muka dawo muka zauna, tunda na kifa kaina akan benci ina kuka har ya gama darasin ya fice ban ɗago ba. Sai da aka tashi tara sannan na fito na wanke fuskana, Sakina ta zauna kusa da ni tana faɗin"don Allah ki daina wannan kuka tun ɗazu fa kike yin sa". Ban kula ta don yanda nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin rufe ni. Ta dafa kaɗata"ki yi haƙuri don Allah". Sai a lokacin na yi ƙarfin halin faɗin"ke fa ki haye maki biyar kuma wanda na yi kika kwafa, kawai ni ɗin ya tsane ni me nayi masa?".
"Bai tsane ki ba hasalima sonki ne ya yi masa da har ya rasa ta yanda zai fara sanar dake. Takaicin ba zai iya tunkarar ki da zancen ba ya sanya shi yi miki waɗannan abubuwan".
Tare muka waiga ni da Sakina don ganin mai maganar, Sabira 'yar ajinmu ce tsaye a bayan mu kafin ta tako ta zauna akan dakalin ƙofar ajin da muke zaune a kai.
"Ke Sabira ke kuma yaya aka yi kika san duk wannan, shi ya faɗa miki?".
Ta yi mana wani kallon da na gaza gane abinda take nufi kafin ta furta"ba shi ya faɗa mini ba amma kowa dake cikin makarantar nan ya san da wannan abunda na faɗa muku yanzu. Malam Suraj son Surayya take yi so mai tsananin gaske, a cikin biyu nan dole akwai dalilin da ya sanya shi yake nuna kamar ya tsane ta a fili. Ko dai yana tunanin ba zai iya samun soyayyarta ba bisa wasu dalilai nashi na karan kan shi, ko kuma ya na tsoron ya sanar da ita ta ƙi amsar sa hakan ta jawo masa raina daga sauran ɗalibai".
Duk shuru muka muna nazarin zantukan bayan daki-daki. Ta katse mana hanzari ta hanyar cewar" kun taɓa lura da cewar duk ranar da ya shigo aji bai ganta ba baya taɓa samun nutsuwa?. Kuma ranar komai cikin sanyin jiki zai aiwatar dashi saɓani in tana cikin ajin. Kullum sai ya ƙira sunanki cikin waɗanda basu haye makin ɗin da yake buƙata a gwajin da yake mana ba, don kawai ya gan ki ko kin yi dai dai fa sai ya ƙira sunanki don kawai ya sama nutsuwa a ransa ya kuma tabbatar da kasantuwarki cikin ajin".
Ƙarƙafan ajiyar zuciya na sauƙe ina zabga tagumi da hannu bibbiyu, kaina gabaɗaya ya kulle na rasa ta inda zan fara tantance zantukan na Sabira na yi musu rankaɗe da rairaya na ware aya na watsar da tsakuwa.
"Maganarki abun dubawa ne tabbas, da akwai alamar ambayar akan abubuwan nan da Malam Suraj yake aikewa. Amma ta yaya zamu tabbatar da abinda kika faɗa".
Sai da ta gyara zaman ta kana ta ce"lokaci ne zai tabbatar da hakan amma ina da tabbacin malam Suraj yana son Surayya. Kuma dole komai daren daɗewa zai furta hakan a gare ta domin ba zai taɓa iya riƙe abin a ransa ba, sannan ko ba ki amshi tayin soyayyar sa ba sai sama nutsuwa domin ta furzar da abinda yake sukar ransa har yake masa zogi a cikin zuciya".
Tsam na miƙe tsaye ina cewa"don Allah ku daina wannan hashashen domin ba zai taɓa zama gaskiya ba". Ina dasa aya a nan na koma cikin aji na zauna, sai dai na gaza samun nutsuwa har aka tashi ban dawo dai dai ba. Kwana nayi da tunanin abin a raina ina kwantanta girman bayyanannen tsanar da yake nuni mini a zahiri, babu yanda za'a yi a ce wai akwai soyayyata ko da misƙala zarratin a cikin zuciyarsa.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR
©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam
LAMBA TA GOMA SHA BIYU
Tsanar da Malam Suraj yake gwada mini kullum ƙara ƙaruwa yake yi, ko yaushe ina cikin waɗanda suka faɗi a gwajinsa. Hatta 'yan uwansa ragowar malamai zai da suka fahimci hakan . Bana taɓa samun nutsuwa idan yana cikin aji haka nan bana taɓa fahimtar darasinsa, sai dai