Showing 21001 words to 24000 words out of 50955 words

Chapter 8 - WATA MAHANGAR BOOK 1 BY Amina Maaji -Iyam

02 Sep 2025

2127

bayan fitar da Sakina ta koyar da ni ƙalilun abubuwan da ta fahimta. Domin zafi da tsananinsa ya sanya ba kowa yake fahimtar darasinsa ba.


A haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwa ta na juyawa har aka yi bikin Anty Sadiya lokacin muna hutun ƙarshen zangon karatu. Muna komawa babu ɗadewa muka zana jarabawar jamb. Koda aka sake sakamako ina ɗaya daga cikin waɗanda suka ci maki mafi yawa a kaf makarantarmu. Da shugaban makarantar ya gabatar da mu a gaban assembly tare da shawarar raguwar sauran ɗalibai da su yi koyi da mu su zamo jajirtattu kuma masu mai da hankali akan harkan karatun su. Ina sauƙa daga izuwa wajen da sauran ɗaliban suke tsaye na ci karo da Malam Suraj yana nufi wajen.


Da hanzari na rusunar da idanuna ƙasa saboda wani kallon da ya jefo mini yana ɗaure fuska tamau tamkar magribar ɗinya. Har aka gama assembly ɗin ba ni da nutsuwa muka koma aji, muna tsaka da gudanar da darasin kusa da na ƙarshe a ranar. Wata yarinya daga ajin bayan mu ta nema izni ta shigo ta na cewar"wai Surayya ta je inji Malam Suraj".


Take na annurin dake fuskana ya kau zuciyata ta shiga dakan lugudan tara-tara sau tara. Muka haɗa ido da Sakina ta jinjina mini kai alamar na tashi na je, a sanyaye na miƙe ina taka ƙafata a hankali har na isa cikin ofishin malamai na shi ne na biyu daga gefen hagu.


Na kai hannu da nufin bubbugawa na ji saurin janyewa, ina runtse idanuna da ƙarfin gaske. Ina karanta duk wani addu'ar da ya fara zuwar mini a rai har na sama nutsuwa a cikin raina. Na ɗaga hannu zan buda aka buɗe ƙofar. Idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna babu shiri na kawar da nawa gefe ina ƙoƙarin danne ruwan da nake jin yana ƙoƙarin zubawa daga koramar idanuna.


"Sai yanzu za ki zo?".


Ya furta a zafafe na jijjiga kaina da sauri alamar a'a. Ya sa ki tsaki yana juyawa ciki na taka a hankali raina cike maƙil da tsoro na bi bayansa. Na daɗe a tsaye ba tare da ya ce da ni komai ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi ga making ɗin wasu takardun dake gabansa. Jin ƙafafunsa sun fara rawa su na alamta mini gajiyarwar su na ɗaukar nauyin gangar jikina ya sanya ni cira kai na kalle shi.


"Malam muna darasi ne na fito".


Sai da na cire rai da samun amsarsa kana ya furta mini"na fi ki sanin hakan ai". Ban kuma cewa komai ba wasu hawaye suka gangaro izuwa kan kuncina.


"Na ji wai ance kina ɗaya daga cikin waɗanda suka fi kowa cin jarabawar jamb a makarantar nan ko?".


"E".


"Ya yi kyau keep up ruwa good work".


A sanyaye na furta"na gode". Shuru ya kuma karaɗe ofishin sai can ya ya ce"ki fice min daga ofishin". Da hanzarina na fita na jawo ƙofar na rufe, sai da na koma cikin aji na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi ina dafe ƙirjina.
Haka har muka fara zana jarabawar waec da neco, yaya Sufyan ya cika mini alƙawarin da ya yi mini na cewar matuƙar na yi ƙoƙari a jarabawar jamb zai saya mini waya.


Sauranmu kwanaki biyar mun kammala jarabawar aka ce mu je ofishin Malam Suraj domin cike abubuwan da za a sanya mana a cikin photo album. Tare da Sakina da kuma Sabira muka je duk da ni ce gaba dasu a layi amma ya ce na jira sai kowa ya gama sannan ni na yi, haka na zauna sai da kowa ya gama sannan ya ba ni na nawa lambar waya, adireshi da wasu abubuwan.


Ina fitowa na iske su tsaye suna jiran fitowata Sakina ta na riƙe da jakata. Ina isa na dafe kaina ina faɗin"wash". Maimakon na tsinci tausayina wahalar da na sha a fuskar Sabira sai ma dariya ta tuntsire dashi tana cewar"Surayyan Malam Suraj".


Tunin na wartsake ina jefan ta da harara"Allah ya kiyaye wallahi".


"Ke dai ina raba ki wallahi yarinya, ki yarda ko kar ki yarda da bawan Allahn nan son ki yake yi. Shin ba ki lura tunda muka fara jarabawar nan ya ƙara shiga cikin wani hali ba?. Kin san dalili?". A tare muka jijjiga mata kai ni da Sakina, ta gyara tsayiwarta kana ta ɗaura da"saboda mun kusa kammala makaranta, zai dai na ganin ki zai daina jin muryarki. Ta wani ɓangaren kuma cire yake da tsoron kar ya rasa damar sa gabaɗaya akan ki".


Taɓe baki na yi ina karɓar jakata na rataya a kafaɗata, muka fara tafiya zamu fice daga cikin makarantar kasancewar duk an fara watsewa daman iya mu da muke zana jarabawar ce muka zo.


"Na fara yarda da zantukanki Sabira wataƙila duk abinda kike faɗa ya kasance gaskiya". Ban tanka musu ba na yi kunne uwar shegu har muka isa bakin gate. Bamu yi jiran mintuna goma ƙwarara ba yaya Sufyan ya iso domin ɗaukar mu. Dai-dai sanda Malam Suraj yake fitowa daga cikin makarantar a bisa kuskure idanuna suka gano mini gefen da yake, ban ƙara gigin ƙars kai idanuna wajen ma muka shige cikin motar.


Sabira aka fara sauƙewa sannan Sakina muka yi sallama cike da son juna. Gidan Momma na ce ya kai ni, ya kallo ni fuskarsa kamar gonar auduga ya ce"an gama ranki ya daɗe".


Murmushi na saka"yaushe zaka koya mini mota?". Ya ɗan zaro ido a lokacin da yake karya kwanar da zata sada shi da unguwar kafin ya furta"so kike Hajiya da Momma su yi min tarin dangi ko?".


"Me yasa to?".


"Su ce zan tsorita musu ɗiya ma, kin san da har yanzu basa yarda su shiga motana. Kullum ƙorafin su wai na cika gudu".


Dariya na saka saboda yanda ya yi maganar har muka isa ban daina ba. Yana gama daidaita parking na fito da guduna na shiga sashin Momma. Shi kuma ya koma makaranta.
Nan na wuni sai bayan sallan magrib ya mai da ya ni gida, bai tafi ba sai ƙarfe goman dare na rako shi har jikin motarsa. Sai da na hana shirin kwanciya tsaf na tuna da wayata, na tashi na ɗauko ta a cikin kayana da nake ajiye ta. Na kunna sannan na koma na kwanta ina latsawa.


Whatsapp na shigo domin tambayar yaya Sufyan ya isa gida lafiya, na ci karo da saƙo da wani baƙuwar lambar an yi mini sallama cikakkiyar. Ban amsa ba sai da na turawa yaya Sufyan saƙon babu jimawa ya maido mini da amsa. Haka muka cigaba da yiwa juna saƙo har dare kusan sha ɗaya ya yi ya ce na kwanta.
Washe garin ranar bayan mun fito tara, wannan yarinyar jiyan ta ƙara dawowa tare da isar mini da saƙon Malam Suraj yana ƙira na. Cikina ya ƙululu muka haɗa ido da Sakina, ta jinjina mini kanka tana ɗaurawa da"ba komai tashi mu je".


Tare da ita muka je ofishin yau su biyu ne a ciki shi da Malam Saminu muka haɗe baki wajen yi musu sallama, shi kaɗai ya amsa mana amma shi gogan ko ɗaga ido bai ya mana kallon arziki ba ya cigaba da latsa wayar dake hannunsa.


"Surayya Sufyan".


Malam Saminu ya furta na amsa masa ina sunkuyar da kaina ƙasa.
"Ko da bayan kun gama nan ki cigaba da maida hankali ga karatunki kamar yanda kika saba, in sha Allah za ki yi nasara". Kaina na jinjina masa ina cewa"in sha Allah ".


"Kuma ce maka yi cewar lalle ne in ta gama nan ɗin ta cigaba, wataƙila aure zata yi don jiya har ƙofar makarantar nan saurayi yazo ya ɗauke su".


"Saurayi kuma?".


Malam Saminu ya furta yana bin mu da kallon mamakin da ya wanzu a fuskarsa. Ban iya furta masa ko kalma ɗaya ba illa Sakina da ta ce"wannan wanda ta dauke mu jiya yayanta ne, kuma mafi yawan lokuta shi yake zuwa ɗaukar ta".


"Yauwa sai yanzu na ji batu".


Sai a lokacin ya ajiye wayar dake hannunsa ya kafe mu da ido"so yanzu kenan auren ne ko kuma karatun?".


"A burina da na Iyayena karatun ne wannan tsarinmu, amma ba mu san yanda Allah ya tsara mana ba. Kuma a ko yaushe zaɓinsa shine daidai".


"Madalla! a ko yaushe maganar hankali ta na fitowa ne daga nagartaccen mutum. Shiyasa a ko yaushe nake girmama kaifin basirarsa".


Furucin Malam Saminu yana tafa mini, a suƙure na ce"na gode". Malam Suraj ya buga uban tsarkin da ya sanya hankulanmu komawa gare shi. Dosara wayar ya yi ya gabansa yana ɓallawa Malam Saminu harara"aikin banza ko meye wani sabon abu cikin kalamanta da ya burge ka har kake yabonta haka oho?. Kar ka ce min ba ka taɓa jin wani ya yi irin wannan maganar da ta faɗa ba?".


Yana kai aya ya miƙe tare da shigewa cikin banɗakin dake cikin ofishin ya maida ƙofar ya rufe da ƙarfin da ya tursasa mini matse idanuna. Murmushi kawai Malam Saminu ya yi ya ce mu koma ajinmu.
Sakina ta riƙo hannuna"ke wallahi yau na gaskaka zancen da Sabira take fada mana, shin ba ki hangi tsantsar kishi a cikin idanunsa ba sa'ilin da Malam Saminu yake yabon ki?".


"Ban gani ba komai ba zan taba gani ba, kuma da kuke ikirarin cewar kuna gani akwai don kun canfa abun ne".


Haka har muka gama rubuta jarabawar kullum na shiga what's app ɗin sai na tarar da an ƙara yi mini sallama da wannan lambar, duk da kuwa bana amsawa saboda kashedin da yaya Sufyan ya yi mini akan takan tsantsan da mutanen yanan gizo. Mun yi walima mun kuma yi ƙwarya ƙwarya party muka cashe da ƙawayen mu. Raina fari ƙal ji nake tamkar babu wanda ya kai ni murnar wannan gamawan da muka yi, domin ko banza na rabu da ganin tsanar Malam Suraj a gare ni.


Ranar da muka y partyn a cikin makaranta, malamai da sauran ɗalibai duk suka taya mu murna. Ban sanya Malam Suraj a idanuna ba domin ko wulgawarsa sai ɗaya ban gani ba. A bakin wasu nake jin cewar bai zo makarantar ba a ranar. Tunda muka yi candy na koma gidan Momma da zama. Yaya Sufyan da Yaya Sa'eed suka tafi ƙarin karatu kasashen ƙetare.


Watarana tsautsayi da rabon tafka da ba sa ni ya sanya ni shiga saƙon da ake turo mini da wannan lambar domin na kwana biyu ban duba ba. Murnar kammala makaranta aka yi mini tare da fatan alkhairi da addu'a sosai.
Haka kawai na tsinci kaina da amsa addu'ar da kalmar amin a bayyane, sannan ya mayar da martanin cewar na gode da manyan baƙaƙe. Ban tashi daga wajen ba aka maido mini da amsa.


Tsoro ya kama ni na tambayi da mace nake magana ko namiji?. Emojis dariya aka turo mini haɗi da cewar na kwantar da hankalina shi mai sona ne kuma sona ya yi tasirin da ba zai taɓa iya cutar da ni ba. Na faɗa wasi-wasi ban ja batun da tsayi na na yi bulokin ɗin layin. Sai dai hakan bai hana ni ganin an ƙara turo mini makamancin saƙon da ake turo mini a baya ba, ko wacce safiya da saƙonsa nake fara cinkaro kana nan kafin na kwanta bacci sai ya turo mini. Tun daga lokacin da ya mayar masa da martani ban ƙara kula sa ba, sai dai nakan buɗe duk wani saƙon da yake turo mini na karanta wani lokacin na yi dariya wani lokacin kuma takaici ya ishe ni.


Sai da aka ɗebi tsawon makonnai uku babu ranar da ya taɓa fashin turo mini wannan saƙonnin. Har ya zama na riƙe lokacin da yake turawa da na ga lokacin ya yi komai nake yi zan bari na shiga what'sapp ɗina ina jira. Da ya turo zan tsinci kaina ina sakin murmushin da ban san ina yi ba ina gama karantawa zan ajiye wayar.
A haka yi kwana uku ban ga saƙonsa ko ɗaya ba, tun bana mayar da hankali har na fara shiga damuwar rashin ji daga gare sa.
[11/4, 21:47] Maman Khairat: WATA MAHANGAR


Story and writings by Amina ma'aji Ahmad Toshiba maimuna Tijjani Iyam


Zaki sanya kuɗin ki ta 400 wannan asusun Amina maaji account no
4271914014 FCMB sai shedar biya ta wannan no 08068748984


LAMBA NA GOMA SHA HUDA


________Murmushi naga yayi mun ya fara ta kowa in da gado na yake a hankali idon shi a kai na ƙura mun ido yayi bakin shi yana son furta wasu a bubuwan amma irin yadda na haɗe rai bai bashi daman magana ba sai da ya jima a kai na kafun naji yace"ya jikin naki dafatan kin fara samun lafiya in baki dage ba da kulawa da kanki da bawa zuciyar ki hutu ta samu sauƙi ba zan tura ki barno a cen zaki dinga kallon likita yanzu me yasaki kuka ?.
Kallon shi nakeyi bana son wata kalma daga gareshi ko da ta farin ciki ne don zuciya ta tafara rashin yadda da wasu mazan na gagara sai ta kaina sannan nayi hawayen ya daina gangarowa daga ƙunci na amma hawayen ba,daga ido na yake zuba ba daga zuciya ta ce ban ,isa in hana shi zuba ba ko yaya ne .


natafi duniyar tinani a karo na biyu kenan da naji zuciya ta tafara ƙarye wa daga samun JB in kuwa halaccin da nayi Wa JB bai sa yayi mun uzuri ba lalle so bai samu matsugu ni a gareni ba .


Jin doctor nayi ya fara magana "me yasa kike son jefa kanki cikin tashin hankali meyasa kike son ki kasa jurewa a kan ƙaddaran ki, soyayya ,itace ke sawa zuciya matsaloli masu tarin yawa ,a da zuciyar ki bata samu raunin da yanzu yake samu ba ,na tambaye ki ,kin fara soyayya ne a lokacin da ,a ka kawo ki na duba ki kin ce a'a to yanzu nagane wannan wanda yake saki damu wa,amma bashi da yan uwa ko bashi da ƙanwa ko dai a zuriyar su babu mai irin jinyar ki .


"Wa Yagaya maka a irin wannan matsalar nake yin kuka kawai dai bansan yaushe ,a ka kawo ni nan ba shine kawai na shiga damuwa a kai " ƙarya bata da ce da fuskar ki ba wannan ya nuna wanda ya fara sanya ki damuwa a lamu ya nuna maƙaryaci ne zai koya miki a bun da ba ɗabi,ar ki ba ce ".


So yake ya ƙureni ga shi ya zauna yaƙi tafiya sai ɗan na wayar shi yake yi cen wayar tafara neman ,a gaji sanya wayar yayi a kunnen shi jinayi yace ganinan zuwa bani minti goma tashi yayi yace zai je asibiti yana zuwa zaije General hospital an kawo wata mara lafiya an nemi jijiyar ta dan a sanya mata drip ba,a samu ba in taya shi da addu,a Allah yasa yayi nasara dan ance tana shan wahala . da to na bishi Allah ya bata lafiya Amin ya ce mun ya fice kafun ya fita ya cire mun drip ɗin don ya ƙare . Hajiya ce ta shigo da su Inna mahaifiyar Ibrahim "sannu uwa ta Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne Ibrahim yace a gaishe ki ɗazu ya kira waya kina bacci bamu tashe kiba duk ya shiga da muwa a jhkan halin da kike "ayya inna ina ji da shi nima ko aure yayi matar shi bata kaini son shi ba "ke ce matar Ibrahim in har ina raye babu wanda zakiaura sama da shi yana sonki ga shi ɗan uwan ki ne, zai kula da ke to meye abun sai kinje wani gidan ko ba haka ba Lubabatu .


Hajiya ta ce tace e inna yafi kam Allah dai ya nuna mana lokacin kawai musha biki mu huta wayaga miskilai guda biyu suna ta maganar su ,ko in kulasu na kashe waya ta tun da nakaranta saƙon JB bana son ya Kirani gara kawai in fara mantawa da shi Inna ce ta miƙo mun wayar ta wai ga Ibrahim amsa nayi muka fara gaisawa "ya jikin ki sannu Allah ya baki lafiya duk na rikice bana gari naje Abuja zan dawo gobe zaki ganni bazan wuce barno ba a nan zan tsaya Allah ya baki lafiya don Allah ki daina sanya kanki cikin damuwa baki san halin da nake shiga ba shiya sa ki tausaya mun . duk naji wayar ta gundire ni ba muyi sallama ba na miƙawa Inna wayar ta abinci a ka sanya mun nací ƙadan na kwanta zuciya na kamar an ɗaura mun ɗutsi mai nauyin gaske jama,a sai zuwa suke tayi asibiti sai ya zama kaman gidan biki maman Sadiq ne tazo duba ni"ƙawata kamar kinyi kwana goma kina jinya kina bani tausayi gaskiya baban su yace in gaishe ki "ina amsa wa,jikin da sauƙi gobe za,a sallame mu, da safe duk asibitin ta,ishe ni nagaji.


"ki bari kisamu sauƙi in kinje gidan ma kwanciyar ce sai tinanin banza" ,munata hira sai kusan mangari ta ,tafi naji daɗi sosai don tabani abun dariya,ni kaina in natino sai in yi dariya ƙarfe tara na dare doctor ya shigo duba ni .
"Ya jikin ki da fatan yanzu kam babu komai allura ce saura guda biyu Barole sannan I v ne zakuyi haƙuri zuwa gobe ko jibi zamu sallame ku"ba komai Allah ya kaimu .


"Amin ya rabbi ".


Bansan yaushe ya tafi ba don nayi bacci farkawar da zanyi a raza ne na farka,wani mummunan mafarki nayi da JB ya ɗaga mun hankali addu,a nayi na kwanta nayi bacci cikin ikon Allah baccin ya sake ɗauƙa na mafarki na sake yi da Muhammad yana roƙo na kar,in bari JB ya cuceni bai dace dani ba ya koya mun abubuwan da bai sanni da shi ba addu,a yatayi mun mafarki da Muhammad ya tasar mun da hankali sosai na sha kuka ban taɓa mafarki da Muhammad ba a she daman abun da yake gayamun na cewa in nací amanar shi zai ɗinga fito mun a fatalwa da gaske ne ,kenan hawaye Masu zafi ne suka zubo daga ido na ,na gagara mantawa da mafarkin duk wanda ya ƙara kallo na yasan a kwai babban damuwa a tattare dani.
buɗe waya ta nayi na rubuta wa doctor saƙo a kan yayi haƙuri ya sallame mu, yaje in ya samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login