Showing 24001 words to 27000 words out of 50955 words

Chapter 9 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2129

lokaci yayi mun Alluran a gida .




Sallamar mu,sukayi na dawo gida ,a nan ma yan unguwar mu suka ta tururuwa wajen zuwa duba ni daga na rufe ido ,na Muhammad nake gani yana roƙona kar ,in bari a ci zarafina .


A darán Ibrahim ya sauƙa bai wuce barno ba a damaturu ya tsaya ban san ya zo ba sai washe gari naga ya shigo duba ni ,banyi mamaki ba .




"Yau she kazo"?


"Wajajen ƙarfe goma kina bacci ya jikin da sauƙi ko ɗan naga ,alama kin sha jiki sosai ,ki daina yawan sa tinani a ranki don Allah wallahi ko da baki aure ni ba ki ɗauke ni a matsayin abokin ki, zaki samu ilimi mai tarin yawa daga gareni ko yaya ne bana son ki shiga wani hali "tinawa nayi da maganar Abba na cewa ya bani kwana sha biyar gashi har yau banga kiran JB ba muna tare da Ibrahim nace ya miƙa mun waya ta zan buɗe "meyasa kika kashe wayar ki bake tinanin a kiraki a gun aiki ne ko dai wani abu mai mahimmanci haba Nusaiba"?.


Buɗe wayar nayi a take nashiga Whatsapp cin karo nayi da saƙon mutane da yawa har da wani number a na roƙona da in buɗe waya ta a kwai matsala nagama karanta wa kenan saƙon JB ya shigo a kan inyi haƙuri zai, gaya mun magana koda a ce zagin shi zan yi in yi mishi afuwa in kula shi haƙuri yata bani ,a kan in har na yadda zan ganshi gobe ya shiga wani hali.


Amsar da na bashi "kayi hakuri JB baka dace da rayuwa taba nasan Kanada rauni sannan nayi maka halacci ka saka mun da tsiya bani da lokacin ka koda, mutuwa zakayi bazance karƙa mutu ba nasan zaka tarar da abun da ka shuka yau she kafara soyayya da har kake ganin nakai matsayin wanda zaka walaƙanta bari kaji nagama da babin ka .




Ibrahim ne yayi mun magana "kin barni sai latse latsen waya kike yi ko dai kuna magana da saurayin ki,ne in barki ki huta don ke nazo garin nan meyasa kike walaƙanta nine haba Nusaiba kiji tausayi na ,mana Abba ya ce in zo akwai magana Allah yasa ba cewa, zai yi yafasa aura mun ke ba .


Ikon Allah !


Ibrahim sirrin zuciya tane bayyana maka wanda nake so koda a, ce bana sonka bazan nuna maka JB ba don rainani zakayi murmushi nayi sai kusan azahar yafita daga ɗakin yana fita na rushe da kuka damuwa tayi mun yawa bayan la,asar sai ga doctor yazo yi mun allura har falon Abba ya ,shiga Ibrahim yana gefe yana kallo neman Jijiyar tawa wahala gareta waje biyu ya bula sai jin muryan Ibrahim nayi"malam ko dan kaga ba jikin ka bane baka san yana mata zafi ba kayi a hankali dan Allah .


Ko kula shi bai yi ba yaci gaba da aikin shi ya gama ya fice ko sallama bai yi mun ba sai naji wani iri a raina yanzu kenan ranshi ya ɓaci kenan .


"Ya Ibrahim meyasa kayi mishi haka doctor nane kodai baka gane shi ba ?


Nagane shi mana


"Kuna da matsala baza ki gane abun da na lura da likitan nan ba sonki yake yi bakiga kallon da yake yi miki ba shiya sa ".


Ficewa nayi na barshi a falon na tafi ɗaki waya ta na ɗauka sai ga kiran JB a dai dai lokacin Ibrahim ya shigo naga ya karbi wayar ya sanya shi ,a kunnen shi sannan ya tsare ni da ido....
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


MARUBUTAN JAHAR YOBE


Story and writing by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam




Kai tsaye ki sanya kuɗin ki ta wannan asusun 400 Amina maaji account no 4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan number 08068748984


LAMBA NA SHA BIYAR


____________Bansan me yace ba sai jinayi yace ga wayar ki "me yasa zaka karɓi waya ta ya Ibrahim me hakan yake nufi kenan"?




Kiyi haƙuri Nusaiba bana son ki shiga wani hali amma kisani bazan jure cin fuska daga kowa ce fanni a gareki ba zuciyar ki ,ta dagule kin cenza ya kamata ki hango wata mahangar in ba haka ba ,muddin kika zurfafa soyayya zakiyi naɗama waye wannan wanda ya kiraki nasan shi shine yayi mun pop na gida na shida wasu yayun shi ɗan barno ne mai ya haɗaki da wannan yaron ?


Ikon Allah ya haka!


Ka tsare ni to babu komai mun saba ne shiya sa kai na bincike ka, dawa kuke waya ne ko dai duk matan da kake, da number su ,ina takura maka "nifa ba wai ina tuhumar ki da sai kingaya mun ko shi waye ba naji yayi wasu kalamai wanda sai wani alaƙa ta soyayya ce keda hakkin furta wannan kalamai .


Zan fita mekike so in kawo Miki gobe zan koma tunda naga kin warke in kuma ina takura miki zan baki lokaci kisani zan nemi yaron nan inji wani matsayi kike da shi, a gun shi "me yasa kake haka ne wallahi girman ka zai zube a ƙasa ya kamata ka gane hakan nasan kana da ,alaƙa da shi tunda ya maka aiki ,kirane ya shigo wayar ya Ibrahim da sauri ya ɗauka naji yace to "Abba yana kiranki wai kije amma yace in rakoki".


Bansan hanya bane ko dai banida ƙafa kaje kayan ka zanje hijabi na ɗauka na nufi hanyar fita ya bini ya nace mun Ibrahim takura ne da shi duk ya gundire ni .da sallama na shiga Abba na ya amsa Hajiya na gefen shi "uwata yaufa saura kwana takwas a kan maganar da mukayi a razane na ɗago fuska ta,na daɗe ban ɗ'ago ba shiru nayi sai da naji muryan Abba ya ƙara magana.


"ba dake nake ba wa kike so ne kigaya mishi yazo gobe ina son ganin shi in kuwa ya wuce gobe bakida miji fiye da Ibrahim ga shi nan shi ɗan uwan ki ne, zai kula da ke a kowa ni hali kika shiga sannan zai yi tattalin ki, zai baki kulawa".


"Abba nifa ya Ibrahim a matsayin yayana na ɗauke shi ban taɓa sawa a zuciya ta,wani alakar soyayya zai shiga tsakanin muba ni auren nema ya fice mun daga raina amma kayi haƙuri Abba .


Kina nufin bake son shi ne ko dai yaya?


Shiru ne ya biyo baya babu macen da zata ga ya Ibrahim tace bata son shi sai dai mara rabo amma mai hankali dole zata ɗau ya Ibrahim yabar JB kodan halin shi ,na gagara magana tashi nayi nace to Abba daga mun hannu yayi ki zauna waya ce miki mun gama ina son a kwanakin da yarage ki kawo mun wanda kike so , sannan muddin kika sanya kanki damuwa ko dai jawowa kanki tashin hankali zan baki mamaki bakida mijin da yakai Ibrahim sannan kisawa ranki da shi zaki zauna zama na har abadan kawai dan saurayin ki ya mutu shikenan kice bazaki kula wani, ba wayon ki ne ya haɗaki da shi kodai ikon Allah ne ya haɗaku.




Ido na ya cika da hawaye jiran zubowar su nake haɗa idon da zanyi,da ya Ibrahim naga hawayen sun gangaro jijjiga mun kai yayi ,alama karnayi kuka"Abba bana son a takura mata tawajen tilastata a kan sai ta aure ni tunda batada ra,ayi a barta kawai zaifi wallahi ba nason ganin ta cikin da muwa babu wanda baya tausaya mata sai mara imani".




Ba komai a hankali zata gane tunda nake gani a kwai wanda take so a ranta amma taƙi bayyana shi ,mujira kwana kin da suka rage .


Lokacin da nabar gun Abba ban ɗaga hankali na ba ,shiru kawai nayi waya ta naɗauko na kira JB sai da natara mishi missed call uku ,a na huɗun ya ɗauƙa ,sanar da shi nayi a kwai matsala gaskiya babba makuwa a na son haɗani da wani ɗan yayan Hajiya sannan saura kwana ki takwas .


"banji mekike cewa ba"?


Ko mai nagaya mishi "kiyi haƙuri har yanzu ban shawo kan iyayena game da auren muba kawai so suke su zaɓa mun ita sunyi shiru a kan maganar banji daga bakin suba wallahi ina son ki a lokacin da na zo miki banzo da yaudara ba manufa mai kyau ce a tattare da ni"banga alamar hakan ba JB kawai dai baka sona ne shikenan duk yadda kayi dai dai ne, nasan zan kai kaina ne in da ba,a damu dani ba iyayen ka basa sona tunda mahaifin ka da kanshi ya karɓe maka wayar ka sannan kace karna kira zai gaya mun magana sosai.


"Me yasa bake mantuwa ne,naga abun nan ya wuce meye na dawo da shi kuma a yanzu da muke shirin iskar wata mahangar agun iyayen ki.shikenan nagode




Na gagara gaya mishi Abba na yana son ganin shi gobe zan bari ya Ibrahim ya tafi babbar da damuwa ta ya zan nuna JB a matsayin wanda nake so bansan wani ƙaddaran ne ta haɗani da JB ba gashi kuwa ,komai yana son tarwatsa mun zuciya na tarasa waza ta zaɓa a cikin su Doctor ko dai ya Ibrahim ko wanne yayi mun halacci har dare ina ta tararraɗin gayawa JB ganin shi nayi yana online rubuta mishi nayi Abba yace yana son ganin ka gobe in ka shirya kazo kuyi magana .


A jiye wayar nayi na nufi ɓangaren Hajiya bayan mun gaisa a cen nasamu ya Ibrahim suna ta hira yara sai cin abun da ya kawo musu,sukeyi sannu da zuwa nayi mishi abinci naje na debo nafara ci naga ya sauƙo ya sa hannu daka mishi harara nayi ko,a jikin sa bada ledar hannun shi yayi ciki da kaya a Aliyu ya kai mun ɗaki na ,bafa yunwar yake jiba gulma ce kawai yake damun shi "Hajiya zanje barno in yi kwana biyu agun Inna da sauri ya Ibrahim ya ɗago .


"Da gaske kike yi "?


Ina ruwan ka ba yanzu ba sai ka tafi zanje kowa yayi tafiyan shi nasan hanya "ai kuwa baza dai ki hau motar kasuwa ba sai dai in zo in ɗauke ki ,kinga kin huta abun ki ,jinayi Hajiya tayi magana"tunda zai tafi gobe ki shirya ku tafi tare mana ba yafi ba sai kiyi sati ki,dawo ".




Hakan ma yafi sati biyu za'tayi kafun ta warke sosai a dole Hajiya tasani nace zamu tafi gobe naga farin ciki agun ya Ibrahim don Fatima tace zata bini mutafi tare tashi nayi na nufi ɗaki na shiga wanka,nayi ban tsaya duba waya taɓa sai da nagama kafun na ɗauko , wayar Whatsapp na shiga naga JB ya rubuto mun bashida kuɗin mota amma in ya samu zan ganshi in yi haƙuri don Allah ,ba shi amsa nayi yanzu mahaifina yana kiranka a ce bakada kuɗin da zaka zo kuyi magana ayya JB abun ka akwai Allah a cikin ta kuwa ba komai ka zauna karma kazo duk wanda ta raɓeka ita da takaici yanzu tafara ganin baƙin ciki tunda ita ta,ɗauka wa,kanta tashin hankali ne kawai.


Jawo ledar da ya Ibrahim ya kawo mun nayi a,bubuwa ne masu tarin yawa ya kashe kuɗi sosai ,dama a ce wannan daga gun JB yake amma shi ,tsiya ce da shi ina son ganin JB yayi mun kyauta ko na meye ne zanji daɗi a rayuwa ta ,kirana yayi a waya na ɗauka "meya sa zakiyi fushi babu ɓoye _boye tsakanin mu ,bani da shi naje nayi sari ne shiyasa in kina da shi kitura mun zan baki in nasamu naje gun mama yanzu ma tace babu kiyi haƙuri karkiyi fishi kinji".


Ko magana ban yi ba na kashe wayar nací gaba da abun da nakeyi a ranar ya Ibrahim bai shigo yayi mun sai da safe ba nata jira shiru har ƙarfe sha biyu sai naga ya tura mun sako , kiyi haƙuri kaina ciwo yake yi sosai shiyasa ban shigo ba sai da safe ki ,kula da kanki banda tinani sannan ki shirya da wuri mutafi ...
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


©️ Amina Ma'aji
Ahmad Toshiba
Maimuna Tijjani Iyam


LAMBA TA GOMA SHA UKU


Tun ina danne abun a cikin zuciyata har lamarin ya soma fin ƙarfina, ba ni da aiki sai danna wayata da zaman jiran saƙo daga gare sa.
Na yi yunƙurin mayar masa da amsa amma wata zuciyar ta na yi mini gargaɗi, cikin wannan halin aka shafe satikai uku. Har wani zazzaɓi ne na ji yana son rufe ni. Juyi kawai nake yi akan gadon ina sauƙe ajiyar zuciya ban san sanda hawaye ya soma kwaranyo daga koramar idanuna ba.


Haka na ƙarar da rabin daren ina saƙa da warwara a cikin raina, tare da tunanin waye wannan wanda yake neman yin tasiri a cikin zuciyata. Ranar na tashi da matuƙar ciwon kai Momma ta kasa zaune ta kasa tsaye duk motsin da na yi sai ta yi mini sannu, tare da tambayar me ke damuna.
Ganin yanda duk ta ruɗe ya tursasa mini daurewa na ce da ita babu inda yake yi mini ciwo, amma ba ta yarda ba sai da ta ƙira likita ya ƙara mini ruwa ta kuma gargaɗe akan kar na sanar da Hajiya hankalinta ya tashe.


Da ƙyar nake buɗe idanuna da nake jin sun yi mini wani nauyin gaske, na dafe kaina da na jin sauƙinsa fiye da ɗazu kafin a sanya alluran bacci cikin ƙarin ruwan da ya fara aiki a jikina. Ajiyar zuciya nake sauƙewa a kai a kai tamkar wacce ta yi gudun ceton rai, haka na cigaba da kwanciya na jawo wayata dake ajiye akan drawer ɗin dake gefen gadon na kai ziyara a shafina na whatsapp.


Take na ji wani ƙarfi da kuzarin da ban san ina dashi a wannan lokacin ya zo mini, zumbur na tashi ba zauna ba tare da na mai da hankali ga zafin da na ji ya ratsa ni daga hannun da aka maƙala mini ƙarin ruwan ba.
Sai da na mirtsike idanuna domin son tabbatar da sahihancin abinda suke hasko mini, tabbas saƙonsa ne ya shigo cikin wayata. Jikina har rawa yake yi na shiga saƙon sai da na karanta aƙalla sau bakwai sannan na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya, ina rungume wayar a ƙirjina ina lumshe shanyayyun idanuna.


Ban san dalilin da ya sanya ni jin wani sanyi yana ratsa shashin ruhina ba, haka nan nake ji na tamkar wacce aka yi wa bushara da shiga gidan aljanna. Jin ƙarar shigowar wani saƙon cikin wayar ya sa ni saurin buɗe lumshashshun idanuna na duba. Shi ne ya kuma yi mini wani saƙon. Yana tambayar a tsawon kwanakin nan shin ban yi kewarsa ba?. Domin shi duk wani bugun da zuciyansa za ta yi sai na faɗo a ransa.


Tsintar kaina kawai na yi ina sakin wani ƙayataccen murmushin da yake fitowa kai tsaye tun daga ƙasa ƙalbina. Ban san sanda ya shigo ba balle zaman da ya yi kusa da ni sai ji na yi kamar daga sama an wafce wayar dake hannuna.


Na zabura tare da ɗauko kaina domin ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, ya katse mini farin ciki da annashuwan da nake ciki. Gabana ya faɗi ganin Sultan ya miƙe tsaye da wayar yana ƙoƙarin duba abinda nake kallo.
Na marairaice tamkar mai shirin yin kuka"Don Allah yaya Sultan ka ba ni wayata wani abun mai muhimmanci nake dubawa".


"Nima wannan abun mai muhimmanci nake son gani da har ya ɗauke hankalinki, ko motsin shigowa ba ki ji ba".


Da sauri na fige ƙarin ruwan zan tashi na karɓa wayata, kallon da ya kafe ni da shi ya sanya ni komawa na zauna ina sunkuyar da kaina ƙasa.
"Wani irin abu ne wannan da bakya son kowa ya gani?. Shin muhimmancin abun har ya ɗara muhimmancin lafiyarki?. Na lura kwana biyun nan gabaɗaya hankalinki yana kan wayar nan, kin ga ki nutsu har ki ɗaura rayuwarki gabaɗaya akan waya domin sharrin dake tattare da ita ya fi alfanunta".


Yana dasa aya ya ajiye mini wayar a kusa ni ya juya ya fice, ban damu da ko ransa ya ɓaci ko akasinn hakan ba. Yana fita na ɗauki wayar ina Allah-Allah ya sa na tarar dashi a online bai sauƙa ba, domin yau na yi ɗamaran mayar masa da amsar duk wani magana da ya yi mini.
A ina ya san ni?. Waya bashi lambar wayata?. Sannan me yake so daga gare ni?. Su ne jerin gwanon tambayoyin da na fara watsa masa. Daki-daki ya ba ni amsar da suka ƙara narƙa da zuciyata cikin son ganin wanene shi a zahiri.


"Kar ka sake yi mini magana, matuƙar ba zaka bayyana kanka a fili na ganka ba".


Na karanta abin da na rubuta a zahiri kana na tura masa, ya dawo mini da amsa cikin faɗin"zan bayyana a gare ki nan ba daɗewa ba. Amma sai na tabbatar da cewar na kafu a cikin zuciyarki, ta yanda ko a wani hali na bayyana a gare ki ba za ki juya min bayana".


Bayyanannen ajiyar zuciya na sauƙe na ƙurawa fuskar wayar kallo, jin ana ƙoƙarin turo ƙofar ɗakin ya sa ni saurin ajiye wayar a gefe ina kafe ƙofar da ido. Ta nufo Ni da hanzari ta cire mini ƙarin ruwan tana faɗin"kina zaune drip ɗin ya ƙare yana tara jikinki, tunanin meye kike yi?". Sai a lokacin na lura da ƙarewar ƙarin ruwan na sadda kai ƙasa don bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen kare kaina musamman da ta tsare ni da idanunta.


Sai da ta zauna a kusa da ni sannan ta furta"yanzu me yake damun ki?".


"Babu inda yake yi mini ciwo, ciwon kai ne daman kuma shima ya daina".


Ta kai hannunta ta tallafo haɓata "Allah ya ƙara sauƙi". Na ƙirƙiro murmushi dole na dasa a fuskata"Amin ya Allah ".


Ta ce na je na yi wanka na yi salla sannan na fito na ci abinci nasha magani, yanda ta faɗa haka na yi na iske su a falo ni kaɗai suke jira. Na saci kallon Sultan na ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login